Showing 48001 words to 51000 words out of 52525 words

Chapter 17 - CIMA ZAUNE Complete by Maman Afrah.txt

30 Aug 2025

1758

hali da kuma kar ya nuna gazawarsa a aikin sai ya yi kamar bai gani ba saboda ba ya so su Baba su fahimci zunzurutun tsoron da yake ciki tun da ya gama faɗa cewa karyar aljani ya gagare shi, ya fi so kamar yadda yake kare kukan ka to yana so idan sun yi gaba su adar saboda ba ya so sunan nan nasa ya sauya don matsawar aka samu akasin lissafi to zai ɓata rawarsa da tsalle ne domin kuwa wanda suke cincirindon zuwa wajensa karɓar magani za su masa tawaye bayan kuma sana'ar maluntakar nan da ita ya dogara. Duk da daji yake zuwa ya samo sassaken bishiyoyi na magani matarsa ta daka a ɗaɗɗaura yana ba wa masu zuwa wajensa abin da ya sa kuma suke ganin maganin yana yi saboda dama duk abin da ka yarda zai maka magani to zai maka ne to matsawar kuwa aka ji ya razana ya kasa cire aljanar akuyar nan ya san sai sunansa ya dushashe.

Daurewa ya yi, ya jure ya yi ta maza ya kara kallon fuskar akuyar nan, kawai sai ya ga ta kashe masa ido ɗaya da ya kara kallo ma sai ya ga fuskar ta sauya zuwa ta mutum kyakkyawar darar mace sai kuma ta rikiɗe ta zama ta akuya duk abin nan da ake yi su Baba basu san wainar da ake toyawa ba musamman su Sagiru da suka runtse idanu suna jiran tsammani. Malam Kailu kai ya sunkuyar yana jan lahaula wala kuwwata, ji yake kamar ya tashi ya zura a guje don ya san da a ce ita ma Baba ta ga abin da ya gani watakila da tuni ta daɗe a hanyar gida su dama su Ahmadu ba a maganarsu tun da su tif da taya suke da akuyar babu damar gudu duk inda za su je to kuwa suna tare.



Kan da ya sunkuyar sai kawai yake ganin fuskar farar matar nan a dab da fuskarsa.

'Innahu min sulaimanu wa innahu bismillahir rahmanir rahim, wailul likulli humazatin lumaza, wattini wazzaitun, tabbat yada abi lahabin wattabbu' Malam waɗannan ayoyin ne ya samo a kwakwalwarsa duk ayar da ya janyo ba ya iya ta gabanta ji yake ya manta cigaban sai dai ya kara kamo wata.

"Malam ya ka dakata?" Ya ji Baba ta jefo masa wannan tambayar ɗagowa ya yi ya kalleta gani ta yi ya haɗa gumi sharkaf zufar sai kwaranya take a fuskaraa da wuyansa idan ma ba idanunsa sun nuna mata ba daidai ba da sai ta ce kamar hawaye ta gani yana fita daga idanun don idanun ma sun yi jajur kamar mai kuka a ɓoye.

Dariyar yake ya sakarwa Baba wacce ta fi kuka ciwo yana ji a ransa yau ya ɗakko aikin da ya fi karfinsa domin kuwa dala ba gammo ce, shi ba ya son mutanen ɓoye tsoronsu yake duk abin da yake faɗa dama cika baki ne. Don akwai lokacin da suka buɗe musu ido shi da matarsa suke ganinsu muraran ranar kwana suka yi basu runtsa ba. Duk da ba wai aljannun suna tsayawa bane kawai dai suna fitowa su ga wulginsu ko kuma suke ji maganganu a ɗakin da kuruftun taɓa kayayaki bare kuma yau da ya yi arba da akuya tana murmushi da kashe ido, ya san yau kam abin ba sauki ciwon arne.

"Malam" Baba ta kira shi ganin gabaɗaya ba ya cikin nutsuwarsa kuma ya ki magana.

