Showing 102001 words to 105000 words out of 119289 words

Chapter 35 - Jikar Maguzawa Complete Hausa Novels Writing by Asma Baffa .txt

28 Nov 2024

7429

Ido na ganki a kwance kin tabbata a goye aka je dake gidan miji tunda ke Baki da hankali na fiki hauka,ni a Yan Iska ma ki tambaya kiji lamba ce dani,duk wani dan Iska nine maganinsa,Kuma bazan sake ki ba kiyi duk abinda Zaki yi kiyi wakar Sani Omo ma ba Sani Sabulu ba,Umma baki bude take kallon Megari taci gaba da wakarta Shuru ma....ta ishi me Hankali......












Masu sharhi Ina Matukar Jin Dadi Ina godiya


















AsmaBaffa🌏JIKAR MAGUZAWA🌏


106-110




NA KUDI NE
MALLAKIN JIKAR MAGUZAWA PAID GROUP






Official


By
AsmaBaffa






SADAUKARWA NE GA ZAINAB GARBA BUTALAWA








Page naku ne


Aunty Samira(Maman Iman)
Firdausi Husaini
Mum Ayman
Teeeema
Maryam Bello
Na'ima Saleh sheka
























Ayi mu gani Shuru ma ta ishi me hankali,Megari Yana jinta bai kulata ba har ta gaji da wakarta tayi shuru,Megari ya gaji gaskiya yanzu mararin Sahura yake yi Umma taci wurin kwana goma,zuwa yayi dakin Sahura tana gyara gadonta ya zauna yace a gaskiya bazai yuwu ba ni na gaji da kyautar nan taki nayi kwana goma Nan Zan dawo inda nafi wayo,Sahura tace yo ni da nake so na Kara maka sati Uku ma kaci Amarci,Megari yace bafa zai yuwu ba malama girki za a raba yau yawwa ya kamata na dawo na dinga gumurzu a nan akan wanne dalili da na Fara abu sai na kawo,Ni nasan malalaci ne bana son motsa jikina haka Allah ya yini bana iya aikin wahala,Barira Kuma a saukake nake kawowa ba tare da na koma doki ba bana wahala,Amma Ni na kasa ganewa lafiya nake ko ba lafiya ba daga na Fara abu sai na kawo gaskiya dole nazo nan na tantance nafi son me dadewar Ina abu wannan gashi nan yajin Ridi Zan daka nayi ta faman cin abinci dashi idan ba Haka ba Naga alama raini zai shiga tsakani,Sahura tace yajin dai naka ba citta bace da garin ganyen zogale da garin yayan zogale sai kaninfari da namijin goro za a hada da ridi ga barkono da daddawa sai hadin Maggi da tafarnuwa yace ae a daka min amma barkonon ya Zama ya ninka hadin su ridin yawa Ina amfani da abuna sai ki ganni shar,Sahura tace to sai ka Kira Barira ka fada Mata baka son kyautar kwanan a gabanta Kar tace laifinane,Megari yace tuni ma an wuce wajen,Umma tana Jin Megari ya fasa ragowar kwanakin a dakinta ta dinga murna kamar me.


