Showing 30001 words to 33000 words out of 119289 words

Chapter 11 - Jikar Maguzawa Complete Hausa Novels Writing by Asma Baffa .txt

28 Nov 2024

7419

nace Kai Hafeez ajiye min Wayar nan na kwaceta daga yau karka sake ka bashi ita,Hafeez yace to,Waleed yace Sorry Aunty tashi nayi tare da dauke hadaddiyar ledar Ina juyawa naga Jawad a tsaye sai da gaba na ya fadi kwarjininsa yasa sai na rude amma duk da haka nace sorry for your self Waleed


Na juya Zan tafi naji su Umma sun fado Palo ba ko sallama ji nayi kawai suna ku shigo Nan ne part dinta,Yan Mata ne rida rida mashaallah ba laifi dogaye masu jiki,Umma ta watsa min kallon banza tace Ina yaran? Shuru nayi Mata tace ke akace Ina yaran matan ko kurma ce ke nace banyi Niyyar amsaki ba sabo da baki sallama ba amma suna kitchen...kafin na rufe baki Asmau ta fito tace Aunty har mun gama aikin kawo ledar a goge ta karba ko kula Umma batayi ba,Umma tayi shewa ehehehe ahayyee anki ayi sharar masallaci gashi ana ta kasuwa,anki Zama dani to gashi an gudu ba a tsira ba aikin ma yanzu kuka Fara Watarana har panties dinta sai Kun wanke,baki na saki Ina kallon ikon Allah shima Jawad bai ce komai ba gaba daya gani yake Umma ta samu matsala a kwakwalwarta


Kayan inners Kuma? na tambaya tace kwarai kuwa,nace to ai kin fadi kadan tsarki zasu min nan gaba ,ashe ke baki da kunya baki da mutunci daga kawo ki jiya yau da safe har kin Fara ciwa dangin miji mutunci yar iska, nace kin rage min matsayi ai ni na gagari Iska sai Guguwa Yar guguwa ce ni,Hafeez ne yayi magana yace gaskiya Umma kin damemu ki kiyayi zagin Aunty yawwa Suka Mike Suka fice,Jawad ta kalla tace ka gani ko ka gani ko shima ya juya ba ko magana ya wuce part dinsa,Meenat tana gwaranci tace ki daina zuwa wajenmu,kin biyo mu Zaki shanye Mana shayi da nama baza mu San Miki ba,yau shinkafa da Miya za muci harda nama
Mikewa Umma tayi tace ku taso mu tafi zaku fada musu,nace ikon Allah ke in banda kalan dangi ta Ina Kika Zama Dangin mijin Kika auri dai Dangin ke ba mijinmu daya ba ki dame ni,Umma taja kwafa tace Zan dawo gidan da Zama zamu ga karyar fitsara Ina maraba dake ki dawo ki gani idan zan raga Miki numfashi ma Sai kin kasa Shaka wlh ba wacce ta Isa a auroni ta ci min mutunci aure fa ba do or die bane,Umma tayi Saraaaaa tana kallona nace kalleni da kyau wlh Nan gaba ashariya Zaki karba ki dawo nan ki gani kullum ashar ta safe daban ta rana daba haka ta dare Kuma ba sai kin kulani ba no kullum sai nazo na Miki ita mu bala'i ba sai an shiga harkar mu ba kwata kwata muke bada ta,fadanmu baya mutuwa Allah ya kawoki ke badan kin ci sa'a ance minus dubu dari ba da yanzu ban dura Miki Yar buhu Uku kinyi gida da ita ba


