Showing 12001 words to 15000 words out of 57328 words
baƙin cikin da take ƙunsa a cikin gidan. Sai da tayi me isarta sannan ta miƙe ta ɗauro alwala ta fara gabatar da sallar nafila tana kaiwa Allah kukanta akan ya magance mata matsololinta da abin da yake damunta. Ta idar da sallah tana tsaka da addu'a tashi motsin Saif ya fito daga ɗakinsa da sauri ta fita dan batasan inda zashi a tsohon daren nan ba tunda ba cikakkiyar lafiya gareshi ba. Tana fita ta riƙe shi tana yi masa sannu, ga mamakinta sai ji tayi yace. " Yauwa Ammi" a taorace ta ɗago ta kalleshi baki a buɗe ta ce. "Saif kaine kuwa?" tafiya ya yi luuu kamar zai faɗi da sauri ta riƙoshi ya dafa kansa yace. "Ammi kaina ciwo yake" Fulani Zaliha ido ta zura masa har lokacin kallonsa take da mamaki har ta kasa furta koda kalma ɗaya sai da ya kuma cewa. "Ammi kaina ciwo juwa nake ji" Riƙoshi tayi ta wuce da shi cikin ɗakinta tana binsa da kallo a gefe ɗaya kuma zuciyarta fal farinciki sai ta nemi damuwar da take ciki ta rasa gabaɗaya.
Gabaɗaya mutanen da suke cikin gidan horo hankalinsu ba ƙaramin tashi ya yi ba, saboda tun da suke ciki basu taɓa ji ko ganin irin makamanciyar guguwar da akayi ba, uwa uba kuma gawarwakin su Badariya da aka wayi gari dasu duk anmurɗe musu wuya, wani babban tashin hankali jikinsu duk ya yi wani dabbare-dabbaren taruwar jini. A ɓangaren Maryo kuwa tana kwance cikin jini da alama ko numfashi bata yi, ga wani irin yalo da tayi shar kamar wacce jinin jikinta ya ƙare. Da sauri Dogarawa suka fara fitar da su ana kwantar da su akan tabarmin kaba, ana ƙoƙarin kaisu gurin da za'a yi musu sutura suka ji Maryo na sauke ajiyar zuciya, da saurinaka cireta daga cikinsu cikin gaggawa aka sanarwa Mai martaba halin da ake ciki. Nan take ya bada umarnin aka kaita asibitinsu kuma ayi musu sutura, bayan da aka wanke su aka Mai martaba da kansa ya sallaci gawarwakinsu sannan aka wuce da su gidansu na gaskiya. Sarki Aminullah da kanshi ya shiga cikin gidan horon dan ganin yadda al'amarin ya kasance, ƙofofi da windunan ɗakunan haka Dogarawa suka dinfa ɗebosu da hannunsu suna ajiyesu a gefe. Sarki Aminullah ba ƙaramin razana da ganin abin da ya faru ya yi ba, jiki a sanyaye ya wuce gida yana ta'ajibun lamarin saboda ko kaɗan babu wata guguwa da akayi a cikin gidan masarautar sai gashi gidan horo yayi fata-fata har da wasu guraren da suka rurrushe, bishiyoyi duk sun kaɗe wasu duk reshinansu sun faɗo.
Kafin wani lokacin tuni labari ya baza ko'ina na cikin masarautar, daga labarin Maryo har zuwa labarin abinda ya farunda halim da take ciki, Inna Habi banda kuka babu abin da takeyi ita da Abu lokaci ɗaya ta zabge ta rame ta lalace kamar wacce tayi jinya. Cikin kuka take faɗin, "Kaico yarinyar nan da wannan ƙaddarar tazo miki tabbas nasan Maryo bazata aikata abin da ake zarginta da shi ba sai dai, idan wani kaidin aka ƙulla mata, Allah ka na kallon baiwarka ƴar marainiyar Allah babu uwa babu uba ka dubi halin da take ciki ka kuɓuto da ita..." Abu ta yi ƙasa da murya ta katse Inna Habi da cewar. "Dan Allah Inna ki daina faɗin haka. Kina ganin yadda mutane suka kallo yanzu haka sai su fahimci cewar bake kika haifi Maryo ba kinga wani ma wata fassarar zai yi miki ta daban."
