Showing 42001 words to 45000 words out of 52525 words
yana ji tashin hankalin kalamanta da ta faɗa a ganinsa kenan ma ba tabbas idan an je gidan malamin babu tabbas za a raba shi da akuyar.
"Na shiga uku na! " Ya furta a zuciyarsa gabansa yana tsananta faɗuwa. Shi kuma abokin nasa sai kaimi ya kara wajen sauri yana so ya wuce Babar tasa don yanzu mugun tsoron akuyar bayan Sagiru yake don gani yake kamar za ta iya yin tsuntsuwa ta koma nasa bayan.
"Ahmadu ka tsaya shi ku tafi tare mana da abokin naka, ka wuce shi ni kuma ina so ake sauri sa ni ko bayanka zan dawo ko na Baba tun da na ga duk kun wuce mu" Suka tsinkayi ajuyar nan tana faɗa.
Kukuiiiit wata bahaguwar tusa ta kwacewa Ahmadu don shi ko Sagiru bai fiya kiransa da sunansa ba sun fi kiran junansu da Baabaa amma kuma ita ga shi ta kira shi da sunan nasa kenan dai sha'anin aljannu sai su.
Ɓeeetɓaɓetttt Baba ma ta saki tata iskar tusar guda biyu a jere jin an ce ita ma za a dawo nata bayan taimakon da Allah ya mata ma tusar iyakar kumnuwanta karan ya ziyarta bai kai kunnuwan su Sagiru ba don ko da ya kai ma ba lallai tashin hankalin da suke ciki ya bari su gane daga inda karan yake ba.
Fuusssssssss Sagiru ma ya saki karan tashi tusar saboda tsoro cikin su yake sace iskar tusa don gabaɗaya sun tsure.
"A'a ranki ya daɗe gaot"
(Akuya) Shi sai ma ya ji ya manta sunanta da hausa shi ya sa ya faɗa da turanci.
"Na... tsaya... shi ...mu tafi... tare" Ya ce cikin ciccira maganar saboda tsoro da ya ji ya kara baibaye shi na ambaton sunansa da kuma na cewa za ta dawo bayansa.
.
'Innahu min sulaimana wa innahu bismillahir rahmanir rahiiiiiiiim" Baba ta ce a zuciyarta ganin ta jefa kanta a wani halin tana ganin in har ita akuya mai magana ta makalewa to ba ma lallai ta samu karfin halin taka ko da kafarta ba saboda tsoro.
A fili kuma sai ta ce
"Ai ba sai an kai ga haka bama ai dama ni taimakon su ne zan yi amma in kika ce in koma gida sai in juya yanzu- yanzu sai su tafi su kaɗai" Baba ta ce don ganin ta tsame kanta daga cikin wannan bala'i don bata taɓa zaton abin zai kai har haka ba da bata shiga ba yanzu ne take jin ba lallai bane ma akuyar ta yarda ta fita tun da gashi har tana ikirarin komawa bayan wani.
"Don Allah Baba kar ki mana haka" Ahmadu ya ce yana danne kukansa don ya fara tunanin in aka bar su su biyu to tabbas in bata zauna a bayan Sagiru ba tabbas bayansa za ta koma in kuma da Babar ne watakila tsautsayin takaba auren shiɗaɗɗe ya sa akuyar ta koma bayan Babar tasa.
"Ku taimaka mini" Cewar Sagiru da yake ɗaga kafarsa dakyar sanadin sanyin tsoron da jikinsa ya yi.
"Nooooooo ke ki shiga gaba, su sai su jeru mu tafi tare ke ai sai ki mana jagora" A kuyar ta faɗa da wata siriryar muryar matashiyar mace a maimakon muryar da take magana da ita kamar ta tsohuwa.
."An gama, an gama, an gama" Su duka ukun suke haɗa baki wajen faɗa don yanzu kuma abin ya shallake tunanin su.
Baba tana gaba amma ba wanu tazara ta basu sosai ba da yake kuma layin gidan Malam Kailun a can karshen sama layi yake kuma shi ne gida na karshe don wajen ma babu gidaje sosai kasancewar sabuwar unguwa ce wannan ya sa ma yanzu duk babu mutane a hanyar da suke bi.
Ahmadu na dawowa kusan Sagiru a ɗarare babu zato ba tsammani ya ji kofaton kafar akuyar nan a jikinsa wato ta sakalo bayansa ta rungumashi a jikin Sagiru ta haɗe su a wuri ɗaya sun zama tamkar tif da taya ya kasance tana bayansu su duka da yake kafafunta huɗu biyu na kasa ta makalawa kowannen su ɗaya biyu na sama sai ta sakala ɗaya a wuyan kowanne ta zamana a tsakiya kanta yana a tsakanin kawunan su kamar an ce Baba ta waiwayo sai kuwa ta yi arba da wannan badakalar.
