Showing 30001 words to 33000 words out of 52525 words

Chapter 11 - CIMA ZAUNE Complete by Maman Afrah.txt

30 Aug 2025

1761

suka sha ruwa babu labarin CI-MA-ZAUNE. Da yake dankalin rabawa aka yi kowa ya ɗauki nasa Dada a biyu ta raba ta ce sai da asuba za ta ci sauran.

"Assalamu alaikum ya mutanen ɗakin nan" Sagiru ya shigo da sallama cike da shekoyanci fuskarsa sanye da wani gilashi, banu wanda ya amsa sai Amina don haka sai da ya nemi wuri ya zauna ya ce

"Babarmu Dada sannu da shan ruwa Allah karɓi ibada" Ya ce yawunsa yana tsinkewa jin wani kamshi hakan ya sa yake fatan a san masa abin daɗin da ake ci shi sai yake jin in ma ba karya hancinsa ya masa ba sai yake jin kamar kamshin doya da kwai. Dada kuwa wani abu ne ya tokare mata a makoshi jin yana ambatar ita ce Babarsa abin takaicin ma tun safe baya nan yanzu ma alamu da dama sun nuna akwai wata a kasa. Jin bata amsa ba kuma babu wanda ya kula shi hatta Amina ya ga sai wani abu take ci a ƴar roba sai karan taunar kowa yake ji amma shi bakinsa wayam.

"Wai anya Amina kina son shiga aljanna kuwa? Yanzu a ce an kai azumi amma mijinki ya dawo ki bar shi haka nan" Ya ce don ya ankarar da ita ta sallame shi.

'Ikon Allah na zaune ya faɗi wato su dai maza har kullum mata suke kaiwa wuta da bakinsu kasancewar an ce aljannar matan tana karkashin mazajan, shi ya sa su mazan suke tunkaho basa ganin abin da suke yi wa matan in ban da laifi ma tudu ne ka danne naka ka hangi na wani ya za a yi tana matsayin matarsa ba ya bata abinci, yau ma tun safe da ya fita ko gishiri bai bar mata ba sai yanzu bayan magriba ya dawo kuma amma shi ba ya tunanin nata hakkin sai nasa to mai ka bar mini da zan kawo maka' Ta ce a zuciyarta a fili kuma sai ta ce

"Ka yi hakuri" Ta ce tana tashi ta ɗakko masa ruwa a wani jug da ta siya ta zo gabansa ta ajiye masa ta koma mazauninta ta zauna. Kuri ya mata da idanu yana jiran ya ga an miko masa wani abun amma ɗif babu niyya ango ya kwana da wando.

."Dada Amina har kashina ta haɗa ta cinye?"

"Kashin uban me wai ka dameni, ka ba wani shege ne ajiyar wani abu da za a yi kashi da kai ka fita idona in rufe ka bar mu muji da ɗawainiyar kanmu da muke ɗauka" Ta ce cikin hargagi don dama a kufule take da shi.

"Maida wukar Dada kamar wanda dama kike jira? To shikenan ai tun da ku kaɗai za ku ci wanda ya ci shi kaɗai kuma shi kaɗai zai mutu" Ya ce yana mikewa ya kama hanyar bedroom ɗin.


"Ashe ma biki aka yi a gidan nan da la'asar ɗazu Baffalo yake bani labari a majalissa" Ya ce lokacin da zai shige bedroom ɗin yana kunshe dariyarsa don Baffalo ya faɗa masa komai ko ɗazu ma da suka je masallaci shan ruwa ya karasa masa a hanyar zuwa masallacin.
Wani uban tsaki Dada ta ja don ta lura cin fuska yake son yi mata.


Amina tana jin takaicin abin da yake sai dai tsoronsa take, su kuma su Hassu sai sun yi yinkurin yin abu sai Dada ta dakatar da su.


