Showing 69001 words to 72000 words out of 119289 words
Chapter 24 - Jikar Maguzawa Complete Hausa Novels Writing by Asma Baffa .txt
10pm kana gida daga aiki sai gida bazan dauki yawace yawace da Zaman majalisa ba,sannan ba cin abinci a waje,Farooq yace Wai kece mijin ne ko matar yau naji ikon Allah, amma ai ni matarka ce Ina da iko da Kai Kamar yanda kake da iko dani,biyayyarka dai zanyi Nima zaka min 50-50,Dariya ta bawa Farooq yace Namiji yafi karfin kanki,Kai karami ba Nawa Babba ne,Farooq Yana kallonta yanda take magana direct,yace Allah ya kaimu a kawo ki gidan ki gani idan Zaki iya tankwara Ni nayi abinda banyi niyya ba,kiyayi kanka Yar gidan Tashuka ka aura,Babana Sanda ya auri Tashuka auren hadi ne Yana wani yanga harda gwada yanda Babanta yake Tashuka kike ko wa ni ba kalarki bane sai dai na lallaba dake sabo da hadin Gwamma ne amma Ni nafi karfinki,Tashukata Allah sarki Bata kaini ba lokacin shekarunta 13 baka ganta ba Yar tatsitsiya,komai yace tace to..to..to akayi aure bai sani ba ashe Tashuka Boss ce ta girmeshi a wayo shi Kam shekarun ne Kawai,har yanzu gashi ya kasa mata kishiya sai yanda tayi da shi har aka Haifeni,Taya ke Kika San zancen bayan ba a haifeki ba ma,Gwamma ce ta fada mana Kuma na yarda,Murmushi Farooq yayi yace yaushe Zan dawo to Naga Amarya na musamman a tanadi dakin zance,Kadada tace Indai zaka zo ka min waya bana son zuwan titse,okay ya furta tace ka fara bin doka kenan Murmushi yayi ta fita,yace ki gaida Ummiya sai na Zo a kiyaye dokokin aure Kar a min Wasa da igiya idan akayi min ba Dadi nima zanyi ba dadi, Kadada tace sai munyi waya Allah ya kaika gida lafiya,inye an Fara koyo,Ido daya Kadada ta kashe Masa ta juya cikin gidan Ummiya ta barshi Yana dariya,Jawad ya Kira Wai yazo ya kaishi airport ya karbi motarsa,Jawad lokacin ma Muna kasan Dan carpet a zaune ya sani tsakanin cinyoyinsa ice cream muke Sha da nama Yana bani abaki Yana ci shima shi yasa yace tab ai wlh bazan fito ba kazo ka ajiye min mota a hotel ka shiga Napep ya kaika,Haka zaka min? Wayarsa ya kashe ma haka Farooq ya dawo ya kawo motar ya shiga Napep ya wuce dare yayi dama night Flight ne shi yasa.
Tahantsi Kuwa har ta Fara bacci Baba ya dawo yaji labarin ta Musulunta dakin ya kwankwasa ganin 8pm, tashi tayi tare da bude kofa taga Baba da murna yace Ashe Kun Musulunta? tace ae sunana Khadija Kadada Kuma Fatima, Mashaallah nayi murna ubangi Allah ya dawwamar da ku a ciki har kashen rayuwa ameen tace,yace Najla tayi bacci ne? Ae yanzu dai ta Shiga bayi,Baba yace tototo so nake dama nace ta Fara shiri ko mahaifiyarta bata yarda ba ta koma dakin mijinta zaman ya Isa Haka bai Dace ba, Tahantsi tace ai sai suruki ya rainaku Baba gaskiya ku bashi matarsa wannan bai Dace ba idan ba so kuke rabo yasa a fara muku dauki dai dai ba ko a dauke ka ko Ummiya gwara ku hakura,Baba yaji tsoro yace hakane gaskiya Kar mutuwa ta riske mu,tana Ina in fada Mata ta koma, Tahantsi tace dama karya nake Baba tana can tare da mijinta a hotel,Baki Baba ya bude tare da furta hotel? Na saduda na hakura baza ku daina karya ba Allah ya shiryeku Kawai, Tahantsi ta Fara dariya tace dama duk fitar Nan da muke muce munje siyayya ko munje karbo Sako duk karya ce Baba wajen mijinta take zuwa Ni dalilin zuwana gidan nan kenan,Baba yace uhm Yan banza makaryata to ta koma wlh tun kafin matsala ta afku a gidana ya juya ya tafi.
