Showing 105001 words to 108000 words out of 119289 words

Chapter 36 - Jikar Maguzawa Complete Hausa Novels Writing by Asma Baffa .txt

28 Nov 2024

7435

a kasa ya tarwatse wani ruwa me doyi da tarkace Suka bayyana,ta kallesu tana kuka tace shike nan ya karye,Sojoji Suka sake tasa keyar Gwamma aka juya da ita Lagos gidan Jawad,Farooq ne ya sallami sojojin da kudade masu yawa da Malamin yace zai neme su.


Lokacin Jawad Yana office Kawai Najla ta Fado masa a ransa tunawa yayi da irin abubuwan da ya dinga Yi Mata tun daga lokacin da ya tashi da safe yaji Kawai bai san wace ba bai gane matarsa ba,yanda take ce Masa Gwamma tace ya tuna,Kansa ya dafe a fili yace meke faruwa ne Kai...idan tace Gwamma tace sai na aikata abu,tunowa ya dinga Yi Gwamma tace Gwamma tace sai yayi abu,yace ah to wace Gwamma ne? Gwamma ya tuno Sanda ta Masa waya tace gwamma ce ya canja abubuwan gidansa da yawa,mikewa yayi zumbur tunawa yayi lokutan da ya Mari Najla yafi a irga,yace kai na Mari Babyna office ya bude ya fito da gudu gudu sauri sauri yaransa suna ta Masa Sannu Ina baya ta tasu gida kawai ko driver bai jira ba ya tuka mota sai gida Yana ta uban gudu da mota Yana cewa na Mari Najla ta da hannuna ni mene ya sameni,fuuuuuuu muka ji mota ta shigo gidan Ina shirya abinci a Dining naji mutum ya Fado daki da gudu yaci wani birki a gabana sai da na tsorata,na taka kafa Zan gudu yace wait Me tukunyar Zuma Ina kallonsa Naga ya zube a kasa Yana cewa dan Allah kiyi hakuri abinda na Miki ki yafe min ni ban San me ya sameni ba Kawai na tuna na mareki sannan in Kika ce Gwamma tace sai nayi abu,Allah ya tsinewa Gwamma ko wace ma Sai ance Gwamma Ni wannan masifa Ina nasan wata Gwamma a rayuwata bani da kowa sai ke wacece Gwamma dan Allah? Nace Kai da zaka min kishiya Tarasulu,Ido ya zaro yace ni din? nace ae yace amma Ni dai bani da mutunci ba karamin butulu bane ni,Dariya ta kamani yazo zai rungumeni nace Gwamma ta hana bata ce ba,bana son sunannan na tsani sunan Wai Gwamma ya fada jikina ya rungumeni Yana ta shishinar jikina Yana furta I miss you...I love you Baby ban Miki ciki ba har yanzu? Nace ba abinda kayi abinda sai Gwamma tace kakeyi me zaka iya,shima kanayi kana kunkuni,yace wlh badai ni ba na shiga tukunyar Zuma nayi kunkuni karya ne waye ya Isa yayiwa nan wajen kallon banza.


