Showing 42001 words to 45000 words out of 119289 words
Chapter 15 - Jikar Maguzawa Complete Hausa Novels Writing by Asma Baffa .txt
nan jinina hawa zaiyi Ina so Ina so inyi masifa an hanani kina ganin zagin dazu ma da Muka yiwa su Umma sai Dan saukakawa mukayi wani Dan kadan bazan iya ba bakina a sake yake bazanzo a takureni ba.
Ni Kuwa ban sani ba Yana cin tuwon shinkafa ko baya ci oho shi dai na dafa na dare na hada lemon kwakwa da dabino ya dau sanyi sai na hada masa da Dambun Naman kazar da nayi na cika Masa wani bowl da shi na dauki tray nayi part dinsa Ina zuwa bakin kofar nayi sallama ya amsa da kyar ma ake Jin muryarsa sabo da yanga,shiga nayi ciki baya Palon ma bedroom na shiga na hango shi yana zabar Kaya zai saka nace ga abincin bai juyo ba yace ajiye tunda bakya Jin magana sai kin kawo min dole bance komai ba na ajiye Zan juya naji muryarsa yace Yara sai hakuri,dama kadan nake jira na fashe da kuka,juyowa yayi tare da kallona yace kudi....Kudi Wai lallashina yayi tunda ya San uwar son kudi ce ni naki nayi Shuru,yace wai ba na dauki mataki ba Kuma mene ne Zaki zo duk Iskanci idan ya tashi ni zaki yiwa,harara na balla Masa Muka hada Ido yayi kamar bai gani ba yace ga kudin Saloon Zan baki ki huta wahalar da kanki ya mike tare da irgo kudi da yawa Ina ganin haka nayi shuru,Dariya na bashi ya murmusa ya juya yana irgo min kudi jikinsa ba kaya sai dan boxers,kusa da shi na matsa Ina bayansa Ina shakar kamshinsa Kamar Zan Shige jikinsa,Yana juyowa na fada jikinsa tare da kankameshi, kici kici yake yanda Zai janyeni a jikinsa a hankali nace Ummiyata na tuna haka nake mata idan raina ya baci na sake kankame shi,da masifa yace sakar min jiki ni Ummiyanki ne,au Fyade Zaki min,Ina jikinsa na dago na kalleshi Jin yayi shuru Ashe Kansa ya dafe da Hannu daya,idonsa na faka sajensa na fisgo da karfi,Kara ya saki da sauri nace dama wayo na maka so nake naji kalarsa ashe karsana ce
A ransa yace lallai ta Raina ni taba gemun babban mutum Irina ai raini ne,sai ya share yace ga kudin jeki,Hannu na miko Zan karba daga nesa ya Miko Ina karba ya damke Hannu na tare da jawo ni,ihu na saki Ina bashi hakuri,Naga kin rainani da yawa da Hannu daya ya daga ni sama da kyar garin kwatar kaina na rike boxers dinsa da hannaye biyu na janye shi kasa da sauri ya sake ni yace tsirara Zaki min ya Fara gyara wandonsa nayi kofar dakin Ina dariya nace na gane Ina da Dadi yau ga Area dinka Nan tana ta numfashi Yasin na Masa gwalo,Ran Jawad ya baci na sutale Masa wando yace sai naci uban Yarinyar nan a gidan uban wa take numfashi sai kace mace me da a cikinta Zan kamaki ne ,part dina na wuce Ina ta dariya tare da haurawa sama na fada bedroom Dina inda su Kadada suke suna zaune saman bed na fada saman gado na tare da jawo blanket na lulluba tashi na sake Yi zumbur nayi waje da gudu na koma part dinsa lokacin har ya Sha shadda tsadajjiya zai fita Yana fesa turare na bude kofa na shiga tare da tsayawa a jikin kofa ta mirror ya ganni Yana taje gashinsa,nace tambaya nazo Yi dan Allah kaciyar asibiti aka maka ko ta gargajiya wanzami ne? a fusace ya juyo yace,bude kofa nayi na fice da gudu na koma sashena
