Showing 42001 words to 45000 words out of 57328 words
hankalin da take ciki ya bayyana ƙarara akan fuskarta ba, Baiwar nisawa tayi ta ƙara rissinawa hankali a tashe ta ce. "Wallahi na matuƙar kaɗuwa da yadda aka ce ta yiwa Waziri nikam anya ba wani asirin ta dawo da shi ba? Ina laɓe fa na hangota ta haƙo abu a wani rabi muna haɗa ido ta watsomini idanunta wallahi bakiji yadda gabana ya faɗi ba..." Maganarta ce ta maƙale lokacin da suka ji shigar Maryo ɗakin ta bankaɗa labule, daga gurin da take ta tsaya tana ƙare musu kallo. Baiwar ce ta miƙe sum sum sum tana cewa. "Na barki lafiya ranki shi daɗe." Maryo wata uwar tsawa ta daka mata ta ce. "Wallahi idan kika fita ba tare da izinina ba kin dinga tafiya kenan har abada." A dai-dai lokacin Maleek ya shigo yana cewa. "Shukra wai me kike yi ne haka? Ki zo mu tafi mana" Fulani ba ƙaramin faɗuwar gaba ta shiga ba amma sai ta dake ta ce. "Ke Shukra lafiya zaki shigo mini ɗaki babu ko sallama..." tun bata rufe baki ba Maryo ta ɗaga mata hannu tana dakatar da ita cikin tsawa ta ce. "Baki cancanci sallama ba tunda bakisan muhimmancinta ba, ki saurara mini ki kuma bani haɗin kan abin da na zo aiwatarwa, idan kika bani haɗin kai zanyi ingama kuma inyanke hukuncin da naga dama amma..." Maleek da sauri ya hankaɗa ta gefe yace. "Wai baki da hankali ne Umma Babba kike gayawa haka?" Fuska babu alamun tsoro Maryo ta kalleshi ta ce. "Akan wannan abar kake ɗaga mini murya? Ka iya bakinka ina raga maka ne saboda abu ɗaya wallahi kaci albarkacinta amma ba dan haka ba da tuni labarin wani ake ba kai ba." Juyawa tayi ta kalli Fulani ta ce. "Maza ki tono mini abin da kika binne yanzun nan?" Fulani rushewa tayi da kuka tana cewa. "Maleek dama kawo matarka kayi dan ta ci mini mutumci ni zata laƙawa sharri ina zaune ƙalau."
Maryo a hassale ta juyo ta ɗauke Fulani da wani irin gigutaccen mari, ba Baiwarta ba hatta Maleek sai da ya zaro ido cikin tashin hankali yana ganin haka yasa hannu itama ya ɗauketa da wani irin gigitaccen mari yana huci yace. "Wannan ya zame miki na farko kuma na ƙarshe, wannan da kike gani kamar Mahaifiyar da ta haifeni haka nake kallanta, wallahi idan kika kuma aikata abin da kika yi yanzu zan baki mamaki, karki rainawa mutane hankali mana." Fulani daɗi taji har cikin ranta sai ma ƙara keɓe baki tayi tana kuka, Maryo murmushi ta fara yi lokaci ɗaya sukaji tana dariya harda ƙyaƙyatawa.
Kallan Maleek tayi tana nuna shi da yatsa fuska a turɓune ta ce. "Wannan shine marin da zaka yi mini na farko na ƙarshe dan wallahi sai na hukunta ka." ta juya ta kalli Fulani Babba ta ce. "Daga yanzu zaki san na shigo cikin gidan nan gado sai ɗan gado gararanba sai ɗan taka haye, sai kin tabbatar da cewa ni ɗinnan dawowata daularmu bazai taɓa yi miki daɗi ba" tana gama faɗa ta ƙarasa dai-dai tsakiyar ɗakin Fulani tana tsayawa a gurin ta tsugunna ta fara bubbuga gurin nan take ƙasar gurin ta fara rozayewa tana fashewa, da ƙarfi ta fara ƙwaƙule gurin tana zura hannunta tana ɗaukowa sai ga wani ƙaton abu a naɗe a cikin fatar bunsuru, zazzagesu ta fara yi sai ga kayan Sarki Abdallah harda rawaninsa na faɗowa, daga gefe ɗaya wata hallita suka gani ita ba mutum ba ita ba dabba ba, Fulani cikinta ne ya kaɗa hankalinta ya tashi saboda ganin an tono abin da tafi shekara sama ashirin da biyar zuwa talatin da binne shi.
