Showing 15001 words to 18000 words out of 52525 words
tana murmusawa jin tsabar hutu ne ya sa ko waya sai a yi ta kira ba a ɗaga ba.
Daga can ɗaya ɓangaren kuwa a lokacin da ake kiran wayar Sagiru rakani kashi wacce tsufa ya samu wajen zama a jikinta tana ta tsitsi kamar kukan gyare amma shi gogan yana kwance a kan buhu a ɗakin yana sharɓar baccin asara saboda dama tun da ya yi aure ɗan wankin da yake ya ce ya daina aikin wahala tun da ya yi aure matarsa take sana'ar cikin gida suna cin abinci. Amina da take zaune a gefe ta yi tagumi saboda lokacin karfe goma ta ɗan gota tana shirin mika hannu ta tashe shi ta sanat masa ana kiransa a waya sai ta ga ya tashi ya ɗauki wayar.
"Eh nine ina ji wa ke magane"
Ta ɗaya ɓangaren Dada har da ɗan rusunawa ta shiga gaishe da shi tamkar gana ganinta.
"Lafiya kalau muke"
"Allah sarki ai tun ɗazu ake kira kiran yana shiga amma ba a ɗauka ba" Dada ta ce cikin ɗan sanyaya murya don ita ya gama mata komai tun da yana mai mugun kuɗi ya yarda ya auri ƴarta ƴar kauye ƴar kauyan ma bazawara.
"Wa yake magana wai?"
"Allah sarki ɗan albarka sirikarka ce Dada Saude dama na ce a kira mini kai mu gaisa in ji lafiyarku to na san baka shaida murya ta bane na san abin ne da yawa wai mutuws ta shiga kasuwa"
"Au to ashe Dada ce ga Aminar to"
Gaisawa suka yi da Aminar Dada ta shiga rattabo mata wasu jawabai wanda da to kawai ta bi ta amma abin na Dada ya zarce hankali da tunani bata ma san halin da take ciki ba.
"Amina ana nan ana cin mai kyau a sha mai kyau a kwanta a mai kyau" Dada wacce duk tunaninta Amina take yi wa magana bata san cewa Sagiru ya karɓi wayar ya kara a kunne, sai da ya gama jin bayanan sanna ya shiga faɗin
"Ai Dada yanzu ma karyawa muke yi da naman kaji da wainar kwai ga kuma shayi mai kauri da ya asha madara" Ya ce yana haɗe rai kar Aminar ta ce ya yi karya. Wani yawu Dada ta haɗiye muduk jin kayan daɗin da ta zayyama mata sai da ta ji tamkar ta yi tsuntsuwa ta ganta a gidan Aminar.
"Allah maka albarka ɗan nan yadda ka auri Amina ka kaita gidan daula Allah sa ta zama silar cigaban arzikin ka" Ta faɗa tana washe baki kamar yana ganinta.
"Amin Dada" Ya ce yana yanke kiran"
"Kai Allah ya mana gyaɗar dogo ban taɓa sa ran wani daga tsatsona zai rakaɓi daula haka ba" Ta ce mika masa wayar ta masa godiya ta juya ta tafi.
Watan azumin ramadan ya karato wanda hakan ya sanya Dada da jikokinta cikin farinciki, saboda shirin ko ta kwana na tafiya birnin Gumel yin azumi a gidan Amina.
"Haba wai kam ke Saude wace irin mace ce da baki da kamun kai ta yaya kuma a wane garin gaɓa-gaɓan kika taɓa ji sirika ta je gidan siriki ta zauna tsawon wata guda kuma ba ma ita kaɗai ba har da waɗannan jikokin yaran da gasu nan sun zama ƴanmata sun isa a kai su ɗakin miji" Malam da Dada ta ishe shi tambayar ya barta tafiya birni gidan Amina su yi azumi ita da su Hassu ya faɗa yana hayayyako mata.
"Malam daga neman izini sai cibi ya zama kari? Kar ka manta ni fa izini na neman ba kuɗin mota ba kuma kai mene ne naka a tafiyata gidan siriki ni a nawa ganin idan ka faɗaɗa tunaninka ai za ka ga nauyi na rage maka nauyin ciyarwa da ɗawainiya tsawon wata guda nake so na yi azumina a can mu murmure abin mu...
"Wai Saude mai ya sa ke duk inda jin nauyi yake baki bi hanyar yanzu gidan sirikin ne za ko je har ki zauna tsawon wata guda? Kuma ni na ce miki na gaji da ɗaukan ɗawainiyarki ne da za ki ce an rage mini haba sai ka ce a garin gaɓa-gaɓa kamar dai baki da mafaɗi...
"Kar dai ka ce mini mahaukaciya don ba yarda zan yi ba kuma wallahi tafiya kamar na yi na gama babu mai hana ni domin ana gobe azumi za ku yada zango a can a tashi azumi da mu washe gari ehe" Ta ce tana tafa hannu a cinya.
