Showing 51001 words to 52525 words out of 52525 words
a'a amma kuma ya ga akuyar bata fahimtar karatun kurman da yake biya mata ta hanya jijjiga kai.
"Haba ɗan lele ka sha maman Babarka mana" Ta ce tana dungura masa maman a baki, sosai ya ji wani warin dabobi ya bugi hancisa har amai yana yunkuro shi amma ya dantse bakin saboda ba ya kaunar bakinsa ya buɗu ko da miskala zarratin bare a samu akasin lissafi.
"Baba mai kosai kasa ta daɗe da rufe idanunta(Ta mutu) Wallahi na sha nono har ya mini karo ki mini afuwa in ina son nonon na sayi kindirmo a wajen fulani a dama mini fura" Ya ce yana kare bakinsa da hannunsa don ma kar a samu akasi yana magana ta saka masa a bakin.
"To in gani kake ka girmi shan nonon ne ai sai in mayar da kai ɗan kundalo(Wada) Yanzun nan zan mayar da kai wada ka kankance ka zama jariri sai ka sha ko?" Ta ce
"Wallahi an yaye ni, an daɗe da yaye ni, har na girma don Allah kar ki mayar da ni ɗan kundalon wada" Baba, Sagiru da Ahmadu wanda suka faki idanun akuya da malam suka sulale da rarrafe suka bar ɗakin ba tare da an lura ba.
Haka suka samu suka kuɓuto suka fita wajen da rarrafe don ma kar a ankara a dawo da su, domin gabaɗaya sun tsorata da lamarin ganin abin da yake wakana sun san layi yana dab da zuwa kansu ma'ana ana gamawa da malam watakila a shiga shayar da su ɗaya bayan ɗaya. Sai ga shi dai cikin ikon Allah sun kuɓuto ba tare da asirinsu ya tonu ba.
A can cikin ɗaki kuwa akuya bata san su Sagiru sun fice ba sai da ta ɗago ta ga wayam don haka sai ta mayar da hankali kan malam tana jira ta gama da shi tukunna. Bata yi kasa a gwiwa ba tana dafa kan malam da yake rawanin ma ya faɗi har hular tana dafa kansa ta yi mismis da baki sai ga malam yana kankancewa sai da ya koma kamar yaro ɗan shekara biyu sannan ta ɗauke kofaton hannun nata daga saman kan nasa. Malam yana ji yana gani ya koma ɗan karamin yaro kukan takaici kawai yake a zuciyarsa wanda ya fi na fili ciwo. A haka ya ga ta tattaro duka maman nata guda biyu ta nufi bakinsa da shi.
"Gwara in ruɓanya maka biyu ko ya fi kosarka" Ta ce
"Wallahi ɗaya ma albarka bare biyu ni a koshe nake ma" Ya ce gabansa yana matsanancin bugawa jin maganar da ya yi ma ta koma muryar kananan yara a take ya shiga tunanin idan yanzu aljanar akuyar nan ta ɓace haka zai rayu ɗan karami kuma da muryar kananan yara. Ita dai bata kula shi ba har yanzu tana kokarin shayar da shi da mamanta biyu kuma har lokacin yana kwance a kanta alamar runguma da ake yi wa yara in za a shayar da su. Malam ganin haka sai ya yi yaki da zuciyarsa ya shiga karanta abin da ya zo bakinsa saboda ya lura addu'a ce kawai za ta kuɓutar da shi da yake yanzu ma ya ɗan kalli wajen da su Baba suke rakuɓe sai ya ga kamar an yi ruwa an ɗauke wato babu su babu dalilinsu babu wata alama da za ta nuna wanzuwwarsu ma a wajen ganin haka sai ya fahimci ya shiga casa'in da tara domin kuwa a nasa ganin ya yi nutsu a cikin rijiya mai gaba dubu da zai yi wuya ya fito.
Fatiha ce ya samu nasarar cafkowa yake karantawa a fili duk da yana jin yadda muryarsa take tamkar ta kananan yara, don har wani dabalbalewa take irin ta yara masu koyan magana ko wanda bakin nasu bai gama buɗewa sosai ba, amma a haka yake karantawa har ya samu nasarar kai karshen fatihar duk da yana jin yadda akuyar take wasu maganganu amma kuma bai saurara ba sai ma ya kamo falaki da nasi ya shiga yi babu saurarawa. Wani kara ya ji akuyar tana yi kamar wata haniniyar doki sai kuma ya ga ta ɗaga shi da hannunta daya ta yi jifa da shi can ya je ya doku da bango ya faɗa kan wasu kwanuka da suke ajiye a ɗakin da ba amfani ake da su ba, kafin ya ga ta tashi ta shiga zaga ɗakin tana kukan su na akuyoyi meeee kafin cikin minti biyu ta bi kofar da mutane suke shigowa ɗakin ta zaure fittt ta fice yana iya jiyo kukanta. Ɗif ya yi kamar an yi ruwa an ɗauke yana tunanin ko su Sagiru sun tsira ko kuwa za ta cin musu da wannan tunanin ya shiga kokarin tashi yana karewa jikinsa kallon yadda ya dawo kamar yaro ɗan shekara biyu sai gemunsa da yake reto jalai-jalai.
