Showing 1 words to 3000 words out of 57328 words

Chapter 1 - Anya Baiwa Ce 1 Complete Hausa Novels.txt

30 Nov 2024

3907

[21/10/2021, 19:43] Ameera Adam🌚: 11..




Maganar Boka Marduska na sauka a kunnen Fulani Maryama ji tayi kamar saukar aradu muryarsa har wani amsa kuwwa take mata a kunne, nan take jikinta ya ɗauki tsuma bakinta har tuntuɓem harsge yake a hargitse ta ce. "Marduska ka taimaka mun ka tallafi rayuwata ka sanar dani ta yaya zan gane wace ce ita?" Boka Marduska wani kallo ya wurga mata yana ci gaba da hura wutar da ke cikin ƙoƙan ƙan ƙwarangwal yace. "Maryama me yasa taurin kai gare ki ne? Wannan maganar ba baƙuwar magana bace a gurinki ni kaina bazan iya ja da wannan yarinyar ba, hasali duk wani bincikena na gagara nemo ainihin kamannin yarinyar, abinda nake ta shakku a raina wai ma mutum ce ko itama ta fito cikin sigar aljanu? Waɗancen da suka shuɗe ɗaya ta fito cikin fararen aljanu ɗaya kuma ta fito daga baƙaƙaen aljanu. Abin da ban sani ba shin wannan ita daga wanne ɓangare take, taimako ɗaya zanyi miki Maryama idan har bincike ya bani dama..." Fulani Maryama har kusan faɗawa kanshi tayi jiki na rawa katse shi. "Marduska ka taimaka mun ko kamanninta ne ka gaya mini ta yadda zan fahimci wace ce daga ciki" Marduska ya tsuke fuska yace. "Maryama me yasa kin fiya rawar kai kamar wacce taci sadakar miji ne? Kinsan Allah da kin faɗa kan wannan wutar da kin gwammaci haɗuwarki da Rayzuta dukda kuwa karonku da ita ba alheri bane, kinsan wannan wutar ko yaya ta taɓa jikinki sannu a hankali nama jikinki zai fara zagwanyewa ga ɗoyin da zaki dinga yi kamar mushe" Fulani Maryama ta russuna ta ce. "Tuba nake sarkin bokayen duniya."


Marduska ya cigaba da bincikensa a cikin wuta yana jefa waɗansu littafan tsafinsa, daga cikin wuta take wani fili ya bayyana, wata matashiyar budurwa ce a tsaye ta juya baya hannunta na saƙale da wani matashin saurayi." Yarfe gumin fuskarsa yayi sannan yace. "Maryama zo ki gani" Da sauri Fulani Maryama ta fara leƙawa fuska ɗauke da damuwa ta ce. "Marduska ban gane komai ba na hangi mace da namiji a tsaye, ka taimaka ka wayar mun da kai ka dubi girman tsafi ka siffanta mini ita" Marduska yace.


"Yarinyar ƴar doguwa ce amma ba tsayi cen sosai ba tana da ɗan kauri kaɗan, kuma ba fara bace ba kuma baƙa wuluk bace. A taƙaice ruwan tarwaɗa ce sai dai a fuska kyakkyawa ce tana ɗauke da manyan idanu da dogon hanci yanayinta kamar na buzaye sai dai har yanzu ainihin siffarta yaƙi bayyana ta yadda zamu gane wace ce ita ya kamanninta yake, ni ina jin tsoron bincike akanta sabida rannan dana tura aljanu su ɗauko mun ruhin baiwarki Bintu ta kashe mun aljanun da suke mun wannan aikin, ina gudun karta fara waiwayo ni saboda tana ɗauke da ƙarfin iko akan mutane da aljanu." Fulani Maryama gabaɗaya ta haɗa gumi sai zare ido take kamar shege a rabon gado, hankali a tashe ta ce. "Marduska gabaɗaya kaina ya kulle ga wannan yarinyar ga warkewar Saif yanzu wane magani zaka bani wanda zai kuma nakasashi kuma idan na gano wace ce ita wane irin mataki zan iya ɗauka a kanta? Zan iya nasaka ta ko kuma na illa ta ta." Marduska wani kallo ya wurga mata sai kuma ya bushe da wata irin dariya har yana ƙyaƙyatawa.


