Showing 6001 words to 9000 words out of 119289 words

Chapter 3 - Jikar Maguzawa Complete Hausa Novels Writing by Asma Baffa .txt

28 Nov 2024

7415

zanyi Alfarma daya Zan maka kayi aure cikin gaggawa ka kwashe yaran nan su koma gidanka sannan matan babanka sun ce su gidansu zasu tafi baza su rike kowa ba aure zasu je suyi har Yan yaran nan da suke Shan Nono tsige su zasu yi su bamu su tafiya zasu yi


Jawad hankalinsa ya tashi ransa Kuma ya baci da Maganar Yayan mahaifinsa ya kalle shi yace yanzu Abba Kuma ka yarda matarka tace Haka Kuma ka amince? To ya zanyi da ita muna zaune lafiya so kake na saketa munafuki,ya za ayi a daura Mata jego ita bada haihuwa ba yaranta Uku azo a bata wahala da Yara gasu nan sunfi goma Sha,Amma Abba kasan Kaka ma ta koma Labenon ni kadai a gidan a Sai Yan aiki ya za ayi na auri mace Kuma na bata jegon Yara yarinya matashiya haba Abba,kaga Jawad nima matata baza tayi Jego ba sannan bazan bari kakarka ta wajen uwa ta rike mana Yara ba ko a kasar nan take zaune bazai yuwu ba Kayi aure ka Karo masu aiki su taya matarka raino Allah ne ya Dora ma,Nima Kaka ko tana nan bazan bata jego ba bare ta koma kasarta ma ta gado,Baki Abba ya tabe yace itaku Kuma wannan Ni ba ruwana in zakayi aure kayi na baka Yan satikai ko na Kori yaran nan daga gidana,Mahaifiyar taka kafin ta rasu wani abin arziki ta shuka, Jawad ransa ya Kara baci yace ba matsala Inshaallah Zan kwashe su dama yanzu duniya ta lalace Dan uwanka Uwa daya uba daya in ka mutu bazai iya rike maka da ba,Rayuwace shima Daddy maganinsa kenan da aure aure kayi ta haifar yara gasu nan Kuma Abba kaci Amanar zumunci wlh ya mike sanye cikin danyar shadda Yana baza kamshi ya fice,Abba yace kaji shegen yaro to bazan rike ba bani nace ya tara yara ba,farko ma dana ce Zan rikesu zafin mutuwa ne yanzu Kuwa na fasa.


Jawad Yana fita compound Hafeez dan Babba da shi yace Yaya Jawad cak ya tsaya da tafiyar da yake zuwa wajen motocinsa har Hafeez ya karaso yace ka gama tafiya zaka Yi,? Jawad yace ae Hafeez ko da matsala?Hafeez yace kudin abinci zaka Bamu Umma iya yaranta ne kadai suke ci suna koshi wallahi mu sau daya take bamu abinci Kuma shima da rana Kawai kwana muke da yunwa har su Meenal,me yasa baku fada min da wuri ba? ya school fa? Hafeez yace a taxi nake zuba kowa mu tafi motocin gidan nan Umma ta Hana driver ya kaimu sai yaranta kudin hannuna ma ya Kare jiya bamu je school ba,ni kadai naje sabo da final Exam takaici ya Kama Jawad yaji tausayinsu Nan yace Kuma baza ka kirani a waya ba Zan kwasheku very soon ku Kara hakuri kunji yace to Yaya,biyoni mota suka jera har mota ya fito da dubu dari ya bashi yace ka boye ko Mene kuyi da shi idan ya Kare ka min waya a kula dasu Meenat sune Yara ku kula da komai nasu kaji, Inshaallah Hafeez yace ya koma ciki Jawad ya Shiga motarsa driver yabawa Umarni ya wuce da shi Office .