"Uhmmm" Ya amsa mata uhmm don yana buɗe bakinsa watakila kuka ya kwace masa a yi abin kunya.

"Na ce aikin nan kuwa zai iyu?"

'Su fa suke ganinmu ba mu muke ganinsu ba da a ce kin yi arba da abin na gani yanzu a tattare da akuyar nan watakila da yanzu kin yi gudun kilomitoci ni ma don babu yadda zan yi ne' Ya ce a zuciyarsa a fili kuma sai ya ɗaga ido ua kalli akuyar a fakaice ya ga har lokacin tana kallonsa kurrr da idanu a wannan karon kuma sai ya ga ta masa wani kallo kamar na soyayya sai kuma ya ga ta turo masa baki wato ta cure bakinta wajen ɗaya ta masa alamar kiss.

"Alif lamra, ha karami minjaye" Ya shiga faɗa cikin ruɗu a fili ba tare da ya sani ba.

"Alif lam ra, ha karami minjaye" Ya ga bakin akuyar ya buɗe ya faɗa har cikin kunnensa amma da alama shi kaɗai ya ji ta maimaita abin da ya ce don da alama su Baba basu ji ba.


"Malama kai da za ka yi rukiyya ka raba su da wannan abu amma duk ka sauya na kasa gane a cikin aikin kake ko a gaba za ka yi aikin? Kuma yanzu sai ka ce alif lam ra, ha karami minjaye don Allah ya kake so a yi daren azumi ne fa an daɗe da yin isha'i da sallar tarawihi ana jimawa kafafun jama'a za su ɗauki....


Kwuuuuuiiiiiuttttt Baba ta ji Malam ya saki wata tusa mai kara kamar an danne kan kwaɗo da alama tusar ya yi yaki da ita ne wato ya zauneta don kar ta bayyana amma ta fito tun da a fitar karan kana jin yadda aka danne karan.

Malam kuwa Baba bata san lokacin da take masa magana kan ajuyar nan ya ga ya zama kai biyu sai kuma daga tsakiya ya ga kan wannan farar matar wannan ne ya tsorata shi ya ji tusa za ta kuɓuce masa don kar su Baba su ji su yi zaton wani abu sai ya danne amma kuma bashi da karfin rike tusar ya hana ta fita wannan dalilin ne ya sa suka ji karan kamar an danne kan kwaɗo musamman da ya lura shi kaɗai ne yake ganin waɗannan abubuwan.


Saura page ɗaya mu gama free pages, ko dai ki biya 500 ko ki yi like

MUHIMMIYAR SANARWA* 👇👇👇

*Assalamu alaikum duk me karatun littafin CI MA ZAUNE ya tsaya ya karanta wannan saƙon ya fahimta. Littafin nan 500 ne za a gama free pages a page 18 sai dai akwai zaɓi biyu ga mai son karantawa har ƙarshe. Ko mutum ya biya ,500 ko kuma ya mini magana in bashi link ɗina ya mini LIKE na gasa idan ya yi zai sa mutane biyu su mini a tura min screen shrt ta PC sai in saka mutum a paid grp ya karanta idan kuma knsan kn yi mini dama to za ki sa mutane biyu su mini sai in saka ki a paid grp amma sai kin fara mini magana a PC na miki bayani. Wanda kuma 500 zai saka zai biya ta asusun faiza abubakar 9030283375 opay shaidar biya ta 09025576222* *Wanda za su yi like ma ta wannn no za su min magana*
[8/25, 9:31 AM] Sadiya Abdulrazak: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
*IMZEED VENTURE*
Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna aiyar da gwanjo me kamar sabo!
Tuntuɓemu 07077532253
Wtsapp/IG/TiktocTikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-8yWWJj3GGri&_r=1