Sai da ya yi me isarsa sannan ya kalli Fulani Maryama da ta haɗe fuska kamar zata yi kuka, yanayinta ba ƙaramin ɗariya ya bashi ba nan take ya kuma bushewa da dariya ya ce. "Lallai Maryama yanzu na ƙara tabbatar da baki da hankali, yarinya da nace miki ta hallaka aljanu ita ce zaki iya karawa da ita? Shin idan hankalinki ya tashi tunaninki gushewa yake yi ne? Bazan ce miki komai ba ga fili ga me doki dan haka jiki magayi, wai bahaushe yace kowar tuba dan wuya ba daɗi. Idan kina ganin zaki iya da ita sai kin gwada, amma ki sani wannan abinda zakiyi kamar tarar aradu da ka ne. Shawara ɗaya zan baki ita ce, bayan kin gano ta kiyi yadda zakiyi Sarki Aminullah ya koreta daga cikin masarauta ta hanyar ƙulla mata sharri ko wani abun, wannan ita ce damar da zakiyi nasara akanta. A ɓangaren yaron kuma maganar gaskiya sai dai kiyi haƙuri dan babu wani abu zan iya aiwatarwa akanshi saboda ina gudun fushinta ya sauka akaina, ina me tabbatar miki wanann kogon da nake ciki tana iya rushe mu dasu gabaɗaya da ni da komai mu hallaka."


Fulani Maryama gabaɗa zuciyarta ta gama dagulewa rasa abin yi tayi nan take ta rushe da wani irin matsanancin kuka.


Sai fa tayi me isarta sannan ta fyace majina ta ce. "Mardusk me yasa al'amura suke ƙoƙarin juya mun baya ne, naji shawararka kuma zanyi amfani da ita kuma ina san ka ƙara mun ƙarfin iko agurin Takawa, ta yadda duk abinda na bashi umarni zai zartar ba tare da ya musa mini ba." Boka Marduska ɗan jim yayi sannan yace. "Wannan kam za'a iya aiwatarwa sai dai me zaki fansar mun saboda banasan na ƙara tura aljanu na nayi asararsu."Fulani Maryama ta ce. "Faɗi duk abinda kake so ya kai wannan babban boka mai cikakken iko" Boka Marduska yace. "Ga wani farin ƙyalle cen a cikin tsohon kabarin ce ki ɗauko shi ki dangwalar min jinin da kike yi na ɓarin cikin da kika yi." Fulani Maryama kanta tsaye ta wuce wajen da Boka Marduska ya nuna mata ta aiwatar da ya umarceta sannan ta dawo gurinsa, tana dawowa Boka Marduska yace. "Tashi karki zaune mini wuce ki tafi wannan buƙatar dai ta biya sai dai wata kuma." Yana gama faɗa ya ɓace daga gurin, Fulani Maryama miƙewa tayi ta fice daga cikin kogon dutsen.



Lokacin da Fulani Zaliha ta ƙarasa gurin Saif da yake ta kwara amai riƙe shi tayi cikin tashin hankali tana kururuwar neman ceto, da sauri wasu bayi suka ƙaraso gurin suka taimaka mata suka rirriƙe shi da alama baya cikin hayyacinsa, jikinsa banda karkarwa babu abinda yake yi ga wani irin zafi da jikinsa ya ɗauka. Hatta da gumin da ke tsattsafowa ta jikinsa da wani irin zafi yake fitowa, Bayin da suka riƙe shi gazawa suka fara ƙoƙarin yi saboda zafin da yake azabtar da hannunwansu. Fulani Zaliha da gudu da nufi fadar Sarki Aminullah ta sanar dashi halin da Saif yake ciki, Salman na gefensa yana jin haka ya fara cika yana batsewa haɗe da wurga mata wani mugun kallo, cikin kallan tsana yace. "Wai kina nufin kwantaccen ne ya tashi?" Sarki Aminullah ya kalleshi yace. "Nima abin da nake mamaki kenan Saif yaron da ko rarrafe bayayi sai jan ciki wannan lamarin da mamaki" Fulani Maryama ranta ba ƙaramin ɓaci yayi ba ta ce. "Kai hawainiyarka ta kiyayi ramata a hir ɗinka banasan rashin kunya wallahi duk ranar da bakinka ya ƙara kuskuren laƙabawa ɗana mummunan suna irin wannan ranka zai yi mugun ɓaci" Salman dariya ya bushe da ita sannan yace. "Ƙarya nayi ba kwantaccen bane ko kina bakin ciki ne baya taka ƙasa har yanzu?" Fulani Zaliha a hassale ta kife Salam da mari ta ce. "Da alama tarbiyya tayi ƙaranci a gurinka..." a zafafe Sarki Aminullah ya katse ta. "Ke Zaliha baki da hankali ne? A gaba na kike niyyar nasaka ɗana saboda naki ɗan nakasasshe ne? Daga yau karki ƙara idan ba haka ba zan ɗauki mata ki akanki kuma matakin bazai miki daɗi ba."


