Showing 21001 words to 24000 words out of 119289 words

Chapter 8 - Jikar Maguzawa Complete Hausa Novels Writing by Asma Baffa .txt

28 Nov 2024

7420

a gidan nan nata ne, iyayenku duk kusan Yan talla ne aka auro su shi yasa Suka zubar daku suka tafi kwadayin sure
Umma tace jaraba na rasa me Suka hango a auren nan ka zubar da yaranka Wai kaje kayi wani auren hauka sai mata,Hafeez tashi yayi tare da Jan hannun su Meenat Suka koma daki abinsu.


Bayan an kawo kudin aurena an saka biki sati biyu kacal,kudin da Asif ya tura min Mama na bawa su na dauki na gyaran jiki da gyaran Amarya Muka Yi dinkuna masu tsada har gidanmu aka yiwa plaster da paint sabo da biki aka Dan gyara shi ba laifi gidanka na talaka, tunda suka tafi Bamu sake magana ba sai Asif ne yake yiwa abokinsa soyayyar tunda shi Yana dan kirana a waya yaji ya shirye shiryen biki sannan Yana jaddada min Kar na fadawa kowa dalilin auren har tsiya ya min wai na ninke shi nace mu biyu ne ashe nice dai Fara din, yau ma Ina zaune tare da su Farisa suna ta kawo min magungunan Mata itama Mama haka take sani Ina Shan na Infection dole da sauran tsumi basu san ba auren soyayya bane,idan taga Ina waya sai tayi tunanin da shi nake waya Nima sai nace shine ai,haka kawayena ai Kuwa nayi kiba nayi kyau Ina wani shining ko Ina na wuce sai kamshi sabo da gyara da ake min,Haka Kakanni na suma sun kawo nasu na gyaran jiki haka nake Sha ya na iya,Farisa na kalla nace Kun gama raba Iv? Shima Iv Asif ne ya Aiko aka kawo min nawa dana Daddy,Baba ma an kaiwa matansa nasa duk da cewa baya gari,haka Dangin Mama kaf an kai musu,nima mun rabawa friends har mazan ajinmu duk an basu kowa bikin ya Zo Masa a titse.


Kadada ce ta bugo min waya tace ya akayi fatan kin hada tsumin da Danbashanana Dariya nayi nace mene haka Danbashanana? Karki raina min hankali gashi Nan a cikin kayan da na kawo Miki ai na nuna miki sabo da haka ki Sha abinki ki baje kiyi ma ango shanana ai ma'anar sunansa kenan Dariya na dinga Yi nace ke Kika sani na kashe wayata
Duk wani shiri anyi shi bangaren ango da Amarya,Jawad sai mamaki yake Wai shi zaiyi auren wuri haka, ana Saura kwana Uku Asif ya kirani a waya kakar Jawad da Matar Yayan Baban Jawad zasu kawo lefe,Mama na fadawa ta sanarwa makwafta Mata biyu da suke mutunci sai matan Baba Suma Suka zo
4pm Suka bi flight suna sauka aka kawowa Asif wata mota Fara me shegen tsada ya karbi key driver ya koma company na Jawad dake kano,Asif kuwa driving yayi har kofar gidanmu suna zuwa Umma ta tabe baki tana yatsina fuska tace amma Jawad yayi asara ya rasa inda zai nemi aure sai wannan gidan jiba unguwararsu geto area ga talauci akan wannan aka taso mu tun daga Lagos har nan,wallahi da nasan Nan zamu zo baza a taba hada Mata lefe haka ba harda wani order komai a kasar waje Kayan lefe irin na first class lady amma sai naga wannan gida akwatuna har goma Sha shida,Kakar Jawad ta wajen uwa da tazo daga kasarsu tana kallon Umma tana Jin hausa sosai amma tana ji bata yi magana ba Asif ya dinga fito da akwatuna masu tsada matasa dake a majalisa a kusa da gidan sai kallo sukeyi suna cewa Allah ya hore Mana muma,Yara aka sa Suka dinga shigarwa ciki kaf Asif ya basu dari biyu biyu kyauta suna ta murna.