*CI-MA-ZAUNE*

NA

MAMAN AFRAH

PAGE 1️⃣8️⃣

MUHIMMIYAR SANARWA* 👇👇👇

*Assalamu alaikum duk me karatun littafin CI MA ZAUNE ya tsaya ya karanta wannan saƙon ya fahimta. Littafin nan 500 ne za a gama free pages a page 18 sai dai akwai zaɓi biyu ga mai son karantawa har ƙarshe. Ko mutum ya biya ,500 ko kuma ya mini magana in bashi link ɗina ya mini LIKE na gasa idan ya yi zai sa mutane biyu su mini a tura min screen shrt ta PC sai in saka mutum a paid grp ya karanta idan kuma knsan kn yi mini dama to za ki sa mutane biyu su mini sai in saka ki a paid grp amma sai kin fara mini magana a PC na miki bayani. Wanda kuma 500 zai saka zai biya ta asusun faiza abubakar 9030283375 opay shaidar biya ta 09025576222* *Wanda za su yi like ma ta wannn no za su min magana*


CI-MA-ZAUNE.


NA


MAMAN AFRAH


🅿️1️⃣8️⃣


'Baki san duniyar da nake ba muraran nake ganin akuyar tana caccanjawa' Ya ce a ransa amma a fili ya danne tsoronsa ya ce

"Yanzu dai nake kan aikin kin san aikin ne babban aiki duk ni a wajena ba wani babba bane" Ya ce tamkar ya yi kuka.

Baba kai ta shiga gyaɗa masa su Ahmadu kuma suna jiran zaman jiran tsamani, akuya kuwa jin abin da malam ya ce wato aikin a wajensa ba wani babban aiki bane kawai sai ta mika kanta ya zaman wuyanta ya kara tsawo ta kai bakinta kusa da na malam.

"Subhanallahi wa bihamdihi subhanallahil azim" Shi ne abin da malam ya shiga ambta a zuciyarsa ganin bakin akuya yana dab da nashi wato akuya tana shirin doɓara bakinta a kan nasa da alama dai sumbata ce za ta masa. Idanu ya runtse yana jin faɗuwar gabansa tana tsananta don a nasa tunani watakila bakinta yana sauka a nata za su iya ɓacewa tare.

Ganin hakan da akuyar ta yi sai ta yi wani tashi tamkar mai tafiya a saman iska bata yi masauki a ko ina ba sai a kan bayan malam ta sakalo kafafunta na gaba a wuyansa. Sagiru da Ahmadu wani irin bugu gabansu ya yi lokacin da suka ji alamar ta bar jikinsu basu ankara ba lokacin sai da suka fara laluma bayansu suka tabbatar bata nana wani daɗi ya rufe su a nasu tunanin malam ne ya raba su da ita musamman da suka ji ya ce ba wani babban aiki bane a wajensa sai dai kuma me? Ashe dara ake yi sai kuma dare ya yi wato dai suna ɗagowa suka yi wa idanunsu masauki a kan akuyar makale da jikin malam. Buɗe bakin da akuyar ta yi ta yi wani kuka shi ya sanya Ahmadu da Sagiru darewa a sukwane cikin gudun ceton rai suka garzaya wajen Baba. Baba wacce kukan akuyar ya sa ta yi zaman ƴan bori ba tare da ta shirya ba, kafafun ta duka biyu a mike da yake ma a jikin bango ta zauna. Don haka su Sagiru suna zuwa kowa ya yi wa kansa masauki a kan cinyarta guda ɗaya, amma kuma Baba bata ma san a kan cinyarta suke ba.

Malam jin saukar abu a gadon bayansa sai ya kwalalo idanu, wanda yake son ta tabbar ta hanyar kallon su Sagiru don dama tun da ya ga bakinta yana dab da nasa sai ya rufe nasa idanun yake jiran tsammani. Ganin babu bakin akuyar a kusa da bakinsa kuma babu akuyar a bayan su Ahmadu sai gabansa ya harba da karfi a sannan ya lura da kawanya da aka yi wa wuyansa da wani abu mai kamar icce cikin karfin hali ya kai hannunsa bayansa don ya tabbatar a kan jelar akuyar ya ɗora hannunsa wacce ta cika da gashi luɓuɓu. Wani tari ne ya kwace masa don sai ya ji ya manta ma yadda ake kuka mai sauti ko tarin ma tsintar kansa ya yi da yi.