Idanun Fulani Maryama ne suka ciko da ƙwala ta ce. "Ranka ya daɗe ni kake cewa mahaukaciya akan wannan yaron shikenan ni ka wulaƙanta akanshi ko? Wallahi na gaji yau tsawon shekaru amma da ashirin ana abu ɗaya nida ɗana bamu da ƴanci sai wulaƙanci da cin zarafi, kullin ka tashi baka taɓa alaƙanta Saif da Ɗanka sai dai kace Ɗanki to babu komai tunda baka ƙaunarmu zamu fita daga rayuwarka, gani kake idan bama tare da kai bazamu iya rayuwa ba ko? Babu komai idan adalci kake mana zaka gani idanma ba adalci kake yi ba zaka ga..." bata ƙarasa maganar ba Sarki Aminullah ya zabga mata wani gigitaccen mari harsai da ta durƙushe a gurin, wani irin matsanancin kuka ta rushe da shi jiki ba ƙwari ta tashi ta fice daga gurin.


Lokacin da ta koma Saif na kwance a gurin yana ta malala wani irin amai, sauran Bayin duk sunyi carko-carko a gurin Fulani Zaliha banda hawaye babu abinda take yi. Da sauri ta kira wasu Dogarai ta sa suka ɗauki Saif suka wuce da shi cen sashenta, wucewarsa da shi yayi dai-dai da dawowar Maryo saboda yadda taga yana aman ba ƙaramin tausayi ya bata ba, hanyar sashen Fulani Zaliha zata bi dan ganin halin da yake ciki, da sauri Abu da janyo ta tace. "Ke Maryo me kike shirin yi haka? Dan kinga yau da safe mun shiga sashen Fulani Zaliha shine yanzu zaki koma?" Bakisan yanzu da bambamci tsakanin ɗazu da yanzu ba? Ke fa yanzu Baiwar Fulani Maryama ce kinsan idan labari ya ishe mata ranki zai yi mummunan ɓaci? Wai ma wace ce ke a gidan nan da zaki dinga tura kanki cikin Mutane masu daraja, karki manta mu fa Bayi ne ƙasƙantattu marasa galihu ɗazu ina ce saƙo muka kai gurin Fulanin" Maryo da idanunta suka ciko da ƙwalla ta ce. "Abu ni kaina bansan me yake damuna ba sai nayi kamar na koma sashen mu sai kuma gangar jikina ta hanani aiwatar da haka, sai in dinga jina kamar yana da haki akaina idan ban taimakeshi ba kamar ban kyauta ba. Wani tsagi na zuciya ta na yawan raya shakku akan ni kuwa ANYA BAIWA CE? Sai in dinga wani irin tunani daban" Abu ta ce. "Wane irin taimako zaki yi masa baki ji labarin da aka bamu ba akace masu magunguna da yawa sun mutu akanshi, ki rufa mana asiri Maryo mu zauna lafiya a gidannan banda ma yaudarar kai har kin dinga tunanin ke ba baiwa bace idan ke ba baiwa bace mece ce?"


Maryo ta ce. "Tambayar da har gobe bani da amsar ta hasalima bansan da me zan taimaka masa ba amma wallahi Abu tun ɗazu da nayi arba da wannan ɗan Sarkin naji zuciyata ta harba akansa lokaci ɗaya naji na kamu da ƙaunarsa." Abu ƙwalalo idanu tayi da sauri ta fisgi hannun Maryo ta ce. "Maza zo mu wuce tun ba'a yanke mana mummuna hukunci ba."