TO FA MEYE HARSASHEN KU?
KUYI HKR BAN TACE SHI BA👏🏻
_LITTAFIN ANYA BAIWA CE? NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI_
[29/10/2021, 19:31] Ameera Adam🌚: 17...
Inna Habi wata uwar harara ta watsawa Abu cikin hassala ta ce. "Su faɗa mana sai me indai za'a dawo mini da Maryo. Allah ya sani yarinyar nan jin ta nake har cikin raina kamar nina haifeta akanme bazanyi beken rashinta ba, yanzu fa shikenan ƙila kashe ta za'a" Inna Habi na zuwa nan a zancenta ta kuma rushewa sa wani irin kuka. Mutanen gurin sai bin ta suke da kallo ƴan ƙananan maganganu suna tashi, daga cen gefe Jakadiya na zaune tana jin abin da Inna Habi take faɗa, cikin zuciyarta ta ce. "Tsinanniyar yarinya ashe ma ɓalɓaltacciya ce duk ta susutamu ni da Maryama, ai koda kasheta za'a yi ankashe banza" Jakadiya wani nazari tayi da sauri ta miƙe ta ƙarasa gurun Inna Habi cikin yanayin damuwa ta dafa cinyar Inna Habi ta ce.
"Kaico Habi dole kiyi kuka wallahi koni yarinyar nan da ba wani daɗewa nayi da ita ba duk ta shiga zuciyata, yanzu haka raina duk a dagule yake Allah dai ya ƙuɓuto da ita ya tashi kafaɗunta ya bata lafiya. Habi ba kuka zakiyi ba Addu'a zamuyi mata." da sauri Inna Habi ta ce. "Jakadiya Bangane Allah ya tashi kafaɗunta ba yarinyar da take tsare a gidan horo" Kafin Inna Habi ta gama magana Jakadiya ta kauda kai gefe a hankali ta ce. "La'ananniya daga cen ma Allah ya datse ranta ko ma huta, Astagafirulla wai ni ce harda yi mata addu'a" sai kuma ta ɗago ta cewa Inna Habi. "Habi ina take gidan horo yarinyar da aka kaita asibiti rai a hannun Allah ance jinin jikinta fa duk ya zuƙe, Allah na tuba wayasan zunubin da yake gidan horon ai shiyasa iftila'in ya tsaya iya kansu cen gayyar tsiya arna a idi." Inna Habi zaro ido tayi ta ce. "Maryo ɗin ce rai a hannun Allah? Yau na shiga uku ni Habi naga ta kaina shikenan sunyi mini sanadiyyarta Allah ya sa kar ciwon zuciyarta ya tashi na shiga uku na lalalce." Inna Habi ta ci gaba da sharɓar kuka cikin ƙunan rai da tashin hankali. Duk wanda yake gurin sai da yaji kukan Inna Habi har cikin zuciyarsa, ba ƙaramin tausayi ta basu ba wasu kuma daga ciki suna ganin kamar saka Maryo akayi saboda a ƴan shekarunta ba yadda za'ayi tayi wannan tunanin tunda ko da ta kashe Sarki Aminullah wace riba zata samu tun har lokacin labari bai je musu na cewar Fulani Zaliha ake zargi da haɗa baki da Maryo akan farmakin da Maryo ta kaiwa Sarki Aminullah.