Zan dawo Ni Kuma mu zuba, Inshaallah mijin naki sai ya talauce ya tsiya ce,sai Kun koma bara,sai kunzo wajena neman taimako,ko zamu tafi tsirara mun fi karfin muzo wajenki Neman taimako,Cikin Fushi Umma tayi waje tare da Yan Mata,suna fita ta juya Kan Yan matan kannenta tace baku da amfani,baku min rana ba Yan Iska masu tsoron jaraba Kun kasa tare min fada na fasa siya muku shaddar da nace Zan siya muku tunda baku da amfani kunyi wani kwashaf da fuska Dan iskan jiki ba shape Kamar ta macen alade,


yanzu Aunty sabo da Allah baki da gaskiya Ina ruwanki da su,ita ba kishiyarki ba,ita ba faccalarki ba a matsayin 'ya suke gareki ita da Jawad amma kin kasa rike marayu ke baki rike ba an kawo wata zata rike kin hana kina ta Shige musu hanci da kudundune,daga kawo Amarya jiya kin zubar da girmanki gashi ta zageki,ai babu bacin ran da ya wuce yaron da ka Haifa ya zageka ko me zakayi baza ka huce ba,wallahi shawara a matsayinmu na Yan uwanki na jini a ajiye batun siya Mana shadda ko wani abu magana ta gaskiya ki gyara,rayuwa ce fa Aunty Yara ma Ina ruwansu Kamar fa hassada kike nunawa,Cikin fushi Umma tace ae ita nake nunawa kuma bazan fasa ba tun farko na tsani baban Jawad komai a jininsa zai kare,Abba ma kina gani shi ya Masa auren fari ya bashi gida komai a kasansa yake, tun ba a je ko Ina ba ga Jawad ya shahara uwarsa wata sadaka yalla Yana ji da kyau,Kuma ya auro wata bare tambadadden yaro ba gwara da acikinku ya auri daya ba da Zan damu ne tunda mu zamu karu to wlh da kaina sai na Kori matar nan tasa Zan fara gwada makirci na sannan idan bai bulle ba na bazama dole ya auri daya cikinku ko zamu rabauta,yanzu nasan kannensa zai Fara koyawa business Yana dorasu akan hanyar arziki nawa yaran suna nan shi yasa na tsani Hafeez tsinannen yaro sai na zuga uwarsa tazo ta dauke abinta har gidansu zanje can garin


Yan matan Suka ce Allah ya ganar dake ke Aunty a hassadar taki ma ba a San a wanne layi kike ba,ae akan na rasa gwara kowa ya rasa ta bare da kowa,ai Kuwa baza ta bare da kowa ba ko kina so ko bakya so arziki na Allah ne shike azurtawa,in Banda son zuciya me Kika Nema Kika rasa?to Jawad bana kaunarsa shi da iri irinsa bana sonsu ku koma gida wlh yau sai Kun koma gida dama dakko ku nayi kuci arziki tunda Baku da kunya to ku koma kuje Allah ya kawo mutumin Kauye talaka ya Kara ta uku ko ta hudu da ku kuje ku dandana talauci tunda bakwa son karuwa ku shiga mota na kaiku tasha tunda asara zaku Mana ai Ina da Yan matan Yayan kawayena wayayyu,su dai kannen Umma suka shiga mota ta tuka zuwa tasha ta sasu a motar garinsu,tace yaran ma na fasa basu su rike a dawo min da su Asmau gaba daya na rike su a hannuna


Umma tana komawa gida ta samu Abba cikin makirci tana shagwaba da kisisina ta wani narke Masa,yace ya akayi ne uwar gida ran gida? Mene ne? Waye ya taba min ke? Umma tace ni dai gaskiya da aka dauke yaran Nan sai naji gidan ba dadi Kamar kango,nayi missing dinsu Dan Allah Abban Auta ka samu Jawad a dawo min da su Hannu na sai na rike su na yarda,min shaku da yaran nan ban San Haka ba sai da basa nan Kuma Yan Uwana sun min fada wallahi sai duniya ta zagemu ace min kasa rike yaran dan uwanka Uwa daya uba daya,an bawa yarinya raino bai kamata ba,Dan Allah ka shawarci danka Jawad Yana Jin maganarka ya dauke uba,bashi da Wanda ya wuce ka,idan ba haka ba Kuma ka nemi izini mu koma can da Zama sai na dinga kula da yaran a can.