Yana Office Asif ya shigo ya zauna a kujera Yana Masa barka da aiki Jawad ya kwashe yanda sukayi da Yayan mahaifinsa ya sanar da Asif da komai ma dake tafiya,Asif yace abinda nace maka kenan Sir kayi aure komai kankantar mace tana da amfani yanda aka maka rashi aka bar maka marayu in ya kamata ace kana da Mata duk ka kwashe yaran su koma gidanka tana kula da su tare da Yan aiki suna taimaka Mata is better basai kana sonta ba a samu me hankali ko biyanta kudi ne sai kayi a aureta ta kula da Yara Kawai ta zauna tare da yaran ko da rayuwar aure bata hadaku ba sai a dinga biyanta,Jawad yace wacce marar gata ce zata yarda a aureta sabo da bautar yaran wani,ai biyanta zaka Yi ta Fadi Nawa zaka bata gaba daya daka Kai sai ita zaku San haka,Jawad yace to wa ka hango? Asif direct yace Fara Jikar Maguzawa naga tafi Najla hankali Yarinyar da muka siyi fura a wajensu da to Yar uwarta wacce ke kauyen Fara alama tana da hankali sannan suna bukatar kudi da gudu zata amince, Jawad yace amma kaje wajen Yarinyar Kai kuyi magana idan ta Amince fine cewar Jawad,Asif ya furta an gama next week zanje Inshaallah.


Umma tana kitchen ana hada abinci tare da Yan aiki tuni iya yaranta su Uku Rayyan, Affan da Nabeela Suna Dining suna breakfast da dankalin turawa da kwai ga shayi me kauri da farfesun kaji suna breakfast shima Abba Yana palonsa a can yake karyawa da lafiyayyen abinci,Kannen Jawad Kuwa tana kitchen din ta sa an dafa musu farar taliya ko wanne ta zuba plate Yar kadan kadan ta kalli me aiki tace to asabe ni nayi na Allah muna da yaji ai sai ki soya musu manja kowa ki zuba Masa ki basu suci su tafi school Kar ki manta Kar Wanda ya bude min fridge ya dauki lemo ko ruwa uban kowa cikinsu ya Sha na pampo,Asabe tace an gama Hajiya,Umma ta fice tare da haurawa saman palon Abba a can itama ta karya da farfesun da bread ga tea hadin kauri,Yaranta Kuwa tuni driver ya tafi kaisu school,Su Meenat Kuwa taliya Suka ci yaran da kansu suka shirya kansu,akwai Nawwara,Asmau da suma da girmansu zata Kai 13yrs itace ta shirya Yan yaran ta hada kansu kaf bayan sunci taliyar irin su Meenat su dama ba a saka su a school ba sunyi kankanta su biyar ne Wanda ko maganar kirki basu iya ba a gida ake barinsu Bayan an musu wanka an shirya su cikin kayan gida sai a barsu a gidan,Hafeez kafin ya wuce School sai da ya yiwa kannensa take away abinci lafiyayye Suka tafi da shi school shi Kuma ya dawo gida ya wuce bangarensu ya bawa su Meenat Suka ci sannan ya gyara su ya samu Binta me aiki duk cikin Yan aikin gidan itace kadai me tausayinsu tare da kula da lamarinsu Yaran ma itace take kula da su a boye,Hafeez godiya ya Mata ya Kara rokonta ta kula dasu Meenat kafin su dawo tace ba matsala sannan ya fita.


Umma Kuwa suna karya wa da Abba a palonsa tace yaran nan naka basu da godiyar Allah ace wai har Taliya nake sawa a dafa musu sabo da cikinsu ya dauka idan sunje school Kar su ji yunwa amma Wai Hafeez shine zai zageni su a gidansu basu San Mai da yaji ba,nace Hafeez Lagos garin arna ne kasuwanci ne ya kawo iyayenku Kar kuce lallai ku sai rayuwar Yan garin zaku dauka bai dace ba,ai sai Kuwa Asmau ta ja min tsaki Wai ai ba gidan ubana bane nan take Hajiya Barira Umma ta fashe da kuka,Alhaji Umar Dankoli Abba ya rikice Yana bata hakuri yace kiyi hakuri Hajiya Bari su dawo daga school zanyi maganinsu