Tahantsi ce ta fito kenan taga Jawad ya rungumeni Yana ta faman makale min Yana bani hakuri, Tahantsi tace shegiya Kadada aiki yayi na sani ma,Kafin ta rufe baki su Farooq sun shigo tare da gwamma Yana gaba tana bayansa zungwi zungwi,da sauri na janye jikina ya sake cafkoni nace Kai mutane fa,yace Farooq ne fa,Dan uwarka ni ka rainani ko cewar Farooq,Jawad ya kalli Gwamma ya watsar Kamar bai santa ba,Nace ga babarka tazo yau baza a canja labile ba,Zama Jawad yayi ya kalli Gwamma ya kalleni yace Baby kiyi hakuri kakarku ce bana son ganinta wallahi, Tahantsi ce tace Gwamma ga shinkafa aci nasan Kadada baza ta bari ki koshi ba,Gwamma da sauri ta zabura tace na siya,Tahantsi ta bude baki tace ban gane ba to ga wake, Gwamma ta sake Zabura da sauri tace na siya, Tahantsi tace to ga kunu fa, Na siya ta furta kafin Tahantsi ta rufe baki,Nima nace ahhh ba lafiya ba wlh to ga mayafinki Gwamma tace Na siya, Tahantsi ta kwalla talla da karfi gaaaaaa kayan miya,Na siya Gwamma ta furta da sauri,gaaaaaa Citta...Na siya,gaaaaaa takalmi...Na siya...Haka Kawai Gwamma take cewa bata iya Maganar komai sai na Siya Kawai komai kace gashi tace Na siya, Tahantsi tace bayin Allah Gwamma ta haukace fa....kafin ta Rufe baki Gwamma tace Na siya da sauri Kuma a zabure,Nima na sake cewa gaaaaaa Hammata da gashinta...Na siya Gwamma tace, Farooq ne ya shiga bawa Jawad labarin duk abinda ya faru da komai,ana labarin Gwamma tana cewa Na Siya.....Na siya....Jawad yace amma Allah ya Isa wallahi Allah ya tsineeeeeeeee.... Miki Albarka....Gwamma tace Na siya....Jawad yace bazan yafe Miki ba...tace Na siya...yace tsohuwa dake ki mallakeni uban me Zan miki...tace Na siya....yace Allah ya rufa min asiri Baby bata nemeni ba da tuni na afkawa Reciever dinta...Gwamma tace Na siya....dukkan mu Muka dinga dariyar Jawad,Nace Allah ya rufa asiri taga dan kyakyawan mijina dan fari ta makale wallahi a rashin Imanin Gwamma sai ta nemeka,Jawad Yace kut ai da Anaconda sai na tsomata a Hypo wlh sai nayi wata uku a asibiti shike nan ni rayuwata tazo karshe,Dariya muke Kamar me amma Gwamma cewa take Na siya...na siya ...ko Dariya taga kayi Kawai na Siya zata ce, Jawad yace taci albarkacin ku Yan uwa ne ,nace a'a wlh bani ba Gwamma kayi Mata koma mene, Tahantsi tace a'a ai taci darajar tsufanta da Kuma jininmu sannan ga hauka ta sameta wannan kadai ya ishi Gwamma ku barta Ni Zan maidata har Kauye ta zauna har ta gangara lahira a haka me yayi saura ku barta ko tana da rabon shiriya ba a sani ba,taci darajar tsufanta,Farooq yace me za a tsinta a jikin Gwamma dama Sai wari....Na Siya...Gwamma ta furta,Kadada ce tayi sallama...Gwamma tace na Siya....Farooq yace waye ya kawoki nan yanzu nace ki fito? Kadada ta sarkafo wuyansa da hannayenta tana dariya tace Naga Shuru ne shi yasa na biyo sahu,Gwamma tace Na Siya ....Kadada ta kalleta tace Wai uban me Kika siya ne tunda na shigo kike ta cewa kin Siya kin siya, Tahantsi tace ciwon hauka ne ya Kama Gwamma fa ke baki ga yanda take zabura ba tana cewa Na siya da sauri,Gwamma ta sake cewa Na siya.....Kadada tace ae ta tabbata kin jawa kanki gaki arniya ga zalunci kin shiga uku...Na siya....Kadada tace dan Allah ku fitar da ita mene Amfanin ajiye mashirkiya a gida,Jawad yace kamar na hadiyi zuciya haka nake ji idan na ganta


Farooq ya kalli Kadadansa da mugunta yace ki dinga tausayi musamman ni ki dinga tausaya min,Jawad yayi dariya yace ai Binta sugar itace dai dai kai gashi ta saita min Kai, Tahantsi tace Yaya Jawad bikina saura wata daya fa,Yace to Allah ya nuna mana,Kadada tace za a Zama Amarya sai azarbabi Tahantsi yarinya, Tahantsi tace Yaya Farooq Zan zagi dan cikin Binta sugar gwara ka Mata fada ta rainani, Farooq yace Sorry Khadija a daina cewa Binta sugar din nan wannan sunan sai ni,Ya mike zasu tafi Gwamma ta mike zumbur tabi su Farooq tana cewa Na Siya...Kadada tace ke muje kin damemu da kin siya, Tahantsi gobe kizo da asuba ki tafi da ita Zan kulleta a daki taje can Kauye tayi ta Siya,Gwamma tace Na siya Suka hada ido da Jawad ya galla Mata harara yace ae kuje wallahi badan su Najla ba har abada kina gidan yari ba ruwana da haukarki da tsufanki,bani ba ke, Tahantsi sai dariya take Jawad Yana ta hararar Gwamma harda Mata kallon Up and down,Kadada tace Gwamma tace ta dagawa Najla gira suka Yi gaba.
Farooq yace Muna zuwa ki kulleta a daki Kar tasa cikina ya zube na tsorata da Matar nan.