Da adungure ya gangaro daga saman kwanukan, ya mike tsaye yana shirin tattara babbar rigarsa ya zuba a guje amma abin mamaki sai kawai ya ga babu babbar riga babu dalilinta asali ma ba kayansa bane a jikinsa riga ce tafe da wando(Over roll, cike da mamaki ya kai hannu kan mazaunansa sai jin pampers ya yi ga fida makale a jikin aljihun rigar da alama ma nonon akuyar ne a ciki saboda wani abu ne fari kamar madara.
."Kai jama'a inda ranka ka sha kallo ni malam kailu mai kare kukan ka ni ne sanya da rigar yara tafe da wando har da nafkin(Pampers) Ga bulunboti(Fida) kai wallahi na ga rayuwa yau dai tabbas wannan aljanar akuyar a cikin musulman aljannun ma da ba a ɗaure ba saboda falalar ramadan ita takidara ce' Ya ce a zuciyarsa yana share hawayen tausayin kansa yana tunanin ko dai zaluntar mutane da yake yi ne Allah ya jarabce shi yau don sai ya ji a ransa ma bai yarda da su Baba ba ya fara zargin su duka ma aljannun ne suka yi ɓadda kama, ga shi yana tunanin yadda za su kare da matsoraciyar matarsa ba lallai ma ta tsaya ya mata bayanin shi ne mijinta ba aljana ce ta mayar da shi haka, watakila ma idan ta faɗa mata aljana ce shikenan ma ta kara tsorata. Da wannan tunanin ya surfafa tsakar gidan a guje.
Kwararaf ya yi tuntuɓe da wata tsohuwar fashashshiyar roba a tsakar gidan sai da ya yi dungurawa uku sannan ya je a zaune. Karan faɗuwarsa ne ya ankarar da matarsa wacce take zaune a kujera a wajen murhu tana kara kaɗa miyar da ya zubar, tana waiwayowa idanunta suka sauka a kan karamin yaro zaune da riga tafe da wando (Over roll) Kafarsa ƴar ɗul a mike kan nan nasa a salsale ya sha kwal kwabo hasken farin wata ya haske kan ral amma kuma abin da ya kara wutar tsoro da bugun zuciyarta ganin zangareran gemo yana jalaitu. Da karfi gabanta ya buga saboda a cikin mintin da bai wuce ɗaya ba ta gama kare masa kallo har sakon ya kai kwakwalwarta cewa aljani ne ba mutum ba don a wannan daren ba yadda za a yi a ga yaro karami da bai fi shekara biyu ba shi kaɗai ba tare da uwarsa ba, domin ita ko karan tafiya bata ji ba karan faɗowar kawai ta ji abu ɗaya da ya fara zuwa a ranta shi ne ko daga sama ya faɗo. Kokarin raba mazaunanta da kujerar da take zaune ta shiga yi amma cikin ikon Allah abin ya gagara sai lokacin take tunanin ashe ma ka ga abin tsoro ka samu damar guduwa arziki ne.
Don gabaɗaya kamar an mata dabaibayi, duka jikinta sai karkarwa yake robar kukar miyar da take kaɗawa da ludan tuni suka yi ɓatan dabo a hannunta kowanne ya kama gabansa.
"Ni ne malam" Ta ji yaron ya furta mata bata ankara ba sai gani ta yi ya dafa kasa ya mike tsaye gemun nasa har kirjinsa ga wata fida tana reto a aljihunsa bata gama gane tana cikin tashin hankali ba sai da ta ga ya nufo ta yana ɗaga mata hannu.
*Tirka tirka, badaƙala, cakwakiya, shin malam zai dawo daga ƙaramin yaron da akuya ta mayar da shi kuwa? Mai zai fari da matar malam da ta ga mijin ta a siffar yara yana magana da muryar yara, shin za ta karɓe shi ko gudunsa za ta yi. Ya batun su Baba da su sagiru shin za su tsira kuwa kun dai san aljanar akuyar nan tana iya zuwa cikin sakanni ma ta cim musu, shin mai zai faru? Ya rayuwar su *Dada za ta kasance shin za ta koma ƙauyen ko kuwa xa ta gwammaci zama a wannan yunwar, akwai wasu ɓangarori da bamu nutsa ba a cikin labarin na sabbin taurari ko dai kar ku bari a yi tafiyar babu ko da 500 ko LIKE za ku sha karatu*
*
*A nan na kawo ƙarshen feee pages mai son cigaba zai biya 500 ta asusun faiza abubakar 9030283375 opay shaidar biya ta 09025576222 opay. Ko kuma a min magana a karɓi link a mini like na saka mutum a paid grp ya karanta.*