Kadada Kuwa tana Shiga gidan Ummiya da murna ta tareta tace Ina murna,Dariya tayi tace sai azo a koyi karatu a fara Sallah Kadada tace ai nasan mura sai ta kamani sabo da yawan taba ruwa,in shiga tsarki inyi Alwala kullum sau biyar,ga wankan tsarki kwaduwa Kawai Ummiya Bari na huta, ta Shiga daki ta cire kayan jikinta tare da shiga wanka tana Fitowa Ummiya ta koya Mata Alwala,Kadada wani facal facal ana dan shafa ruwa kadan,kisa ruwa in Zaki saka mene Haka? Uhm uhm Mura Ummiya,garin shakar hanci ta ja ruwa da yawa a hancita ta fatalar da buta sabo da azaba sai da ta dade Ummiya tace sai ancanja sabuwa wannan bata Yi ba,aka sake sabuwa facal facal hancin ma Sai dan gefen kafar aka shafawa ruwa Taki ta canja sai haka aka kyaleta,Karatuma haka aka Sha fama kafin ta iya,Ummiya tace Addini sai da Hakuri da Dangana,Kadada ta harari Ummiya,Dan ubanki mene sa'arki ce? to ni me nace amma ai kin San sunan Surukina ne,Danganan? Kadada ta Dora hannaye a Kai gashi Nan kin Kara fada Kamar zata Yi kuka,Dariya ma ta bawa Ummiya tace amma ai sunan ubanki da uwarki fada kike har a gabansu da gaban kowa,sai a Kan suruki Dan ance Dangana sunansa daban abinda muke nufi daban, ya sunansa complete? Kadada tace tab ni na fada bada ni ba,Amma ai kin San sunan me shagon kofar gidan Nan ko? Ummiya tace Ibrahim? Da sauri Kadada tace ae sai ki hada da sunan Hakuri da Kika fada,Ibrahim Dangana cewar? Ummiya a zuciyarki nace ki fada fa Ummiya Dariya Ummiya tayi tace to Shikenan matar Farooq Ibrahim Dangana duk an kwashe Mana ku kunyi Lagos Saura Tahantsi ta dawo nan in kin tafi,da Tahantsi zamu tafi tayi min zaman daki cewar Kadada,Ummiya tace baki da hankali katuwa ta hantsi ce zata Miki zaman daki Tahantsi da take da son girma Allah ya kawota ki fada a gabanta kya Sha ashariya,Dariya Kadada tayi ta dauki Wayarta tace Ummiya kije Daddy ya dawo kin barshi shi kadai kuyi soyayyarku ta dattijai,sai naci ubanki Ummiya ta juyo tare tallafewa Kadada keya Yar Iska fitsararriya,Ummiya sorry ai na zaci Kun tsufa Kun hakura sai mu Ashe....baki ta gwabe Mata tashi Yar Iska ki tada Sallah Ina gani ai na koya miki,Kadada ta zumbula hijab ta Fara Sallah gata Nan dai raka'ar farko ta Fara lankwashe kafa bata taba Yi ba ihu ta saki wayyo kafafuna zasu balle Ummiya tace Sallah sabuwa ta lalace ta farko kinyi magana,Ummi ta koya Mata yanda zata lallaba tayi,Kadada tace ai sai kice zaman rakumi kafata ballewa zata Yi Ummiya,kafar dama zakisa ta danne ta hagu Kinga gani kalli aka koya Mata tana ta ihu Kashi na sai Daddy ya fito yace Kai lafiya yaga ashe duk koyon Sallah ne ya koma ciki, sai kyaleta akayi tayi yanda zata iya har tayi sallolinta,Ummiya tashi tayi ta ta Mata sai da safe tace in Zaki ci abinci Yana kitchen tace to