HAPPY WEEKEND🥰
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[16/11/2021, 13:32] Ameera Adam🌚: 29...
Tattaro Jarumta Sarki Aminullah ya yi sannan ya kalli Salman yace. "Lafiya Salman me kake yi anan da daren nan?" Salman da idanunsa suka yi jawur ya furzar da iska mai zafi yana jefawa Sarki Aminullah mugun kallo a daƙile yace. "Ba komai" yanayinsa ba ƙaramin tsorashi ya yi ba, haɗiye yawu ya yi cikin ɗari-ɗari sannan yace. "To shikenan ka wuce sai da safe" Salman tsaye ya yi kamar bai ji me Takawa yace ba, har ya ɗan fara takawa ya juyo yace. "Ranka shi daɗe me yasa ka bada yarinyar cen suka tafi da ita alhalin ba ka tabbatar da cewar matarsa ce ko ba matarsa bace?" Sarki Aminullah ba ƙaramin faɗuwar gaba ya shiga ba, tashi ya yi zaune yace. "Saboda ita kanta yarinyar ta furta da bakinta kuma ga shaida nan mun gani" Salman ya wurga masa idanunsa da sukayi jawur kamar gauta, Sarki Aminullah kasa ci gaba ya yi da kallan ƙwayar idon Salman, Salman yaja gajeren tsaki sannan yace. "Wallahi ba matarsa bace dani tafi dacewa dan haka duk abin da zai faru sai ya faru" yana gama faɗa ya fice daga cikin turakar.
Abu ba ƙaramin jindaɗi yadda ake tarairayarta a sashen Fulani Zaliha taji ba, tun tana ɗari-ɗari har ta sake ta fara harkokinta a cikin gidan, bata aikin fari bare na baƙi sai dai taci ta sha ta kwanta. Sallah da abubuwan da suka zame mata dole su kaɗai take yi, kasancewar Fulani Zaliha na matuƙar san ƴa mace kuma bata da ita yasa ta ɗauki so da kulawa ta ɗora akan Abu wacce a yanzu suke kiranta da Zainab. Saif shi yake koya mata karatu addini dukda a lokacin ba'a wani waye da makarantar boko ba, hakan yasa basu wani damu da ita ba. Tayi matuƙar mamakin yadda Saif ya iya karatun alƙur'ani tiryen-tiryen tun da kowa yasan irin rashin lafiyar da Saif ya yi, sosai take gane karatunsa saboda mutum ne me sauƙin kai. Sai da suka fara wannan mu'amalar da shi ta fahimci yadda yake da saukin kai kamar ba Ɗan sarki ba, gashi akwai barkwanci da iya magana. Abu ɗaya ta lura da shi daga cikin ɗabi'unsa ba yasan raini ko kaɗan sai dai shi mutum ne ba me ruƙo ba kuma da kayi abu zai nuna maka kuskurenka. A gefe ɗaya kuma idan ta kalleshi sai ta ga kamar ba shi ba musamman idan ta tuna yadda yake yiwa ƴar uwarta sai ta ji babu daɗi, sai ta yi kamar zata yi masa maganarta sai kuma tsoro da fargaba su ɗarsu a zuciyarta.
