Showing 111001 words to 114000 words out of 119289 words

Chapter 38 - Jikar Maguzawa Complete Hausa Novels Writing by Asma Baffa .txt

28 Nov 2024

7445

da ita ba,gidan ma ya Zama Kamar gidansu tunda makwafta ne.


Bayan Bilal ya gama Secondary school dinsa ya tafi birni ya gama NCE Kuma Allah ya taimakeshi ya samu aiki da wuri lokacin babu Matsalar samun aiki,yace da Iyayensa shi a birni zai zauna ayi Masa aure,tunda suna da arziki sai Babansa ya siya Masa dan karamin gida a kano,har Allah yasa dai da kyar aka Yi bikinsa da Hakuri Ummiya,aka Kai Ummiya birni,Suka Fara zaman aure sannan ana dadin amarci ya saka Ummiya a Makaranta ta Fara NCE itama shi Kuma ya koma degree ba a fi wata biyar ba Bilal ya fara dukan Ummiya ashe Yana da wani irin zafin hali da saurin duka ga masifa da rashin adalci,Babu dama Ummiya tayi magana sai ya Kare Mata cin mutunci sannan ga duka kusan kullum sai ya jibgeta,ita Kuma tana da hakuri amma dai jinin Maguzawa tun tana Hakuri bata ramawa har ta Fara maida martani haka zai nada Mata duka Watarana ma Sai taje asibiti,inda yake abin kirki Kuma gidansa ba yunwa akwai ci da sha da sutura masu kyau,fannin kudi bata da matsala Yana bata har ta taimaki wani ma shi dai da cin mutunci da duka zagi kala kala.


A haka har Ummiya ta samu ciki lokacin watanta takwas da aure ba wani girma ne da ita ba amma Baba ba ruwansa da cikinta haka zai Kama Ummiya ya nada Mata dukan tsiya,ko shekara batayi ba yace zai Kara aure,ka duba mace ace ko shekara baka Yi da aure ba amma za a maka kishiya,Iyayen Ummiya tun suna kawaici Suka Fara gazawa sabo da har Dangin Baba basu kyale Ummiya ta zauna lafiya ba Suma har gida suke zuwa su Kare Mata tanadi ta mallake musu dan uwa tayi Masa tsafi shegu Maguzawa arna abubuwa kala kala.
Haka aka sake daurawa Baba Aure da wata Bushra,tunda tazo gidan ba mutunci ta shigo sabo da dama wasu matan kafin aure sai sunji ya uwar gida take zaune a gidanta,tana zuwa abin ya sake hadewa Ummiya Kishiya tayi mata cin mutunci shima mijin idan yazo ya dora da nasa harda duka,duk hasken Ummiya da kiba sai da ta dawo Kamar tsinke tayi Baki sabo da bacin rai,a Haka Ummiya ta Haifi yarta mace ranar suna naci suna Najla,tsabar cin mutunci ko arba'in bata Yi ba Baba ya saketa saki daya, Kuma a haka suna kaunar juna,ba a dade ba ya auri wata matar Intisar sai soyayya ta tashi daga Kan Bushra ta koma Kan Intisar nan ma ya dinga jibgar Bushra ga cin mutunci yanda yayiwa Ummiya,Intisar tana fara sanewa ya haukace ya koma bikon Ummiya Lokacin Ummiya kyawunta ya dawo tayi kiba bulbul abinta,kullum Baba Yana hanyar kauyen har dai Ummiya ta koma,bayan ta koma ko wata bata Yi ba ta koma gidan jiya haka babu wani kauna tsakaninsa da Dan da ya Haifa haka itama matarsa Bushra bata Haihu ba har aka yayeni Ummiya ta samu wani cikin haka dai ko yaushe duka da wulakanci ga kishi na kishiyoyi kala daban daban,a dinga lalatawa kishiya Kaya,wani kayan ma na sawa idan Ummiya ta shanya su sace su zubar sai dai a neme su a rasa,haka kayan kitchen dinta suke fasawa da mugunta,Dangin Baba Kuwa basa kaunar Ummiya sunce itace ta hana matan Baba haihuwa ita Kuwa gata Nan tana ta haihuwa a haka Ummiya ta Haifi Bassam kanina,Sannan Baba ya sake Karo mace ta hudu Intisar, tana zuwa bata dade ba ta samu ciki,Ni Kuwa tun bani da wayo nake kallon yanda Baba yake dukan Ummiya ya dura Mata zagi kala kala yaci mutuncinta,Suma sauran kishiyoyin haka yake dukansu Yana wulakantasu har ya saki Bushra ya auri wata,Ni kaina tsakaninmu sai harara shi Kuma baka Isa kace bai son Yara ba tunda komai Yana Mana sai dai ba sakin Fuska,Bayan shekara biyu Ummiya ta haifi danta namiji yaro na uku kenan, bayan ta yaye shi Baba ya sake sakinta Karo na biyu, ya auri wata Salamatu,Lokacin Intisar tana da Yara biyu itama,Salamatu tunda taji baza ta iya Zama ba tace sai ya saketa da kyar ta samu Suka rabu,Suna rabuwa ya koma zai dawo da Ummiya ga Ummiya tana mugun sonsa shima Yana sonta,Iyayenta Suka ce baza ta koma ba,danginsa a hankali Suka fahimci Baba shine da matsala lokacin da Mahaifiyarsa ta riga ta rasu dama ita ke rura wutar,Ummiya gaba daya gashi idan ta tafi gida yaji ko ya saketa to fa mu a gidan take barinmu,Sam Sam Baba baya shiga harkar mu,ga kishiyoyi suna mana mugunta iri iri har dai Baba baya daukan wani mataki akai,idan ya kaimu kauyensu Watarana haka nake zuwa nayi ta yiwa Ummiya kuka akan ta dawo tausayinmu yasa ta yarda ta dawo har ta Haifi kaninmu Namiji na hudu kenan,lokacin da na shiga Jss3 lokacin Baba yayi sabuwar Amarya ya saki Ummiya,igiyoyi sun Kare dole ta dauke Ni ta bar Masa mazan Muka koma gidan Maguzawa,Bayan tayi Idda shine ta hadu da Daddy Yusuf ya aureta shi ya taba Aure matarsa ta rasu bai taba haihuwa ba,sabo da bashi da kudi yace baiyi Alkawari zai dauki nauyi na ba Ummiya tace ba matsala