Abba ba tauna magana ba komai yace kece ai Kika ce baza ki iya ba amma Ni nasan Yara Shiga rai ne da su to gashi tun ba a je ko Ina ba,Zan samu Jawad din nace ya dawo da su nan gabanmu,idan Kuma bai Amince ba abinda Kika tsara shi za ayi ya zanyi da sarauniyata,Umma ta shafa gemun Abba Wanda ya Zama fari fat sabo da furfura tace shi yasa nake sonka mijina,yace na sani ai ba abinda bazan Miki ba banki na tube ana sheka ruwan sama yana dukana ina Miki wanki ba anan gidan ko Mene shi Zan Miki bare wannan


Ummiya ta aurar da yarta sai ta samu nutsuwa da farin ciki tace yanzu sai naji da sauran Yara dake hannun kishiyoyi,Babana Yana China amma sai da ya Kira Ummiya,Bata San shi bane taga number kasar waje Kawai ta daga,Jin muryar Baba yasa ta kasa kashe wayar bata so Yana kiranta da aurenta amma baya ji,ita Kuma da zarar taji muryar Baba bata iya kashe Wayar takan tsinci kanta cikin nishadi da farin ciki,Bayan sun gaisa tace me ya faru? yace ba komai kiranki nayi naji muryarki Ina sonki dan Allah ki kashe auren nan ya Zama kisan wuta...kafin ya rufe baki ta kashe wayarta gaba daya ta kwantar da kanta saman hannun kujera tare da fashewa da kuka


Kadada ce ta shigo Dake ta koma wajen Ummiya da zama amma har yanzu bata Jin zata iya shiga musulunci,Ummiya ta gani tana kuka tasan ma dalili tunda taji tana waya ta ambaci sunan tsohon mijinta, Kadada tace Ummiya ita soyayya sai hakuri,Ummiya bata San Sanda ta Mari Kadada ba ubanwaye yace soyayya nake,sa'arki ce ni ku dama Yan gidanmu Kun Saba rashin kunya rashin addini hauka ne, wlh sai na maida ki kauye, Kadada dafe da kumatu tace Alhaji Usman ne ya ja min mari Yasin idan naje gidan Fara Lagos sai na rama a kanta tunda Babanta ne sila,Ummiya ta bita zata kamata tayi waje da gudu sabo ashariyar kadada duk unguwar nan an santa,Karo taci da wani mutum ta bige shi dake bai shirya ba ya fada Kan wani Mai baro,Kadada ta dafe Kai tace Sannu yi hakuri,Matashi ne kyakyawa dan chamai chamai Dan gayu,ransa a bace yace Allah ya Isa wallahi Allah ya tsine Miki albarka,Kadada ta kyalkyale da dariya tace karka Yi hakurin Nima na janye hakurin dana baka,Kato dakai kakai sa'an mijin Fara Amma kana min Allah ya Isa harda tsinuwa,tashi yayi Yana goge fararen kayansa yace bazan taba yafe Miki ba ya juya yayi tafiyarsa,Kadada tace can ta matse maka ta koma gida.


Jawad Yana fita wayarsa ta fara ringing yaga daga office dinsa ne Yana dagawa yace Salim nace bazan shigo ba Kayi abinda ya dace,Salim Wanda a karkashin Jawad yake aiki yace sir documents din jiya zaka fada min inda suke sabo da ya kamata yau na shigar dasu,Jawad ya zauna saman bed dinsa Yana magana kamar me rada ya furta ka duba saman table dina suna nan kawai ya datse kiran tare da kwanciya bai dade ba bacci ya sace shi,Sallar azahar ce ta tashe shi bayan yayi Sallah ya koma bacci har 4pm sannan ya tashi yana mugun Jin yunwa,Wanka ya sheka tare da shiryawa cikin kana Nan Kaya marasa nauyi sannan ya gabatar da sallah ya fito hayaniyar su meenat yaji a garden suna ta wasa,Palona ya shigo a nutse banji motsi ba sai kamshinsa ko Ina na gidan kamshinsa yake shi yasa banyi tunanin shine ya shigo ba,Abeed yana jikina sai nono yake nema Yana ja min riga nace Kai yaro kiyayi kanka wannan yafi karfinka sai me tafiya da kafafunsa Kai ko rarrafe baka Fara ba wannan na babban mutum ne me hakora 32,yawwa yaro Abeedi wannan sai Bayya Maganarsa naji daga sama Bayyan uban waye zai kula wannan tarkacen