"Wallahi ba zan barki ki tafi ba son ki je ki kashewa yarinya aure"
"To tun da haka ka ce mu zuba mu gani ɗan halak ka fasa kuma ko yaran nan da kake batun zan tafi da su Allah na tuba nawa suke yaran da ko shekaru sha biyar basu rufawa baya ba kawai girman jiki ne yo ni ko tahowa na tashi yi ai sai in bar su a can su mata zaman ɗaki in Allah ya sa suka samu miji a can ba shikenan ba ai ni tun da na ji daɗin aurar da ƴa a birni gidan naira to fa ba gudu ba ja da baya "
Saura kwana biyu a tashi da azumi Saude da su Usai sai shiri suke, gabaɗaya sun wanke kayayyakin wankin su, saboda Dada ta ce ko azumin ya kare sai sun warware sun maida ramar azumi sannan za su dawo duk da tana ikirarin cewa ba lallai bane ma in suna cin mai kyau su yi ramar azumi. Gabaɗaya cikin kauyan sun gama yaɗawa cewa a birni za su yi azumi hatta Dada gidan mutuwa ko suna ko biki idan ta je sai ta ɓinta cewa ita bana azumi a birni za ta yi sirikinta ya ce ta je can ta huta. Bare su Hassu duk sun gama faɗawa kawaye suna firiritar tafiya can.
Malam yana zaune a kofar gida inda yake saka tabarma ya huta, suna ɗan tattaunawa da abokinsa sakon kiran mai gari ya riske shi duk da ya yi mamakin kiran bagatatan amma sai ya dangana hakan sa cewa ko mutuwa ma da tashin kiyama bagatatan za su zo wa mutane ba tare da sun shirya ko sun tsammaci zuwansu a wannan lokacin ba.
Shi da abokin nasa suka rankaya domin jin ba'asin kiran, tun daga nesa ya hango Dada zaune a gaba mai gari ga su Hassu ma duk suna zaune a gefenta sun saka ta a tsakiya ga mutane nan a zazzaune a wurin. Cike da mamakin ban al'ajabi ya karasa wajen yana tunanin dalilin kasantuwar su Dada a wajen don shi tuni ma ya manta da wani tafiyarta birni a tunaninsa ta janye kudurin nata ganin bai amince ba.
"Malam na ji daɗi da ka amsa kiranmu a kan lokaci dama iyalinka ce ta ga na isa a matsayina na shugaba kuma jagora da na isa da kowa a garin nan, a kan waya da kuma aiken sa sirikinta yake mata ta je can birnin ta huta ta yi azumi amma kasa ka tsare ka hanata tafiya" Mai gari ya ce yana kallonsa.
Bakin magana Malam ɗin ya rasa sai bin Dada da su Hassu da suke share hawaye.
"Da kai fa ake magana" Mai gari ya ce yana kallonsa.
"Allah ja da ran mai gari ni a matsayina na mijinta na bata umarni a kan kar ta tafi amma bayana haka ni ban san wani aike da kuma waya da shi sirikin nata yake yi ba".
"Ai yanzu ka ji, domin bakina da nata ta faɗa mini ga ta nan zaune ai kana gani.
"Jiya ma sai da ya mini waya a kan cewa ko dai ban ɗauke shi a matsayin ɗa ba da zan ki zuwa in yi azumi bayan shi ko kaura na yi gidansa zai rikeni ko har abada ne domin uwa ya ɗauke ni" Ta faɗa tana sakin kukan kissa.
"To yanzu tun da ka ji da kunnuwanka ka barta ta je ta azumin"
"To ba komai na amince tun da abin har ya kai ba za mu kashe magana a gida ba sai ta kawo mi fada gaban jama'a ana mana shari'a" Ya ce cike da takaici don ganin kowa ya yi tsit shi ake kallo ana ɗan jijjiga kai kuma ya san duk mazan da suke wajen dole su ba matansu labari.
Ganin ya amince mai gari ya sallame shi, bayan sun tafi Dada ta shiga yi wa mai gari godiya har da bashi ɗari biyar wai ya ci goro ya karɓa yana washe baki. Haka suka baro wajen cike da murna don gobe suke so su tafi ya yi daidai da azumi saura kwana ɗaya. Tun da suka baro fada suke jin ana musu a dawo lafiya da alama labari ya gama baza kauyan. Don ko da suka dawo gidan ma su Ladiyo suke musu wani kallo ana ɗan kuskus na bakin cikin ganin za su tafi birni suke cin kayan daɗi.
Ko da daddare da Dada ta je ɗakin Malam ko fuska bai bata ba bare su yi magana mugun haushinta yake ji yadda ta je ta kai shi gaban hukuma a kan gaskiyar da ya faɗa mata.