Kadada Wayarta ta jawo tare da Kiran Tahantsi tana dagawa su irin musulmai harda salamu alaikun, Tahantsi tace ke Binta Alaikum aka ce to naji idan za a kaini mu tafi Mana dake ki min zaman daki, Tahantsi ta kutuntumo ashar tafi goma kin Raina min hankali sa'arku ce ni,sai naci ubanku wlh ke da Fara haka tace dazu na bita to bazan je ba Ina gidan Ummiya,Kadada ta kyalkyale da dariya tace ko soyayya Kya kalla ki koya Tahantsi Muje Nana Khadija,Bazan je ba ki wuce turaka ana ta kwalwaleki ni Ina can tsuru bada Ni ba wannan Farooq din naki idonsa a tsakar kai wani Hakuri zai iya, Tahantsi tace dazu fa Ina kallonsa Yana kallon kirjina Ina tuna nin ma Hannu zai Kai na hade rai sabo da Ni ba Fara bace, Tahantsi tace keee Na saduda da Farooq na tsinke da lamarinsa,kwana nan labbaki zasu koma yellow Dan naki inaga sai dai yellow ba ja ba ko suyi kore kore,Wayyo Vamfire Kawai cewar Kadada,na Fara tausayin kaina Blue sai su dawo ma, Tahantsi tana ta dariya tace can Kuwa Ma'aikatar shike nan sai ta Allah ,Kadada ta saka kuka tace gwara na Fara tun yanzu,Ummiya nasan gobe zata Fara gyaraki tace tuni ma dazu ma ta bani wani Abu na Sha Wai na infection,Kadada na tausaya Miki kin Shiga Uku har Tashuka sai kin nemo,Kadada tace abinda Kuwa Kika ga yasa na koma Kauye wajen Iyaye to ba karami bane,bari na Kira Fara ta koya min dabaru kare Kai tun kafin, Tahantsi tace tana wajen terrorist dinta ki kiyayi Jawad ba karamin criminal bane terror ne na kirki,Suka kyalkyale da dariya har da dura ashar amma sai kiga Fara a Fuska shar kullum wani kyau take karawa da haske Tahantsi tace yo ta samu collagen din jikinsa ba dole ba,Tahantsi akwai daukan darasi ko ya taga Abu ko taji ta rike,Kadada tace bari na bashi haushi na dinga surfa Mata kira ta kashe waya ta Kira Ni
Lokacin ma Yana zaune a gefen bed Yana aiki da system Ina kwance a saman bed kaina Yana saitin bayansa nayi sama da kafafuna na Dora su jikin fuskar bed Ina ta Masa tafiyar tsutsa a baya Watarana yayi dariya ya noke jiki Watarana ya shareni,waya ce rike a hannunsa ana fada Masa Abu Yana shigarwa,Kadada ta addabeni da kira yace daga please bana Jin me ake cewa,a hankali nayi magana Kadada lfy,Ki bude murya mana Fara Hira na bugo muyi ki Kira Farooq mana,to ni da Yar uwata zanyi in Kuma bakya so na to,to Ina jinki Ina Terror dinki,wa? Terror Jawad dariya ta bani nace Zan fada Masa ai Yana ji,
Jawadiririya Dan tsako da yaji bikin Iya sai fakat Kadada ta rero wakar da su Gwamma suke wa Yara,nace Farooq Kika yiwa back to sender,Jawad ne ya juyo yace bana ji fa kiyi ki gama,katse wayar nayi yaci gaba da tasa.
Farooq bayan ya sauka yayi wanka tare da Shirin bacci,Farooq fari ne Amma ba Kar ba Dan fari fari dai Haka,dogo ne har ya danfi Jawad tsayi da kyauri kadan,Iyayensa su biyu Suka Haifa rak shi da kanwarsa Na'ima wacce tuni an Mata aure da yaranta biyu,Babansa me kudi ne sosai shi,sannan aiki Babba yake a Nnpc Lagos,asalinsu Yan Katsina state ne da Mamansa Hajiya Marwa da Babansa Ibrahim Dangana,sabo da hakurin Babansa tun Yana yaro Iyayensa Suka sa Masa Dangana,Basu da wata matsala daga uwar Farooq har ubansa.