Zama yayi a saman bed tare da tunanin wanne irin rashin mutunci zai min ne ai,Tsaki ya ja ya fito zai fito compound Yana tafiya dake tsakaninmu da gate akwai tazara sannan direct babu wani Dan aiki da zai ganka ko ka ganshi har sai kaje bangaren gate,shi yasa naje da sauri Muka jera Ina gwada yanda yake tafiya yana wani basarwa,Hanya ya canja na sake jerawa da shi Muna tafiya Tsaki yaja Yana so yayi dariya Yana fuskewa amma ya kasa sai da yayi dariya yanda nake gwada tafiyarsa,kina da matsala ya furta,yanda yake magana na kwaikwaiya kana da matsala remote na mota ya Danna tun kafin ya karasa inda take ya bude itama wasu wurin parking din basu da alaka da gate sai ka fito da mota kayi tafiya sannan ka Isa gate, yau da alama shi daya zai fita,Muna karasawa jikin motar na bude Masa mazaunin driver kallo na yayi sannan ya Shiga nace ice cream da Shawarma please harda shagwaba na fada,yace wai ke sonki nake ne? Akan me deal ne fa ya kawo ni ba so nake ka so ni ba nima baka bukata na soka,a dawo lafiya,kallo na yayi a hankali na turo Masa lips nayi sign na kiss muuuuaaahhh na dan duka a bakin kofar motar
Harara ya galla min da masifa yace rufe min mota,har na rufe na sake budewa tare da gyara Masa gefen rigarsa da ta fito sannan na rufe sannan na tafi,Ina mamaki da baya iya min komai,Ina da dalilin da nayi Masa hakan Nima,dan bai Isa na kai kaina ba.
Har dare yayi Nawwara basu ci abincin dare ba Haka na hakura na zuba musu ita da Waleed sauran su sunci tuni,a hakan ma da suna karba sai zumbura baki suke,a ranar Kuma Asmau taji haushi itama na hana Yan uwansu abinci ta dinga harara ta sabo da Nawwara ta Fara zuga Asmau a kaina,Bayan munyi wanka munyi Shirin bacci har su Kadada room dinsu daban, Asmau da kanta tazo ta kwashe kannensu su uku Farida,Meenat da Ayanah irin baza su kwana a wajena ba,tsiyar Dan wani kenan shi yasa idan baka haifi naka ba sai bakin ciki ya kashe ka,Ina kallonsu bance komai ba nayi kwanciyata na manta ma nace Jawad ya siyo Mana Ice cream banyi tunanin zai siyo ba ashe ya siyo sai ya Kira Asmau ya bata ta kawo min,ko kawo min bata Yi ba ta Shige dakinsu da kayan Suka raba Suka shanye sai washe gari da sassafe naga sun watso robobin Palo da ledoji duk sun faca faca da palon da bedroom dinsu sabo da ga baiwa na gyara musu Wanda a baya ba haka suke ba.
Ina gani kawai nasa masu aiki Suka gyara ko Ina na gidan har room din su Asmau lokacin duk sun tafi school har su Meenat an sasu a school dasu aka koma dawowarsu gidan Jawad,Humaira,Abeed da Ayanah sune Kawai Basu Isa zuwa makaranta ba.
Washe gari ma
Ko da safe basu jira an shirya su ba da kansu suka shirya kansu da kannensu Suka tafiyarsu makaranta ko sallama basu min ba,Kadada basu gane komai ba sabo da kwanansu daya Kawai a gidan,harkarsu suke Yi kawai daga kallon tv sai ci da sha sai bacci.