Maryo ba dan ta so ba ta bi Abu suka wuce cen saahen su na Bayi kai tsaye suka wuce madafa domin sarrafa abincin da zasu ci. Bayan magari ba suna zaune a tsakar gida saboda zafi suna shan iska, daga cen nesa ta fara ganin giftawar mutane kamar wacce a ka tsikara haka ta tashi, suna ganin tasowarta suka juya suka fice daga gurin ita kuma ta rufa musu baya. Basu tsaya a ko'ina ba sai tsakankanin manyan bishiyoyin kukar nan guda biyu. Tana zuwa gurun ta hangi mace mai kama da ita sak tana rungume da wani namiji jikinsa duk jini da alama baya numfashi, matsawa ta fara yi a hankali tana ƙare mata kallo sai dai da alama kuka take rerawa cikin wata irin murya. Maryo matsawa tayi zata taɓa ta sai ji tayi ance. "Kije ki ceci rayuwarsa yana cikin wani hali wannan ne kawai taimakon da zaki iya yi masa."




_LITTAFIN ANYA BAIWA CE? NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[23/10/2021, 19:44] Ameera Adam🌚: 12...


Ɗaga kanta tayi tana waigen me maganar amma babu shi babu alamarsa dawo da kallonta tayi wajen me kama da ita, tsugunnawa tayi tana ƙare musu kallo, a hankali ta sa hannu zata taɓa ta saboda yadda taga tana gursheƙen kuka, ba ƙaramin tausayi ta bata ba. Tana kai hannu taji ta ce."Dan Allah ki ceci rayuwarsa iya abinda zan iya sanar da ke kenan bana fatan sake rasa shi" tana nan durƙushe ta hango wani ya tunkaro gurinta kafin ta ankara taji ya fara fisgarta da ƙarfin tsiya, Maryo so take ta ƙwace amma ta gagara saboda mutumin ya fita ƙarfi nesa ba kusa ba, yana cikin janta ta fara kururuwar neman taimako tana ihu haɗe da roƙo kamar wacce ta tuna abu haka ta fara karanto addu'in da duk suka zo bakinta, nan take taji ya saketa kuma ya ɓacewa ganinta.


Waigawa tayi ta hango har zuwa lokacin wannan mace da namijin suna zaune da hawaye ɗauke a fuskarta, daga cen nesa taji ana ƙwala mata kira ba ƙaƙƙautawa jiki a sanyaye ta juya da niyyar ta ƙarasa gurin da take hango wannan mace da namijin da sauri taji Inna Habi ta ja hannunta tana cewa.


"Ke Maryo kanki ɗaya kuwa me yake damunki zaki taho dokar daji a daren nan lafiyarki kuwa?" Maryo idanunta ne suka ciko da ƙwalla ta ce. "Inna wallahi sai roƙona suke akan na taimaka musu ni bansan taimakon da zanyi musu ba, amma wallahi da alama suna buƙatar taimako na Inna" Inna Habi zaro idanu tayi tana kallan gurin da Maryo take kallo tana mata magana, amma ita bata ga komai ba. Inna Habi hannun Maryo ta ja ta ce. "Maryo anya kuwa makarai basu fara buɗe miki ido ba? yanzu cikin dokar dajin nan kizo kice wai wasu na yi miki magana, maza wuce mu tafi karki jaza mana masifa" Maryo juyawa tayi ta ga waccen me kama da ita tana hawaye ta miƙe tsaye ta riƙo namijin yana ɗingishi suka ɓace daga gurin. Maryo hannu ta fusge ta ce. "Shikenan Inno wallahi sun tafi kuma yana cikin wani hali nidai Inna gaskiya..." Da saurin Inna Habi ta fisgi hannunta suka fara tafiya har sai da suka baro gurin, suna shiga sashensu Abu ta ce. "Maryo ina kika je tun ɗazu Fulani Maryama ta aiko kiranki?" ɗigon jinin hancinta da ya fito ta goge kanta na ci gaba da sarawa, idanunta take suka rune jawur hannuwa biyu ta sa ta dafe kanta ta ce. "Abu kije a madadina wallahi bana jin daɗin jikina" Abu zaro ido tayi ta ce. "Fulani Maryama fa ita take kiranki gaskiya bazan iya zuwa ba, ki lallaɓa ko a hankali ne kije kuma kisan ƙaryar da zakiyi mata dan ta aiko kiranki yafi a irga." Inna Habi ta ce. "Gaskiya Maryo akwai abinda yake damunki anya bazamu fara nema miki maganin makarai ba, wannan jikin naki ba lau ba yanzu ki wuce kije kiran da Fulani Maryama take miki banasan abinda zaki yi wanda za'a hukunta ki da horo me tsanani." Maryo tafiya ta fara yi tana haɗa hanya hannunta ɗaya dafe har ta ƙarasa sashen Fulani Maryama. Tana gabda shiga rumfar Fulani Maryama ta yanke jiki ta faɗi wanda yayi dai-dai da shigowar Jakadiya.