*DARE*


Ko da ya dawo daga yawonsa a buge ya dawo don haka sai ya shige ɗakin ya samu wuri ya zauna da yake lokacin da ya shigo ma sai da ya so yi wa Dada tijara amma sai ta watsa yinsa duk da a bigen yake amma Amina ta ko haushin bakaken maganganun da ya yi saboda haka yana shigewa ɗakin Amina ta bi bayansa a fusace.

"Sagiru ya isheka haka ba a wasa dan iyaye kuma uwa ko mahaukaciya ce sunanta uwa" Ta ce tana kama tsantsa banza ya mata sai da ya bari ta kai aya tana huci ya tashi tsaye ya ɗaga hannu hagu da dama ya faffalla mata mari. Wani uban kara Amina ta saka wanda da karan marukan da ta sha da kuma karan da ta kwalla Dada bata san wanda ya ɗugunzuma zuciyarta ba tana jin zunzurutun bakinciki da takaici cikin takun da bai wuce huɗu ba ta ganta a bedroom ɗin ta ma manta da cewa mata da miji ne kuma siriki ne tafin hannunta har kaikayi yake mata a kan marin da takanas ta je don ta ramawa Amina ta nuna wa Sagiru cewa Aminar tana da gata ba kamar yadda yake ganin bata da galihu bane. Tana shiga ta gan su a tsaye carko-carko Aminar rike da kumatu shi kuma yana rike da kugu sai huce yake kamar wanda ya yi tsaren gudu, Dada har za ta ɗaga hannu ta dalla masa nasa marukan kamar an ce ta kalli kwayar idanunsa ta cikin hasken fitila wani irin jaaa ta ga idanun nasa sun yi tamkar jini ya taru wannan ya tabbatar mata da ba karamin buguwa ya yi ba wato a maye yake hannunta ta damke tana ba kanta hakuri a zuciyarta. Cikin karfin hali ta daddage ta ce

"Zo mu tafi Amina Allah zai saka miki" Ta ce tana kama hannun Aminar suka fito daga ɗakin don tana tsoron ta mare shi ya mata tijara dama ya lafiyar kura bare ta yi hauka, tun da idan ba a buge yake bama fitsararre ne bare kuma ya bugu.


Ki yi kwanciyarki kin ji ai Allah yana madakata zai yi maganin duk wani azzalumi " Dada ta ce

"Haba don Allah Dada na ɗauka ma rama mata za ki yi" Usai ta faɗa
.
"Ni wallahi duk a zatona idan kika shiga sai dai muke jin karan mari falfalfal' Hassu ta ce

'Haba ɗiyan nan yo karen hauka ne ya cijeni ko kuwa hauka nake wannan yaro mai ido a tsakiyar ka kamar duniya haka kawai ya je ga mangareni a banza in shiga uku shi da ba a hayyacinsa yake ba' Dada ta faɗa. Shiru suka yi babu wanda ya sake magana sai karan sheshshekar kukan Aminar da suke ji.

'Da mai ya kai ki musu da miji ai ko kana mutunci ba ka zakewa amma kya tsaya faɗi in faɗa da miji' Cewar Dada don ganin ta kawar da maganar.

"Ke kuwa Dada tun da aka zo garin nan kamar an dakusar da zuciyarki yanzu sa,insar ce da miji babu kyau bayan ...

"Ke ni kar ki dame ni kin fi so take masa musu yana jigbarta a aikin banza ko ni da girmana sai in ke shiga faɗan ma,aurata" Ta ce cikin waskewa don ganin ta dakatar da maganar.

Bayan kowa ya yi bacci Dada da ta ajiye sauran kununta a kofi fa kuma sauran dankalinta a yar roba ta ce idan ta tashi da shi za ta yi sahur. Sagiru da cikin dare ya falka daga baccin lokacin mayen ya sake shi sai wata yunwa da yake ji falon ya nufo da rarrafe ta hasken farin watan da ya shigo ɗakin ta window ga Dada wacce take jikin bango dan kafin hali sai ya karasa ganin kofi da ɗan kwano, dibara ce ta faɗo masa ya lallaɓa ya kai bakinsa jikin yatsun kafarta hakori ya saka ya shiga ɗan gwigwiyar yatsun da hakori Dada cikin bacci ta ji ana gwagwiyar kafarta hannu ta kai cikin bacci ta doke kafar ta cigaba da bacci sai da ya mata karo uku sannan ya tabbatar baccin take kofin kunun ya ɗauka ya kurɓe duka yana jin yadda zakin ya ji kakau har yana lashe baki.