Bayan biki kuma ta Fara sana'ar dinki da fura har Kuma ta samu teaching a private school tana Yi Muna zaune har nayi candy lokacin muka hadu da Kai,shi Kuma Baba haka Kawai Allah ya shirye shi ya daina dukan Mata da cin mutuncin Mata,shine yake tare da Intisar da Bushra suna zaune duk da Mata ba a rasa su da kishi amma ta fannin Baba da sauki ya daina duk wannan,sannan a hankali Allah ya azurtashi Yana aikin gomanti Yana Siyasa ga kasuwanci har ya Zama shahararren me kudi,ya hakura Yana zaune da iyalinsa lafiya amma tun asali Allah ya jarabci Ummiya da Baba da son junansu.
Jawad yana gama ji yace Wai Allah ya kyauta Amma tunda Allah yasa ya canja sai ki bar Ummiya tayi aurenta ta koma Inshaallah ba abinda zai faru sai hakuri kowa da kaddararsa,nace dama nasan ma baza taji maganata ba.


Bayan wata biyu Ummiya bata koma gidan Baba ba dukkanmu Ni da Kadada Muka tafi bikin Tahantsi gidan Ummiya,dangi sunzo amma Yan gidan Maguzawa basu fi mutum uku ba, Amarya an Sha gyara an tsula kyau ta wani nutsu,duk iya shegen Tahantsi Babu sai yanda aka ce da ita,idan ance ayi kaza tace to,yanzu ma muna shirya Mata kayan Dinner da za a saka nace wannan takalmin Zaki sa,tace to yanda kuka ce,Kadada Kuwa ciki ya isheta ya hanata sukuni ko yaushe tana kwance,Abu kadan sai ta fara masifa sai Ummiya ta sata a gaba ta Mata Nasiha,yanzu ma daga nace gobe da wuri zamu tafi makeup sai hawaye tace ni yanzu shike nan bazan Yi kyau ba Farooq ya jawo min Masifa ya mirgina min ciki a gaban Ummiya da su Farisa ta fada kunya ta kama mu,Kadada tace Allah ni yanzu nayi hankali na dawo daga rakiyar Yan maza,Dariya ta kamani na dan gimtse ta, Tahantsi aure ya jawo an nutsu tace dan Allah karki dame mu Sanda Kika samu cikin ba Iyayi Kika dinga Mana ba,yanzu wato ya fara girma kinji wahala,Kadada bata ce komai ba ta rabu damu Muna ta shirinmu,washe gari dinner da Yamma Muka je make up har Kadada mun zuba kyau Farisa ma da Fauziyya an kusa bikinsu da kawayen Tahantsi Yan school da nawa Wanda na bari a kano mun hallara sai Yan matan gidan Maguzawa su Uku da Suka Zo suma sai Kawayen Ummiya da makwafta da abokan arzuka,Barin angwaye,danginsa da abokan ango duk anje abu ya hadu ya kayatar Amarya da ango an zuba kyau karshe munci mun Sha an cashe anyi barin kudi.
Washe gari daurin aure Jawad,Asif da Farooq Suka zo,dama Yara suna wajen Safna,duk munsha wankan shadda ni da Kadada anko Muka Yi, Tahantsi lace ta zuba,masallacin unguwar an cika an batse angwaye Baba shine waliyin Tahantsi ya daura ma Khadija aure da Angonta Aliyu,ana gamawa aka daura Auren Ummiya da Baba an maida aure.


Ina Jin haka Raina ya baci na dinga Jin haushi Ina kunkuni,Ummiya ko a jikinta harda tara kawayenta,Kallona Binta sugar tayi tace kalli Ummiya tana ta bashare baki sabo da murna,Baki na Kara turowa gaba nace mutum Yana zamansa lafiya ya komawa tagaigayar rayuwa,angwaye ne Suka shigo aka Sha hotuna suna fita Jawad da Farooq Suka shigo suka gaisa da su Ummiya,Farooq ne ya iya tambaya Ina Fatima Jawad dai kunya bai sa ya tambayeni ba Kuma har yau ba Wanda Muka fadawa Ina da ciki in Banda Kadada da