Sai da yayi Shirin bacci sannan ya Kira Kadada,sai da tayi ringing har ta katse tana kallo tana kwance itama tayi Shirin baccinta,sake Kira yayi sai data kusa katsewa ta daga da wata iriyar murya an wani narke an shagwabe,Farooq yaji tsigar jikinsa ta tashi yarrrrr sau da dama yakan ji haka idan Kadada tayi magana da salo,Bai San Sanda yace my Binta sugar...My Shugar...Kadada aka ji wani dadi aka Kara shagwaba Kan ta baya tun yaushe kaje gida sai yanzu zaka kirani Ina ta tunanin ko kaje lafiya uhmm....aka karasa da wani da jaaaa shi Kansa Farooq sai da yayi dariya a boye, yace to kiyi hakuri ai gashi na kira mene labari? Tsaya ai ban Gama ba ya lafiyar iyayena? Wai surukanta Kadada an iya duniyanci,Farooq har da Jin dadi yace suna nan lafiya,na kusa dai nazo na dinga zuwa Ina gaisheta Allah yasa gida Daya zamu zauna na dinga Tayata aiki itama ta huta,Farooq shi kam iyayin Kadada Dariya yake bashi sai kace bazawa irin Wanda sun San Kan tsiya,ba shiri ya Danna recording sabo da ya dinga kamowa Yana ji Yana dariya,Yace ai tana da Yan aiki,Wa yake ta Yan aiki ga surukarta,Farooq Yana ta dariya kasa kasa,yace to ai gidanki daban sai dai Watarana na dinga kaiki,to shikenan cewar Kadada a ranta tace gwara da ba gida Daya zamu zauna ba nazo na samu suruka irin Umma Watarana na saki layi Tasha ashariya Allah ya taimakeni surukan yanzu masu shegen son da ga kishi da matar da a dinga bin kwakwafi idan Allah yayi tana cikin na kirki shike nan,Haka ta dinga Iyayi Yana ta Jin Dadi Yana Kara sonta bai sani ba har Suka gama waya Bai San dare ya ja da yawa ba sabo da iya hira ta Kadada.
Umma yau kaca kaca sukayi da Abba sakamakon asara da yayi a Harkar kasuwancinsa Rabin jarinsa kaf babu Kuma Umma ta nace sai ya Bata million biyar zata cika ta sai fili,Fitowa yayi cikin Fushi yana bin steps ta fito cikin Fushi ta cakumo rigarsa ta baya ba inda zakaje sai ka bani wallahi,cikin Fushi Abba ya juyo ya dinga kashe Umma da Mari har sai da taje kasa sannan ya hau jibgarta Kamar zai kasheta sai da ya Mata ligif sannan yace na sake,Igiyarki dama Saura Daya na karasheta,Umma ta kurma ihu wayyo na shiga Uku Saura Daya dama ka karasa,Nasiru ka tuna soyayyar mu ka rufa asiri muci gaba da zamanmu ba tare da kowa ya sani ba,Alhaji Nasir Yana mugun son matarsa Yana sakinta sai Kuma abin duniya ya cunkushe Masa kwakwalwa,Allah yasa yaran basa nan ba kowa a kusa sai ya fashe da kuka yace kin cuceni Ina sonki kin San na karasa igiyar data rage bazan iya jure ki auri wani kiyi auren kisan wuta ba,babu kyau mun sani muci gaba da Zaman mu ba Wanda ya sani amma Kar mu bari wani abu ya shiga tsakaninmu,Umma tana kuka duk iskancinta tace nasan akwai da yawa yanzu wallahi babu aure a tsakaninsu mazajen sun sakesu Amma so yasa sun kasa fadawa kowa baza ta iya wani aure ta fito ba sunyi Shuru sunci gaba da rayuwarsu suna ta ci gaba da haihuwa da yaransu duk Yayan Zina,Ni bazan iya ba dole mu hakura da juna ka biya kudi na samu wani gara Nan gaba na aura sati yayi yawa ya sakeni sai na dawo a daura Mana aure,Abba ya yarda yace tabbas ba kyau Amma kije ki auri na kauyenku gwara Yan Kauye da basu waye ba Kinga da wuri zai sallamo min ke,Umma tace Inshaallah tana goge hawaye,Abba yace Ashe Maman Najla tazo ta dauke yarta wai? Umma Ina yanzu ta kanta take ta daina ta wata Najla tace kowa yaji da matsalarsa Nima gashi gobe Zan tafi kauyenmu da saki ta rushe da kuka,shima Abba ya zauna a step ya fashe da kuka Suka dinga yi babu me lallashin wani