Fulani Maryama zaune take a turakar Mai martaba fuskarta ɗauke da damuwa ta ce. "Allah ya taimakeka naji ka aika kira na" Sarki Aminullah har lokacin fuskarsa ɗauke da damuwa yace. "Maryama na kiraki ne domin na tambayeki" Cikin Maryama ne ya ɗuru ruwa nan take gumi ya shiga tsatssafo mata tayi ƙarfin halin cewar. "Tambayar me ranka shi daɗe" Ajiyar zuciya Sarki Aminulla ya sauke ya ce. "Akan maganar da kika zo mini da ita" A firgice Maryama ta ɗago ta kalleshi ta ce. "Ina jinka Mai Martaba" Sarki Aminullah yace. "Ina san naji bayan ni wa kika sanarwa da maganar jiya" Ajiyar zuciya Fulani Maryama ta sauke ta ce. "Wa zan sanarwa Mai Martaba idan nayi haka ai kamar ban kyauta maka ba" Gyaɗa mata kai ya yi yace. "Ya yi kyau shiyasa nake ƙara ƙaunarki saboda kyawawan ɗabi'unki, zan gargaɗe kinda karki sake maganar nan ta fita banasan naji zancen a waje, yarinya dai mun turata gidan horo ita kuma Zaliha zamu ci gaba da zama da ida saboda rufin asirinmu, dan haka ki kiyaye" Fulani Maryama sam ba haka ta so ba ta so itama Fulani Zaliha an haɗa da ita amma ba yadda ta iya, ƙaƙalo murmushin ƙarya tayi ta ce. "Godiya nake ranka shi daɗe ai dole na ne tunda mutuncinka mutuncinmu ne gabaɗaya" yaji daɗi kalamanta nan take ya ci gaba da sa mata albarka sannan Fulani Maryama ta ci gaba da yi masa kalaman ƙarya, daga har ta lura da baccin da ya fara ɗaukan Mai Martaba, tashi tayi ta bashi guri sannan ya kishingiɗa nan da nan bacci yayi awon gaba da shi.
A cen asibitin Murtala Maryo kwance take kamar gawa ta kuma yin wani yello shar su kansu likitocin sunyi mamaki dan basu taɓa cin karo da mara lafiya kamar ta ba, gwajin jini aka dnga yi dan a samu jinin da zai yi dai-dai da nata, Babban amintaccen Dogarin da Sarki Aminullah ya wakilta da shi ake ta shige da fice dan ganin an ceto rayuwar Maryo, haka ya dinga kiran ƴan uwansa fadawa ana gwada jininsu dan aga ko zai yi dai-dai da na Maryo amma gabaɗaya babu wanda yayi dai-dai. Ba ƙaramin damuwa likitocin suka shiga ba, haka daga gurin Babban Dogarin Sarki, yana tsaye a bakin ƙofa cikin damuwa wata almajira tazo bara wajensa tana neman taimako, cikin ƙosawa da zancenta yace. "Iya dan Allah ki saurara mini inji da abinda yake damuna, da yarinyar cen zanji ko da roƙon da kike mini" Tsohuwar cikin jimami ta tambayeshi a nan yake labarta mata abin da yake faruwa da Maryo, bayan ta tausaya mata ta ce. "Yaro me zai hana muje a ɗauki jini na?" da mamaki ya kalleta yace. "Iya majiya ƙarfima an gwada baiyi ba bare ke tsofai-tsofai, ganin ta dage yasa ya amince mata su kansu likitocin da farko ƙin amincewa sukayi dan gudun kar aje a ɓata biyu ɗaya bata gyaru ba. Sai daga baya suka amince ana ɗaukan jininta da aka gwada aka ga yayi dai-dai dana Maryo, yana ƙara mata jinin ta fara wani irin karkarwa da wani irin gumi da yake tsatssafo mata, bayan awa guda da ƙara mata jinin ta buɗe idanunta, da sauri Dogarin ya kira likitocin yana leƙawa dan ya kira tsohowar da ta taimakawa Maryo ya neme ta ya rasa, Likitocin na zuwa suka fara jero mata sannu, bata amsa musu ba tabi window da kallo a hankali ta furta. "Rujayma" sai kuma ta saki murmushi, tsohuwar da ta kira da Rujayma ta ce. "Na barki lafiya ya shugaba ta."
_LITTAFIN ANYA BAIWA CE? NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI_
[30/10/2021, 19:28] Ameera Adam🌚: 18...
Maryo na ganin wucewar Tsohuwar ta saki wani malalacin murmushi sannan ta lumshe idonta, Likitan ne ya fara kiran sunanta amma ɗif kake ji ba magana da sauri ya fara bubbuga ƙafarta a hankali ta buɗe idonta ta kuma limshe su, da sauri ya kira sauran likitoci suka ci gaba da bata agajin gaggawa dan ganin sun ceto rayuwarta. Sunfi kusan awa guda akanta sannan suka samu ta sake farfaɗowa, tana farfaɗowa ta fara wata irin shaƙuwa babu jimawa tari ya sarƙe ta sannan ta fara wani irin aman jini, hankulan mutanen gurin gabaɗaya ya tashi ganin wannan aman jinin da take yi. Sai da suka yi mata allurai sannan suka samu aman jinin ya tsagaita.