Tahantsi,Ummiya nasan ta gane Kawai kallo na takeyi nima bance Mata komai ba Shuru nayi,Binta sugar ana Jin Oga ya iso aka gyara Fuska ta fito palon da ba kowa inda su Jawad suke Ummiya tasa an Kai musu abinci da lemuka da ruwa Asif shi tunda aka gaisa yana waje,Kadada tayi sallama ta shiga Jawad Yana ta latsa waya shi dai bai dago ba yaji Kadada tana ta karantawa Farooq Matsalar cikinta suna ta kus kus,Yana ji tace kabirin nan ya dameni Muna komawa muje asibiti a gani ko ya Isa haihuwa,Farooq yace 7mnths din za a haihu,ka sani ko bakwaini Zan Haifa yaron nan da alama yayi kwari wutsil wutsil dinsa yayi yawa so yake yazo duniya,ni Inshaallahu bakwaini Zan haifa ba sai ya Kai wata taran ba,ai ance bakwaini ma sunfi lafiya tunda suna rayuwa mene ne a ciki,Jawad baiyi niyar magana ba sai da yayi yace Bintalo har yau kin kasa fahimtar Allah yanzu Farooq ne zai sa ki Haihu ko Allah,kiyi hakuri haka kowacce tayi Hakuri ta haihu,Kadada tace to ni na gani gaskiya ka fadawa abokinka,Kuma ni Allah ya gani gida Zan je na samu Naga iyayena ko zasu yafe min Kar na mutu wajen haihuwa sai yanzu nake ganin kokarin Uwata ashe haka tayi fama dani Ni dai ba ruwana gaskiya bazan biyewa da Namiji ba ka aureni uwata tana can bama gaisawa,Jawad yayi dariya yace duk wahala ce tasa kike fadan haka Fati,Farooq yace Malam ya isheka haka kace Bintalo kace Wani Fati kana ta lalata mana suna,Kadada tace sunana dai ai ni yanzu na dawo daga rakiyarka babu wani dadin baki da zaka min wani Baby mun Zama daya,my love waye waye gashi nan kana ta Jin dadin rayuwarka ni Kuwa yanzu dandanon Madara ya daina min dadi,insha shayi da Madara ya gagareni,inci taliya baza ta yuwu ba sai amai ta dinga zarowa tana Fitowa Kamar hanji, Farooq Suka Yi dariya kamar me yace na shiga Uku Kuma da mita yanzu sai kowa yaji Farooq dai Farooq dai haba Sweetie ya dafa Kadada ta cire hannunsa tace bari na Kira Najla,Jawad yace Aunty Najla? dariya Kadada tayi tace au Auntynka ce ma? Jawad yace ae mana,Aunty,kanwata,kawata,matata sannan uwar 'yayana,Kadada a ranta tace ana kwashe Mata zuma ai dole kace kawarka, Farooq tashi yayi suka fito da Kadada suna hira ta ganni na rako wasu tace kije nace to ai ya kirani a waya,palon na Shiga da Sallama ya dago Yana kallona Yana Murmushi naje Zan zauna a gefensa ya fisgo ni saman cinyarsa na zauna ya rungumeni yace nayi missing naki,nace Yan biki fa ana sintiri Kar su ganmu,yace to ku dama Yan Kano matar mutum ma bazai rike ko Hannu ba sai ace dan Iska ne,Komawa nayi gefe na zauna nace duk dangi ne ai sai ace bamu da kunya yace uhm naji ni yaushe Zaki dawo Kawai? Jibi Mana yace gobe fa za a Kai Amarya me Zaki Yi,Ummiya Zan raka dakin mijinta,kin rainani gobe lallai ki taho Ni bana son wannan kwanakin a unguwa ki tabbatar gobe na ganki a gida,nace to ai naji Zan taho,sai me kike bukata? Nace ba komai Ni farar kasa ta isheni rayuwa,ki dinga ci kadan ke bakya ji,Kuma karki sake naji kinci gawayi,Murmushi nayi nace ai ban ci ba,yace Good girl tare da shafa kumatuna ya mike yace zamu wuce sai goben akwai amarci,nace Kai dai hmmm baka gajiya na raka shi Suka tafi.