Ranar da Megari ya koma dakin Sahura Wai dama Sahura ba Sanya tayi gyara na musamman,Megari yaji Sahura zakwai shike nan ta koma Amarya,gashi ya Dade Yana Jin Dadi sabanin Umma da ya fara sai ya kawo,Umma tana kallonsa washe gari ya rasa inda zai saka Sahura sai ji yake da ita,duk da bata sonsa ranta ya dan sosu tunda yace can Yana dadewa yana aiki ita kuwa ana farawa yake kawowa,suna Haka Megari shi Sam yanzu baya so ma kwanan Umma ya dawo bakin ciki yake yi,Sahura tana masa style sun Saba da juna gashi kishiya tasa ta Kare dagewa da gyara kanta tayi ta Masa salo,Sam Megari sai ya daina ta Umma gaba daya idan kwananta ne yana zuwa amma Sam bai nemanta irin da baccinsa yake yi,Ita Kuma Umma ga gajen hakuri ta matsu lallai sai ya saketa shi Kuma yace bazai saki ba,ga yaki sakinta ga wulakanci iri iri hakan yasa Umma ta raina kanta duk wani kuri da Jin Kai ita wata ce ita wayayya ce ta zubar shi a gefe ta hakura tasan an fita tun a Nan Kauye ba a je birni ba ma,Zama tayi tana tuna tsohon mijinta tana wanke wanke sai hawaye takeyi,tuna irin wulakancin data dinga Masa tana sa shi har kawaye ya musu girki,Abba ya nuna Mata so da halacci,yayi Hakuri da ita, Umma tunawa tayi yanda take cin kwalar Abba ta Masa rashin mutunci a Gaban yaransa,hawaye ya sake kwararowa Umma nadama da Dana sani suka baibayeta,ta tuna yanda ta dinga zuga Abba Yana yiwa Yan Uwansa na jini rashin mutunci iri iri har tazo Kan irin yanda Dan Uwansa uwa daya uba daya ya mutu tace baza ta rike yaran ba,ya yarda da duk wata zugarta Suka ki kula da marayu,ta dinga Zane Yara basu ji ba basu gani ba sabo da sun zauna a gidan mijinta,nata yaran suci me kyau ta dafa da Mai da yaji ta bawa Yara marayu,ta tattarasu duk yawansu a daki Daya Mata da maza Suka dinga kwana waje daya bayan tasan wasu mazan sun fara balaga haka matan ma.


Umma kanta ta dafe tunawa da tayi Sanda tace tare zasu dinga kwana in yaso mazan su lalata matan ba ruwanta,a Gaban kawayenta zata dinga wulakanta mijinta suna kallo suna zugata sai gashi yanzu Yar kawarta mijinta ke aure,Umma tunawa taci gaba da Yi tun Sanda Alhaji Nasir ya aureta tun lokacin take shuka tsiya iri iri tana zuga mijinta karshe sai data hanashi zuwa Kauye ganin Yan Uwansa sai da ta hanashi alaka da kowa ta lalata zumuncinsu, tana tunawa tayi dana sani da nadama,ta Fara kuka wiwi tace dole Alhaji Nasir bazai so ni ba bai ma kamata ya maida ni gidansa ba,ban cika mace ta gari ba,sai yanzu na tabbatar Megari ma rufa min asiri yayi,Ina so na zauna da yarana na rike yarana amma kash lokaci ya kure min ko an sakeni Alhaji Nasir bazai kalleni ba,hasali ma babu kyau kayi auren kisan wuta dan ka fita ka koma gidan mijinka,Umma hannaye ta daga sama tace Allah na tuba Allah ka yafe min,nayi nadamar halayena,ta goge hawayenta tace na hakura Zan zauna nayi ibada Zan zauna da Megari na Masa biyayya yafi min kawai na karbi kaddara duk da bana sonsa Allah ya gani amma Haka Zan zauna,duk abinda takeyi Sahura tana kallonta.


Umma tana gama nadamarta taci gaba da aikinta ta gama yau kwananta ne harda zuba uban kwalliya me gari ya Shiga da tsire yasha mamaki ganin harda zuwa kitchen ta kawo Masa abinci tana Masa Sannu da zuwa,Megari tsoro ya kamashi yace ke Barira ki kiyayeni karki kashewa Sahura miji anya ba shinkafar bera Kika zuba min ba naci na mutu sabo da naki sakinki,Murmushi Umma tayi tace wlh ko daya a baya ma nayi maka abubuwa marasa kyau kayi hakuri ka yafe min na gane ba dai dai nake Yi ba nayi nadama Kuma inshaallah bazan sake ba, Megari yace Allahu Akbar Allah da girma yake na yafe Miki kiyi Hakuri ni dai bazanci abincinki ba ban yarda dake ba,da safe in fita da bacin ranki in dawo da Yamma kice kin shiryu ta Ina Zan yarda Yar gudulle,da kyar Megari ya yarda da Umma amma bai yarda yaci abincin ba,Megari yace idan so kike na sallameki ki fada min ba sai kin Sa min guba ba,Umma tayi dariya tace wallahi bana fata ka sakeni na hakura na zubar da makamai na tsakani da Allah Zan zauna da Kai na hakura da komawa gidan Alhaji Nasir sabo da nasan ko na fita ma ba maida Ni zaiyi ba,na hakura zanyi zaman aure dakai zanyi Ibada har karshen rayuwata.