Anyi ruwan sama kin bar Yara suna Wasa a garden Yana fadar haka yaja tsaki yayi waje,mamaki ya kashe ni sai kace ni na haifesu na Shiga Uku ni daga wannan sai wancan ban Saba ba,Abeed na bawa Bintu na saka Hijab na tafi garden na tattaro su Ayana Muka dawo ciki nace wanka za ayi sai azo ayi karatu,Humaira Nanny ta kawo min daga Ni sai Yan yaran su Asmau suna bedroom,Hafeez Kuwa sun fita duk yaran ne masara wayo da su Ameera,Meenat ta fisu kiriniya ita na sura nace bari a fara miki na tafi da ita bedroom,Kaya na cire mata,na daura towel nima sabo da Kar na jika kayan jikina shi yasa na cire su na daura towel,Muka Shiga na Fara Mata wanka su Kuma can Ameera da shukrah suna fada akan remote,Garin fada suka bige Kuma gaba daya suka kwalla ihun kuka,Jawad Kansa yaji da sauri yazo palon garin Zan fito ruwa a toilet yasa na subale na fadi towel ya fadi nono a waje Allah yasa daga sama ya zame kasan a rufe yake, Meenat sai dariya da tsalle kyalkyal yaro ba hankali babu tunanin ko naji rauni ita faduwar Dariya ta bata kafin na tashi ta fito da gudu jikinta duk kumfa tana kwalawa Yaya Jawad Kira,a Palo ta ganshi yana raba fada tace kuzo Aunty ta Fadi ta sake shekewa da dariya harda rawa wallahi Naga nononta Yaya Zo ka gani yafi na Aunty Nawwara,Kaga Yaya yanda ta aura towel sai ya ballo wul ta juya sama da gudu tana tafi da tsalle,Jawad Kamar shi aka gani ya zuba tagumi ga Yara wannan yayi kuka wannan ya Fadi wannan yayi ta'adi, gashi sai rike shi sukeyi suna hayewa jikinsa yace Kai bala'in duniya sai kace Yayan mage


Ina ciki na tashi Meenat tana shigowa na fara Mata bala'i nace wallahi idan Kika fada sai na zaneki da Kika fita wa Kika fadawa? Meenat tayi Miki Miki tace bance komi ba,Yaya Jawad Kawai na fadawa,babu ruwanki da naji ciwo shine kike min Dariya haka duniya tace? abinda Zaki min kenan na Fadi kiyi dariya ba tausayi,Meenat yarinya ba ganewa take ba dariyarta take boyewa ta rike Hannu na tana faman dariya Allah Aunty kece ai....ta sake kyalkyalewa da dariya nace fita na fasa Miki wankan sai dai ki zauna da kumfarki get out na koreta tayi waje da gudu,na leka na hango Jawad a Palo da yaran nace wata ta shigo layi ya ja, Kamar me screening,Ameera ta taho na Mata ta tafi bedroom,na sake lekowa nace wata ta shigo wasu Suka taho su biyu su ma,Meenat Kuwa da kuka ta koma wajen Jawad da kumfarta tace ni anki a karasa min wankan Kuma shopping za aje da su Yaya Hafeez, Jawad yace matsa ko na mareki babu me Miki wanka yau tunda baki da hankali ke da wanka sai kinyi hankali tunda Kika ce Kinga Aunty ba kaya,.