*MUHIMMIYAR SANARWA* 👇👇👇
*Assalamu alaikum duk me karatun littafin CI MA ZAUNE ya tsaya ya karanta wannan saƙon ya fahimta. Littafin nan 500 ne za a gama free pages a page 18 sai dai akwai zaɓi biyu ga mai son karantawa har ƙarshe. Ko mutum ya biya ,500 ko kuma ya mini magana in bashi link ɗina ya mini LIKE na gasa idan ya yi zai sa mutane biyu su mini a tura min screen shrt ta PC sai in saka mutum a paid grp ya karanta idan kuma knsan kn yi mini dama to za ki sa mutane biyu su mini sai in saka ki a paid grp amma sai kin fara mini magana a PC na miki bayani. Wanda kuma 500 zai saka zai biya ta asusun faiza abubakar 9030283375 opay shaidar biya ta 09025576222* *Wanda za su yi like ma ta wannn no za su min magana*
[8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
*IMZEED VENTURE*
Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna aiyar da gwanjo me kamar sabo!
Tuntuɓemu 07077532253
Wtsapp/IG/TiktocTikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-8yWWJj3GGri&_r=1
CI-MA-ZAUNE
NA
MAMAN AFRAH
🅿️1️⃣6️⃣
SANARWA
*Assalamu alaikum CI MA ZAUNE 500 ne za a gama free pages a page 18 sai dai akwai zaɓi biyu ga mai son karantawa har ƙarshe. Ko mutum ya biya ,500 ko kuma ya mini magana in bashi link ɗina ya mini LIKE na gasa idan ya yi zai sa mutane biyu su mini a tura min screen shrt ta PC sai in saka mutum a paid grp ya karanta idan kuma knsan kn yi mini dama to za ki sa mutane biyu su mini sai in saka ki a paid grp ki fara min magana PC na miki bayani. Wanda 500 zai saka ta asusun faiza abubakar 9030283375 opay shaidar biya ta 09025576222* *Wanda za su yi like ma ta wannn no za su min magana*
Wani yawu Baba ta haɗiye mukut tana jin wani tsoro yana baibayeta, tabbas yau suna ganin harkalla. Sauri-sauri ta fara don ta matsu su karasa gidan Malam Kailu in ya so su ta bar su a can ta yi tafiyarta dama ai duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa yake duka.
Sagiru kuwa da abokinsa ba sai an faɗi yanayin da suke ciki ba duk da Sagirun ya ji daɗin yanzu dai ba shi kaɗai ne a makale a bayansa ba yanzu kam sun zama su biyu amma duk da haka fargabarsa ta karu don yanzu ya tabbatar akuyar nan ba da wasa yake ba shi ba don kar ya musu baki bama da sai ya ce ba lallai ta yarda ta ɓanɓaru daga jikinsu ba amma dai bahaushe ya ce wai sai an gwada a kan san na kwarai. Ahmadu kuwa faɗa ma ɓata baki ne don Allah kaɗai ya san halin da yake ciki ji yake ina ma ya buɗe idanunsa ya ga mafarki yake ba da gaske bane.
"Baba saurin naki ya yi yawa fa" Baba da ta ɗan dage da sauri-sauri gudu-gudu ta tsinkayi muryar akuyar nan ta sake magana sai dai wannan karon da muryar yara ta yi maganar.
Baba kuwa bata san lokacin da ta ja wani uban burki ba, tamkar wata mota ko machine, bata tsaya a nan ba bayan ta ja birkin sai ta shiga yin da baya da baya don gudun yin laifi don duk abin da zai sa a ce akuyar nan ta yi kawanya da ita da su Sagiru to ba kaunarsa take ba, sai da ta ga ta kusa zuwa inda suke sannan ta fara wata tafiya mai kamar sanɗa tamkar wanda take tsoron wani ya ji takun tafiyar ta
Ahmadu kuwa bakinsa ne ya shiga kaiwa da komowa yana ta addu'ar da ko da za a saka masa wuka a makoshi bai san mai yake karantawa ba ya dai san yana motsa baki ne kuma motsa bakin da yake na neman tsaru ne daga ukubar wannan akuyar saboda shi idan ya ji ta yi magama da muryar mutane ba karamin ruɗani yake shiga ba musamman da ya kasance tana yin muryoyi idan ta yi ta tsofaffi sai ta yi ta ƴan mata yanzu kuma ga shi ta yi muryar yara. Sagiru kuwa shi zuwa yanzu ma bai san a halin da nasa bakin yake ba abu guda ya sani shi ne yana nin yadda bakin nasa yake ta kaiwa da komowa yana jin yadda yake motsawa.