Megari yaji dadi yace lallai kinyi hankali Kuma kinyi basira Allah ya Kara shirya ki,sai lokacin suka ci Naman da ya kawo Umma harda bawa Megari a baki,Megari yayi wata shagwaba yace ah abin haka ya koma uhum ..uhum...Yana karar da Kai Umma tayi dariya Megari harda shewa kamar mace Ahayye ya rungume Umma,Umma ta dinga kallon ikon Allah Namiji da suna Hajara,ranar da Megari ya nemeta bata Yi musu ba sai ya fasa yace yau barinki zanyi ki huta,Umma a ranta Kamar an Mata bushara da Aljanna da yace bazai yi ba ranar kwanan farin ciki sukayi,Da sassafe yaje wajen Sahura yace Wai da gaske ne Barira nadama tayi? Sahura tace wlh jiya kuka wiwi ta dinga Yi tana tuna rayuwarta ta baya Nan Umma ta kwashe labari ta fadawa Megari yace haka ake so ta taimaki kanta ta zaci rashin mutunci zai bata abu,ai duk abinda arziki bai baka ba tsiya baza ta baka ba,mu haka muke maganin duk wani dan Iska tayi kuskuren zabo ni da tayi,Sahura tace uhm ai ka gyara ta kayi maganinta,Megari yau shayi da kwai aka Sha a gidansa sannan Umma ce tayi girkin,da Rana ma ita tayi girkin ta tattara kayan Megari Kamar yanda Sahura ke Yi ta wanke su ta Masa guga,da Yamma itace tayiwa yaran Megari wanka Wanda basu iya ba su biyu,tayi girkin dare suna ta hira da Sahura tana taya Umma aiki,Megari Yana ta uban sintiri Yana Shan kallo,washe gari ma haka Umma ta fita daga girki Sahura ta karba amma komai na gidan da Umma ake yinsa abin gwanin sha'awa amma duk da haka a ranta tsohon mijinta ne bata son Megari hakuri Kawai tayi ba yanda zata yi,sai da ta Kara kwana biyar zamansu normal a gidan cikin farin ciki,ta samu Megari tace zata siyo furniture a sa Mata a dakinta itama ta gaji da katifa,Megari ya tabbatar da gaske ta shirya zaman aure sai ya tashi ya Shiga dakinta tabi bayansa, Yana Shiga ya bude wata jakarsa ya dakko takarda a aljihun wandonsa ya mikawa Umma,ta karba tana tambaya ta mece? Megari yace ta saki ce na sakeki saki daya na sallameki kije ki koma wajen tsohon mijinki ki rike yaranki idan kinyi idda,Umma sai ta fashe da kuka tana Jin dadi a ranta wani bangaren Kuma ta Saba da Sahura da Megari da gidan duk da bata sonsa,Megari yace Kinga wallahi nima ba aurenki nayi da Niyyar soyayya ba,Kinga Sahura duk duniya bani da kamarta,Kawai ni nasan auren kisan wuta zakiyi da ni shi yasa na aureki sabo da na nuna Miki ba kowanne Dan Kauye bane gara Kuma ba kowanne dan birni bane wayayye,a Kauye akwai Dan birni a birni akwai Dan Kauye,kin Raina min hankali ni Megari Zaki auren kisan wuta dani kin maidani gara da mulki na da komai,Kuma naga kwata kwata kin kasa ganewa Allah daya ne shi yasa na nuna miki hanya,sabo da haka ki Sani rayuwa ko kin koma hannun mijinki kisan me kikeyi,Umma tana hawaye tace yanzu da ka sakeni ai bazai maida ni gidansa ba,Megari yace kije kiyi iddarki Ni Kuma Zan taimaka Miki ki koma ki rike yaranki duk yanda wani zai rike maka yara bai Kai ya uwar da ba,Ni dai da kike rainawa kike ganina a gara ni Kuma Zan Miki sila Inshaallah Zaki koma gidan mijinki,sabo da haka ki sani dan Adam daraja ce dashi ko Yaya yake karki dauka ke kadai ce me wayo,Umma harda durkusawa tana faman yiwa Megari godiya yace da kinbi ta lalama da tuni na sallameki sai Kika nuna min tsiwa,Sahura mace ce abar kauna ta cancanci ka sota cewar Umma, Megari yace ai ba sai kin fada min ba ni da kayata nasan abata wani abin ma Sai dare yayi dare a saman shimfida ni bazan iya hada Sahura da kowa ba,yanda ban shiga ranki ba haka nima baki min ba Sam ba kalata bace ke, ga Sahura ta doguwa ga diri har rawar India take min in tayi juyi Malam Kamar balbela, Ina Zan iya dake abu babbar halitta haka,Umma ita dai tunda ya saketa duk cin mutuncin bai dameta ba,tace Nima wani a haka a wajensa babu kamata,kaima baka min ba rago da Kai,Megari yace wallahi sai na maida ke idan Kika Yi Wasa yanzu sai ki koma matata,Umma tana Jin haka tace katifar ma na barwa yaranka wlh ta tattara kayanta akwati guda tace gasu na barwa Sahura,Megari yace ke kin Isa ki bawa matata sutura, Kinga matata da rashin sutura ko talauci,Megari ne fa ni da arzikina ba talaka bane ki kalli suturar da Sahura ke sawa da yarana,kayanki ai ba Size din Sahura bane sun Mata yawa tsayin skert dinki Kuma yayi Mata kadan idan Sahura ta saka skert dinki ai iya gwiwarta zai tsaya,Sabo da ga wada ko? cewar Umma,Megari yace wlh baza tasa kwance ba munfi karfin sutura ki bawa talakawa na Yan gari,Umma tace to tasan tabbas Megari baiyi karya ba Sahura kayan sawa ne da ita Kamar hauka Kuma masu kyau dan Megari ma baya bayar da dinkin iyalinsa a Kauye birni yake Kai musu ayi mata da yaransa sabo da idan sun saka ya gansu cass,Kuma gidansa akwai cima me kyau ba laifi gashi ba kazanta komai Chass Megari a waye yake sai iya shege kala kala,Umma dai nata ya nata ta hada ta fito,Sahura tayi Murmushi tace tafiyar ce? Umma tace wlh Allah ya nufa,nagode nagode Sahura zamu dinga zumunci idan na canja waya Zan karbi number ki,Sahura tace ba komai a yafi juna sai nazo gidan naku,Megari ya fito yace matar da bata kaunata Sahura me Zaki da ita mene amfaninta,ai ni duk Wanda baya so na Nima bana kaunarsa har abada me mutum zai fada maka ke dalla ware baza kuyi zumunci ba munafukai Megari Yana ta masifa Umma dai ta tafi baki har kunne.