Daki Tahantsi ta wuce dagani sai Jawad yace Ina yaran ne?nace sun tafi hutu gidan Abba Safna ce tazo ta kwashe su,yace uhm ta kyauta ban zata zata Yi hankali haka ba,nace sai ma kaga abin ta bani mamaki,baza ka koma Office ba? Jawad yace wanne office ai sai nayi 2weeks Ina amarci,nace amma zamuje Kano ka gaida Ummiya gobe zata fita daga takaba sai muje tare,Jawad yace sai muje Next week Inshaallah,mikewa yayi tare da Mika min hannu Wai na taso,nace Gwamma fa bata ce ba,Fuska ya bata yace bana son sunan nan Allah Ina Jin Binta Sugar tana ce Miki Gwamma tace ai nasan me kuke nufi ni dai ba dan Gwamma tace bane Allah Kika sake ce min Gwamma tace Zaki ga rashin mutunci,Dariya nayi ya dauke ni cak muka nufi part dinsa Yana cewa bari mu Kira su Hafeez muji me suke shukawa.

























AsmaBaffa🌏JIKAR MAGUZAWA🌏


111-115




NA KUDI NE
MALLAKIN JIKAR MAGUZAWA PAID GROUP






Official




By
AsmaBaffa








SADAUKARWA NE GA ZAINAB GARBA BUTALAWA








Page naku ne


Teegana's Kitchen
Auta






Ina gaisuwa mutuniyar kirki,Allah ya biya miki bukatunki
AIDA MAMAN TASNIM
















Muna karasawa Part dinsa ya ajiyeni tare da dakko wayarsa ya Kira wayar Hafeez,bugu biyu ya dauka ya gaida Jawad yace Ina Aunty? tana nan lfy tana jinka ma,ya karatu bana son shiririta da kule kulen Yan Mata nasan halinka Hafeez,Dariya Hafeez yayi yace na samu ta aure ni ba ruwa da kula Yar wani,a Ina ka samu ta auren? Yaya Baturiya ce baka sani ba,ka canja ma tun da wuri Ni bazan daura maka aure da baturiya ba idan ma zaka canja ka canja,Kai Yaya Wai Mamanka fa balarabiya ce shine ni zakace bazan auri baturiya ba,Tsaki Jawad Yaja tare da furta baka hankali bana son kule kulen Yan Mata fa na fada maka,Hafeez yace to Yaya ni ya zanyi na hakura wacce kake so shike nan,Jawad yace ae naji shi yasa Ahmad ya fika hankali shi duk irin wannan baya Yi ba ruwansa,Hafeez yaji fadan yayi yawa yace bawa Aunty wayar,Mika min Jawad yayi Muka gaisa Hafeez yace Aunty ko Kira babu shike Nan ai kin manta da kaninki a wata kasar,Murmushi nayi nace kaji da shi Muka fara hira Jawad yaga Shuru Shuru Muna ta waya Muna surutu Hafeez Yana bani labarin kasar waje Jawad ya kwace Wayar ya kashe yace Kanin Miji ne fa kiyi ta labari Yana Jin muryarki haka,Murmushi na saki nace Allah ya yaye maka yace Ameen Kuwa,yawwa iceko kin tabbatar ban kebe daki daya da Gwamma ba? nayi dariya nace ko daya yace yawwa Alhmdllh Kar naje ko mun kebe daban yanzu naji hankalina ya kwanta ki kawo min abinci,tashi nayi na kawo Masa abincin dana shirya,abincin na shiga bashi a baki Ina ci Nima har Muka koshi sannan ya hakke akaina ya fara gurzata son ransa yau nasan yayi missing dina sai dana gudu sannan ya hakura.


