Showing 36001 words to 39000 words out of 52525 words

Chapter 13 - CIMA ZAUNE Complete by Maman Afrah.txt

30 Aug 2025

1759

ji kunya ga doki har doki amma kofato na sakaina" '

Tsakar gidan tsitt kamar an yi shara kowa yana ɗaki amma ɗakin Baffalo a kulle yake. Kana ganin Sagiru za ka ga rashin gaskiya ya bayyana a tare da shi kuru-kuru saboda sai kalle -kalle yake a tsakar gidan yana son kara tabbatarwa da babu kowa domin yana son aiwatar da kudurinsa.

Sai da ya tabbatar komai yana tafiya yadda ya dace sumi-sumi ya shige wurin jigon dabobin da yake an sanya langa- langa an zagaya wurin. Sai da ya shige ya karasa wajen jigon akuyar Dada ya buɗe ledar tashi ya fito da zani ya ɗaura a kan kayan jikinsa ya kunce akuyar ya damke mata bakin ya saka wani danko ya ɗauro bakin ya kai wajen wuyanta ya ɗaure tam-tam ya ɗauke ta ta saɓa ta a bayansa ya ɗauko ɗaya zanin a cikin ledar ya goye ta tsaf tamkar ɗan mutum ya ɗauko hijabi a cikin ledar ya saka ya ɗauki ledar wacce a ciki saura dusar da Dada ta siyawa akuya ita ma a falo suka ajiye ya ɗauka. Saɗaf-saɗaf ya fito daga jigon ya fara nufar kofar gidan sai kawai ya hangi Dada ta fito daga ɗaki ta tsaya ta kafe shi da idanu da alama so take ta gane waye watakila bai mata kama da mutanen gidan ba.

"Ina wuni an sha ruwa lafiya" Sagiru da ya makale murya ya mayar ta mata ya ce yana kallon Dada.

"Lafiya kalau, ruwa kam an sha Alhamdulillah" Ta ce tana kallonsa a yadda yake gani sai yake gani tamkar dai hankalinta bai kwanta ba shi kuwa ba zai bari ta masa sakiyar da ba ruwa ba haka kawai ya gama bajat ɗinsa na zai taɓa bari ta rusa masa ba.

Digdifdif ya kuya ya yi hanyar kofar gida yana zuwa zaure da yake akwai duhu, sai ya laɓe a wani ɗan lungu don ya san da ganin matar nan za ta yi bin kwakkwafi saboda ya ga bata yarda da shi ba sai kallon rashin sani take masa.

Sagiru kuwa kamar wanda ya yi duba domin kuwa Dada bata yarda da matar ba tun da ta ga hijabi ranta bai kiyasta mata komai ba, amma dai ta san da walakin goro a miya. Saɗaf-saɗaf ta bi bayan wacce ta fita domin so take ta gane mai matar ta shigo yi gidan da har take sanɗa ko dai wani abu ta ɗauka a gidan. Sagiru kuwa dama ya gama tama ta saboda ya ji karan tahowarta..


"Ba ke mai bin kwakkwafi ba daga yau za ki daina amma bari kafin sannan in bambance miki aya da tsakuwa in nuna miki a
sirikin zamani" Ya ce yana saita inda za ta bi ya bari sai da ta dab da wurin tana cewa

"Ai sai na san wacece don daga ganinta babu l
A
alamun rashin gaskiya ne a tare da ita suka bayyana murara... Kafar da Sagiru ya sanya mata ta yi tuntuɓe ita ce ta hana ta karasa maganar tata. Jirif kake jin karan faɗuwarta, tana faɗuwa ya yi sauri yin wufff ya fice ya barta a duhun zauren.


"Amina, Hassu, Usai ku zo ku kawo mini ɗauka jama'a" Dada ta ce cikin jin zafin faɗuwar gashi kuma tana kyautata zaton babu wanda ya ji maganarta don haka dakyar ta samu hawa kan gwiwoyinta ta rarrafa ta koma cikin gidan don kar a je a latse mata kai ta shiga uku saboda bata lura da ya fice ba.