Maryo kallan Fulani Babba tayi ta saki wani malalacin murmushi ta ce. "Wannan abun ba ke kika binne shi ba shekara talatin da suka wuce?" Fulani Babba ta zauna daɓar kamar wacce aka zarewa laka sai kuma ta fashe da kuka ta ce. "Kai jama'a wai saboda a wulaƙantani a tozartani shine za'a ƙirƙiro waɗannan abubuwan ina ji ina gani ace daga ɗakina suke, akan idanun kowa kika aiwatar da siddabarun ki amma dan ni kaɗai kika tsana kice wai nina binnesu." Baiwar Fulani Babba jikinta ne ya yi sanyi dan tasan sarai Fulani zata iya aikata abin da ya fi wannan ma, amma kuma ya akayi Shukra tasan da wannan abubuwan to ko ta fara tsafi ne kamar yadda tayi tsammani. Shi kansa Maleek ba ƙaramin mamaki ya yi ba amma kuma ya akayi ita ta san da wannan abun, sannan kuma anya ba sharri take san ƙagawa Fulani Babba ba tun da dama cen ba jituwa suke yi ba. Maryo ce ta yi wata ɗariya sannan ta ce. "Ni da kika ganni bana ƙwai na sai da zakara ki gama matse-matsen hawayenki wannan kukan yanzu kika fara, dan wallahi sai na bankaɗa sirrin ki na ɓoye kowa ya gane kalarki da ke da munafukan cikin masarautar nan, kin ƙaryatani kin ce sharri na yi miki ko?" Fulani Babba tayi zuru saboda tashin hankali cikinta ban da rugugi babu abin da yake yi. Kasa amsa tambayar da Maryo tayi mata tai sai binta da take da kallo tana fargabar karta ƙara bankaɗo wani mugun ƙullin da ta ɓoye shi. Maleek ya tamke fuska yace. "Shukra dan Allah kizo mu wuce banasan waɗannan abubuwan da kike yi, wannan abun fa kamar kina neman tada hankalin masarauta ne." Maryo itama tamke fuska tayi tasa farin ƙyalle data wanke shi bai gama bushewa ta goge jinin da ya ɗigo daga hancinta ta ce. "Ai dama babban burina kenan in tayar da hankalin Masarauta a fahimci bambamcin ina nan da bana nan, ka bar wahalar da bakinka dan duk faɗin masarautar nan mutum biyu ne zasu iya dakatar dani daga aikata abin da nayi niyya." tana gama faɗa ta wuce ta wajen damɓasheshiyar kujerar da Fulani Babba take zaune, ƙirjin Fulani ne ya shiga bugawa ba ƙaƙƙautawa saboda fargabar abinda zata zaluƙo. Da sauri Maryo ta sa hannu ta riƙo hannun Fulani ta ɗaga ta daga kan kujerar, ganin haka yasa Maleek takawa zuwan gurin da niyyar janye ta, tana juyowa ta ce. "Hurmin ga ajiya na baku" Maleek duk yadda yaso ɗaga ƙafarsa ya ƙarasa gurin kasawa ya yi, Maryo ƙafa ɗaya tasa ta ture kujerar wata ƙwarangwal ɗin mage suka gani a tsugunne da alama da ranta aka ajiye ta agurin har ta mutu ta bushe a haka, Fulani Babba shiru tayi gumi na keto mata sai a lokacin Maryo ta kalli Maleek ta ce."Ku sake shi" Fulani da Baiwarta juyawa suka yi dan su dai basu ga kowa ba, amma sun tabbata bokan da ya bata sa'a to da makarai take aiki. Maleek ƙarasawa ya yi gurin ya ga busasshiyar magen nan, Maryo ta kalleshi ta ce. "Ganin buzu a masallaci ya isa tinkiya tayi karatun ta nutsu, idan wannan kawai bai hankaltar da ku ba akwai wasu ƙullin a gaba amma wannan da kanta zata kunce su, idan kuma tayi gaddama sai na tara mutanen garin nan sannan na kunce su da kaina." Ta juya tana kallan Fulani da gumi ya gama wanke mata fuska ta ce. "Na baki wunin yau ko ki samu Sarki Abdallah ki sanar da shi da iyalansa abin da kika aikata musu ko kuma na fallasaki da kaina hatta da mutuwar Mai babban Ɗaki" A firgice Fulani Babba ta ɗago tana kallan Maryo, Maryo tai mata murmushi ta ce. "Kina mamaki ne? Ai ni ginshiƙin dutse nake kowa yayi karo dani shi zai faɗi. Idan kin aiwatar da abin da na umarce ki akwai wani a gaba dan kinsan ƙullin naki da yawa." Maryo na gama faɗa ta wuce fuuuuu kamar zata tashi sama. Tana tafe Maleek na bin ta a baya kamar jela duk inda suka wuce sai dai kaga ana binsu da kallo, dan ma ba ƙaramin tsoron Maleek suke ji ba hakan yasa suna ganinsa kowa zai ci gaba da aikin da yake yi, sai sun wuce kaji ƙananan maganganu na tashi.
