Showing 18001 words to 21000 words out of 119289 words

Chapter 7 - Jikar Maguzawa Complete Hausa Novels Writing by Asma Baffa .txt

28 Nov 2024

7422

na haura sama,knocking nayi sannan na Shiga palonsa dauke da sallama a bakina,Yana zaune Yana kallo matarsa tana gefe suna Hira tana kallona ta balla min harara ni dai ban ko kulata ba


Gaban Baba na karasa ko gaishesa banyi ba Raina a bace Ina cika Ina batsewa da kyar nace Barka da asuba bakin sun Zo,kice Ina zuwa Kawai ya furta kafin ya rufe baki na fice zuwa palon dake kasa kitchen na shiga a ciki na iske dayar matar Baba tana aiki ko kulata banyi na Bude fridge na zuba abinda Zan zuba a katon tire nayi waje Ina jinta ta buga tsaki Nima na juyo na Kora mata nawa tsakin na wuce palon baki inda su Jawad suke a gabansu na ajiye tire din na kayan Sha,Asif ne Kawai ya Sha lemon me sanyi sannan ya kalleni tare da furta kinyi Shuru,idanuwa na dago tare da satar kallon Jawad naga Kawai ya harde kafafu Yana chat a wayarsa,idona na sauke kasa a hankali cike da karyewar zuciya ganin ko kallo ban isheshi ba sannan nace to me zance..Baba ne ya shigo yasha shadda


Ko da Wasa banyi zaton Jawad zai rusunawa Baba ba kasancewar yanda yake da mugun Izza da gadara da Isa gashi magana wahala take Masa amma abin mamaki sai gani nayi ya duka har kasa sosai shi da Asif cike da girmamawa suna gaisar da Baba,da fara'a ya amsa sai da ya basu izini su koma su zauna sannan Suka Zauna Baba ya kallesu yace Maman Najla ta sanar min komai Kuma nayi bincike a kanka Alhmdllh duk da cewa Kai ba boyayyen mutum bane ko a kafafen yada labarai ana ganinka Kuma ana Jin labarinka amma shi aure ba abin Wasa ba ne dole sai da bincike Kuma Alhmdllh babu matsala kuje wajen Daddy dinta shine zaiyi komai nata tunda ba a hannuna take ba,Asif yace dama mun gama magana da shi,to..to..to ba laifi sai ka turo manyanka cewar Baba,nidai Ina gefe na mike Zan bar wajen Baba yace zauna,komawa nayi tare da Zama,Baba ya kalleni yace to kinga dai aure zakiyi wani saurin Fushi da zuciya ba naki bane sannan hakuri akeyi da rayuwa,banda zuwa a nuna halin Maguzanci


Ba soyayyar da kukeyi a waje ita zakuyi a gida ba,ke 'yata ce Kinga soyayya dan ubanki kiyi ta kanki ki haka rami da wuri ki binne ta kafin shi ya binne Miki ita da Kansa,halinki na gari shi zai ceceki,Kinga wani I love you da sweetheart to ki boye kalamanki akwai Randa zasu daina Masa dadi,sabo da haka tun yanzu kuyi soyayyarku kuyi ta zuba Kalamai kafin a shiga gidan shahada,Gidan aure gidan Shahada kenan Saura kadan su Jawad suyi dariya da kyar suka danne ganin Baba ya dage Wai fada yake ma yarsa,nidai na fada Miki ki haka rami ki binne wani soyayya mu Nan hausawa ne ba turawa ba sabo da haka ki cire burin samun soyayya irin ta turawa yawwa nasanki da shegen kallon India to wallahi soyayya ko irin ta su Ali Nuhu baza ki samu ba bare ta Yan India in zaki nutsu ki nutsu naji Mamanki tace Wai Nan da 2wks za'a daura auren,Najla soyayya ta rufe Miki Ido wato har wani gaggawar auren kike ko aure kike so shike Nan Allah yasa haka ne mafi alkhairi,Asif ya amsa da Ameen,Baba ya kalli Jawad yace Kai Kuma halin mace sai hakuri Musamman yarinya irin Najla, aure kusa a ranku ibada zakuyi sai ku zauna lafiya kana da hankali kasan darajar aure kasan hakkinka akan matarka to ka sauke banda wulakanci karka auri mace dan kyawunta ka aureta dan Allah da zuciya daya, Amana ce a gareka dan Allah,Jawad yace Inshaallah,Baba yace abinda yasa nake fada muku haka tafiya ce ta taso min zuwa China bana kasar za a daura auren next week Zan tafi Kuma Kira ne me muhimmanci,Allah ya tsare cewar Asif haka Baba ya dinga Nasiha sannan ya sallame mu,Ina ta dariya a Raina Baba yayi zaton soyayyace ta sa bai San aikin kudi zanyi ba,Basu dade a gidanmu ba suka ce zasu tafi Jawad ya ajiyewa Matan babanmu dubu dari Yan dubu dubu da kyar Baba ya bari suka karba na fito Zan rakasu sai da Muka tsaya da Asif ya tsara min bikin yanda za ayi ba batun dinner ko party aure Kawai za a daura abinci Kuma zasu Mana order har na kawayena da mutanensu,Kuma da Amarya zasu tafi,ficika iyayena baza su kashe ba har mutanen su Jawad ya dau nauyin komai sai Murna nakeyi a raina,Jawad Yana cikin mota Yana jiran Asif