"Dada lafiya?" Su Amina da suka iyo kanta suke tambayarta ganin ta shigo ɗakin da rarrafe bayan da kafafunta ta fita. Sun ma fi zaton ko Sani ne ya mata wani abu, babu wanda ya cewa kala kawai ta karasa ta zauna tana mayar da numfashi inda su Hassu suka ɗan leka tsakar gidan amma abin mamaki babu kowa sai Baffalo suka gani da shigowarsa kenan yana buɗe ɗaki.

"Dada lafiya kuwa mai ya faru" Amina da hankalinta ya tashi ta tambaya a kiɗime don ta tsorata da lamarin.

."Anty kuma fa babu kowa a tsakar gidan sai Baffalo da shigowarsa gidan ma kenan" Usai ta faɗa tana kallon Dada.


"Kayya! Ku daina ɓata bakin ku, wata mata ce ta mini wannan aikin ni dai da na fita na hangi wata mata da hijabi har ta gaishe ni ta mini sannu da shan ruwa to ni dai ban yarda da ita ba hakan ya sa na bi bayanta in ga wacece ashe almurarar yarinyar nan tana laɓe a zauren sai da ta bari na shiga ra saka mini wata shegiyar kafarta mai kama da katako na faɗi" Cewar Dada tana matsa kwabrinta. Usai da Hassu danne dariyar da take cin su suka yi jin wai kwakkwafi ta bi.

."Dada ya za a yi gidan hayar har ki ce sai kin san waye ya shigo waye ya fita waye kuma zai a ciki ba ba kuma saboda gidan haya gidan ka zo na zo ne tun da ba mu kaɗai bane"

"To uwata Amina wannan kenan na ce miki ban san gidan haya bane?'Ta hayayyako ta

*Kar a gaji da ni a mini like a link ɗin youtube ɗin can na saman page gasar marubuta ce aka saka like ɗin ne za a tantance da shi 👍ko bakya yin youtube za ki iya taɓa link ɗin ki yi, ya Allah wanda ya yi mini domin ka ka yaye masa damuwar sa ka sanyaya ransa da frnck mai ɗorewa amin.*

09025576222



[8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
*IMZEED VENTURE*
Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna aiyar da gwanjo me kamar sabo!
Tuntuɓemu 07077532253
Wtsapp/IG/TiktocTikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-8yWWJj3GGri&_r=1


*Ku shiga link ɗin nan ku danna min like pls*
👇👇👇👇👇
https://youtu.be/LF5ghcuWK8E?si=r18ACby14OehC-P_


h: CI-MA-ZAUNE


NA


MAMAN AFRAH


🅿️1️⃣4️⃣


*SAGIRU*

Yana fita daga gidan sauri ya fara duk da ya san da wuya Dada har ta tashi ta biyo bayansa, ko da a ce za ta tashi sai dai ta nemi taimako a ɗaga ta kafin a zo a kawo mata ɗauki har a bi bayan wanda ya kayar da ita ya san lokacin ya tsira. Wajen abokinsa ya nufa wanda da shi suka yi shawarar yadda zai sato musu akuyar don hatta zannuwan da hijabin ma shi ya nemo.


"Shegen sama wai kura ta hangi biri a saman bishiya wato dai komai ya tafi kamar yadda muka tsara" Abokin Sagiru da yake zaune a benci yana jiran zuwan Sagirun ya faɗa.

"Ka bari Baabaa ai wannan matar mai shegen sa idon jaraba sai da ta yi kokwanto a kaina" Sagiru ya ce yana zaunawa a kan bancin goye da akuyar da take ta mutsu-mutsu da alama tana son yin kuka jin bakon al"amarin da ya same ta ga shi an goyata kamar ɗan mutum ga kuma an ɗaure mata baki.