Gwamma duk ta rakwarkwabe tsufa ya kamata duk da taji sauki ta rage fadar na siya ba sosai ba,yau wanka Gwamma ta shiga ta fito sai ta Kira Naroro da wata Matar Yabanya tace kunga yau wanne irin sabulu ne na hadu da shi na goga na dirza na gurza yaki kumfa,Yabanya tace mu gani Ina sabulun? Gwamma ta nuna musu a hannunta sai Suka ga kudi ne Yan Naira biyar biyar Guda biyu a linke da kauri,suka ce ai kudi ne ba sabulu ba,Gwamma ta wafce tace ku bani Yan kut....ta zunduma musu ashar sabo da yanzu haushin kowa take Kara ji taji yaran gida matasa suna ta Musulunta ana ta samun karuwa duk ta zare sabo da takaici.


Umma an gama Idda tuni sai sintiri takeyi akan megari ya Mata hanya Kamar yanda yayi Alkawari,Megari ya sa musu rana yace ta shirya su tafi Lagos,Umma bata da ko sisi kudin tafiya gashi bata da hanyar samu ga me gari yace bazai biya Mata ba tunda bata kaunarsa Kiri Kiri Taki zama da shi,Ummiya tana da dubu biyu sai ta Fara soya chin chin na siyarwa tana kaiwa makarantar Yara duk garin nan dariya ake Mata ana gulmarta dama Kauye kowa yasan kowa, ai Kuwa ganin haka Megari ya kirata har gida
Umma tana zuwa ya kalleta yace gaskiya kina son mijinki ya zaro wayarsa ya danna number Abba ya Kira bugu daya Abba ya daga Suka gaisa yace yaya Maganar mu da mukayi da Kai lokaci fa yayi,Abba yace Ina sane munyi magana da matata Amarya tace ta yarda ba matsala kasan mutuniyar kirki ce itace da kanta ma take rokona akan na dawo da tsohuwar matata to kasan ni gaskiya Muna zaune lafiya bana son tashin hankali yanzu sai dai na raba musu gida ita Barira idan ta dawo sai na kaita daya karamin gidana dana siya ta zauna da yaranta kaga babu tashin hankali a ciki Amma Ina sonta dama laifinta ne,Megari yace Ina zuwa Zan kiraka sai Ya kashe wayar ya kalli Umma yace to yanzu Zan hada ku Saura ki ba da Mata ki zubar da ajikinki,ki ja ajinki yawwa Naga sai zare Ido kike Yi Kar Ina baki waya ki saki layi sabo da kina son kome ke in banda kin rako Mata taya Zaki shirya ki bini har Lagos wajen da Namiji sabo da kina son ya maida ke idan ya wulakantaki fa,ai na gama Yi Miki komai tunda Kika Yi Idda munyi komai da shi Kuma Yana sonki har yanzu,Umma ta zabura tace Allah? Megari yace ai Kinga irinta ki dinga nutsuwa karki jawa kanki ciwo akan son Miji,to yanzu na yarda kinyi hankali dama ya turo dubu Hamsim yace a baki tun rannan ni na hanaki sabo da na tabbatar kin nutsu sai gashi oh harda yin Chin Chin za a tara kudin tafiya Lagos,Umma tace na gode ashe haduwata da Kai Alkhairi ce,Megari yace hummm....sai yanzu Kika sani da kin daukeni wani gajaja ko?na wuce gaja a wajenki sai dai gajaja, ki fara shirinku na Mata sati me zuwa za a daura aure zanje muyi magana da iyayenki Kuma sabo da Allah na Miki badan komai ba,jeki Sahura tana gaishe ki na fasa hadaki da shi sai an maida aure,Maigari ya zaro dubu Hamsim ya bawa Umma ta tafi tana ta Murna da farin ciki,taje gida kasa hakura tayi sai data basu labarin,su kansu Iyayen nata sunji dadi sosai.