Haka dai ake tafiyar marar daɗi babu daɗaɗawa har suka kusa isa gidan Malam ɗin kowa yana tafiya a sannu-sannu gudun yin gagarumin laifi. A lokacin ne suka ji wani.
Dururumdummmm wannan karan ne ya sanya Baba ta sheka a mugun guje ba tare da ta shirya ba, gudu kawai take zabgawa abin ka dama da wanda yake cikin tsoro, ba iya Baba kaɗai ba hatta Sagiru da abokinsa sun razana musamman ma su da sula ji karan a dab da su wanda karan ya fi musu kama da na bindiga don su ma sun so zabgawa da gudun amma sai suka ji an kara manna su a waje ɗaya don su hatta kunnuwan su sai dai suka yi dummm saboda karan.
Baba babu zato babu tsammani sai ji ta yi ana mayar da ita baya, kafin ta yi yunkuri sai ganinta ta yi a wajen su Sagiru. Da aka kara sakin wani karan sai kawai aka kasa tsere daga Baba har su Sagiru suna cikin gudun ne suka ji tamkar an rike musu kafafun don babu wanda ya samun karfin gwiwar ko da ɗaga kafa ɗaya ne.
"Haba ku kuwa sai an muku abu kuke ganin ba a kyauta muku ba ko? Haka kawai saboda na saki tusa sai kuke tsorata a kan mai daga tahowar mu nan a hanya kowanne a cikin ku sai da ya saki tusa son ransa wa na hana ko wa na toshewa kofar fitowar tusa? Sai ni don na yi za kuke fita da gudu to tusar ƴan shayi ce(Kaciya) Kowa ya san dai ƴan kaciya da sakin tusa to ni ma ɗan shayi ne Baba ko ƴan shayi basa tusa?" Akuyar nan ta faɗa da muryar wani katon gardi.
"Su...su...su...na...yi" Baba ta ce a ciccire saboda gabaɗaya ta razana yanzu duk uban karan nan da suka ji tamkar an saki booom amma a ce wai karan tusa ne wannan tusar ma ta ƴan shayi wannan karan ma bai yi kama da ta yara ba.
"Sagiru da Ahmadu ku lokacin da aka muku shayi(Kaciya) Bakwa tusa?" Muryar gardi mai kamar ka zura da gudu ta tambaya.
"Wallahi muna yi" Suka haɗa baki wajen faɗa tamkar za su fashe da kuka.
"Yawwa ko da na ji to daga yanzu kar kowa ya kara tsorata da karan tusa ta" Ta ce su sai yanzu ma suka ji warin tusar duk ya buɗaɗe hanyar da suke.
A haka suka tafi kowa a firgice har suka je kofar gidan Malam wani abu bai sake faruwa ba.
"Ku jira in yi iso" Baba ta ce tana kallon Sagiru da Ahmadu ga kuma kan akuya a tsakanin kawunansu.
Babu wanda ya samu zarafin bata amsa, cikin gidan ta shiga tun daga zauren gidan ta ci karo da cincirindon mata a zazzaune da alama a layi suke kowa tana jiran layinta ya zo da yake lokacin ma an yi sallar isha'i tun daɗewa, haka ita ma ta bi sahu ta zaune ta kifa uban tagumi haka suka ringa shiga suna fitowa da ɗan kullin magani sai da matar da ta fito ta karshe wacce daga ita sai Babar ta ɗan taɓa Babar ta ce
"Baiwar Allah layinki fa ya zo amma na ga kamar ma baki sani ba"
"Wallahi kuwa ban sani bama"
"Allah sarki wannan daga gani kina cikin ukubar kishiya, irin kishiyoyin nan masu hana wali" Cewar matar tana yin gaba.Baba kuwa bata tanka mata ba don da ta san dalilin da ya saka ta a halin da take ciki da bata kwatanta da kishiya ba don ai kishiya ita bil adama ce amma karo da aljani ba daɗi take raya hakan a zuciyarta ta je bakin kofar ta rafka sallama amsa mata aka yi ta bankaɗa labulan ta shiga mutum ne wanda a kalla zai kai shekaru sittin yana sanye da shadda ruwan omo (Blue) Sai wani uban rawanin da aka riɓa hiramin biyu sai kuma wani jan hirami da yake shimfiɗe a kafaɗarsa, ga wani faranti mai kasa da kuma kwarya ita ma kasarce a ciki.
Bayan sun gaisa ko ma a ce bayan ya gaishe ta tun da ita gabaɗaya ma firgice ya sa ta manta ana wani abu wai gaisawa a duniya tun da take bata taɓa shiga tashin hankali mai tsoratarwa muraran ba irin na yau a ce akuya tana magana irin ta mutane kuma da kalolin muryoyi.
"Wallahi malam wannan ce matsalar...