A hankali take sauke wahalallan numfashi fuskarta tayi fayau da alama tana jin jiki, bacci ne ya ɗauke ta sannan likitocin suka fice daga ɗakin suna sharce gumi, Dr Musa shine likita da ragamar kula da lafiyar Maryo yake hannunsa, yana zaune a office ya aika aka kira masa Babban Dogarin sarki da ke cikin asibitin, bayan ya shiga ya zauna yace. "Likita naji ka aika kirana Allah yasa dai lafiya?" Dr Musa ajiyar zuciya ya sauke yana ajiye biron dake hannunsa yace. "Lafiya ba lau ba. Gaskiya yarinyar nan tana cikin mawuyacin hali, rayuwarta na fuskantar barazanar mutuwa me kukayi mata haka da ya tayar mata da ciwon zuciyarta, kasan matakin da ciwonta ya kai kuwa? Gaskiya na tsorata sosai akan lamarinta kana ganin dai wahalar da aka sha kafin a samu me kalar jininta, abin da zan gaya muku akanta bai wuce kula da lafiyarta ba. Wai ma ya akayi kuka bari ciwon zuciya ya kama ƴar ƙanƙanuwar yarinya kamar wannan? Kuma me kuka aikata mata na ɓacin rai da ya tayar mata da ciwon nata?" Likitan ya faɗa yana tsattsare Dogarin da kallo.
Dogarin ɗagowa ya yi yace. "Likita nifa waɗannan tambayoyin gabaɗaya bani da amsarta, ni da ka ganni aikin Allah ma nake yi saboda Baiwar Sarki ce bani da tabbacin lokacin da ta haɗu da wannan ciwon, nidai nasan a anwayi gari da samun gawarwaki har da ita a cikinsu sai ita kaɗai ce ta rayu ka ga kuwa bana ce ga silar ciwon nata ba" Likitan yace. "Ba dai sune gawarwakin da Mai martaba ya sallace su ba?" Dogarin yace. "Eh sune fa" Dafe kai Likitan ya yi yace. "Kaga inda aka samu matsala da angwada gawarwakin wata ƙila a samu silar mutuwar ta su, ita dai a namu binciken ciwon zuciyarta ne ya tashi sakamakon mumman fargaba da ɓacin ran da ta shiga, to kuwa ka ga baza'a ce duka ciwo ɗaya ne yayi silar ajalinsu ba." Dogarin tsai ya yi yana nazari yace. "Maganarka haka take Likita, sai dai a kiyaye gaba dan wannan dai ya faru Allah kuma ya bata lafiya." Likitan ya amsa da Ameen sannan ya ci gaba da bashi shawarwarin da ya kamata. Shi dai Dogarin binsa yake da "Eh a'a" dan yasan wannan dokokin babu inda zasu je tunda Yarinyar da ake zarginma kashe ta za'a yi wane ƙa'idoji za'a shimfiɗa akanta. Sai da ya gama sauraronsa sannan ya tashi ya fice daga Ofishin nasu.
Fulani Zaliha na shiga ɗaki Saif ya zauna yana dafe kansa, har lokacin binsa take da kallan mamaki cikin zuciyarta take ayyana wai yau Saif ɗinta shi ne yake furta magana da bakinsa, ɗaga hannu tayi tana godiya ga Ubangijin sammai da ƙassai sai kuma ta fashe da kukan farin cikin, Saif dukda yana cikin wani irin yanayi sai da ya zubda ƙwallah ga mahaifiyarsa saboda yadda yaga tana cikin tsananin farinciki, cikin sanyin murya yace. "Ammi ki daina kuka godiya zakiyi wa Allah subhanahu wata'ala" Gyaɗa masa kai tayi ta ce. "Tabbas maganarka haka take Saif amma kukan da nake yi na farincik ne , Saif tun da na haifeka ban taɓa jin ka furta koda wata kalma bace kaga kuwa dole nayi kuka na godewa Ubangiji tabbas Mahaƙurci mawadaci ne" Fulani Zaliha sun jima suna hira ita Saife sai gabannin asuba Saif ya wuce ɗakinsa ya kwanta itama tayi kwanciyarta, a daren ranar sai ta nemi ɓacin ran da ta taho dashi daga gurin Mai Martana ta tasa amma taci alwashin kafin ya ƙara ganinta a turakarsa za'a jima kuma taci alwashin bakinta da nashi bazata taɓa gaya masa Saif ya warke ba sai dai yaji a gari.