'Yau na janyo jafa'i ni Kailu aka ce ana ɗaure aljannu da azumi to ko dai musulmin ba a ɗaure su?" Ya jefawa kansa tambayar.

"Malam Kailu mai kare kukan ka" Ya ji ta raɗa masa a kunne jin haka sai hawaye suka shiga sirnano masa, domin gabaɗaya ya fashimci kashin sa ya bushe.

Ganin abin yana neman fin karfinsa sai ya shiga kokarin rarrafawa saboda ya saka a ransa cewa babu yadda za a yi su Baba su zo su goga masa kashin kaji. Dakyar ya iya jan gwiwarsa ya nufi wajan su Babar a ransa yana jinjina kokarin su Sagiru da suka iya jurewa ko dom idan ma basu jure ba ya za su yi tun da basu da mafita. Baba da take son su samu su suɓuce su gudu tun da har Allah ya taimake su akuyar ta bar jikin su Ahmad amma sai ta hango Malam ɗin ya nufo su da rarrafe. Kokarin mikewa tsaye ta shiga yi amma sai ta ji kafafun nata kamar an ɗaɗɗaure baya san cea su Sagiru ne suka yada zango a kan su ba.

"Ku taimaka wa malam
Kailu jama'a musulmi ɗan uwan musulmi ne" Cewar malam lokacin da ya taho wajen su yana ta maimaita musulmi ɗan uwan musulmi ne tamkar wanda ya samu karatun fatiha. Kowa da kallo ya bishi ganin shi gabaɗaya ya rakwakwkwaɓe tamkar wani karamin yaro.

"Malam kai da muka kawo wurinka ai sai ka yi addu'ar ta fita amma mu ina za.mu iya wannan sha'ani sa za mu iya da bamu kawo wurinka b...

"Ni dai an cuce ni an zaluncr ni haka kawai ina zaman-zamana an watsa mini hatsi kaji suna bina" Malam ya katse Baba cikin gunjin kuka don yana ganin su ne ummul aba'isin komai.

"Ka yi addu'ar mana"

."Ina ma zan iya addu'ar gabaɗaya an dagula mini lissafi duk ayoyin da na gaddace a kan nan nawa amma yanzu in biya ɗaya ma abin ya faskara duk sun gudu sun bar ni"
Su Baba ganin ya zo dab da su sai suka cure a waje ɗaya tamkar kuli-kuli(Karago).

"Wallahi ni ma cikin ku zan kwatsima ba zan zauna ni kadai ba gwara a yi wake da shinkafa" Ya ce yana kara saurin rarrafensa.

"Kar ka kuskura ka karasa wajen su" Ya ji muryar akuyar raɗau a kunnensa. Kittt ya ja wani uban birki ga koshi ga kwanan yunwa.

"Ki taimaka ki sauka daha bayana" Ya ce da kuka shaɓe-shaɓe.

"Ka yarda da sharaɗi?"

"Ni ba ma sai kin faɗa mini sharaɗin ba in dai za ki sauka daga jikina...

Tun bai kar karshen maganar ba ya ga akuyar ta sauka ta tsaya a tsakiyar ɗakin sai aka shiga kallom kallo tsakanin malam da akuya da su Baba. Dama shi ya yi hakan saboda ya ribace ta, ta sauka yanzu kuma shammatar ta yake so ya yi ya fice da gudu daga ɗakin ya je turakarsa ya rufe don gabaɗaya ma ya manta cewa ko ta bango za ya iya shiga ta masa hukunci daidai da laifinsa.