Bangaren kannen Jawad ma duk da cewar ba abinda Suka Nema suka rasa basa Jin Dadi Sam sabo da rashin Najla,ga Jawad ma tunda ta tafi baya Zama Yana Kano ya tare sai dai kullum su kirashi suna cewa dan Allah ya dawo musu da Aunty sai dai yace musu to Kawai,Maman Hafeez Kuwa dama tunda ta sheka taga ba kwaya ta hakura ta gudu gida taga Harkar Umma sai ita
AsmaBaffa🌏JIKAR MAGUZAWA 🌏
71-75
NA KUDI NE MALLAKIN JIKAR MAGUZAWA PAID GROUP
Official
By
AsmaBaffa
SADAUKARWA NE GA ZAINAB GARBA BUTALAWA
Page naku ne
Maman Afrah
Binta Idris
Hafsa Abdullahi
@jinddah
Auntyn Khairat
Maryam Bello
Maryam T Baliya
Umma ko da yaranta Suka da dawo daga school karya ta musu tace zata tafi kauye ganin gida amma zata Dade bata dawo ba sai dai a dinga Kai Mata su hutu,Yan aiki ma cewa tayi zata je Kauye ganin gida a kular Mata da Yara kafin ta dawo,Shiri tayi Yan aiki Basu San dalili ba anga dai ta jibgi Uban kaya ta Jibga a mota Driver ya tafi kaita,ko da ta Isa garisu da dare Babar Umma tana ganinta lokacin duk suna tsakar gida suna cin tuwon dare,salati Inna Babar Umma ta saki ta karasa da Innalillahi wa inna ilayhirraju'un,Allahumma ajirni min azabi jahannama la haula wala kuwwata Muhammada Dan Abdullahi Barira wannan kayan bana lfy bane kinyi tsiya dayar igiyar ta karasa ko? Umma ta fashe da kuka,Kannen Umma Yan Mata suka ce sai da Muka fada Miki gashi kin jawo Mana Dan kudin makarantar da kike biya mana ta Kare yanzu,hakkin Marayu ne Dana matar Jawad kin takurawa bayin Allah ke ba kishiyarta ba ke ba komai ba kin sa an maida ta gida tana zaman Aurenta ai gashi kema an sakeki,Umma tayi mukus,Dattijon tsoho Babanta Yana zaune Yana cin tuwonsa me zafi ko kulata baiyi tunda sai da aka dauki lokaci yace Wanda baiji Bari ba ai yaji hoho,Kuma Kika Zo Nan Zaki Mana fitsara wallahi ubanki Zaki ci sai in Miki dukan tsiya bar ganinki shirgegiya sai In Miki raga raga Yar me bakin hali,Inna tace bankadaddiya me mugun Hali,Zaki bar nan ko sai na karya ki cewar Baban Umma,kayanta ta shigar cikin daki tayi Shuru a ciki a nan dai aka Kai Mata tuwon dawar miyar kubewa danya ta hau zilillikar abinta.
Washe gari kafin kace me zance ya cika kauyen Hajiya Barira an Mata saki uku
Ni Kuwa a daren tare Muka Yi bacci da Jawad Ina kirjinsa Nasha latse latse ranar,da Asuba Kadada take ta uban kirana naki dagawa har Jawad yace ki daga ko ba lafiya ba,na daga Ina dagawa tace ki taho gidan Ummiya Daddy ya rasu fa,ji nayi Kamar an buga min guduma nace me? Daddy akace dalla ta karasa da kuka jiya cikin dare ya fara ciwon ciki kafin mu tafi kaishi asibiti ya rasu,Allah da gaske nake Miki Kadada tana ta kuka ta kashe waya,Jawad yaji komai a kunnensa yace Subhannallahi Innalillahi wa inna ilayhirraju'un Allah yaji kansa,Kuka na saki na mike ya rikeni yace ki bari muyi Sallah sai mu tafi, Ummiya dai babu bakin magana tana ta kuka Kadada ce ta dinga Kiran Yan Uwa a waya,har Dangin Daddy ta Kira da Wayar Ummiya ta fada musu,Da asubar sai gashi makwafta da abokan arziki har sun cika gida,Tahantsi a lokacin ta taho ba tsoro Babane yasa driver ya kawota kafin shima yazo,Nima Muna idar da Sallah gari yayi shaaaa Muka shirya Jawad ya tada mota muka tafi gidan Ummiya,mutane an cika damkam Yan Uwansa sunzo har an hada shi,na Masa Addua Ina hawaye aka tafi dashi makwancinsa,Daddy mutumin kirki baida zafi,Bai taba haihuwa ba,Ummiya ce ma Sai anyi zaton cike ne da ita sai aga ba ciki ashe, anji mutuwar yayi jama'a,Iyayen Ummiya ne kawai Suka Zo Banda Yan gidan Gwamma tace babu me zuwa tunda su Kadada