Umma tana gadara Suka shiga sai yatsina takeyi tana toshe hanci,Kaka Aisha itace tayi sallama aka amsa Mata kawayena su Uku sai guda sukeyi da makwaftanmu an kawo abin arziki ko ta Kan Umma basu bi ba kyawun Kaya ya tafi da imaninsu, ni Kuwa Ina daki na leko ta window Ina kallo ana bude Kaya bayan an sauki baki da lemuka da ruwa kala kala ga abinci iri iri an gaisa amma Umma sai tsaki take ja,Kamar akan Kaya take tace da Aisha taso mu tafi please Mama tace da wuri haka ko abinci baku ci ba,Aisha tace kyaleta kije mota ke Ni sai naci abincin bayin Allah arziki ya kawo mu ba tsiya ba hausarta bata fita sosai amma sunji me tace,Wata ciki tace inda ake arziki ai ba a tsiya me arziki bai gaji wulakanci ba,Umma tuni tayi waje tana bakin ciki,Asif ne yasa aka Kira Masa Amarya,hijab na saka na fito a jikin motar Muka tsaya muna hira har Kaka Aisha ta fito tana walwali da gani kasan daga kasar waje take gata balarabiya ta Sha sutura me tsada Umma ma kyakyawa ce ta cakare matuka sai kamshi suke kana kallonsu dole sai ka Raina kanka,Tsokana ta tayi da Wasa tace itace zata kwace min miji,Nayi Murmushi Kawai na musu sallama Umma harara ta balla min tana daga cikin mota sabo da ko a cikin gida bata amsa gaisuwa ta ba, Ni dai na juya na koma gida abina.
Kowa sai santin kayan yake ana ta zuwa gani.


Muna shiri har Muka karasa Exam dinmu lafiya
Duk wani shiri na Gama shi kayana ma na hada su kaf na sawa Wanda Zan tafi da su Wanda bazan tafi da su ba duk na bayar da su baifi ma kala Uku na dauka a kayana ba duk na bayar da su ganin irin kayan da aka hado min na lefe,ana gobe daurin aure dukkan Dangin Mama Maguzawa Suka zo,bangaren Daddy ma sunzo,bangaren Babana Kuwa a gidansa Suka Yi masauki sabo da gidanmu yayi kadan babu waje hakan ma Sai makwafta wasu zasu kwana tunda 2 bedroom ne kawai sai palo ga toilet ga kitchen gidan ba girma,Ni kuwa da kawayena Muna gidan Wata makwafciyarmu Amarya ce gidanta kato ne sosai Kuma me kyau kasancewar mijinta Yana da rufin asirinsa sannan baya gari yayi tafiya shi yasa muke walawa a gidan duk munje mun Sha lalle da gyaran gashi nawa na musamman ne ni Amarya.


Mu wajen takwas ne a gidan,Farisa,Hamziyya,Murja,Zuhriyya,Safiyya,sai Yan Uwana Yan Mata Ta noma,Kadada sai Tahantsi,duk ciki Tanoma ce kadai me aure sabo da itace naje bikinta kauyen,Muna Palo ana ta hira Tanoma ta kalleni tace Fara kin Shiga Uku ranar farko,Kadada tana ji ta duro ashariyar data firgita kowa sai da ta bamu dariya ma tace Amaryar me Naira Jawad ,Tahantsi ma ta duro ashar tace to me bada taimako yau kina gidansa dan bura.....karki manta damu, Tanoma tace har na matsu gari ya waye wlh mu sake ganin angon nan a tafi damu Lagos a jirgi wayyo Ubangin dodon tsafi ya taimake mu mu Kuwa,nayi Dariya nace wlh duk Yar iskar da tayi Mana sabo a Nan zata gane kurenta Saura angwaye suzo ku kunyata Ni da ashariya,su Farisa su dai Dariya suke yanda maguzawan ke abu.