Kowa da mamaki yake kallon akuya ganin ta zauna ɗam a kan mazaunanta, malam da yake fakonta kuwa ba ta ita yake ba so yake ya garzaya zuwa kofa ba ma ta mamakin zaman da ta yi yake ba tun da ta yi magana shi bai ga wani abu da za ta kasa yi ba baya ta juya musu hakan ya sa malam cikin sanɗar rarrafansa ya durfafi kofa su ma su Baba ganin haka suka shiga akamantawa juna yana fita za su fice. Ai malam yana dab da fita bai yi aune ba sai ji ya yi an damko wuyansa aka ɗaga shi sama cidik, idanu ya shiga zarewa sai dai bai ga wanda ya ɗauke shi ba har yanzu kawai dai an ɗaga shi ɗin ne kuma yana reto sannan akuya dai tana yadda take wato ta juya bayansa. Kana kallon fuskar malam za ka ga a firgice yake don yanzu tsoronsa ya ruɓanya jin an ɗaga shi amma ko alama bai ga wanda ya ɗaga shin ba.

Su Baba sai suka yi ɗiff suna ganin ikon Allah saboda yanzu an cire musu sha'awar fita don ganin an ɗaga malam yana reto a saman iska, ba a ɗau wani lokaci ba sai ga malam zaune a cinyar akuya ta rungume shi a kan cinyarta ko dai kafafu ne ma oho.

Malam kawai zare ido yake saboda ya nemi addu'a ma ya rasa shi yakin da yake ma da numfashinsa wajen shaka kaɗai ya ishe shi bare kuma akuyar nan da ba ya kaunar ganinta.


"Na daina tarkar fita a mini afuwa ina bada hakuri cikin kwando" Ya ce yana haɗa hannu alamar roko. Kafadunta na gaba ta saka ta dokewa malam hannun inda ya ji wajen kofaton ya buge shi da sauri ya janye hannayen gabansa yana bugawa.

Akuyar nan mamanta ɗaya ta kamo(Breast) Malam yana jiran ya ga mai za ta yi da shi sai kuwa ta nufi bakinsa da shi, har wani kara rungume shi ta yi irin yadda ake yi wa yara in za a shayar da su. Malam bakinsa ya shiga dantsewa da mugun karfi don shi ba zai taɓa yarda aljanar akuya ta shayar da shi ba ya je ma ya zuki maman ya haɗiye ya ɓace ɓata ya koma jinsin aljannu. Bata masa magana ba bata kuma fara nufar bakin nasa da maman ba.

'Na shiga uku ni Kailu bayan gyatumata da ta shayar da ni wata goma sha takwas yanzu a ce in sha nonon akuya, nonon akuyar ma ba kindirmo ba a jikinta kuma akuyar ma aljana jama'a ku kawo ɗauki Malam Kailu mai kare kukan ka zai fita daga jinsin bil adama ya koma jinsin aljannu taimako jama'a wayyo ni aradu maluntar ma na daina kowa ya je ya ji da jinyar da take damunsa tun da abin ya zama haka daga taimako sai a ɗora mini JALLI JOGA( Shin kin karanta littafina JALLI JOGA kin ji yadda matan makaho suke kishi bayan kuma aminai ne tun na yarinta badakalar bata tsaya a nan ba yadda uwar gida da jikarta suka sunkuma sabuwar amarya a kasan gado suka cinye kazar amarcin turka-turkar sai kin karanta dariya kuwa sai cikin ki ya faɗa miki tuntuɓe ni a 09013181851). "Malam ya ce a zuciyarsa yana jin da na sani wacce ta kasance keya ce!

Akuya dai bata saurare shi ba ta sake cafo gabaɗaya maman nata(Breast) Wanda yake dogo jalailai da shi ta sake tunkarar malam, tuni malam hawayen tausayin kansa ya gama wanke masa fuska sai jujjuya kai yake alamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login