A hankali ya ɗauki robar dankalin, ya kwashe duka ya zuba a aljijunsa ya juya yana lallaɓawa don kar wani ya ji shi. Har ya shige bedrioom ɗin babu wanda ya ko da motsawa ne a haka ya samu wuri ya kwanta yana mika hannu cikin aljihun yana ɗakko dankalin ya jefawa a baki.


*Masoya domin ƙaunar Allah da manzon sa S.A.W ku yi searching littafina MALAMIN BOGI a youtube ku danna min like 👍masu min magana suna cewa basu gane mai za a yi ba, kawai daga kun shiga wajen hoton hannun nan za ki taɓa, a taimakawa mar,atus saliha gasa ce aka sanya mana ta marubuta. Sannn ina ɗora Link ɗin a saman page a duba a ɗauka Luv you Fisabilillah😍🥰*
🤝
09025576222
[8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
*IMZEED VENTURE*
Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna aiyar da gwanjo me kamar sabo!
Tuntuɓemu 07077532253
Wtsapp/IG/TiktocTikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t ZS-8yWWJj3GGri&_r=1
👇
https://youtu.be/34d9aLUO7k4?si=4Zjm3y9K90Kja14G
*Assalamu alaikum! Don Allah a taimaka mini da LIKE a wannan Link ɗin gasar rubutu aka saka mana a youtube. Link ɗin nan a sama👆 Na gode sosai*

*Daga marubuciyar*
*Ƙazamin miji,* *Malamin bogi, Bonono, Ruɓaɓɓiyar igiya, Ƴar zaman wanka, ƴan adaidaita sahu, Jalli joga, Ƙara,in inna delu, Beelal da sauransu 09025576222*

CI-MA-ZAUNE

NA

MAMAN AFRAH

🅿️1️⃣2️⃣

Budurwa ce ƴar kimanin shekara ashirin take sakkowa daga matakalar benen sanye take da riga da farare mai pink ɗin plower a gaban rigar kanta babu ɗankwali ta yi parkin na gashin kanta da ribon hannunta rike da waya tana tahowa kamar bata son taka kasa. Fara ce amma kana ganin farin ka san na mai ne don gabaɗaya tabon kuraje ya fito jefi-jefi a fuskar.

Tana gama sakkowa daga step ɗin ta karasa kan ɗaya daga cikin kujerun tangamemen falon da suka kawata shi. Baka jin karan komai a falon sai karan TV da take ta aikinta gabaɗaya kana ganin fuskar budurwar ka san tana cikin ɓacin rai lokaci-lokaci tana saka wayar a kunne sai kuma ya cire ta saki wani guntun tsaki da alama wani take son samu a wayar kuma bata same shi ba. Cilli ta yi da wayar a kan kujerar ta saka tafin duka hannunta ta rufe fuskarta tana jin raunin zuciyarta na karuwa a gefe ɗaya son da take masa tana jin yadda wutar son nasa take ruruwa tana kara yaɗo a dukkan sassan jikinta cikin jini da tsoka tabbas ko da ba a faɗa mata ba ta san ba za ta iya rayuwa a duniya ba matsawar bata tare da SURAJ ba domin shi ne farincikinta kuma shi ne walwalarta matsawar aka samu saɓanin hakan wato bata same shi a matsayin abokin rayuwa tana ganin daga ranar numfashinta zai tsaya za ta yi bankwana da duniyar ma baki ɗaya idan kuwa har mutuwa bata ɗauke ta ba to za ta rayu cikin matsanancin hali da kunci wanda har sai ranar da numfashinta ya bar gangar jikinta don ta tabbatar da son SURAJ za ta mutu!.