Kadada ce ta mike tare da wanko fuskarta ta dawo ai sai Tahantsi tace sai na fadawa Nomau kin Fara kokarin shiga addinin su Fara kin wanke Fuska dama jiya ma da safe Naga kin wanke fuskarki so kike ki koyi Sallah,da sabulu fa na wanke ba haka Kawai ba dan gyaran Fuska ne,Ni dai na fada Miki ki daina,Dan Allah karki fada Masa zai iya korata a gidan,Ni dai Muna jinsu har mukayi bacci
Washe gari da wuri muka tashi tare da gabatar da Sallah Muka koma bacci, Ina ta bacci kamar ba nice Amaryar ba sai Kadada ce ta zunguri kafata da kafarta dalla tashi banza har da wani yin mika, ko kulata banyi ba sai Farisa ce tace Kai Kai 11am angwaye sunzo,zumbur na mike nace Yana Ina?Dariya Suka saki min na ja tsaki ganin 8am tashi nayi na iske an kawo Mana tuwon shinkafa da miyar taushe daga gidanmu da ruwa ga waina,ga kunu da kosai me zafi,su tuni sunyi brush ma suna cin abinsu,Nima brush nayi nazo na narki kunu da kosai na sannan na Dora da tuwo da Waina sai da naji nayi dam sannan na kwaso kayan shayina na ajiye gefe sai an daura aure Zan kora,sauran tsumin na Sha abina


Wanka muka Yi tare da zuba kayanmu a jaka muka wuce wurin make-up,a can Muka shirya aka fara Yi musu kaf duk Ni na biya kudin aka musu Yar sama sama da dauri,Nima na shirya aka fara tsara min ta Amarya,11am aka gama sannan aka Yi Mana pics zafafa tare da tura Mana a waya sannan nace su Fara tafiya zamu taho da Farisa Suka shiga Napep biyu suka taho gida


Bangaren Angwaye da kyar Asif ya yaki Jawad ya yarda zai zo daurin aurensa,Haka Hafeez,Waleed,Ahmad kannen Jawad sune manyan Yan samari duk a secondary school suke Hafeez shine yayi Candy duk sun shirya cikin Shadda ta gaske Silver sun dora hula dai dai su cif gasu kyawawa Yan Fulani,Asmau da Nawwara,sun sha wani material me tsada Golden color sun zuba kyau da su za a tafi sune manya a cikin Mata,sauran yaran da za a bari a gida Kuwa duk sun Sha wanka,mutane Dangin Jawad na Uwa sunzo da yawa maza su biyar samari da dattijai da su za a tafi larabawa matan Kuwa su biyar suna bangaren da Kakar Jawad take a gidan Abba Nan ta dawo sabo da bikin a hadu a karbi baki,Uwar gayya Umma danginta sun cika gida sai Iyayi suke kamar gidan ubansu,Dangin uban Jawad gasu Nan Dana Kauye Dana birni duk suna gidan Abba ana ta shagali,Umma da danginta Dj Kawai Suka kafa suna ta cashewa sabo da za a kwashe Mata Yara daga gidanta tana murna


Asif da matarsa zai tafi tana wajen Amarya Zahiyya ta sha lace Sky shima Shadda dinsa sky dukkansu sabo dal sai walwali sukeyi,Abba ma da Dattijai danginsa duk sun shirya sai labari yake Basu yanda yake kula da marayu kannen Jawad,Yace yo mene Amfanina a duniya Dan danuwanka idan baka rike shi ba to Ina zai je ai dole naka sai naka,matata ma da zata kawo min shirme ita baza ta rike Dan wani ba na zare Mata Ido sai da na Mata ba Dadi sannan ta hakura,wasu mazan suna bani mamaki sai su bari matansu suyi ta juya su ni na isa da gidana,matata ko haushin Kare nace shi nake bukata ta kwana tana Yi min dole sai ta yi,wani dattijo yace ka kyauta,Haba Baffa Mudi ai idan ihu nace tayi sai ta kwana tana zunduma shi sai idan nine nace ta bari,yanda nace haka akeyi,kafin nace ma anyi shi yasa yaran Nan lafiya suke zaune,kasan tarbiyar yaro sai an dage,Dangi suna ta Jin Dadi suna yabonsa tsofaffi harda sa Masa Albarka karka sake naka ya lalace,Abba yace Umman yaran nan abinda ma bata yiwa yaranta haka take ma yaran Dan Uwana sabo da na tsaya musu na tare musu komai,shi yasa ma na dage lallai sai Jawad yayi aure shima sabo da ya Zama cikaken mutum rayuwarsa ta inganta,amma saurayi da kudi ba aure ai barna za a yi zaka ci ka Sha karshe me zaka nema mace,to fa idan baka samu ba sai a runtuma bariki,Abba harda nunawa da hannaye Yana uban bayani suna gaskiya ne haka ne ana yabonsa,duk abinda yake fada Umma tana labe tana jinsa,tace wato har haushin Kare ma idan yace Yi zanyi zai gane kurensa bari a gama biki,Fitowa tayi inda suke tsaye gaba daya Abba Yana ganinta yayi kus sai ya koma cewa ai ita Yar Albarka ce ba abinda bata min ga biyayya Ni Kam nayi dacen mace,idon mutane ta faka ta zabgawa Abba harara ta wuce,gaba Daya sai ya rikice drivers din Jawad ne Suka Zo da motoci Su Hafeez su Uku da Mata biyu Suka shiga mota daya, Su Abbu ma Haka,Ango daga motarsa ya fito wow ya Sha farar shadda ta musamman babbar riga ya diga kyau kamar a sace shi,cikin gidan ya shiga Yana zuba kamshi,dangi sai tsokanarsa akeyi Yana shiga Palo sai ga su Meenat duk sun Sha wanka har Wanda ake bawa Madara an hadesu da kananan Kaya duk Umma ce ta shiryasu sabo da Dangin Abbu su yabe ta,da kanta ta bawa Wanda aka tsige su daga Shan Nono madararsu,