Salman tafe yake kai tsaye ya shiga sashen Mahaifiyarsa babu ko sallama, Fulani Maryama tana zaune tana hutawa ta ɗaga kai ta kalleshi. Zama ya yi kusa da ita yace. "Mama wai ina wannan Baiwar taki dana taɓa ganinta anan" Fulani Maryama sarai ta san wacce yake nufi ta yamutsa fuska ta ce. "Wace Baiwa fa kasan Bayin da yawa?" Guntum tsaki ya yi yace. "Wacce kika mareni akanta" Fulani Maryama ta yamutsa fuska tace. "oh! Wai Maryo?" Bai kalli gurin da take ba yace. "Eh ita fa" Fulani Maryama ta ce. "La'ananniya zaka ce, kai wannan yarinya anyi makira Allah dai ya tsine mata..." Wani hautsinannan kallo ya wurga mata ta ja bakinta tayi shiru bata ƙarasa abinda tayi niyyar faɗa ba. A hargitse yace. "Me tayi kike mata wannan zagin?"
Fulani Maryama ta ce. "Meye ma batayi ba? Yarinyar da aka kama da wuƙa a turakar Mahaifinka zata kashe shi" Murmushi ta ga ya fara yi a hankali zuwa wani lokaci ta ga ya ci gaba da ƙyaƙyata dariya sannan ya tsuke fuska yace. "Waye ya tura ta?" Fulani Maryama ta saci kallan bakin ƙofa murya ƙasa-ƙasa ta ce. "An ce Fulani Zaliha ce ta tura ta" Kallan Mahaifiyarsa ya yi yace. "Kai badai Uwar kwantacce ba matar da sam bata san ma kanta ba har ita zata iya sawa a kashe Takawa ki nemo wata dai ba ita ba. Kai ni banajin ma Yarinyar nan zata aikata abin da kika faɗa gaskiya"
A hassale Fulani Maryama ta ce. "Wato ƙarya nake yi maka ko?" Salman yace. "Abu a duhu...Nifa gaskiya jikina bai yarda ba kuma zansa Mai Martaba ya fito da ita dan gaskiya santa nake yi bazan bari a kashe ta ba ina ji ina gani" Yana gama faɗa ya miƙe tsaye Fulani Maryama baki a sake ta kalleshi ta ce. " Da ta kashe Mahaifinka fa sakarai kawai?" Ya juyo yace. "Da batayi kuskure ba tunda ko yanzu zan iya riƙe ragamar masarautar Kano." Yana zuwa nan a maganarsa ya fice. A ɗan tsorace Fulani Marayama ta bi bayansa da kallo tana jujjuya maganganunsa a zuciyarsa. Miƙewa tsaye ta yi tana kaiwa da kawowa tace. "Tabbas dole na ɗauki mataki a kanka Salman."
Mai martaba sarki Aminullah ne zaune a ɗaya daga cikin manyan tantuna (Rumfuna) da aka tanada saboda manyan baƙi, harabar filin da ke bayan gidan Sarki cike yake da mutane da baƙi daga sassa daga garuruwa waɗanda suke zuwa duk shekara dan taya Sarki Aminullah murnar wasan al'ada da suke yi duk shekara, ƴaƴan Sarakai da manyan daga jikin Gwamnati na halartar wannan taro saboda masarautar Kano babbar masarauta ce da ta kafa tarihi a ƙasar hausa.
Mai Martaba Aminullah zaune yake da manyan Abokansa Sarkin Adamawa da Sarkin Nupe, lokaci-lokaci suke kallan wasan suna ɗan tattaunawa a junansu saboda ba ƙaramin ƙayatar da su yake ba.
Maƙera ne suka fito suka fara gudanar da wasanninsu da wuta gwanin birgewa, sanye suke da wasu kayan saƙi da hulunan fatar ɓauna abun ya ƙayatar sai wanda ya gani. A bisa al'ada idan Maƙera sukayi wasansu na