Wanka nayi na shirya cikin wata silk gown me Dan siririn hannu doguwa har kasa Yar straight Haka marar nauyi dark blue,ta fito da asalin surata sosai na sheka kyau Kamar baturiya,ko dankwali ban daura ba,Su Kadada suna garden na fito Palo na duka Zan dauki Remote Jawad ya shigo yace yau ba a bawa su Nawwara kudin break ba? Sunzo suna kirana a waya,mikewa nayi tsaye ya Kare min kallo lokaci guda nace Basu Sanar dani ba Kawai tafiyarsu Suka Yi sai tashi nayi naga basa gidan Ahmad ne Kawai yace Kansa na ciwo yau bazai iya zuwa ba,sai Hafeez Kuma suna part dinsu,ya kamata ka tara yaran nan ka musu magana bayan Nawwara da Waleed jiya Asmau ta Fara hararata shine na tashi na iske sunyi faca faca da palon nan da robobin ice cream da ledojin chocolate da snacks Wanda da ba haka suke Yi ba,na rasa me na musu Ni dai nasan Allah Yana kallo ban taba zaluntar yaro ba ko kanne na wlh bana musu abinda nake musu,kitso na dade da daina yinsa amma dake sune ba Kalar da bana musu Kawai Ina ganin marayu ne ko ba komai lada mutum zai samu,karsu kaini bango ka tsawatar tun kafin na dauki mataki Asmau da Nawwara ai ba Yara bane .
Jawad ya gama ji na tsab yace Ina gida yau bari su dawo haka Kawai ya furta ya juya part dinsa yace kawo min Breakfast,mikewa nayi na soya masa dankalin turawa da kwai sai na shirya Masa komai a tray na wuce part dinsa,Ina Shiga ya bini da kallo yace su Hafeez suna gidan nan ba Wai kishi ba addini ya haramta kanin miji yaga jikin matar mutum,Kuma su Hafeez suna Nan kin sani addini na tuna Miki ba Wai kishi ko wani Abu ba,kije kiss hijab ko ki canja Kaya amma idan Kinga ke haka kike so shike nan Zaki iya zamanki koma waye ya gani ni bani da damuwa,nace haka Zan zauna Ni,fine ya furta Yana tabe baki yaja abincinsa ya fara ci,saman center carpet na kwanta,yace Wai me kike nufi dani ne tunda kin kawo min abinci ki tafi Mana naci In peace,allow me to enjoy my self haba, Yana zaune a saman kujera kafafunsa na kalla nace yatsanka me kyau na ja kafarsa daya nace mu ganiii.....kafarsa ya fisge,Hannu nasa na dauki chips guda biyu Ina daga kwance na miko Hannu nace San min,duk kin dameni na rasa ya zanyi dake,dariya nayi kawai a raina nace zaka sani akwai ranar da Zan rama yanzu ma Ina da dalilin da nake haka wlh sai ka magantu
Remote na dauka na juya daga kwance nayi ruf da ciki na daga kafafu na sama Ina watsal watsal da su,Riga ta ce ta sauke ta dawo iya gwiwa farin kwauri na ya bayyana luwai luwai da shi,Jawad ya kalla ya dauke Kansa harda Jan tsaki, tashi nayi na mike na juya Masa baya tsayawa nayi da ina canja chanel ya bini da kallo bai San ma ya tsaya da cin abincin ba,Yana tunawa Kuma ya bata rai yace ke fitar min a room, remote na ajiye nayi waje abina na barshi,Yana ganin na fita yace haka kawai daga auren Reno kizo ki takura min,Yana ta masifa shi daya har ya gama cin abinci yaje ya sake sabon shiri ya fito,ashariyar su Kadada yaji akan Kawai suna kallon film,Kadada ta daddanawa star ashar na film din tana ai gashi can ka kasa kula da matarka an sace ta,duk namijin da baya kula da matarsa yaci Kaza kazansa...Jawad yace wannan dani suke Kawai ya fice abinsa,haka Kawai sai kwakwalwarsa ta hango masa haduwar mu ta farko dana Zo karbar tallafi,Ina a tallafi shugabar marayu,Dariya ya saki bai shirya ba,ya tuno Sanda ya ganni na kawo musu fura,ya dinga dariya yace nayi missing furar Nan,hayyacinsa ya dawo yace Wai me yasa nake tunata ne yaja Tsaki yaci gaba da tafiya,Baccina a motarsa ya sake tunowa Ina mafarki ya murmusa yace banzar yarinya uwar son kudi ai kudi ne ya kawo ta Kai da kake Neman ta gari Kai shareta,mota ya shiga Yana tafiya ya tuno lokacin biki da kannensa da su Kadada sai ya kyalkyale da dariya ya furta Kadada tafi ma komai Ina Fara baki ba Sam,Fara ya tuno yace Kai gwara Tahantsi ma,wata zuciyar tace karya ne,duk yanda yaso kushe Najla ya kasa haka ya fara driving Yana tafiya Yana tunanin Najla har ya manta da Driving babbar mota tazo tayi gaba da shi gaba daya,mutane Suka Fara salati aka taru akan motar Jawad ko motsi baya yi sabo da Yana tafiya Kawai sitiyari ya tsinke gashi Yana ta gudu Yana sauri zai je Office.