Gwamma ce ta dinga rangadawa Jawad Kira Jawad dana, Yarona kana ina? Kadada ce taje jikin kofar tace idan Zaki warware ki warware a gidan Kadada kike yanzu ba gidan Jawad ba,Gwamma tana Jin ance gidan Kadada ga muryar Kadada taji sai ta fashe da kuka tace yau na gama yawo an kawoni gidan muguwa,tunda Naga babu gashin Hammatata nasan kece azzaluma tsinanniya,Duk Wanda ya aske min gashin Hammata sai yaci.....Gwamma ta dankaro ashariya ta Sosa hammatarta tace abu lagwai lagwai ba dadin tabawa fatata tayi wani iri iska ta ko Ina sanyi zai shigeni,Indai Corona ta shigeni dake za a killace mu tare munafuka Yar kaza kaza....akan ki aske min gashin Hammata ta gwara ki min kwalkwabo a kaina gwara ki aske min gashin kaina Kuma Zaki ga abinda Zan Miki,sai kin haifo dan ruwa,Kadada tana ta dariya tace ki gode ma da bamuyi Miki zigidir mun aske na kasa ba, Tahantsi tace Wai da munsha kallo sai dai muga Gwamma Fatsarrrrrrrr......Gwamma tace sai dai kuga uwarku Yan kutm.....kofa ta daka tace ni ku bani abinci yunwa zata kasheni,Kadada tace idan kina son abinci ki Fadi irin tsafin da Kika yiwa Jawad ki karya tsafin idan ba haka ba wallahi baza ki Sha ko ruwa ba a gidan Kadada kike Imani babu,idan Zaki nutsu ki nutsu ba Wasa nake Miki ba ko Zaki mutu ba abinda ya Sha kaina,Gwamma Hannu tasa tana ta faman taba hammatarta taji bakon yanayi tace ashe zaku mutu Kuwa mu zauna a haka, Tahantsi tace ba matsala Suka koma Suka zauna