Washe gari da Yamma aka tafi Kai Amarya 5pm Muna gidan Amarya a gidanta hadadde,Yan Kai Amarya danki a ranar Suka dawo tunda flight ne,daga ni sai kadada aka bari a gidan Muka Kara gyara ko Ina sannan Jawad yazo daukanmu, Tahantsi harda kuka nace to zamu tafi yau sai aji kalar Anaconda,Tahantsi tana hawaye tace yanzu da shi zamu kwanta? Kadada tace a'a da mu Zaki kwanta Yar rainin hankali, Tahantsi tace bazan yi bacci ba? Nace Kinga muje Binta sugar Bata da aikin yi ne idan Aliyu ya shigo ya baki amsa Muka fita, Tahantsi ta rushe da sabon kuka tana ku dawo,Sako Zan baku amma Ina munyi gaba abinmu,Jawad gida ya sauke Kadada da kayanta Muka wuce gida sai sauri yake sabo da Wai yayi Missing.


Tahantsi dai tana ganin ango ya shigo ta sake fashewa da kuka,ya zauna a gefen bed Yana bulbula kamshi anci shadda Yana sheki,yace haba Baby yau ai ranar farin ciki ce...kafin ya rufe baki tace ba wannan zance ni dama ban Isa aure ba,Murmushi yayi ya dinga lallashinta da kyar taci kazar ma sannan tayi wanka da Alwala shima haka Yana Fitowa ya iske Tahantsi ta zuba tagumi a ranta tana ko da wanne idon Zan kalli Anaconda oho har ya shirya tana sanye da hijab tabi bayansa Suka Yi Sallar nafeela ya musu Adduoi sannan taki tashi yayi yayi ta tashi taki, yace ko Aljanu ne dake ne ki tashi mu kwanta Mana, tayi shuru,yace idan sune yanzu Zan Miki Rukayya ai ya dauketa ya daurata saman bed, Tahantsi ta tsure har da salati Kamar wacce za a saka a kabari




























AsmaBaffa🌏JIKAR MAGUZAWA🌏


121-125



NA KUDI NE
MALLAKIN JIKAR MAGUZAWA PAID GROUP






Official


By
AsmaBaffa






SADAUKARWA NE GA ZAINAB GARBA BUTALAWA










Page naki ne












Ina Mata Wanda basa bukata Hammatar su ta kasance irin ta Gwamma to ga dama ta samu
Armpit powder me saka kamshi da tsane gumin hammata tare da gusar da duk wani wari ko wani Dirty,Yar uwa karki bari Hammatarki ta Zama irin ta Gwamma
Armpit powder Ina ga masu siyen daya ko sari dari biyu da Hamsim ce
250 ba tsada dai dai talaka ga yawa Kuma
Masu bukata ku tuntubi wannan number


+234 806 343 3559














Page

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login