"Malam ka san dai shiga abin hawa yana da haɗari shi ya sa ake yi wa mutane fatan sauka lafiya amma kai na zo har ɗakin ka kana wofantar da ni sai ka ce wanda na kashe ma mutum"
"To dama ni na ce miki bana miki fatan sauka lafiya ne ki je umma ta gaishe da ashshe kuma indai tusa tana huta wuta ai ga wurin nan" Ya ce yana juya mata baya.
."Tun da haka ka ce ai babu komai rana dai bata karya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya gobe ya wannan muna can ana ta yi wa ciki hidima" Ta ce tana sakin murmushi tare da ficewa ta bar masa ɗakin.
"Ni wallahi na matsu gobe ta yi mu je mu ci kayan daɗi" Hassu ta ce tana murmusawa.
"Ni kuma kawai so nake in ga na kara shiga wannan katuwar kofar(Get) Wanda ko mota sai a buɗe mata ta shige ciki" Usai ta ce ita ma cike da murna.
"Yara kenan manyan gobe ku ɗin ma kenan da kuka taɓa zuwa bare ni da sai labari nake ji ai sai na fiku ɗoki" Dada ta ce tana hango yadda za ta ga tsararran gida da Aminarta a ciki ta murmure.
"Wai Dada dama har aike mijin Anty Aminar yake a kan mu je har yana miki waya" Hassu ta ce tana tsare Dada da ido, Usai ma tsare ta da idanun ta yi domin tana son jin amsar.
"Yo in fa ni dai ce na faɗi hakan don wancan kakan naku ya barni kuma shi ma Mai garin ai da ban ce haka ba ba lallai ne ya karɓar mini fansa ba dama bukatar maje hajji sallah, shi kuma wannan yaro Sagiru idan ya ga mun je ai babu yadda zai yi da mu tun da dangin matarsa ne to dama ya gara ta kan yi da dutse ai sai kallo"
"Wallahi kuwa Dada Allah dai ya kaimu lafiya don ni cikina zan buɗe in yi ta lodar abinci" Hassu ta ce tana dariya.
"Ni kuma naman kaza idan na kafa kahon zuka sai dai a ga kasusuwan" Usai ma ta ce tana tata dariyar.
"Ni fa ina ga ko bacci ba zan iya ba sai dai in ɓarawo, ji nake tamkar am mini albishir ɗin samun aljanna saboda daɗi"
Tun da asuba suka tashi Hassu da Usai suka balbala wuta bayan sun yi sallah suka ɗora ruwan zafin wanka, garin na gama yin haske suka yi wanka Dada ma ta yi suka shirya tsaf su Usai an sha uban jambaki kan ta kile ga wata ɗamara da ka ci a kugu. Karfe tara suka fito tsakar gidan lokacin Malam tuni ya fita sai Ladiyo da Mero sun kafa kujeru a tsakar gidan sun kasa sun tsare sun son ganin kwakwaf. Hassu ce ta datse ɗakin Dada an sha atamfa har da jambaki su Usai suka shafa mata a leɓe, Usai ta ɗauki bakkon kayan ta ɗora a kanta ita kuma Hassu jakar wasu kayan a hannunta.
"To mutanen gida mun fito mu za mu tafi, birni ta yi kira shi ya sa bahaushe ya ce ɗa mai rana ko kana gudu haifi ka yada, yau dai za mu ci gajiyar haihuwa saduwar alheri mu da ku ga kafafunmu a gidan nan watakila ma sai watan babbar sallah wato bayan sallar layya ah to ai sai an yanka mini katon tirkakken rago mai kamar saniya in sha Allahu zan taho muku da kakide(Kitse) Kwa ke cin tuwo" Ta ce tana musu dariyar irin ta in fitsari banza ne kaza ma ta yi mana.
Kafin a samu mai bata amsa sai ga Malam ya shigo da sallama, Ladiyo ce ta amsa ko kallon kurar da ya ɗakko su Dada bai yi ba.
"To Malam za mu tafi in da rai za mu gana wata rana" Dada da ta bishi ɗaki ta ce tana daga tsaye don ta san zaman ma aiki zai zame mata.
"Sauka lafiya ya ce yana ɗaukan rediyonsa ya kunna. Baki ya taɓe ta juya ta fito suka fita tana jin su Ladiyo suna kuskus ta san gulmarta suke yi.
Gaba ta yi rike da igiyar akuyarta don ta ce ba za a ci daɗin birni babu ita ba dole ita ma akuyar ta murmure.
KAMAR YADDA NA SAKA LINK NA YOUTUBE CHANNEL A SAMAN PAGE ƊIN NAN DAN GIRMAN ALLAH KU SHIGA KU DANNA MIN LIKE 👍 NA SAN NA FI ƘARFIN NEMAN ALFARMA A WAJENKU LIKE ƊIN DA ZA KU MIN ZAI BANI DAMAR LASHE GASA GA LINK👇
https://youtu.be/xYBCkQuUxnQ?si=-0h_Dapw86VBXeE1
[8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
*IMZEED VENTURE*
Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna aiyar da gwanjo me kamar sabo!