Hajiya Barira tana hawayen karya tace Alhaji ka kyalesu ba komai Zan rike yaran nan idan Jawad yayi aure Naga gidansa ya hadu ka duba gidan da ya kera kamar wani Dan kwallon kafa duniya guda me zai hana mu koma can ni da yarana ya bamu part Daya ya saka matarsa a part daya da kannensa tana kula da su kaga zai Fi yarinya karama zai aura baza ta iya tarbiyyarsu ba,Abba yace gidana Honey me kyau ne Ina samu dai dai gwargwado me zai sa na koma gidan yaro da Zama Ina Yayan mahaifinsa,Amma kasan Jawad ya fika kudi ko wallahi in ya kawo wata Bamu San azabtar da yaran nan da zata Yi ba amma idan Muna kusa shike nan kasan rayuwa sai ta mallake shi yanzu Mata mallakar Miji sukeyi suna jefa shi a bala'i da asiri,Nan take Abba yace hakane Kuma bari zamu koma gidan idan zancen auren ya taso Umma Murmushi ta saki tace Alhmdllh ko kaifa shi yasa nake sonka ka waye da yawa Dariya suka Yi gaba daya


Meenat ce tayi kashi a wando ga me dan kula dasu bata kusa Umma ta hanata shiga part din,Fitowa Meenat tayi Kashi na bin cinyoyinta Lokacin Umma ta fito taji wari ta kalli Meenat tana rakubewa a bango jikinta ya hau rawa cikin maganarta da bata iya sosai ba tace dan Allah kiyi hakuyi Umma,Umma wata uwar tsawa ta buga Mata Kashi dan ubanki Kika Yi a wandon yau Zaki ci ubanki dake kabari, cikin Yan aikinta Binta ta kwalawa Kira ta fito da sauri tace wankewa Yarinyar Kashi da kayan jikinta ki gyara ko Ina data bata sannan ki kawo min ita main Palo,Hajiya me gadi ta Kira tace tsinko min bulala lafiyayya maza ka kawo min ya fita da gudu ya samo ta bishiyar dalbejiya katuwa me kauri ga tsayi ta karba tace good tare da kwalawa Asabe Kira Tace kawo min man shanu a kitchen Asabe ta kawo da sauri Umma ta dangwali man shanu ta shafe jikin bulalar da shi tana maiko tace tafi zafi ance,Asabe maida man kitchen


Kamar yanda tace haka Binta ta gama ta kawo Mata Meenat tana kuka Binta tana Jin tausayin Yarinyar ya ta iya,Meenat tuni ta fara tsaga ihu Umma ba tausayi ta cire Mata kayan da aka sa Mata Yan kanti ta bar yarinya tsirara tare da riketa Kam ta fara shafda Mata bulala tana ihu sai da ta farfasawa Meenat jiki sannan ta hankadar da ita ta Fadi bakinta ya fashe,Hajiya bulalar ta jefar sannan ta wanke hannunta tare da haurawa sama ta kwanta a makeken bed dinta bacci ya kwashe ta,Meenat tana Palo tana birgima tana ihu gashi Umma tace Kar wani me aiki ya taba ta suna ji Binta harda kuka ta fita daga part din gaba Daya sabo da tausayi.


Tana fita Jawad ya shigo gidan a motarsa ta Alfarma Fara tas yau shi ke driving Kansa sanye cikin 3qutr da t-shirt masu tsada sai shining yake Yana kamshi tun daga compound yake Jin kukan Meenat da sauri ya karaso cikin palon ya isketa tsirara jikinta yayi rudu rudu wani wajen ma ya fashe abinka da me haske ganin Jawad zumbur ta Mike tare da fadawa jikinsa tana rusa kuka,Tausayi ta bashi ya tuna matan Babansa duk da ba yaransu bane dukkan yaran sun hada sun rike babu wacce take zaluntarsu duk da kusan kowa Mamansa daban daban amma ba a samu muguwa ba kowacce Daddynsa ya aura tana rike yaran da Amana,daukan Meenat yayi Yana lallashinta