Meenat ta Kara volume na kuka tace ai ni bance ba Kaya na ganta ba Nononta na gani sai ta sake kyalkyalewa da dariya ta daina kukan tace Yaya kaga yanda ta Fadi tana gwada irin faduwar da nayi ta bawa Jawad dariya shima,yace to karki sake fadawa kowa ba kyau kinji tace to,yace jeki ki durkusa ki bata hakuri kice baza ki sake ba,ta koma da gudu tayi yanda Jawad yace sannan na Mata wankan itama,a haka dukkan su sai da na musu wanka Saura su Humaira da Abeed Yan Yara,hijab na saka na tafi karbo su Abeed Humaira tana cinyarsa na karasa gabansa ya kalleni yaso yayi dariya yace ai gwara ki jefar da towel a gaba na yanzu ke wacce rashin basira ce zata sa ki zauna da towel gaban Yara ki godewa Allah su Hafeez basa nan da yanzu sunji,baki na turo da shagwaba nace ni bani yarinya na tafi,na dauke Humaira na juya,Jawad harda cewa inda kwadayi da wulakanci,yarinya tayi auren kudi za aci bati dama kin Fara bawa Abeed nono Yana Sha tunda Kinga ba a dade da tsige shi ba nono bai isheshi ba sai na siyo Miki magani kina Sha ruwan nono zaizo tunda naji ance sun girma sai ki shayar da su sai na Kara Miki kudin.


Juyowa nayi idona ya kawo kwalla nace kaga ba ruwana da Kai babu ruwana da Kai ka daina kulani shikenan,Kuma wallahi sai dai na shayar da Kai yafi karfin Yara,Kuma Allah zai kaimu sai kazo tukun Allah yasa naga bakinka saina bara shi gida biyu ka jawa kanka,Jawad dama shi baya so tayi nishadi yafi so yayi ta bata haushi,waye zai kula wannan trash din naki,tarkace na Miki Kama da kalarki, Juyawa nayi na tafi kawai Ina saka tsiyar da Zan tsula masa


Su Hafeez ne Suka dawo abinda nace su siyo Suka siyo min,Bayan Nima nayi wanka Muka Yi Sallar la'asar,Yara ga cin abinci da tsuro tsuro in ka zuba suci kadan,anjima su Kuma dawowa haka nake fama,kwata kwata na hanasu kallon tashar cartoon sai dan lokaci kadan kadan sabo da ba birgewa bace Kuma ba wayewa bace a bar Yara basu da aiki sai kallon cartoon duty na mace ta koyawa Yara addini Susan waye Allah iya mu'amula sabo da su amfani alumma Nan gaba,ba Kawai yaro sabo da kudi ko wayewa basu da aiki sai wasanni da kallon film ko cartoon basu San waye Allah ba Basu San addini ba bare mu'amula me kyau,shi yasa nake hanasu kallo sai dai nayi ta koya musu karatun Qurani da hadisai ta sigar da yaro zai iya dauka,Susan waye Allah menene Islam Haka na Fara kokarin fahimtar dasu kafin ma su koma school.


Da dare ma yaran duk tuwo suke so manyan ne basa so Muna kitchen da su Nawwara mukayi aikin suna tayani Ina koya musu,Muka gama na yiwa su Hafeez faten doya da kifi sai Kuma kowa ya dawo shi faten yake so,yara sai hakuri haka na basu ban San ko gogan Yana cin tuwo ba ban ma kulashi da abincin ba.


Shima bai fita ba bare ya siyo yayi tunanin Zan kawo Masa tunda Ina kawowa sai yaga Shuru,shima bai Nema ba yasha Madara sa snacks, su Ayana su Uku Suka tafi can wajensa aka barni da su farida,Salma,Sultan da sauran Hafeez ma muna zaune Muna ta labari,Hafeez yace Aunty Wai Ina Yar uwar Nan taki sarkin ashariya ya sunanta ma? nace Kadad a sunanta,nace Nima na iya Kawai akwai dalilin da bana dura muku ita,a Raina kudina na tuna yace idan nayi ashar a Gaban Yara minus dubu dari,nace dubu dari ba nan take ba ni nayi ashariya Allah kiyaye,Hafeez yace Aunty Nima Yaya yace Ina gama degree zai min aure nace Kai ka kiyayi kanka kana yaronka ka fada matsala,yanzu ga misali ka gani a kaina tunda aka min aure yau kwana na daya tal amma ban huta ba tun safe nake kula da Yara gashi da dare ban huta ba,duk abinda akace ibadane ba dadi tawa kaddarar ta raino ce shi yasa Babana yace sai hakuri,Waleed yace amma ai akwai soyayya,nace Kai Waleedi kyale Harkar Nan Kawai Allah ya bamu lada,da Sanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login