"Caɓ ka ce ka tsallake rijiya da baya kuma ya aka yi ka kuɓuta?" .

."Kai dai bari ai laɓewa na yi a zauren tana zuwa na mata arangama da kafata ji kake tikkk ta sha kasa na sulale na tafi abuna"

."Kafin daidai maganinta ma kenan wa ya ce mata ana bin bayan ɓarawo in ba tsautsayin takaba auren shaɗaɗɗe ba".

"Waye ɓarawon?"

"Kamar ya to kana da wani sunan da ya wuce wannan ne yanzu ma da sata ka yi"

"Ya isheka yanzu dai ya za a yi?"

."Daga nan sai inda muka saba zuwa in mun yi ɗauki ɗam baka ajiye ba(Sata) Dama na faɗa masa za mu zo in an dace ka ga kuwa yanzu muna zuwa ciniki za a yi in kuma ka fi so a yanka ta to in je gida in samo wuka mu yi watanda da namanta ka ga kai sai ka si gidanka a dafa maka tun da kana da aure ni kuma sai in samu wajen masu tsire in sayar musu ko su mayar mini da shi tsiren"

"Amma kai dau dukan iska ne baka da hankali to in dai kai ba sha tara bane ta yaya ni da na ɗauko akuya kuma in kai naman gida ai dole ma a ɗora mini zargi"

."To mu je a ci kasuwarta"

Tafiya wajen wani wanda yake siyan kayan sata a wajensu suka yi, dama duka abin da suka samo a wjensa suke siyarwa.

"Kun iso kenan amma ya na ganku sinkin fakitin?" Ya ce yana kallonsu.

.."Ita ce fa a baya aka goya saboda gudun ɓacin rana duk da dai ana cewa akwai ranar tonuwar asiri ga mai mumafurci?"

"Sagiru wai sama kai ne da hijabi ni fa na ɗauka mace ce " Ya ce yana bushewa da dariya.

."Ah ka manta mata-maza ne"

"Mu yi abin da ya kawo mu" Abokin Sagirun ya ce.

"Gata ai sai ka mata kuɗi" ! Na sanka da siyan abu babu daraja to a kan akuyar nan dai ba za mu lamunta ba" Sagiru ya ce yana ɗaga hijabin ya juyo masa baya wai ya gani .

"Taɓ a ina ka taɓa ganin an yi cinikin biri a sama? Ai ja sakkota kawai in kare mata kallo sai in mata kuɗi" Goyon kuwa ya since zanin amma kuma abin mamaki da al'ajabi akuya ta ki sakkowa.


"Ke tun da ba bayan tsohuwarki bane sai kin sakko har da wani makalkalewa" Ya ce yana fisgota amma ko gezau bata yi ba bare ya sa ran za ta sauka.


Tun abin suna ɗauka wasa har ta kai sun yi tarayya suna kokarim sauke akuya amma gaba ɗaya kamar a jikin Sagiru aka halicce ta.

"Baabaa anya kuwa wannan akuya ce ka ɗakko?" Cewar abokin Sagiru da mamaki.


"Ubanka ne to a bayana in ba akuya ba".

"To ni dai akuya ce na ɗakko.

"Ko dai wannan mahaukacin na gidan ne aljnnunsa suka mayar da shi akuya ka goyo shi... Abokin Sagiru bai karasa ba maganar kirjin Sagiru ya yi wata irin mugun bugawa da karfi, da sauri ya saka hannunsa yana kara fisgo akuyar don so yake ya ɓanɓato ta ba ya ma fatan maganar ta zama gaskiya. Amma sai ya ji tamkar mayen karfe haka akuyar ta lake a jikinsa don yanzu ta buɗe kafafun nata ta kara kankame bayan Sagiru kamar a bayan aka halicce ta.