Asif yace yanzu gyaran jiki da komai nawa ne zai isheki har suturar da Zaki saka?nace ko Nawa kuka bayar ba damuwa,Okay kina da accnt? Kai na daga Masa,good bani accnt number na Miki transfer,karanta Masa nayi nan take sai ga dubu dari uku ta shigo farin ciki ya kamani ban San Sanda nace a gaisar min da kannen nawa kafin nazo na kula da su,Asif yayi dariya yace ko Mene ki kirani baza mu dawo ba sai ranar daurin aure,nace to na gode fa, Asif tuni wannan zuwan ya tantance gaskiya Najla nice dai ta Kauye Shuru ya min baiyi zancen ba nima Kuma nasan ya gane Sallama mukayi ya shiga mota Yana Shiga Jawad ya balbalesa da masifa yace dan iskanci kasan fa Zan je shirye shiryen masu Interview gobe yau Ina da meeting ka wani zamanka ya ja tsaki tare kallon agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa gucci ya Masa kyau,har Suka tafi Jawad yana tsaki an bata Masa lokaci,Asif Yana ta dariya abinsa,Suka sauka hotel ya Kama musu ko wanka basuyi ba Suka wuce meeting bayan sun dawo suna hanya a cikin wata sabuwar motar Jawad Benz arsh,driver ke tukasu,Asif waya yake da matarsa yace gobe zamu dawo gashi tunda naji muryarki har na mike ya furta kasa kasa yanda driver bazai ji shi ba,Jawad kallonsa yayi da lumsasu idanuwansa sabo da yaji tabbas iskancin Wayar da Asif yake da matarsa,ta cikin wayar matar Asif tana Murmushi tace i miss you so much darling Ina madugu uban yaki gashi nan Kuma na fada Miki halin da yake ciki yanzu,Jawad dauke Kansa yayi daga kallon Asif sai da Asif ya gama yace kwarton banza baka da aiki sai mace wannan ta shiga Uku


Asif Yana dariya yace wlh kamar ka sani yanzu ma ji nake Kamar nayi tsuntsu Kai ka zauna sai mafarki kasa a gaba kullum fa sai kayi mafarkin kana sex,inji uban wa? Ni da na gani da Ido na haba Jawad sau Nawa na kwana da kai sai ka wani yi ruf da ciki Kai ta yiwa katifa,Allah ya tsinewa me karya cewar Jawad Yana lumshe Ido yaja Tsaki tare da juya ganinsa Kan wayarsa,Asif yace ka so Najla dinka yarinya Kyakyawa ka huce a kanta ka daina wahala da mafarki,zaka fita a motar nan Allah,Shuru Asif yayi yace me yasa baka sonta Wai yarinya kyakyawa Haka jajir da ita anya kalau kake kuwa? Driver Jawad ya Kira tare da furta stop the car,da sauri Asif yace sorry Oga na daina,Sai lokacin Jawad yace muje Yana latsa waya Suka ci gaba da tafiya zuwa masaukinsu
Kowanne room dinsa ya wuce wanka Suka Yi tare da cin abinci sannan Asif ya fita yawo wajen abokansa shi kuwa Jawad bacci ya kwanta Yana faman yi.