Su Meenat zasu Yi tsalle su daneshi ya matsa gefe Kar su bata Masa kaya, ya Mika musu Hannu Suka dinga tafawa yaga Wanda ake bawa Madara sunyi bul bul da su me aikin Daya bawa Amana tana aikinta bintu,fita yayi da sauri dukkan motocin sun tafi sai ta Asif da su Hafeez,Yana zuwa ya leka motar su Hafeez ta window,Suka sauke glass da sauri kallo ya Kare musu yace Inye wannan wanka haka Hafeez ko na bar maka Amaryar ne a daura da Kai,Dariya sukayi yace Yaya da Allah ya biyaka da Aljanna kuwa ka gina min gida ko Ina a sa roopping sabo da Kar wani ya ganmu sannan mu kulle kofa Ni da ita ai shike nan Ni Kuma sai na shekara Zan fito,Mamaki ya Kama Jawad Wai Dan secondary ke fadar haka Wanda yanzu yayi candy ma,Dariya Jawad yayi yace Allah ya shiryeka Hafeez dariya Suka yi ya Mika musu hannu duk suka gaisa,Nawwara tana tsakiyarsu Asmau tana gaba Jawad yace Kai Hafeez koma gaba Asmau ta dawo gefen Nawwara taya zaku sa min kanwa a tsakiya,Nawwara ta dawo gefe Asmau ta shigo itama yace Yan Mata kunyi kyau ya kalli Nawwara da Asmau duk sun Fara irgan dangi motar ya bude ya gyara musu mayafinsu da Kansa yace a dinga rufe jiki Kun Fara girma,kunya Suka ji,Asmau ta radawa Nawwara tace Kinga Yaya ya gano mu shima mu dinga rufe jiki,Nawwara tace na matsu na Fara sa bra Yan Iska su basu girma ba su basu bace ba an rasa ya za ayi da su,Dariya sukayi,Jawad tuni ya shiga motarsa driver yaja sun wuce Airport.












Masu Sharhi godiya dubu
Aci gaba please












AsmaBaffa
08033933642🌏JIKAR MAGUZAWA🌏


21-25




Official


By
AsmaBaffa




SADAUKARWA NE GA
ZAINAB GARBA BUTALAWA




MASU SIYEN WANNAN NOVEL NA CIRE ACCNT NUMBER NA FARKO DANA SAKA SABO DA WATA MATSALA


MASU TRANSFER TA BANK


ACCNT NO
0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD
GTBANK


MASU TURA KATI MTN
08033933642


'YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39




Duk wacce batayi anfani da sabulunnan ba anbarta abaya acan karshen bayama kuwa duk Mai tantama akan sabulai nagyaranjiki cewa basa Aiki toh yacire mg's domin kankat ne insha Allah babu Wanda yayi anfani dasabulunmu yace baiyi ba koyaushe mg's sai sanbarka amare da uwargidaye hardama yanmata kuhanzarta kusamu naku ba karya domin bama cika Baki kugwada kubada labari da bakunanku sabulu daya tamkar dubu wadandama basasan using cream sabulun mg's herbal whitening black soap yawadacemuku jikinku zaiyi kyau koyaushe kukasance clean cikin kamshi Kuna glowing koda bakusa turare ba🤗