."Baabaa wallahi ba dabba bace da alama a bayanka ka ga yadda take kara kankameka kuwa... Tun kafin abokin nasa ya kai aya hawaye ga riga karasa maganar fitowa tuni da na sani da kuma mugun fargaba masu tsanani sun cika zuciyar Sagiru musamman da ya ga abokinsa da wanda yake siyan kayan sata idan sun samo sun fara ja da baya alamu sun nuna suna son nesanta kanau daga gare shi saboda su tsorata. Wani abin tashin hankalin ma yadda Sagiru ya ji akuyar ta kafa bakinta a kashin hannunsa wanda yake a baya tana gwagwiya idanu ya zaro.


."Baabaa kur'ani nono take nema ka ga yadda take kafa maka baki kuwa?" Cewar abokin Sagiru yana zare ido kamar wanda ya yi wa sarki karya.

Kafin ya yi wani yunkuri sai gani ya yi da abokinsa da mai siyan kayan sun dare ɗaya ya kama hanyar gabas ɗaya ya yi yamma bai gama tabbatar da yana cikin tashin hankali tsamo-tsamo ba sai sa ya ji akuya ta buɗe baki cikin ɗaga murya tana cewa" Ku bil adama ku tsaya mu mana" Kafin akuyar ta gama maganat fitsarin da Sagiru ya saki daga tsaye ya gama wanke kafafunsa su kuma jiyo muryar akuya tana magana da wata murya kamar ta tsahuwa tukuf sai kowanne ya kara cikawa wandonsa iska ko waiwaiye basa yi bare Sagirun ya sa ran za su tsaya shi ga shi kuma wajen ko alamar mutane babu da yake dama wajen sayan kayan satar a inda babu idanun jama'ar saboda tsaro ba don tsoro ba.


Kuka yake tun karfinsa hawaye yana zuba fitsari ma yana zuba ya ma rasa dalilin da ya sa fitsarin ya ki daina zuba sai dai ya alakanta hakan da cewa ruɗun sa yake ciki ne ya ma kasa dakatar sa shi tun da ya san dai shi ma bai san ya aka yi yake zubowar ba.

"Mu ma mu bisu mana" Ya ji akuyar ta sake cewa bayan ta ɗauke bakinta daga jikinsa da yake da ta yi maganar ɗazu sai ta maida bakin ta cigaba da gwagwiya don shi yanzu ya san ma ta yaga masa rigar da yake yana jin alamar hakoranta a jikin fatarsa. Bare wannan maganar ta kara tsorata shi don tun da yake bai taɓa jin inda aka ce akuya ta yi magana ba ko da a labarai kuwa kai shi ko a labaran nan da ake cewa inda ranka ka sha kallo bai taɓa ji ba sai yau ga shi ya faru a kansa. Ba komai yake kara hauhawar tashin hankalinsa ba sai ganin shi kaɗai babu kowa bare ma yanzu ya san va akuya bace tun da da kunnuwansa ya ji ta ce musu bil adama.

"Mu tafi mana" Ta sake faɗa bata san shi firgice take saka shi ba idan ta yi magana so yake ya yi dabarar yadda zai ɓanɓareta daga jikinsa ma amma gabaɗaya kansa ya kulle ya ma rasa tunanin da zai tabbas ya yi da na sanin sato akuyar nan ga shi nan shi bai ci nanin- nanin ba nanin tana neman cinsa da ya san haka ne da a hannu ya kamo ta, da yanzu ya sake ta ya zura da gudun yanzu kuwa ko da ya gudun suna manne kamar tif da taya.

"Kawai ka fita a guje da kanta za ta gaji ta sake ka, ka huta da alakakai" Wani ɓangare daga cikin zuciyarsa ya kissama masa wannan shawarar da yake gani tamkar gurguwar shawara ce amma dai zai jaraba.