"Ai da baki ɓata bakin ki ba wajen bani bayani don muna da labarin zuwanku da kuma abin da zai kawo ku an faɗa mana shi dalla-dalla, ai karyar aljani wallahi karyarsa dubu, karyarsa ta sha karya don buhun ubansa ni malam kare kukan ka na ci dubu sai ceto ko kukar bulukiya ce sai mun yi maganinta bare wata karamar alhakin aljana da take zama akuya, na bari ne dama ki faɗa da bakin ki kin san ƴan magana sun ce waka a bakin mai ita ta fi daɗin ji" Malam Kailu da ya yanko wata uwar karya ya faɗa yana kallonta don babu wani labarim zuwanta da kuma abin da zai kawo su da ya sani kawai dai ya faɗa ne don a kara yarda da maluntarsa to in ma ba mai aiki da aljannu ba ya za a yi ya san labarin in ba aljannun ne za su faɗa masa ba.
"Allah sarki malam ai dama shi ya sa muka zo nan ni ma sau ɗaya na taɓa rako wata kawata nan ta karɓi maganin mallakar miji kuma da ka bata ta turara masa ta mallake shi don yanzu ko wurin zama sai ta nuna masa yake zama" Ta ce cikin jin ɗan karfin gwiwar sun samu warakar damuwarsu ita dai ta san ta rako kawarta wajensa to amma a ciki basu san maganin wane malami bane ya yi maganin tun da wuri biyu suka je ita.
"Allahu akbar a mu nan kare kukan ka sunanmu shi ya sa wasu har sunana na Malam Kailu ya ɓata a wajensu sai dai ki ji ana kiran Malam mai kare kukan ka" Ya ce yana ƴar dariya.
"Bari na turo maka su" Ta ce don a nata shirin daga ta turo su za ta san na yi don guduwa za ta yi in an cire musu sa taho tun da dama ba ita ta aike su ba.
"Tare za ku zo nan ɗin ai babu wata damuwa kinsan aljani shege ne za su iya binki gida gwara ki tsaya rukiya zan yi in fitar da ita" Ya ce mata, ɗan jim ta yi amma dai jin ya ce za a iya bin ya gida sai ta ji ma zuwa gidan ya fita daga ranta kuma ma ta tsorata da zuwa gidan gwara ta tsaya a gama ɗin kamar yadda ya ce mata shi kare kukanka sunan shi kenan kuwa ai kikan su ya kare.
Tana shirin tashi ta fito ta ji wani uban kara daram-dam-dammmm bata yi aune ba sai ganinta ta yi ita da Malam kare kukan ka sun nufi kofar shiga cikin gida da yake kofar guda biyu ce a ɗakin nasa akwai ɗaya ta zaure wanda bakinsa suke shigowa akwai kuma ɗaya wacce in ka bi za ta kai ka cikin gida. Malam shi kansa abin ya razana shi har ya manta da maluntakar tashi don haka dama ya ɗaga kwarya zai yi zane a cikin kasar da take cikin kwaryar ai yana jin karan nan sai ma ya manta da Baba da take zaune a gaban malam mai kare kukan ka, sai gasu sun tashi a guje suna tseren fita daga kofar har malam ɗin yana bangaje Baba, a haka suka shiga tsakar gidan Malam, matar malam ma da take gurin murhu tana za ta kaɗa miya jin karan da kuma ganin malam da kansa ya sheko da mugun gudu babbar rigarsa tana cin saɓularsa tana taɗe shi yana neman faɗuwa da wata mata tana binsa ita ma da gudun, ita ma a sukwane cikin rashin sanin makamar abin yi ta kinkimi zazzafar tukunyar miyar mai ɗaukr da ludan da za ta kaɗa miyar ta take wa su malam baya da suka nufi turakarsa shi da matar da bata san ma wace ce ba.
Bata da burin da ya wuce ta isa ɗakin kar su banko kofar su tashe ta tsaye don a yadda ta ji karan tashin boom ɗin nan ta san ba mutane kaɗan ba zai sa su yi bankwana da duniya ba, kuma ta san watakila ƴan bindigar da suka saka boom ɗin su bi gida-gida hakan ya sa ta gwammaci ta kasance tare da mutane a kan ta je ɗakinta ita kaɗai. Shi ma malam ɗin dama can ɗakin zauren wajen karɓar bakinsa ne. Har an bankamo kofa an kusa rufewa cikin zafin nama ta bangaza kofar ta shige tana ɗauke da tukunyar miyar da ita kanta bata san dalilin ɗakkota ba ga wani uban zafo don bata da nutsuwar kama tukunyar da tsumma.
A can ma kofar gidan malam lokacin da akuyar nan ta jijjiga mazaunanta tare da kaɗa