Sorry my Angel waye ya dukar min ke Haka? tana shesheka tace um..Umma ce akan nayi Kashi a wando Kuma babu me kaini toilet shi yasa,eyya sorry idan kina Jin Kashi daga yau ki fadawa me aiki kinji tace ai ban gansu ba,yace to kiyi a pow din Ayanah kinji Kai ta daga masa, ransa ya baci sosai da irin dukan da aka yiwa Meenat Yarinyar da bata San me take ba ko ba kanwarsa bace dole me Imani yaji tausayi


Yace Ina Ayanah fa? an kunna musu Cartoon let's go na gansu,dakinsu ya shiga ya iske shi kaca kaca babu me kulasu Binta ce ma take dan gyara su kullum tana kula da su duk sunyi bacci su hudu,kowacce a kasan tiles ga uban ac,Jawad Kansa ya daga sama yace dole nayi aure ko hayar Mata zanyi dole nayi,Meenat ya ajiye tare da sa Mata kayanta tace Yaya yau abinci me Dadi muka ci Yaya Hafeez ya siya Mana,Sauran yaran ne Suka tashi su ma duk Kamar Meenat suke Ayanah ce Bata kaisu ba,na kusa saku a school Kuma ai kunyi wayo murna Suka Fara suna tsalle,bedroom din ya gyara musu da Kansa ya shirya komai neat sannan ya dauki Ayanah ya Mata wanka da ruwan zafi ya ajiyeta a saman bed,ya dauki Nee'ema itama ya wanketa tas ya ajiyeta ya dauki Ameera ya Mata sannan Khairat da Meenat ya musu su biyar duk ya shirya su harda gyara musu gashi suna ta murna sunyi kyau suna ta kamshi,Binta ya Kira yace ta taho Masa da sauran a mota shi Kuma ya dauki Ayanah da Meenat ya sa su a Bayan mota,Umma ce ta fito da sauri ta karaso compound din wajen motarsa tace yanzu Jawad ka shigo baza ka tsaya mu gaisa ba sabo da Allah hakan ya dace?


Jawad ya sake daure Fuska ya ja Tsaki ko kulata baiyi ba har Binta tazo ta zuba Masa yaran a bayan mota su biyar yace da Binta Shiga gaba keda Ayanah itace karama ta Shiga Kuwa shima ya kunna mota Yaja Suka fice abinsu,Umma tace Binta Binta Zaki dawo ki sameni ku Kuma nasan bazai wuce shopping zai Kai ku ba wato ni bazai jira ya hada da yarana ba Yan guda uku sai dai iya kannensa sune Yan Uwansa zaka gani ai zaka dawo ka barsu dani wulakancin daka min a kansu Zan fanshe Dan banza marar tarbiyya duk kasar waje ta lalata shi dama dan wata sadaka yalla ne zai gaji arziki,Wai wani Yan Lebonon a gidan uban wa we shall see taja Tsaki tare da komawa part dinta.

Jawad Kuwa yawo ya kaisu suka je wuraren shakatawa da yaran tare da Binta Yar aiki 2pm suka Yi lunch a wani Eatery sannan ya musu shopping na kayan ciye ciye na Yara suka dawo gida suna parking a mota ya iske dukkan kannensa sun dawo daga school ga Salamatu matar Babansa da Aziza itama Amaryar Babansa ce Yara ne matasa Salamatu shekararta ashirin da takwas da yaronta data yaye Abeed while Aziza 24yrs take da yarinyarta Humaira itama nono take Sha amma an kusa yayeta
A Palo ya iskesu dukkan kannensa suka dinga fitowa Mata da maza suna gaisar da shi yana amsawa mazan Kuwa Hannu ya basu suna ta tafawa tsarabarsu ya basu sannan suka gaisa da matan Babansa Ya zauna Ayanah tana jikinsa Aziza tace dama wajen Abba da Kai muka zo duk da cewa kullum kana zuwa gida Kuma komai na Abinci da sutura babu abinda ka Gaza mana Alhmdllh mun gode,Jawad ya kallesu yace amma fa Kuna takaba ai da Kiran mu kuka Yi gidan,Salamatu tace a'a dole ce taso mu,Suna Haka sai ga Abba ya shigo palon