Umma Zaune take ta hakimce a Palo yaranta ne suka dawo daga school suna shigowa ta tarbesu da murna Suka rungumeta tace aje Nanny ta gyara min ku ta muku wanka maza kuzo ga abinci lafiyayye na shirya muku da kaina,suna murna suka wuce da gudu,bangaren kannen Jawad Kuwa suna shigowa palon kowannensu dauke da school bag ta watsa musu harara tare da Jan tsaki,Sannu Suka Mata ko kallonsu bata Yi ba,ta mike tazo zata wuce ta hankade Nawwara Nan take Umma ta fisgo ta tare da fyalla Mata Mari Dan ubanki ni Zaki bangaje? Nawwara ta fashe da kuka tayi hanyar bedroom dinsu tana zuwa bakin kofa tace Allah ya isa,ai Umma kamar an tsira Mata allura haka ta zabura Nawwara ta fada bedroom tare da rufe kofa da key, Umma tace wlh yanzu dole su Hafeez su koma dakinku da kwana ba wani dakin maza da na Mata daban,tare zaku dinga kwana a daki daya Mata da maza har Asmau duk da ta fara nono haka zaku kwana da su Hafeez zaku ci ubanku in yaso mazan ma su latse ku ba abinda ya dameni


Washe gari da sassafe na shirya tafiya Interview sai farin ciki nakeyi,Farisa sai waya take buga min nayi sauri yau har Hamziyya za aje taji yanda Muka ci kayan Dadi itama ta shirya ka rantse wajen arziki zamu yanda Muka Sha wanka yau Hijab nasa har kasa arsh me Hannu nayi kyau ,takarda na karbo daga secondary school dinmu tunda bamu gama zana Exam ba bare waec ta fito nace lallai sai pc ta rubuta min na hada da su birth certificate na tafi Ummiya tace yau ma Lesson din ne? nace ae Ummiya,kudi ta bani na Napep na sake karbewa na fito bakin titi,Ina Fitowa sai ga saurayina Salisu a cikin napep ya tsaya a gaba,mamaki yasa nace yaushe ka samu sana'ar Napep? yace tun sati biyu da Suka wuce,Takaici ya kamani ga Napep na banza ban sani ba na dinga hawa na kudi Ina biyan kudi na a banza


Shiga nayi ciki na zauna yace gimbiya Ina zuwa haka nace wlh Baby wani aiki nake Nema,Salisu sai yaji wani banbarakwai tunda muke da shi bana saurararsa bare har na kirashi da Baby sai yau da Naga Napep na bati,duk da haka shi yaji dadin yanda na kirashi amma yace me Kika ce Najla? Nace Baby love muje please Zan makara,ya ja Napep Yana murna bai San na kusa aure ba,nace in mu gama ka dawo ka daukeni yace an gama Najla,gobe Kuma zaka kaini school da Yamma zaka kaimu kasuwa ni da kawayena Salisu yace sai abinda kike so ashe kina so na Haka nace Hmmm ai mu Mata zurfin ciki ne Damu ba kasafai muke soyayya a fili ba komai Naga Ina sonsa har Napep din nan,Salisu Kamar yayi tsalle haka yake ji yace ai Napep din ma naki ne ko Ina kike so Kawai ki min waya nazo na kaiki,nace to Baby,A hanya Muka dauki Hamziyya da Farisa