Suna shiga sashen su Maryo ta shige ɗaki ta datse kofar duk yadda yaso ta buɗe haka ya ƙaraci tsaiwarsa ya bar gurin har sai da Bayin gurin suka fara fahimtar halin da suke ciki. Yana nan tsaye saƙo ya iso masa daga fadar Mai martaba, jiki a sanyaye ya wuce fadar dan yasan ba akan komai za'ayi masa wannan neman na gaggawa ba sai akan matarsa. Yana zuwa ya yi sallama cikin fadar ya shiga ya zaune daga cen gefen Sarki Abdallah, Maleek yace. "Allah ya taimakeka ance kana nema na" Sarki Abdallah ya numfasa yace. "Maleek mun aika kiranka ne ba dan komai ba sai dan muna ganin kamar akwai matsala tattare da iyalinka." Galadima da ke gefe ya gyaɗa kai, Maleek ya russuna yace. "Haka ne Ranka shi daɗe nima na fahimci haka, saboda na ga canje-caje daga yanayin mu'amalarmu da ita." Sarki Abdallah ya jinjina kai yace. "Dan haka ya zama wajibi a nema mata magani saboda gudun abin da kaje yazo, yanzu kana gani da ba'a kusa me kake tunani zai faru da Waziri" Maleek ya kai kallonsa ga Waziri da har lokacin da alama bai gama dawowa dai-dai ba. Maleek yace. "Insha Allah za'ayi yadda kace" Sarki Abdallah ya kuma gyara zama yace. "Abu na gaba da nake so da kai, ka yi bakin ƙoƙarinka wajen ganin ka hanata fitowa waje har sai ta samu lafiya." Maleek ya gyaɗa kai ya russuna cikin girmamawa yace. "Insha Allah ranka shi daɗe" daga haka Sarki Abdallah ya sallami Maleek sannan suka ci gaba da tattaunawa. Galadima ne ya kalli Takawa yace. "Allah ya taimake ka nifa lamarin yarinyar nan ina ganin kamar harda makarai" Waziri da ke gefe yace. "Wallahi babu wani makarai nina fi zargin aikota akayi kawai ta halakani" Sarki Abdallah yace. "Waziri bana tunanin wani zai turo Shukra ta kashe ka, saboda idan ta kashe ka ribar me zata samu tunda ita ba kowa gareta ba, nafi aminta da maganar Galadima saboda ga dukkan alamau akwai shafar jinnu a jikinta." Waziri da yake ganin kamar sun take gaskiya ne ya rufe baki cikin takaici. Sarki Abdallah ya kalli Galadima yace. "Galadima a nemo masu magunguna saboda a tari matsalar da wuri kar matsalar ta nemi gagarar kundila." Galadima ya amsa sannan suka ci gaba da tattaunawa
Bayan kwana biyu zaman Maryo da Maleek ba wata matsala sai dai babu mai kula wani a tsakaninsu daga gaisuwa sai gaisuwa abin da yake haɗa su kenan, Fulani da farko ta so ta samu Sarki Abdallah da maganar amma da ta yi wani tunani sai ta barshi dan ra'ayin kanta saboda wani shiri da take ƙullawa. Da safiyar ranar Laraba Maleek ya tafi da Maryo ɗakin baya da aka tanada saboda masu magani anan zasu dinga dubata, suna zuwa Maryo ta nemi guri ta zauna tana ƙarewa Mai ganin kallo. Wani ɗan busasshen saurayi ne yana maƙale da jakarsa fa maganjɓi, zama ya yi ya fara ciro da kayan aikinsa. Daga cikin jakar yaga hayaƙi na fitowa lokaci ɗaya suka ga wuta ta kama Jakar, tana ƙoƙarin lasar Mai maganin. Maleek baya ya ja cikin ta'ajibi Maryo kallan Mai maganin ta yi ta ce. "Idan na kuma ganinka ƙafarka a gurin nan ba jakarka ba hatta kai kanka sai na ƙone ka." tun bata gama faɗa ba Mai maganin ya fice a guje ko waiwaye baya yi.