Jakadiya na ganin haka ta rafka salati tana tafa hannuwa ta ce. "Yau me nake gani ni Kubura ke ƴar nan ya na ganki a sheme kamar gawar goɗiya jama'a ku kawo ɗauki" Fulani Maryama ce ta leƙo ta ce. "Jakadiya ihun me kike yi?" Jakadiya ta zaro ido ta ce. "Wannan mai kama da ƴar bararojin ce na samu ta faɗi a gurin" a yatsine Fulani Maryama ta kalleta ta ce. "Jakadiya maza ki fitar mun da ita idan kin kaita cen sashen su ki dawo ina san ganinki"


Jakadiya ta kalli Maryo da take wani irin karkarwa ta ce. "To Allah gamu gareka Bawan sarki ya rasa doki, yanzu ki rasa inda zaki yi farfaɗiyar ta ki a babban sashe na Fulani Maryama, kekam ki haɗani da jaraba ɗaukar kamar ki ai sai na shirya. Ga dai yarinya a haka da ƙuruciya kamar na nauyi amma wallahi wannan sai ta kusa ɓalle mun baya, gwara na kira waɗancen ƴan iskan dogarawan su zo su tayani kwasar..." Fulani Maryama gajiya tayi da surutan Jakadiya ta ce.


"Jakadiya bansan surutu a kwashe mini ita daga gurin nan?"


Jakadiya juyawa tayi fara ƙwalawa Dogaran bakin ƙofa tana magana. "Kai Badaru kana ina kuzo" kafin su ƙaraso Maryo ta ɗan jin saukin yanayin da take ciki miƙewa tayi jiki ba ƙwari jiri na ɗaukanta, Jakadiya juyowa tayi ta taɓe baki ta ce. "Feleƙe ratayar jaka a duwawu dama farfaɗiyar ba ta gaske bace, to muje karki jazawa uwar ɗakina masifa ki mushe mata mu shiga uku." Jakadiya tasa Maryo tayi a gaba tana tafe tana zazzaga mata surutai suna gabda wuce tsoron tsakiya Maryo ta fara haɗa hanya, ji tayi ta yi karo da abu wanda yayi dai-dai da tafiyarta luuuuuuu. Kafin ta kai ƙasa ya taro ta dukda idanunsa a rufe suke jin alamun mutum yasa yayi saurin taro ta. Jakadiya ta kuma rafka salati tana cewa. "Shikenan wannan yarinyar zata ja mun taɓa gawa ina zaman zamana" Fulani Zaliha hannunta da yake sarƙe dana Saif ta ce. "Subhanallah Jakadiya lafiya?" Jakadiya ta ce.


"Allah ya taimake ki wallahi yarinyar nan ce tana zuwa zata shiga sashen Fulani Maryama kawai ta zube ƙasa" Jakadiya ta ɗaga kai cen ta fara hange-hange sannan tayi ƙasa da murya ta ce. "Kinsan dai ba kowa yake da wadataccen Imani ba banda haka ya yarinya tana cikin wannan halin ace wai a fita da ita kamar wata kayan wanki" Fulani Zaliha ta ce. "Jakadiya ba wannan na tambayeki ba yanzu ina zaki kaita" Jakadiya ta taɓe baki saboda duk yadda zata kawowa Fualani Zaliha gulma ba ta bata goyon baya sannan ta ce. "A'a to Allah ya baki yawan rai ina kuwa zan kaita cen sashensu zan kaita" Kafin Fulani Zaliha tayi magana Saif ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login