Karasowa yayi ya zauna bayan an gaisa yace Salamatu lafiya dai ko Kuna takaba zaku fito bai dace ba wallahi yanzu ana Wasa da addini ana Wasa da takaba ko Idda wanne irin abu ne zaisa sai kunzo nan,Yara ne munga sun muku yawa a halin da kuke ciki na rashi duk da nasan dan uwan nawa baza ku shekara biyu a gidansa ba tare da ya sakeku ya auro wasu kamar yanda ya Saba,ana baku ci da sha me kuke nema? Allah yasa ba kudi kuka Zo Nema ba daga mutuwa an tara muku kudin sadaka mene sai Kun dakko kafa Kun taho gidana to ku sani bani da kudin da zan baku kuci ku koshi ku zauna lafiya ga gida nan tangameme sai nan gaba za a raba muku gado..


Aziza baki ta tabe tace Allah sarki ai dai ka bari kaji me ya kawo mu ko,Umma ce ta fito tasha wanka cikin lace fari tayi kyau dama gata kyakyawa Zama tayi kusa da mijinta tana Jin zance,Aziza tace dama mun yanke hukunci kowacce gidan Iyayenta zata tafi mu karasa takaba a can,gida mu kadai kamar mayu baza mu iya ba kowa tana da iyaye gabansu zamu koma ya halatta idan da dalili me karfi mace ta fita ta karasa Takaba a gidan Iyayenta ko Yan uwanta sabo da Haka duk mun yaye Yara har Humaira na tsigeta a Shan nono zamu ajiye muku idan mun gama takaba Aure zamu Yi.


Nan take Hajiya Barira tace wallahi bazanyi jego ba bazan karba ba yawwa ba dai a part Dina ba wancan ma yaran masu girma sun isheni Allah ya gani,Abba yace to Kai Jawad kaji baza ta iya ba ya za kayi kaifa aka mutu aka barwa ka shiga Uku da kazo a Da na farko babba,Jawad cike da bacin rai yace ba damuwa ku ajiye yaran kuje,Umma Zan kawo Nanny Guda biyu masu kula da yaran kafin nayi auren, duk da haka Umma Fuska ta bata tace kayi sauri gaskiya bana son Jin kukan yaro wannan ma sun isheni mutunci Kawai nake muku,Salamatu ce ta ajiye Abeed itama Aziza ta ajiye Humaira yaran suka hau ihun kuka sabo da kiwa amma haka su Aziza suka fice tare da barin gidan abinsu duk da cewa a ransu son yaransu da tausayinsu sun cika musu zuciya amma hakan bai hanasu tafiya ba,Abba yace Kai wannan Yara da kukan tsiya suke yaja Tsaki ya tashi tare da haurawa sama abinsa,Umma ma mikewa tayi tare da kallon Humaira data Fadi sabo da kuka tana Mika Hannu inda taga mamanta ta bi,Tsaki Umma taja tace yarinya ki dinga kuka haka sai kace ana yankaki shegen Kai kamar na kwado,Jawad ka sani ko ka dauki Nanny dole fa sai kayi aure sabo da Nanny akwai mugun hali ni dai bazan iya ba amma Kai dai ka sani tana fadar haka ta wuce sashen mijinta aka bar Jawad da Yara suna uban kuka a palo.


Binta me aiki ya kwalawa Kira tare da daukan Abeed ya lallashe shi tare da mikawa Binta shi ya dauki Humaira,yace Zan biyaki kudi masu yawa duk runtsi ki kular min da kannena,Binta tace zanyi kokari duk da cewa Watarana Umma tana hanani Shiga dakin yaran,kiyi kokari dai please tace Inshaallah,dubu talatin ya bata ta karba tana godiya fita yayi direct Office ya wuce...
Hadadden Building dinsa yaje Wanda ke Lekki Lagos yana zuwa ya sallami kaf ma'aikatansa sannan ya Shiga lift zuwa Hawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login