Tuntuɓemu 07077532253
Wtsapp/IG/TiktocTikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-8yWWJj3GGri&_r=1
Ku shiga wannn youtube channel ɗin ku danna min like 👍 gasa ce kuma da like za a fitar da sakamako
👇👇👇👇👇
https://youtu.be/xYBCkQuUxnQ?si=-0h_Dapw86VBXeE1
: CI-MA-ZAUNE
NA
MAMAN AFRAH
🅿️7️⃣
Wurin motar da za ta tashi suka je wacce take a tsakiyar dandalin garin, tun da suka fito suke sallama da mutane ana ta musu fatan alkairi kowa yana ta cewa ƴarta ta auri mutumin arziki har yana aikowa ta je can ta huta harkar arziki ta yi ana ta mata sambarka wasu har tana cikin mota ma sai da suka je suka mata sallama har tana rasa wa za ta amsawa yadda suke dafifi wajen zuwa.
"Mutane kenan kowa yana so ya raɓe ka idan kana da arziki in kuwa talaka ne kai babu mai raɓar inda kake sai dai gani daga nesa wani ma in ya ce warin talauci kake, idan ma baka da kuɗin ko magana baka iya ba yo wa ma zai saurare ka" Cewar Dada lokacin har mota ta tashi sun ɗau hanya akuyarta a boot aka saka mata ita.
"Ai dama yanzu rayuwa sai kana da shi idan baka da shi kare ma ya fika" Wata mata da take kusa da Dada ta ari zancen ta yafa, da yake so Hassu a boot aka saka su. Haka dai suke hira da labaran duniya har suka isa birnin Gumel a tasha direba ua faka suka sauka bayan Dada ta biya kuɗin mota.
"Ya sunan unguwar ma?" Dada ta tambayi su Usai sunan unguwar da gidan Aminar take.
"Mayanka sunanta" Usai ta ce tana gyara rikon jakar hannunta. Napep suka tare suka shiga Dada tana rike da akuyarta ya ɗauki hanyar unguwar da suka faɗa masa kowa sai washe baki yake yi.
."Ke daina kan ki akuya sai kin san arziki ya shigo dangi , ah to ai daga yau kin daina cin dusa da ciyawa abincin mutane za kike ci mai rai da lafiya", Cewar Dada jin akuya tana kuka.
"Wallahi kuwa ai shi ya sa aka ce da arziki a garin wasu gwara a garinku" Su Usai suka ce suna dariya.
"Za dai ku gane gidan ko, kar fa mu je muke bulayi"
"To Dada da tun a can baki tambayi za mu gane gidan ba sai yanzu" Hassu ta ce tana kyakkyalewa da dariyar shekiyanci.
"Haba bayin Allah dama baku san gidan da za ku je ba shi ne kuka taho da ni son mu je muke bulayi man nan mai shegiyar wahala ya kare mini a banza" Mai napep da yake tuki ya ce cikin kakkausar murya dama saurayi ne ɗan bana bakwai.
"Kai yaro bar ganin mun zo daga kauye ka zata bamu san mai birnin take ciki ba to da in baka ɓata mai ba mene ne amfanin zubawa ni nan na sam duniya ciki da bayanta ka bar mini kallon kitse a maimakon rogo" Dada ta faɗa cikij hargagi ɗan napep bai kara magana ba ya ja bakinsa ya yi shiru dama faɗan da ya fi karfinka wasa kake mayar da shi.
"Ni zan gane gidan ma babu wani bulayi"Usai ta faɗa.
"Yo yarinya mene ne na ɓata bakin ki, ai na san dai gida kamar gidan Alhaji Sagiru ba zai yi wuyar gani ba saboda duk inda gida ya bambanta da saura to fa da wuya ka kasa sanin wandaya san shi"
A bakin get ɗin ya sauke su Dada ta bashi kuɗinsa ya tafi Hassu da Usai har rige-rigen zuwa buga get ake yi kowa baki a washe kamar gonar auduga"
"Ku buga a sannu mana watakila ta shiga banɗaki ne mu jira" Dada ta ce tana waige-waigen karewa unguwar kallo take yi.
"Wallahi na kasa gaskata cewa ba mafarki ba nake a zahiri ne Aminata ce a wannan rantsatssan gidan kai Alhamdulullahi Allah kadiran na ga annabi in na yi hali na gari yanzu wannan gidan aljannar duniya ake mini bakinciki ba zan zo in ci arziki in barshi a nan"
Mai gadi da yake banɗaki jin ana bugun kamar me ya yi