Sai da ya saita hanyar da zai yi kawai sai ya shiga yin girgiza da karfi don ganin akuyar ta fita amma ina abin ya ci tura! Zanin jikinsa ya tattare wanda ya ɗaura a saman wandonsa don yin basaja da zai saci akuyar, yana gama tatrarewa ya zuba a guje saboda yana ganin hakan ba karamin mafita bace don kar ta ga babu idanun mutane kar ma ya je ta cinye shi da wannan gwagwiyar saboda sannu-sannu ba ta hana zuwa don a haka sai ta cinye shi ko ma in ta ga babu kowa ta gudu da shi tono yadda Sani ɗan Inna yake cewa zai sa aljannu su tafi da mutum hakan ba karamin tashin hankali ya kara saka shi ba yana jin zunzurutun damuwa.

Cike da alhinin halin da ya saka kansa a sanadin son zuciya yake falfala gudu, jin hijabin wuyansa yana shake shi ya cikwikuyo shi ya yi jifa da shi yana kara wutar gudun sai kafafunsa yake hanga tsilli-tsilli don takalminsa ma tuni ya cire shi ya baro shi a can.


Yana cikim gudu zanin ya taɗe shi, rigif ya zube a cikin caɓalin wata makwaranyar wani gida kasa tashi ya yi yana tuno rashin imanin da ya yi wa tsohuwa ɗazu wato sirikarsa ya saka kafa da gangan ya kwalfe ta yanzu shi ma ga faɗuwar ta zo kansa tabbas ya ji faɗuwar musamman ma yadda kirjinsa ya bugu da kuma yadda ruwan kwatar ya fallatsu a fuskarsa har bakinsa. Ammin duk faɗuwar nan da ya yi bai ji alamar akuyar za ta sauka ba sai ma kara kaimi da take wajen gurgurar bayan nasa. Dibara ce ta faɗo masa ya saka hunnunsa ya cire zanin jikinsa yana daga kwance rubda ciki don a rubda cikin ta faɗi. Kwantawa ya yi reran ya zamana yana kwance a kan akuyar ita tana kasa ya shiga murtsuka bayan nasa a kan akuyar ransa fari kal har wani murmushin jin daɗi yake da ketar ya samu hanyar da zai rama fargabar da ya shiga a dalilinta, ai yana jin ta fara kukan su na akuyoyi meeee ya ji a ransa ukubar da yake bata tana tasiri.

."Sai na kashe ki murus har lahira" Ya furta a fili bai gama tantancewa ba ya ji ta daddage karfinta ta yanka masa wani uban cizo.

A kiɗime ya mike zaune daga kwance da yake, babu zato ta sake sakar masa wano cizo wanda ya yi kiyasi tun da ya zo duniya bai taɓa jin cizon wannan mai masifar zafi da raɗaɗi irin wannan ba.

Da mugun sauri sa tsananin gigicewa ya mike tsaye har santsin wajen yana neman ya kayar da shi amma a haka ya tashi ya yanka a guje. Shi kansa bai san ya karaso inda da jama'a ba sai da ya ga duk inda ya gifta yana jin ana cewa.

"Jama' a a kauce ga mahaukaci nan" Shi dai ya ga mutane suna ta gudu to sa yake shi ma a matse yake da ya fita daga ukubar da yake ciki ba wacce yake ganin gwara mahaukaci sau dubu a kan damuwar da yake ciki. Shi bai ma san da shi ake magana da aka ganshi da akuya a goye a baya daga shi har akuyar kamar sun yi wanka da taɓo ga shi ko takalmi babu a kafarsa kuma ga akuyar tana ta cewa meeee.


Majalissar su da suke zama ya nufa don ya san tabbas zai samun CI-MA-ZAUNE ƴan uwansa. A guje ya shawo kwanar bai ma lura ba kowa a wajen ba sai da ya zo dab da wurin wani uban birki ya ja yana sakin wani marayan kukan tausauyin kansa.


"Ka koma gida Amina za ta san yadda za ta raba ka da ita" Kai ya shiga girgizawa don ba ya so ya je gidan saboda shi ma ya san ko giyar wake ya sha ba zai maido dadar kuɗin ba.


Kara kwasa ya yi a guje

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login