Showing 24001 words to 27000 words out of 52525 words

Chapter 9 - CIMA ZAUNE Complete by Maman Afrah.txt

30 Aug 2025

1751

ce ta cire kuɗi aka siyo musu alala sannan suka samu suka farfaɗo ƴaƴan hanjin su daga doguwar suman da suka yi.

Har magriba Sagiru bai dawo ba duk da Dada shirya masa tijara tana so ya zo ta juye masa kwandon masifa da jaraba duk da Amina ma ta faɗa mata shi ba ba kanwar lasa bane ba mutunci ne ya ishe shi ba, ita ta yadda za ta samu ta ga Ɗan Ibra ma shi ne abin da ya fi damunta don duk sai sun raina kan su a kan yaudarar da suka mata duk da har lokacin ta kasa ganin laifinta a kan son abin duniya da son ganin ƴarta ta auri mai hannu da shuni.


"Dada ni gaskiya yunwa nake ji" Usai ta ce kamar ta saki kuka dama alalar da suka ci ba wani koshi suka yi ba.

"Ke dalla rufewa mutane baki ni nan da kika gani cikina tun daɗewa yake kiran ciroma kawai dai dan ba yadda zan yi ne, haka kawai ni ba da cin shinkafa da kaza ba abinci kowane iri ma ya gagareni ai wallahi na yi dana sanin auran Sagiru da Amina ta yi don wulakanci ina sirikarsa ya ganni ya wofantar da zuwana saboda takamar yana auran ɗiyata auran ma na cin amana da yaudara da karya shi ne bai isa ma ya gaishe ni bare in sa ran zai mini sannu da zuwa ya sheka yawon gararamba ya barmu da ciki fal yunwa" Ta ce har vakinta yana kumfa tsabar faɗan da take yi.

"Dada dama fa shi ko da yana nan ba ya kawo abinci na faɗa miki CI-MA-ZAUNE ne" Amina ta ce cikin takaici duk da ba laifinta bane laifin Dadar ne da ta aura mata shi a shegen san samun nata amma kuma tana jin tausayinta ga shi ita ma naira saba'in ne kuɗinta.

"Kar ki kara ɗunguma ɓacin raina Amina, kar fa ki manta gobe za a tashi da azumi to don Allah wanda ya wuni da yunwa ina zai tashi da yin azumi ni wallahi ba don na yi tijara a kauye ba da gwara na koma can duk tsiya dai ina da tsayayyan abincin ci amma kwaɗayi ya sa na zo inda abincin ma ba zan samu" Ta ce kamar ta kai wa Amina duka.

"Haba Dada ba ita ta kai zomon na fa rataya aka bata ya za kike neman ɗaura mata laifi bayan ke kika matsa mata ta aure shi ai maganin... Kafin Hassu ta kai karshen maganar Dada haushi ya sa ta kai wa bakinta bugu. Ɗif ta yi kamar an yi ruwa an tsafe. Suna nan zaune har aka fara kiran sallar isha'i babu Sagiru babu dalilinsa Dada ta kara ɗaukan dubu ɗaya da ɗari biyar su Hassu suka fita suka siyo awara ta ɗari biyar biredi na dubu ɗaya haka Dada ta raba har ƴar akuyarta.

."Haba Dada wai ya za a yi kike raba mana abinci da akuya don Allah mu bamu koshi ba ita bata koshi ba dabba ai ciyawa ya kamata a bata ta ci ba abincin mutane ba.

",Ki kiyaye ni Usai idan ba a bata abincin mutanen ba ina na ga dusa ko ciyawa ko so kike in barta da yunwa ta je ta mutu in yi asara, ni da na taho da ita ta murmure amma kina gani wuni ɗaya dk cikinta ya faɗa"

"Ke ma kan ki kin faɗa bare ita" Hassu ta ce tana danne dariyarta ganin idanun Dada duk sun yi zuru-zuru sun faɗa ga wannan uban ɗaurin ɗankwali duk ya zame fatar bakin nan duk a bushe tana ganinta ko sallar isha'i a zaune ta yi saboda yunwa wai jiri take ji ta ringa jin kamar za ta faɗi.