Tunda Farooq ya fece sai gashi washegari ya dawo yamma ya dawo,su Kadada ya iske a compound yace Hey....Kadada ta galla Masa harara,yace kun kwana lafiya? Har da kai da kafafu Muka kwana gamu ka gammu,Farooq yayi dariya,Kadada tace kinga shima Yana da abun lobawa a kumatu irin na Fara da Hakuri....Kutmar.....babbar........ashe Yana da kyau,ya akayi ban kula ba tunda na ganka sau biyu sai a na uku? Farooq ya dinga dariya tace lallai da dodo shima kyau ne da shi,to ai shike nan jeka kawai,Farooq yace zance nazo fa wajenki,tab saurayi na ka Zama saurayina hmmm ai Kai sai Yan birni,mufa a Kauye muke Nan ma da kaga mun Fara gogewa Fara ce take gyara mu,amma ni yanzu Ina gaban Ummiyan Fara,Kuma ni bazan Yi saurayi da me addininku ba,azo a rinjayeni bada Ni ba,gobe ma Zamu Yi tafiyar mu kullum Fara sai taji wa'azi tayi ta kunna tv me wa'azi bazan iya ba,Farooq zaiyi magana tace nasan me zaka ce shedan ko,to mukam ya gama Yi Mana fitsarinsa a Kai ruwa Kawai muke sawa Muna daurarewa bada Kadada ba ga Tahantsi na baka itace me sha'awar addininku,Tahantsi tace ke kiyayeni bada ni ba,tabani Namiji yayi sai nayi wankan tsarki bazan iya ba
Suna dariya aka Kira Farooq dama shine last call na Farooq akace me Wayar yayi hatsari
AsmaBaffa
08033933642🌏 JIKAR MAGUZAWA 🌏
41-45
Official
By
AsmaBaffa
SADAUKARWA NE GA ZAINAB GARBA BUTALAWA
MASU BUKAR SHIGA PAID GROUP NA JIKAR MAGUZAWA 300 NE
ACCOUNT NUMBER
0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD
GTBANK
TURA KATIN MTN
08033933642
'YAN NIGER
+227 90 79 59 39
MASU MAIDA MIN NOVEL AUDIO WASU BASA SANARWA BADA IZNI NA BA,A DINGA SANARWA
_Ina mata y'an kwalisa ma'abuta gyaran jiki macce Mai gyara daban take ga zuciya mijinta muna da kayan mata da supplement na gyaran jiki kala muna hadin amare da uwargida Dana masu jego muna da set Mai hade da kaza Mai kwai 3 da cicicibe da kifi da galam 3 na tsime da Burkett din gumba 2 da garuruka da zuma wanna set na maccen da ta isa ne muna hadin shi 20k akwai karami set na 15k akwai na 10k akwai na 5k_
_Muna da zuma Bata gindin kishiya ga wadda kishiya ke muzguna mata wanna Zuma In kinyi anfani da ita miji salab zaiji Daya shiyasa indai ba macce cikin matsala take ba bamu Bata ita_
_Muna da magunguna masu jawo hankali maigida da kara martaba dasa alhere ga maruwacin namiji_
_Akwai Zuma kiba da hip sati Daya Kinga result_
_Muna hadin kiba duk ramar ki duk bushewa ki kinka sha shi sai ke ciciko_
_Fanin supplement ma ba'a bar mmn mujaheed abaya ba tana da nagyaran fata da kara haske akwai na gyaran brst na gyaran hip na kiba
Kamar su Lady capsule 4500
Sugar wanita 3500
Glutathione 3500
Vitamin e 3k
Gluta white 3500
Royal jelly 3500
Apetamin 3k_
_Frozen collagen 3500
Da sauran su insha Allah duk Wani supplement Zaki same su ga mmn mujaheed y'ar mutan skwatawa
Ina wadda sanyi ke Hana ta jindadin gidan miji_