Washe gari da wuri Tahantsi tayi Mana sallama ita tafiya zata yi Jawad ya hada Mata Sha Tara ta arziki,Kadada harda bata dubu ashirin sannan Tahantsi tace fito min da Gwamma,Kadada ta bude Gwamma tace ke fito jiki bakikirin sai kace Dinya, Tahantsi tace mugun dinya ma,Gwamma tace Na siya...taki Fitowa,Suka buga suka raya Gwamma taki Fitowa ita taga wajen zama,Kadada tace ai Kuwa sai kin bar min gida room din Zan gyara ta jawo hannun Gwamma ta yo waje da ita, Tahantsi tace yau naga ta kaina Aliyu ne ya kirata a waya Yana tambaya kin tafi ne? Tace yanzu dai Zan tafi yace ki jirani mubi flight hanyar Nan bata da kyau Kar a jawo min asara, Tahantsi akan Gwamma ta Shiga jirgi gwara su tafi a motar haya,taki yarda ita tafi son mota,Aliyu ya buga ya buga Tahantsi tace Allah a mota Zan tafi yace to gani nan,15mnt yazo ya kaisu Tasha ya saka su a mota sannan ya biya kudin motar Gwamma tana ta faman cewa Na siya,kowa yayi magana a motar sai ta zabura tace Na siya,Aliyu Yana jikin window saitin Tahantsi yace Baby me take yi ne haka? Tahantsi tace dama a gidan mahaukata take sai ta gudu ashe Nan tayo shine akace an ganta a nan lagos nazo na dauke ta Zan maida ita can gidan mahaukata,Aliyu yace Allah ya bata lafiya karaf Gwamma tace na siya sai da motarsu ta tashi sannan ya bar tashar.
Har dare suka je gwamma tana ta faman furta na Siya, Tahantsi tace tsakar dare Ina Zan kaiki kauye ta jata Suka tafi gidan Ummiya.


Umma gidansu ta koma da Kaya niki niki tunda Suka ganta suka tabbatar an saketa duk ba Wanda ya kulata sai Inna babarta dake uwa duk inda take Uwa ce Umma tana ta faman kuka tasan iyayenta ba sauki,Inna tace bankadaddiya mu Mene ya damemu kiyi ta zama Allah ya shiryeki,Babansu Kuwa bai ce komai ba har Umma ta ajiye kayanta ta fito kannenta suna aiki ta karbi aikin taci gaba da Yi ita dai Indai zata koma gidan Abba to kowacce wahala ce zata jure ba matsala,tankade take Yi zata ci gaba da girkin data karba a hannunsu cike take da nishadi abinta.
Megari Kuwa Umma tana tafiya yace a ransa na huta haba tunda aka aureki ba hutu ba komai Ina amfaninki Yar Kurkura,Sahura ce tace Naga kana tunani lafiya? Megari ya harareta yace baza dai kiyi kawance da ita ba na fada miki matar da bata kaunar sahibinki abin Alfaharinki me zakiyi da ita,Sahura tace can da matsalarka yo ni tace bata so Ina ruwana,haushi kaji sabo da ka saketa,yace rufe min baki Yana fadan haka yayi waje.


Tahantsi Kuwa suna shiga gidan Ummiya ta gansu su biyu Gwamma tana ta zaro Ido tana kalle kalle tana furta Na Siya,Ummiya tace lafiya Kika taho da ita daga Ina kuke? Tahantsi ko Zama batayi ba sai data bawa Ummiya labarin duk abinda ya faru,Ummiya tayi mamaki tace tab ai Kuwa gobe da sassafe ki tafi kauye da ita Gwamma tana ta faman Na Siya dinta, Tahantsi ta kaita daki daban ta bata abinci da ruwa dake tana cin komai da kanta,washe Gari Kuwa da sassafe ta dauki Gwamma sai Kauye suna zuwa ta shiga har gidan,Yan gida Suka yo caa Kan Tahantsi a Ina Kika samo gwamma? Tahantsi tace a hanya Muka hadu da ita,dama haushinsu suke ji kawai Suka yo Kan Tahantsi zasu daketa suna dura Mata ashar kamar basu santa ba Kamar ba Yan uwanta ba garin za a daki Tahantsi aka tankade Gwamma ta fada Kan kujera kashin kugunta ya goce, Tahantsi sai bangaren Iyayen Ummiya ta shiga da kyar Baban Ummiya ya fitar da ita ita daga gidan yace tayi sauri ta tafi,Babar Tahantsi sai kuka take tana tsinewa Ummiya da Najla sun rabata da yarta.