"Bari dai ɗiyar nan ai bansan inda Sagiru zai kai tulin alhakina da ya ɗauka yau ba" Ta ce tana jan ɗankwalinta ta gyara ɗaurin ta rufe kunnuwan ruf sai fuskar ta yi tamkar ta biri.


"Dada ko akwai zannuwa a cikin kayan naku in shimfiɗa muku" Cewar Amina tana gyara hannun rigarta da kafaɗar take zamewa.

"Ai sai ki duba ki gani ni wallahi kaɗan ma na jefar da su Allah ne kawai ya takaita mini asarw a zatona idan na zo kaya za a ɗinka mini masu yawa" Ta ce cikin takaici.

"Wai to Dada ya za a yi kwana ɗaki ɗaya da siriki, zaman mu fa kamar ba zai iyu ba da a ce kwanciyar zafi ce ma sai mu kwanta a waje" Hassu ta ce.

"Ke ni ina ruwana da wani siriki ba ciki da falo bane sa kwanta da matarsa a can ciki mu sai mu kwanta a nan ɗin in ba larura bam auren namiji da ƴaƴa ta yaya ma zan kwana a ɗakin nan bare har na kwana ɗaki ɗaya da siriki ni da na taho a niyyata a ware mana ɓangare guda mu yi yadda muke so da ɗakuna masu luntsuma -luntsuman gadaje da katifu ashe dai ɗakin da zan kwana ko albarkacin ledar tsakar ɗaki ban samu a ciki ba f...

"Gafaranmu dai" Sagiru ya shigo ɗakin yana haɗa hanya kaɗan ya rage ya faɗa kan Dada wacce ta yi saurin yin gefe guda gudun tsautsayi da ba ya wuce rana.

Baki buɗe Dada take kallonsa ganin a buge ma yake, har ya gota ta ya sake yin ribas tsautsayi ya sa ya take mata yatsan hannu har suka bada sautin kasss. Da sauri ta janye.

"Sorry Dadancy ban gani ba don Allah yaushe kika zo kin mana ba zata" Ya ce cikin muryar wanda ya sha ya bugu.

Salati Dada take jerowa tana sakewa.
.
."Amin bayan CI-MA ZAINE ne hallaw ɗan ganye mashayi kika aura ?"

"Yo ai yanzu shaye ,,,-shaye ya zama wayewa ke ma kan ki Dada na ɗakko... Ya shiga faɗa cikin maye


"Inda ranka ka sha kallo ni ina nan ina jiran ka dawo ka same ni ashe dai a buge za ka dawo kwakwalwa a hargitse" Cewar Dada ita kuma Amina ɗaki ta ja Sagirun ta dawo tana share hawaye. Dada ta buga uban tagumi abin duniya ya haɗe mata goma da ashirin.

"Ni Saude yau kaza mai tone-tone yau dai ta tono wukar yankanta, yanzu haka yaran nan Sagiru da Ɗan Ibra suka ci amata banda rigar bakin talauci da ya masa kakagida har da zuke-zuken iska yake" Ta ce tana jin tamkar ta rusa kuka don takaici.

'Dada yanzu ɗaki ɗaya za mu kwanta' Usai ta ce

"Ke ban sani ba idan kin guji wannan kin fita wajen tsakiyar gidan kina dai gani wani duk karti runtumeman kato ya isa a saka shi a lalle wato ya isa aure amma don tijara wai zai hau fooo ya yi kashi, ga kuma wani mai ruwan inyamurai da ya zo wai don tijara da ɗora hau gado wai ni zai kira da baby ' Ta ce tana rushewa da kuka ita abin ya fi ɗaga mata hankali shi ne yadda za ta kwanta da yunwa ga azumi gobe ga shi ko kyakkyawan koshi gabaɗaya an dagula mata lissafi . Ko ta kan Amina da su Hassu bata bi ba ta tashi fuuu kamar tana tafiya a saman iska ta shige bedroom ɗin tana shiga wani uban wari ya daki hancinta amma ba ta warin take yi ba ita dai ta saukewa Sagiru kwandon bala'i ko ta ji dama-dama. Ita dai Amina tsoron masifar Dada ya sa bata samun karfin gwiwar mata magana ba kar ta sauke a kanta. Bare kuma Hassu da Usai da duk yunwa ta rage musu kuzari.