Sannu a hankali shaƙuwa ta fara shiga tsakin Abu da Saif dan bashi da abokiyar hira sama da Abu, itama kuma haka yanzu hatta shan iska idan zai fita sai ya nemi rakiyar Abu suna tafe suna hira har suje gurin da zasu je. Kamar kullin yauma Abu ce ta shirya cikin kayanta masu kyau, Fulani Zaliha ce ta bata kuɗin kayan kwalliya su jagira da gazal harda kuɗin kallabi saboda na Abu sun ɗan yi ƙaranci. Har ta fito tsakar gida Saif ya dakatar da ita suka tafi tare suna tafe suna hira, duk inda suka wuce a cikin gidan sai anyi gulmarsu saboda wasu har sun fara yi musu wata fassara, wasu suce soyayya suke wasu kuma suce shaƙuwa ce kawai kowa dai da abin da yake faɗa. Kai tsaye kasuwar rimi suka wuce Abu take ta siyayya har ta kammalla, wasu kayan Saifa ne yake riƙe mata wasu kuma ita take riƙewa. Kamar almara ta hango Maryo gaban wani me sayar da kayan ƙore da jigidar mata, sakin baki tayi da murnarta tana nunawa Saif ta ce. "Maryo! Yaushe kuka zo?" Saif yace. "Wace Maryo kuma" gurin da take nuna masa ya kalla hango ya yi tsaye itama su take kallo, nan take ya tsuke fuska Abu ta matsa zata ƙarasa gurin da sauri ya riƙe hannunta yana cewa. "Wallahi idan kika matsa daga nan sai ranki ya ɓaci" juyowa tayi ta kalleshi idanta cike da hawaye ta ce. "Maryo ce fa ƴar uwata" fisge hannu tayi da niyyar zuwa gurinta amma ga mamakinta sama ko ƙasa haka ta nemi Maryo ta rasa.
_LITTAFIN ANY BAIWA CE NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[17/11/2021, 11:17] Ameera Adam🌚: 30...
Kurɗawa ta dinga yi cikin mutane tana laluben Maryo haɗe da ambatar sunanta, tana gaba Saif yana biye da ita yana kiranta. Idanunta ne suka ciko da ƙwallah ganin har zuwa wannan lokacin babu Maryo babu alaminta, gefe tana tana zubda hawaye ta ce. "Maryo ina kika shiga ne me yasa kika tafi ne?" Saif ya ƙaraso gurinta fuska a ɗaure yace. "Baza fa ki ganta ba." Abu ta goge ƙwallar idonta ta ce. "Saboda me?" Saif ya ɗaga kafaɗarsa alamun shima bai sani ba sannan yace. "Da tana so ki ganta da baza ta tafi ta barki ba kinga kuwa tana sani ta ɓoye miki, dama ke kika damu da ita ban da haka da ta damu dake bazata..." da sauri ta katse shi da cewar, "A'a wallahi akwai dalilinta na san ɓoye mini. Maryo ba yadda ka fassara ta take ba, na fi kowa sanin wacece ita amma..." Shima katse ta ya yi yana tsareta da dara-daran idanuwansa yana faɗin. "Wuce mu tafi ina ga ta fara yi miki gizo ne dan da ita ce a yadda kika faɗa kinga bazata tafi ba" Ganin zata ɓata musu lokaci yasa ya riƙo hannunta suka wuce tana tafe tana waiwaye, har sai da ya ga sun bar wajen kasuwar sannan ya sakar mata hannu. Har lokacin Abu hawaye take dan zuciyata taƙi aminta da cewar wai gizo Maryo take yi mata, suna ƙarasawa gida a gaggauce ta ƙarasa gurin Fulani Zaliha ta ajiye kayan da suka siyo kai tsaye ta wuce sashen Fulani Maryama.
Sallama ɗauke a bakinta ta shiga sashe sai da ta fara shiga wurin Fulani Maryama ta gaisheta, sama-sama Fulani Maryama ta amsa fuska a tsuke ta ce. "Lafiya me kika zo yi a nan?"