Kowacce da file Salisu ya sauke mu a kamfanin Muka iske mutane da yawa a ciki ana duba takardunsu ashe Sabo da mu Jawad yace Kar a Bari masu takardun primary su shugo Masa Bai San mun canja taku ba,Muna zuwa bakin gate Hamziyya ta Fara Mika takardun Yayarta Haleesa na NCE data sato mata bata sani ba,ana dubawa akace ya sunanki? Tace Haleesa Tahir sai sukace shiga ciki ta wuce,kafin a duba Nawa dana Farisa nace shi yace mu dawo yau sabo da jiya akwai wata takarda da bamu sa ciki ba,dama jiya sun ganmu sun gane mu Suka ce mu Shiga,Muna Shiga ko kallon bangaren da ake interview bamuyi ba muka wuce wajen cin abinci


Masu bada abinci suna ganinmu sai da Suka Yi gulmar mu amma Kawai Suka tambaya me za a kawo? Nace hot tea, Chinese Friedrice,da katon kifi karfasa,sai a kawo Mana Sauran kayan Kari gaba daya,Suka kawo Mana Kuwa Muka Fara ci ba ruwanmu da cokali,Hamziyya tace tab ashe an barni a baya wannan kifin ya sunansa Najla? Nace kalli bakinsa sunansa Shark,me cinye mutane fa inji Farisa nace idan shi bai cinye mu ba ai gashi yau mu zamu cinye shi,ba kowa a wajen cin abincin sai mu shi yasa muke ci yanda Muka ga dama,sai da Muka ci Muka koshi mun cinye komai tas Muka wanke hannayenmu sai wajen Interview Muna zuwa Saura mutum daya gashi 12:30pm ma tayi,Yana Fitowa Muka shiga gaba dayan mu ciki,Yana saman kujerarsa me jujjuyawa Yana rubuce rubuce,bai San mune ba sai da yaji murya ta nace Sir Ina yini? da sauri ya dago ya kallemu Yana mamaki ta ya aka bari muka shigo Masa kamfani a ransa yace zaku gane kurenku na bakin gate


Muna tsaye bai kula mu ba Yana ta aikinsa Yana daga waya har aka kawo Masa Juice ya tashi ya shige cikin room din Office din,Ina tabbatarwa ya shige na lallaba na dauki juice dinsa nayi Masa kurba Uku sannan na dauki ruwan robar daya rage na zuba a cikin lemon ya dawo dai dai yanda aka kawo Masa abinsa,Farisa tace wallahi mu dai ba ruwanmu


Minti biyu sai gashi ya dawo ya zauna Kamar ya ajiye Iska ya dauki lemonsa ya kurba sai yaji ba taste Kamar ruwa Fuska ya bata ya ture shi gefe sai lokacin ya Miko Hannu yace ku bani,Muka Mika Masa files dinmu


Na Hamziyya ya Fara dubawa yace Haleesa Tahir takardun wa Kika sato,tsoro ya Kama Hamziyya ta ya zai gane, ta rude tace na yayata Ido na runtse Jin ta kwafsa mana, tana aiki? a'a ta Nema bata samu ba bamu da hanya,takardun ya ajiye a gefe yace asirinki ashe zai tonu,kuka Hamziyya ta saki tace wlh Najla ce da Farisa Suka zugani abinci muka zo ci me Dadi shine Najla tace sai munzo mun bata maka lokaci baza ta taba bari ka huta ba a duniya ta tsani taga kana hutawa haka kawai,Farisa tace dama haka Zaki Mana Hamziyya? Jawad dariya yayi a ransa yace to Zan bawa yayarki aiki ki fada mata tazo gobe by 8am in ta wuce 8am ta rasa, Hamziyya sai ta koma murna ta dinga godiya,Najla tace na daina kawa dake algunguma sai nazo na hada miki jini da majina har gida Hamziyya ki jirani har gaban uwarki Hamziyya tace haba ai Muna tare iya wuya ta fice abinta tana jiranmu a waje tana ta Murna tace yanzu kayan abincinmu duk wata Aunty Haleesa zata dinga siya mana mun daina kaiwa da kyar.