"Sagiru???" Dada ta shiga kwaɗa masa uban kira kamar za ta kai masa duka. Sagiru da yake kwance shame -shame a tsakiyar ɗakin da ko arzikin shimfiɗa bai samu ba.


"Yeeeeesssss" Ya amsa dakyar saboda buguwa.

"Yassso, na ce yasso uban waye ya ce ka tafi ka bar mini ƴa babu abinci sai dare za ka dawo bayan ka tafi da kuɗin rogo amma babu kai babu rogo yanzu ka shigowa mutane gida hannu yana dukan cinya ka mana same-same? Dama kai matsiyaci ne ashe baka da ko sisi kuka yaudari mutane ka sa na ɗauki zankaɗeɗiyar ƴar na baka amma ka mayar mini da ita mai sayar da daddawa da kukar kaɗi" Ta kai karshen maganar tama wani huci kamar kubuwa ga ta rike kugu kamar mai shirin yin dambe.

"A sha ruwa ba laifi bane" Sagirun ya ce yana gyara kwanciyarsa daga kwanciyar gefe ya yi reran cikin maye ya mika hannu ya kai jikin maɗaurin wandonsa ya fisgi karamin wanda idan an ka yake sincewa. A sukwane Dada ya juya har tana yin tuntuɓe a bakin kofar ɗakin tama saurin riko zaninta da ya kwance ta ɗaura hankali tashe ta fito daga ɗakin ba shiri.

Su Amina da suke zaune sai ganin Dada suka yi bidik ta fito kamar an jefo ta ga shi ta yi shiru da jarabar da suka ji ta fara yi wa Sagirun. Babu wanda ta tankawa sai ganinta suka yi ta koma mazauninta da ta tashi ta zauna daɓas tana muzurai tare da sakin wata ajiyar zuciya.

"Ni Saude na ga ta kaina ashe ɗan duniya na aurawa Amina, yanzu a gabana shegen yaron nan yake jan maɗaurin wando yanzu ba don Allah ya sa na fito ba da shikenan tsirara zai yi" Ta ce a zuciyarta tana jin da na sani ya fi cikin kwando na son zuciyar da ta tafka ta aurawa Amina tantirin mashayi.

Haka kowa ya kwanta jiki babu kwari, ko da lokacin sahur ma ya yi babu abin da suka ci sai ruwa kowa ya sha.

"Ni dai ba azumin da zan yi gobe haka kawai na wuni da yunwa babu abincin kirki dama da yunwar na kwanta kuma in sha ruwa in ɗore azumi taɓ" Usai ta ce tana zuɓura baki.

."To kar ki yi mana duk wanda ba zai yi azumu bama wunin yunwa zai yi saboda babu wani abincin da mutum zai ci su ma masu abincin sayarwa basa yi da azumi in ma suna yi to sai dai idan satowa za ki don ni da ko biyar ba zan bayar ba. Ah to in ji ma da kuɗin da zan ke sayan abin buɗa baki tun da shi wannan saunan mijin na Amina ba kawowa zai yi ba don na ga ba niyya wai ango ya kwana da wando shi ma dai kuma gani ya kwalfi ruwa ya sha, tun da muka kawo kanmu haka za mu jure ukuba mu rungumi kaddara don ni dai a kan in koma kauye a saka ni a waka da goro da habaici da zunɗe gwara na zauna duk tsananin wuya har sai azumin nan ya kare" Dada ta ce cikin takaici.