_Y'ar uwa kiyi bayani abaki dai2 da type dinki indai sanyi ki Hana Miki jindadin aure ku budewa GABA ku rashin niima to kedai yima mmn mujaheed bayani zata baki dai2 Dake mun tanade set din maganin sanyi 4500 Wanda zai fatataki sanyi Kuna kashe ne_
_Mmn mujaheed y'ar mutan skwatawa muna zaune garin kebbi state
08066726866_
_Kayan mu iya kudinka iya shagalin kane_
Page Naki ne
MUFEEDAH
Farooq ko gama ji baiyi ba yace a Ina ne?ana bashi address bai fadawa kowa ba Kawai cewa yayi Ina zuwa ya juya da sauri ya juya ya shiga motarsa ya fita Kamar zai tashi sama,Su Kadada Suka ce ba kalau ba wannan Kiran bana lafiya bane zo mu koma ciki mu zauna muci gaba da tagumi,su ma su Kadada basu fada min ba naga dai sun dawo sun zauna sunyi tsuru,nace lafiya ku Kuma? Labari Suka bani abinda suka gani,tsoro naji na wuce part din su Hafeez naga har Ahmad sun fice Kawai mota naji Hafeez ya kunna sun Kara gaba,kiransa na dinga Yi a waya bai dauka ba,Nima ban San komai ba na koma inda su Kadada suke nayi shuru tare da zuba tagumi,ganin tagumi bazai kaini ba na dakko carbi Ina ja Ina karanta Innalillahi wa inna ilayhirraju'un
Bangaren Jawad Kuwa tare da Yan Sanda aka Yi private hospital dinsa da shi baya motsi ko Daya,su Hafeez har sun fara kuka,Farooq ne ya shige gaba har likitoci Suka shiga duba shi cikin gaggawa,Nan take aka Yi wasu gwaje gwaje har karfe biyu Shuru babu su Hafeez ba labarinsu Kuma sunki daga waya,Munyi Shuru Kamar anyi mana mutuwa har Yara Suka dawo daga makaranta nayi kokarin dannewa duk da yanzu Kuma Naga da yawan yaran a ciki basu kulani ba Suka Yi wucewarsu, Meenat ce da Ayanah Kawai Suka taho wajena suna Dariya Suka fada jikina,Meenat tace Aunty yau Aunty Nawwara Suka Yi ta gulmar ki Suka ce Kar mu kulaki ita da Asmau Kuma kince ba kyau gulma suka ce Wai mu zageki ko me Kika ce muyi Kar muyi,Kuma ai zagin Babba ba kyau Ni dai ba ruwanmu ni da Ayanah,nace to ba matsala karku damu kinji Banda zagi da gulma,Suka ce to nace kuje wajen Bintu sabo da ni Sam hankalina baya jikina,haka suka ce mu wlh ke Zaki Mana wanka,da kyar suka yarda Kadada zata musu Suka tafi,sauran Kuwa duk Wanda Suka Fara wayo ba Wanda ya shiga harkata,abincin ma Asmau ce ta shiga kitchen taga banyi ba sabo da bana cikin hayyacina,ko magana Basu min ba ji nayi kawai suna ta dafa indomie a kitchen din da kansu har kannen nasu Suka dafawa,kyalesu nayi kawai.
Bangaren su Farooq Kuwa suna ta jiran Kiran likita har sai 5pm ya fito da takardu yace to ku godewa Allah ba abinda ya sameshi Kawai tsoratar da yayi ne tasa yaki farfadowa amma yanzu yama farfado sai raunika da ya samu gobe zamu sallameku Amma idan ya tashi ma normal zamu iya sallamarsa,ku shiga ku ganshi,da sauri Suka shigo gaba daya ganin Jawad ya bude Ido ga drip a hannunsa Yana lumshe Ido ya Kira Farooq da Hafeez nan take suka Fara murna Ina yaran suke? Suka ce suna gida,yace okay,Asif ne ya shigo da gudu sabo da Farooq ya kirashi yaga motar yanda tayi fata fata