Bayan sati daya yau komai normal tare muka je wajen Ummiya tun safe nida Jawad, muna Palo a zaune Sai kallona yake idan Muka hada sai ya kashe min Ido daya, da sauri nake dauke kaina, Ummiya ce ta tashi tace zaku Sha furar? Jawad yace ae Ummiya,tana fita ya kalleni yana Murmushi kasa kasa nace dan Allah karka kunyata ni, yace Gwamma tace ayi,Dariya mukayi nace to kayi din a nan mu gani,kusa dani ya matso tare da rike hannuna ya mamuke ni Yana min rada a kunne yace Wai ni har yanzu banyi ajiyar Baby ba ya furta Yana shafa cikina,nace dan Allah Ummiya zata shigo Ni wlh nayi hankali yanzu Ina Jin kunyar Ummiya,aure ya gyara ni irin kaddarar data afka min a auren nan naka dole na Kara hankali,Jawad yana dariya ya kwantar da Kansa a kafada ta sai ga Ummiya kamar an jefo ta ta shigo da sauri na matsa gefe duk na rude sabo da kunya,kaina na sosa na mike tsaye na karbi kayan hannunta na ajiye,kallo na tayi ta tabe baki tace gashi nan kusha sai me Zan dafa muku Kuma?nace Ummiya faten Tsaki da yakuwa,Jawad yace wanne faten tsaki? ban iya Sha ba,Ummiya juyawa tayi ta fita a ranta tace kaji Yara zasu maida ni Yar aikinsu,Kitchen ta Shiga ta yiwa Jawad girkinsa lafiyayye daban ni Kuma tayi min faten tsakin da nace da yakuwa .


Ina fahimtar ta gama na mike naje Zan karbo Mana mayafina na ninke na ajiye a saman Handbag dina,Jawad ya kalleni yace kin Fara Zama Yar lukuta My love,nace a hakan yace ke baki ga yanda Kika Kara wani ja da kiba ba,Ina zuwa kitchen na iske Ummiya ta shirya komai naje dauka ta kalleni tace Najla Kuma anya baki da ciki? Kunya ta kamani na juya baya da sauri nace babu komai fa Ummiya nayi maza na dauki abinci nayi palo na kaiwa Jawad,na dawo na dauki Nawa sai da Muka koshi sannan yayi Sallah yace zaije wurin wasu mutanensa a branch dinsa na Kano ya fita ya barmu daga ni sai Ummiya dama Tahantsi ta tafi makaranta ita, Ummiya tace na kusa aure,dagowa nayi da sauri na kalleta tace kwarai Kawai na hakura Zan koma gidan Babanki,nace gidan Baba Kuma haba Ummiya duk abinda ya Miki ni wlh ban yarda ba bada yawu na ba,Kawai dan Yana ta zuwa Yana daukan nauyinki sai kice Zaki koma idan ya Kuma wahalar dake fa? Ummiya ta tsaya tana kallon ikon Allah sai da na gama tace Sannu uwata,Ni gaskiya baza ki koma ba na furta Ina turo baki gaba,Tsaki ta ja Kawai ta bani waje,kujera na dakko na zauna a tsakar gida Ina ta faman Fushi Ina cika Ina batsewa har yamma tayi bayan 5pm sai ga Jawad ya dawo gidan ganina yayi Ina ta fushi bai tambaya ba yace tashi mu tafi driver zai Kai mu airport,tashi nayi na shiga ciki


Ummiya tana bedroom nace zamu tafi ya dawo ta mike daga zaune tace ki sake Masa godiya wannan irin abin arziki haka yanzu bikin Tahantsi lafiya ba ruwanmu to ya gama komai,nace to 100k na bawa Ummiya nace gashi yace kiyi cefane,Ummiya tace ke ki mayar masa wannan irin kyauta haka nace in Zaki karba ki karba ai ba roka Kika Yi ba mutum ya baki Abu Kuma ace a maida ai bazai ji Dadi ba,dadin Zama da yarki yasa ake Miki yanzu da tsiya nake shuka Masa ai bazai ma saurare mu ba amma yarki tana abin kirki a gidan Miji kice baza ki karba ba,Ummiya aike Ummiyan me hankali ce yarki hankali ne da ita,bazan mayar Masa ba idan million ya baki karba zamu yi,Ummiya tace har yau dai da ragowar son kudin nan a ranki Najla,yo wa yaki kudi kowa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login