"Yo ke ma Dada ai da kin masa wankin babban bargo da ko ina ne zai ke zuwa yana samowa amma sai da kika shiga ɗakin jiya sai gaki kin fito ba tare da kin gama masa tass ba yana baki hakuri" Hassu ta ce tana wani haɗe rai tun da basu san dalilin da ya fito da ita lokaci guda ba.


'Ta yaro kyau take bata karko, yaro man kaza ni dai in ba tsautsayin takaba auren shiɗaɗɗe ba mai zai saka na kara kaɗaicewa da fitsararran yaron can Sagiru ba, ai sai dai in mutu da yunwa a kan in bishi cikin ɗaki mutumin da kunya ta yi gabas ya yi yamma' Ta ce a zuciyarta a fili kuma sai ta ce.

"Uhmmm in ji mai ciwon hakori kuma mahakurci mawadaci" Ta ce tana tsuke bakinta ta cigaba da lazimi kafin a shiga sallah ta gabatar da sallar.

Da safe suna zaune zugum-zugum don kowa tun lokacin har sun fara jin azumin kasancewar kuma yau rana a buɗe take. Sagiru ne ya fito daga cikin kuryar ɗakin ya zo zai wuce ba tare da ya kalli Dada ba ya ce

"Barkanmu da safiya, an zo lafiya ya aka baro su, ashe kun zo yin ramadan to Allah baku ku bamu" Ya ce yana mikawa kofar ɗakin ya fara kokarin saka silifas ɗinsa da ya ji jiki tsabar takaici Dada bata ko kalli inda yake ba.

'Asararre CI-MA-ZAUNEN banza wai don mutuwar zuciya Allah bamu mu basu, wato ba ma Allah bashi mu samu ba himm ai wallahi da sake ɗaurin aure da fatalwar bazawara' Dada ta ce a zuciyarta tana jan mayafinta ta rufe fuska. Amina kuwa kai ta sunkuyar ganin Dada ta samu daidai da ita.

"Wallahi har gwara auren gidan Alhaji Sabo sau miliyan a kan auren wannan sha ka tafin, duk tsiya dai a gidan Alhaji Sabo akwai tuwon burabusko da miyar kuka amma a nan ko ina kayau " Dada ta ce fuskarta a rufe har lokacin shi kuwa Sagiru ya fice abinsa.


"Dada Allah ba don ba don ba da mun lakaɗawa Sagirun nan dukan kawo wuka da ya saitu tuni zai dawo hayyacinsa kinsan dai mu dama ya lafiyar kura bare ta yi hauka mu ba a taɓo mu bama masifa muke bare kuma da dalili da tuni mun tunatar da shi dangin wa ya aura" Usai ta ce cikin cije leɓe don ta ga abin na Sagiru ya fara wuce gona da iri.

"Wallahi dai ni ma haka na gani ai da ko yaya rainin wayon ya yi sauki amma ya yaudari mutane sannan kuma ya zo yana yi wa mutane rainin wayo" Hassu ma ta ce cikin ɓacin rai.

Shiru Dada ta yi don ita gabaɗaya ma tsoro Sagirun yake bata tantirancinsa ya yi yawa ai a kalla ko laushi ne ya yi ya ji kunyar abin da ya aikata amma ko a kwalar rigarsa uzurinsa yake hankali kwance.

"Ku ne za ku masa dukan?" Amina ta ce cikin tamke fuska.

"A'a ni uwaki ce zan masa shegiya figaggiya kar dai ki ce mini Amina kamuwa kika yi da son wannan mai idanun a tsaitsaye?" Shiru Aminar ta yi bata ce komai ba.