Kayanmu bana bleaching bn organic ne sunagyarajiki fiye da tsammaninku zaifiddomuku da ainihin natural beauty dinkine Wanda yagwada shi zaitabbar amare kuyi kokari kumallaki mg's domin baruwanku da zuwa adirjemuku jiki zakuga yanda fatarku zata dinga walwali
Ina masu pimples
Tabo(spot)
Sunburn dama dukwani matsalar fata kuyi kokari kunemi soap dinnan before 2weeks zaisharemuku hawaye kuzama abun kwatance
Sister's masu nankarwa kuma kunemi soap dinnan Yana rage nankarwa sosai🧖🏻‍♀️duk me shakku tayi kokari tagwada mg's insha Allah bazakiso rabuwa dashi ba


Akwai maisa haske Amma kayanmu nafada bana bleaching bn zaifiddomiki d ainihin halittarkine yagoge dukkan dattin jiki


Akwai Kuma Wanda zaimiki maintaining skin dinki yasaki fresh fatanki tazama kalar hutu


Pls bamacika Baki you HV to try it and see for yourself
100%tested nd trusted


Soap price:3k
Location:kaduna buh munaturawa ko Ina Amma delivery is not free


Maiso kindly message 08062991549
07046881166
Call 08064532391


Note:Babu inda zakusami mg's herbal whitening black soap sai a number dinnan bairiga yakai market b inyakai we will let you know buh as for now wnn numbern ne kawai🙏


Maiso yahanzarta before yaji sold out akwaisu available now insunkare you HV to wait akawo so maiso yahanzarta🙏adade anayi sai gsky🤭🤝


Mg's skincare






PAGE NAKU NE
NAFEE


MASU YOUTUBE CHANNEL KU DAINA MAIDA MIN NOVEL AUDIO BA TARE DA SANI NA BA DAN ALLAH.








Page naku ne


~-
Kherdee dodo
Fancy Honey
Maman Samha
Rouqayya Bello
Binta Nadada
Aunty Nice
Sadiya
Sadiya Muhammad Bala
Jiddatulkhair
Khadijamuhammadsani41
Maman Afrah
Aisha Lawan
Maman Baby
Bilkisuu
Mbello
Naima Saleh Sheka








A airport can Suka iske friends da yawa duk Ango ya dau nayi,wasu Kuma duk sun tafi da kansu,Asmau da Nawwara sun saka Jawad a tsakiya su Hafeez suna bayansu haka Suka shiga jirgi suna sauka a Kano motoci na Alfarma sun zo Suka wuce masallacin dake kusa da gidan mu,wasu Kuwa gidan da Amare suke Kato ne an shirya kujeru farare an kawo duk kalolin abincin da Suka Yi Order da masu serving, Jawad ya biya su suna nan suna jiran angwaye duk sun sa uniform dinsu na resturant din da suke aiki an shirya komai har da wani zuwa da katuwar speakers sun wani kunna kida suna ta rawa kafin su Fara bada abinci Mata da maza


Ni Kuwa sai da aka Gama shiryani cikin Wata Gown sea blue,Gogoron da aka nada min silver da takalmi da jakata duka silver masu tsada a lefe na dauki takalmi da jakar gown din Kuwa material na siya na dubu talatin me shegen kyau aka dinka min ta Amare na zuba kyau ba karya ana gama make up na shafa turaruka na musamman sannan na Kira Asif yace Yana Hanya ya kusa karasowa inda muke,sauran Kuwa duk sun tafi a Napep,Ni da Farisa da Hamziyya Kawai za a dauka,Yana zuwa Muka fito yaga irin kyan dana zuba da kyar ya ganeni ya dinga kallona har sai dai danaji kunya Farisa ce ta shiga gaba mu Muna baya aka tafi Muna ta hira da Asif sama sama yace ku fa ake jira an daura,nace haba an daura? Yace kwarai kuwa nace haba shi yasa dazu naji wani yarrrrr tsigar jikina tana tashi Ina Jin wani amai amai Yana taso min ashe anyi abin,Dariya Suka dinga yi har su hamziyya, Farisa tace ke da Kika ce zakiyi kuka ai sai ki fara,Nace haba ai sai da dare idan za a kaini,Asif yace to

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login