Gwamma hannunta Yana cikin rigarta tana ta faman Sosa Hammatarta ta kwanta har Yamma Shuru,har dare abu ya ishi Gwamma ta mike tazo bakin kofa ta shiga bugun kofa Kamar zata ballata tana ku bani abinci Zan mutu,Kadada tace ki karya tsafinki na baki abinci kawai,Gwamma tace ai a kasan Murhu na binne a kauyenmu,Kadada tace wa Zaki wa wayo in Zaki Fadi makari ki fada sai kici abinci, Gwamma taki magana har tsakar dare,yunwa da kishirwa Kamar zata kasheta amma haka ta kwana, Farooq ba yanda baiyi ba akan Kadada ta bawa Gwamma abinci karta mutu amma Kadada taki yarda, Tahantsi ta koma gidan Najla tun dare da gari ya waye Gwamma da kyar take motsi sabo da yunwa ga fitsari tana ji ga Kadada ta dannawa Toilet dinta key Gwamma ta rasa yanda zata Yi ta tsula fitsarinta a kasa,da Sassafe ta Fara buga kofa lokacin Farooq ya tafi dakko Malam a airport,Kadada taje tace kin shirya cin abinci? Gwamma murya bata fita sosai tace asirin Yana tsohuwar makabartar kauyenmu a jikin wani kabari kuje ku cire,Kadada tace idan ba a cire ba fa? Gwamma tace ko wanne malami ne bazai iya karya tsafin ba dole sai an tono an fasa shike Nan ya karye,Kadada tana recording da waya tace dame dame Kika hada tsafin? Gwamma tace takalmin Najla nasa aka sato min a gidan Ummiya Babarta tsohon takalmi data bari,sai kayanta lokacin da kuka Zo gidan karshe Sanda zaku Musulunta lokacin nasa Almakashi na yanki gefen rigarta doguwa bata kula ba,Kadada tace to Jawad sai Kika mallakeshi ta ya? Dana hada ita Najla nasa ya manta wace a wajensa shi Kuma da na mallake shi sawun takalminsa na ebi kasar wajen na hada da dodon tsafi ya bani sa'a,Kadada tace to yanzu idan aka cire Bai karye ba sai sojoji sun kamaki wallahi Kuma na nadi maganarki kaf a waya,Gwamma tace to Dan kutmar....kije ki gwada ku gani ke kin Isa na Miki karya,Kadada taje ta hadowa Gwamma abinci sannan ta bude kofa da sauri Gwamma ta yo waje da gudu tana Fitowa ta kwashe Kadada da Mari sannan ta fisgi abincin ta hau ci sai kace kura hannunta daya Yana hammatarta tana susa,sai da taci ta cinye tace a Karo Kadada tace baza a karo ba,Gwamma ta Sha ruwa sai ga Farooq da malami,Suna shigowa Gwamma ta dinga dura musu ashariya kala kala haka Kawai,Kadada ta kunna musu muryar Gwamma abinda tace,Gwamma tace ni Jawad ne dan Uwana shine dana na daina Yan Uwa da ku ga me arziki,Malamin ya kalli Gwamma yace ke dai kinyi asara tirr da kaka irinki jininki kike yiwa haka Ina ga bare,Gwamma ta nuna Malam da yatsa ta kutuntuma Masa ashar ta gaske,Malam ya bude baki, Farooq yace yanzu ai dole Zama bai gammu ba muje ta nuna Mana inda ta binne a cire,Gwamma tace dan kaza kazanku na fasa bazan nuna wajen dana binne ba


Farooq yace ku shigo sai ga sojoji sunfi ashirin da bindigu sun shugo,Gwamma ta tsure jikinta ya fara rawa ta mike zumbur tace muje na nuna muku sai hawaye sharrr, Nan take Farooq,Gwamma,Malam da sojoji uku Suka bi flight aka tasa keyar Gwamma har Kano sai kauyen su Gwamma,suna zuwa Gwamma har makabartar ta kaisu ana binsu ana kallo Yara da manya, ta hako wani katon dan tulu irin na ruwa da tarkace a ciki,tana dakkowa ta saki tulun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login