Da yamma Dada ta fito yin alwalar la'asar sai bin bango take kamar kadangaruwa, tsabar yadda take jin juwa tana kewayata don ji ma take kamar iska ma za ta iya ɗagata


*A je dai youtube a min like👍 a MALAMIN BOGI plsss kun ji mutanena😍🤝 ku min in ci gasar nan* 🥺

MAMAN AFRAH *09025576222*
[8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
*IMZEED VENTURE*
Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna aiyar da gwanjo me kamar sabo!
Tuntuɓemu 07077532253
Wtsapp/IG/TiktocTikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-8yWWJj3GGri&_r=1


*Ku shiga link ɗin nan ku danna min like pls*
👇👇👇👇👇
https://youtu.be/coj7sT4KTro?si=GbgZ6t-pReZv1Quf

*Marubuciyar*
*Ƙazamin miji, Malamin bogi, Bonono,* *Ruɓaɓɓiyar igiya, ƙara,in inna delu, Jalli joga, Beelal, Ƴar zaman wanka, ƴan adaidaita sahu sauran su*
*09025576222*


CI-MA-ZAUNE


NA


MAMAN AFRAH

🅿️1️⃣0️⃣


Dakyar ta kama ruwa a bayin ma ta yi alwala ta kama bango ta mike tsaye dakyar, idanun suna mata hazo-hazo .

"Yau ba za ki fita daga nan ba sai kin goya ni" Ta tsinkayi muryar sakaran yaron nan wanda ta ji Amina tana bata labari jiya wai aljannu dubu uku ne a kansa shi ya sa ma kwakwalwarsa ta taɓu dama kuma haka aka haifeshi babu cikakkiyar lafiya. Gabanta ne ya yi mugun bugawa da karfi ga shi da ta waiwayo ma sai juwa take rufe mata ido bata hangarsa.

"Ni dai ki goya ni ko a yi bikin aljannu dubu a cikin bayin nan"

Kulululuu Cikin Dada ya bada wani sauti na tsurewa da na yunwar da har zuwa yanzu ma babu abin da za su yi buɗa baki da shi don shi Sagiru ma tun da ya fita ko keyarsa basu gani ba bare har su saka ran zai kawo wani abu.

" Bikin aljannu dubu? A waran ramadanan? Dama ana samun aljannu har su yi biki da ramadan ko dan akwai musulmai ai' Dada ta ce a zuciyarta tana ba kanta amsa. A gefe guda tana ta kokarin yin addu'a a zuciyarta sai dai ruɗanin da take ciki na kasancewarsu ita da Sani ɗan Inna da kuma jirin yunwa da azumin da take ya sa idan ta buɗe idanun duhu take gani yana gilmawa, ga bayin da ɗan tsawonsa haka yake zototo kamar shantu. Dada jin takun tafiyarsa a cikin bayin da yake ko takalmi baya sakawa jin sa a daf da ita sai ta fara bin bango tana shafawa tamkar ta samu ka'aba.

"Aljannu ko saka mana kiɗa mu sha rawa" Ya ce yana mika hannu ya rafko Dada, sai a lokacin Dada ta samu nasarar buɗuwar idanunta ta sauke a kan Sani Ɗan Inna da yake sanye cikin rigunan mata kusan guda biyar ya ɗora wata kan wata da alama ma na Innarsa ce rigunan sai hula ta maza wata wacce tsabar dauɗa ta rinar da ita daga fara zuwa ruwan kasa, sai wandonsa wani jabgegen tiri kwata wanda kafar wandon ta yi a saka kafar mutane uku. Hannunsa rike da wata sharɓeɓiyar sabuwar wukar adda sai sheki take da alama ma sabuce. Wani yawu Dada ta haɗiye mukut har tana rike numfashinta na wasu sakanni kafin ta sakin numfashin da wata doguwar ajiyar zuciya.

A take ta ji ta daina jin jirin da take ji duk karfinta da take jin wuyar azumi ta tafi da shi sai ji ta yi duk ya gushe. Ta wutsiyar ido ta kara kallon addar sai kuwa ta shammace shi ta yi can karshen bayin ta je ta raɓe daga jikin bango kusa da shaddar da take mata kallon ta kusa ruftawa.

"Ki zo ga baki na sun cika suna jiran zuwanmu amaryarta ya kike gudun angonki" Ya ce yana ɗaga addar nan yake wulwulata take wani walwal ga bakin nan nasa sai zubar da yawu yake. So take ta buɗe baki ta yi magana amma ta kasa ga shi tana so ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login