"Haba zuciyata ta yaya kike kaunar wanda ba ya kaunarki? Kin san a duk lokacin da aka samu saɓanin zuciyoyi ɗaya tana so ɗaya bata so to dole sai wacce take son ta fuskanci matsaloli da kalubale kai ko da a ce ɗayar nata son ya fi yawa to sai ta yi hakuri ta jure daga wacce nata son ya zama kaɗan" Ta ce a zuciyarta tana tunani wanda take kaunar ma bata gabansa dama ya faɗa mata shi ba ya son ta abin da ta kasa ganewa ta rasa wane irin murɗaɗɗan mutum ne Suraj da duk abin da ya saka a gaba shi yake yi babu ruwansa da kowa.


"Baby Iky" Ta tsinkayi muryar mahaifiyarta, duk kokarinta na son ganin ta danne kwallar da ta taru a idanunta amma kuma sai da ta ganganro da sauri ta sanya hannun nata da ta kare fuskar da shi ta share hawaye, Mummy tata kuwa da sanyin jiki ta karaso ta zauna a kusa da ita ta dafa kafaɗarta tana jin babu daɗi a zuciyarta ganin ɗiyarta tilo a cikin damuwa.

"SURAJ" Mummy ta ambata don ta san duk duniya ƴarta bata da damuwar da ya wuce SURAJ ɗin babu abin da ta nema ta rasa sai shi, shi kaɗai ne matsala da damuwarta ko da hawayenta sum zuba to ta dalilinsa ne.

"Shi ne Mummy tun jiya nake kiran wayarsa amma ya ki ɗauka kuma tana shiga wani lokacin ma sai dai ya katse mini" Ta ce tana kifa fuskarta a kan cinyar Mummyn ta rushe da kuka.

"Ni na rasa yaron nan mai yake takama da shi, duk son nan da kike masa amma a banza to ya yake so ki masa ko so yake ki ciro zuciyarki ji danka masa ya gani sannan ya yarda da son da kike masa" Mummy ta ce cikin faɗa.

"Zan iya komai ma a kansa zan iya ɗayo fatar jikina na shimfiɗa masa ya taka ya wuce zan iya bashi komai Mummy amma ba yarda ne bai yi ina son sa ba shi kawai so na ne ba ya yi" Ta ce cikin muryar kuka.

"Na gaji da wulakancin nan da yake miki kuma ki rubuta ki ajiye sai SURAJ ya so ki kamar ya mutu don duk hanyar sa zan bi sai na bi ko zan yi yawo tsirara kan bin malamai da bokaye sai kin mallake shi, ba wai ke ce za ki shimfiɗa masa fatar jikin ki don so ba shi da kan shi ne zai so ki kamar ya mutu sai ya zo yana durkusa miki yana neman soyayyarki a lokacin ne za ki mayar masa da hannun agogo baya don sai ya ɗanɗana kuɗarsa".

"Ina son ki Mummy in kika mini haka kin min komai a rayuwa, ni kuma duk ranar da na samu damar nan sai ya gwammace kiɗa da karatu don sai ya zama tamkar bawa a fadar saraki sai na wulakanta shi na kaskantar da shi" Ta ce cikin cin alwashi don tana ganin babu wani abu da yake sosa ranta sama da SURAJ kuma ba wai wulakanta ta yake yi ba kawai yana nuna halin ko in kula a kanta wannan ne abin da yake ci mata tuwo a kwarya saboda tana ganin ta fi karfin ko wane irin cin kashi a duniya.


"Yawwa my Baby ai dama maganin kowane shege karen maguzawa kuma in baki musgunawa namiji ba ai ba ni na haife ki ba, ai namiji zuma ne sai da wuta!"