Farisa ya karbi nata ya gani ya bata yace Out ta fice a tamanin,Najla na Mika Masa ko a jikina ya bude yaga an saka
To WHOM IT MAY CONCERN wato ko Exam ma basu gama ba ta Ssce shine ta karbo Masa To Whom ta raina Masa hankali
Yace ke me yasa kike so ki bata min lokacin? Najla na turo baki nace yo sabo da Allah Jin dadin ai yayi maka yawa,ba kece Zan dauke ki rainon Yara ba? a raina nace kut raino ba aure ba Kan uba,a fili nace Yar uwatace ta Kauye Fara su Suka Saba da wahala wani kallo ya Mani na fisgi takarduna na gudu.


Muna fita Muka koma wajen Abinci ba abinda Bamu ci ba karshe kasusuwan Naman da suke cikin romo su na koma dauka Ina dangwalar romon Ina tsotse Kashi Kamar Ina dangwalar romo da Bread,sai da Muka gama mun Mike zamu tafi cikin masu bada abinci yazo dauke da biro da takarda yace Hajiya kudin ta 🏧 card zaku biya ko cash?
Baki Muka saki nace ba kyauta bane? Yace ai oga iya na jiya dana dazu da safe shine kyauta amma daga 1pm ya koma na kudi dama na kudi ne wancan da kuka ci duk cikin na kyauta ne ga masu Interview sabo da Haka yanzu ku biya kudinku,Hamziyya sarkin tsoro tuni ta fara kuka,Farisa tace wallahi bamu da ko sisi dan Allah kuyi hakuri,nace ku taimaka Mana me yasa tun farko baku fada Mana ba?Sanda Kika zo kina ta Mana masifa da gadara me zamu ce muku sabo da Haka wlh ku biya kudi ko na Kira Yan Sanda yanzu a tafi daku.


Mutane Suka Fara tara Mana na kamfani ga Jawad Muna kallo ya tafi ko kallonmu baiyi ba Yana ji kuma,su Farisa basu San shi Zan aura ba,nace mu rufawa kanmu asiri mu basu wayoyinmu Kawai,nace kudin Nawa? Yace dubu talatin da biyar nace Haba Malam sai kace a Dubai, Securities ya Kira Suka tare kofa haka Muka cire simcard dinmu gaba daya muka basu wayoyinmu Allah yasa jagwal ne, sai lokacin aka barmu Muka tafi Muna ta zage zage, Muna ji wani yace oga ne yace ayi musu haka yanda baza su dawo ba,nace kunji balagagge ko Ashe Jawad ne ya sasu ba komai Zan rama.
Ko a gida kowacce cewa tayi sacewa akayi haka Ummiya ta siya min wata karamar washe gari.

Umma Kuwa tun daga ranar ta kora su Hafeez dakin su Nawwara a nan suke kwana matan da mazan wasu a kasa yaran suna saman bed Kamar gidan Arna haka Suka koma kwana gaba daya,Sun fadawa Jawad yace suyi hakuri an kusa zai kawo musu Aunty me kirki
Suna Jin zaiyi aure sai Murna da ihu suke Meenat har da rawa,babu Wanda Umma ta tsana a yaran irin manyan Hafeez ,Asmau da Nawwara sune Suka dan tasa sosai
Yau Hafeez Yana zaune a main Palo sai ga Umma ta fito tana ganinsa ta Fara harare harare, Zama tayi a kujera can gefe tace Kai bani remote tana tsaki, tashi yayi tare da Mika Mata ta wani fisge ta chanja chanel tana masifa kallo ma baza a Bari ka kalla in peace ba sai an Zo an dameka Kai da palonka,Su Ayanah ne Suka fito da gudu suna Wasa da su Meenat,tsawa Umma ta buga musu Kai dalla Kun cika min kunne da Kara ku tafi ku bani waje ko na tashi naci ubanku,Abba ne ya fito dai dai lokacin ya tsinci zancen Kawai shima ya kalli yaran yace wallahi uwarku zaku ci Yana zare musu Ido kunzo duk kalli yanda kuka lalata gidan nan idan Kuna gadara gidan yayan Mahaifinku ne to furniture din gidan Nan kaf bani na zuba ba kudin Umma ne yawwa sai ku taka a Sannu gidana ne kayan ciki Kuwa daidai da cokali

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login