"Shi dai ramin kura kurarre ne kuma sannu-sannu ba ta hana zuwa sai dai a daɗe ba a je ba" Murya Alhaji da ta karaɗe musu kunnuwa ta cika falon.

"Daddy barka da safiya" Ikram (Iky) Ta ce cikin wayancewa.

"Barka" Ya ce kawai yana nufar dining domin karyawa saboda shi dai a duniya ya san bai yi sa'ar mata ba wacce za ta ba ƴarsa tarbiya ingantacciya kullum tufka yake tana masa warwara duk ɗorim da ya yi wa Ikram to sai Mumynta ta sauke mata haddar ta nuna mata nata karatun da bashi da madogatara ko hanyar ɓullewa.

Wata matashiyar budurwa ce ta shigo falon bakinya da sallama tana rike da tire mai ɗauke da filas guda biyu da wasi plates a gefe ta zo ta jera a kan dining ɗin dama ta kawo komai waɗannan ne suka rage. Tana gama ajiyewa ta koma da tiren, Ikram da Mummy ne suka nufi dining ɗin suka zauna Mummy sai wani taɓe baki take tana aikawa Daddy harara. Da kansa ya zuba abin da yake bukata Ikram ce ma ta ɗauki kofi ta haɗa masa tea don ita Mummy dama ya san bata da lokacin masa aiki.

"Allah miki albarka" Ya ce yana ɗaukan cibi (Fork) Ya yi Bismillah ya kai dankali da kwan wanda aka yi wa sorce bakinsa.


"Amin Daddy" Ikram ta ce tana kurɓat tea.


"Mu ma da ba a saka mana albarkar ba tuni namu iyayen sun saka mana" Cewar Mummy tana haɗa custard. Bai kula ta ba don tuni ya bai wa bango ajiyarta, har ya kammala ya ɗauki jakar tafiya office ya fita direba ya ja motar suka tafi.

"Baby zan tafi office fa " Mummy ta ce tana rike da hand bag tata.


"To Mummy ni ma yanzu zan fita scul... Bata kai karshen maganar ba tsohuwar da take kwashe kwanukan da suka kammala cin abinci ce kofin glass ya kufce daga hannunta ya faɗi ya fashe sai ruwan ya fatsu a fuskar Ikram a harzuke ta tashi daga danna wayar da take ta ajiye wayar a kan kujera ta ɗaga hannu hagu da dama ta kai wa tsohuwar kyawawan maruka guda biyu.
.
"Da kyau Baby Iky kin min daidai su talakawa basu san darajar kaya ba gani suke masu kuɗi kamar a bola suke tsintar kuɗin da muke siyan kayan, kuma ki sani a cikin albashinki zan cire kuɗin kofin da kika fasa" Ta ce hankali kwance tana juyawa ta fice abinta.


"Minti biyu na baki ki zo ki sharewa mutane wajen nan sakarai kawai" Ikram ta ce tana haurawa sama. Tsohuwar da take dafe da kuncinta tsabar zafin marin da ya ziyarci fuskarta da ta fara yamushewa saboda girma a kalla ta haifi Mummyn ma amma rashin tausayi da rashin sanin darajar ɗan adam ya sa suke wulakanta duk wani wanda yake karkarshin su saboda Allah ya basu dama.

A hankali ta fita daga falon jikinta yana sanyi kalau ga kuma karkarwa da jikinta yake na zafin marin da yarinyar da ta yi jika da ita ta mata su amma kuma mahaifiyar yarinyar ma tana nuna mata cewar daidai ta yi saboda babu tarbiya da sanin ya kamata.

"Allah na gode maka kai ka san dalilin da ya sa baka bani haihuwa ba da a ce na haihu da ƴaƴana ba za su bari a ci zarafina ba, da a ce na huihu ƴaƴana ba za su bari na taho nema ba su za su nemo mini amma kasancewar bani da ƴaƴa kuma mijina ya mutu saboda nake samun abinci nake aikin nan Allah ka bani hakuri da juriya a kan neman halal"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login