Showing 33001 words to 36000 words out of 52525 words

Chapter 12 - CIMA ZAUNE Complete by Maman Afrah.txt

30 Aug 2025

1765

Ta ce lokacin da take wanke kwanukan a kicin don tana cikin share kofin da ya fashe lkram ɗin ta fito sanye da wani karamin mayafi da ta yi rolling ta fito tamkar ba ƴar musulmi ba ta fice, tana jiyo karan fitar motarta daga gidan.


*SURAJ*


Fitowarsa daga wanka kenan bayan ya saka fararen kaya doguwar tazarce da hula ya feshe jikinsa sa turaruka masu kamshi, sallaya ya shimfiɗa ya gabatar da sallar walaha tare da yin addu'a ya shafa ya ɗakko carbinsa na dannawa white colour ya sakala a ɗan yatsan sa, sumar kansa da take a kwance ya kara fesa mata turaren gashi mai sanyin kamshi ya saka brush kumb ya kara kwantar da ita sai ya ɗora hula jakar office ɗinsa ya ɗauka har zai fita ya tsaya kara kallon gadonsa da yake a ɗame da zanin gado mai kyau wanda jiya Hajiya ta bashi ya shimfiɗa to da ya tashi da safe sai ya kara gyara gadon yana kara yaba kyau da ingancin yadin da kuma ɗinkin da aka yi wa zanin gadon tamkar ba a Nigeri,a aka ɗinka ba. A al'darsa bai yarda kowa ya shigar masa ɗaki ba shi ya sa yake gyara komai nasa amma bai yarda ƴan aikin gidan sub gyara masa ba saboda yana da tsantsani ba ya so ma su gyara masa.


Ɗauke da jakarsa da take sakale a kafaɗarsa ya fito daga ɓangarensa sai kamshin turarensa da yake tashi. Babban falon ya shiga bakinsa da sallama sai da aka amsa sannan ya shiga, har sun zazauna a dining ɗin suna taɓa hira da alama shi kawai ake jira. Kan kujera ya karasa ya ajiye jakar sannan ya karasa dining ɗin kafin ya zauna ya durkusa ya gaishe da Abbansa, sannan ya gaishe da Umminsa.

"Yaya ina kwana"

"Lafiya lau my Ruma, ya saukin jikin ki" Ya ce yana zaunawa.

"Da sauki Yaya gobe zan fara zuwa scul tun da na ware" Yarinyar ƴar shekara goma ta ce tana dariya.

"Yawwa haka ake so Allah kara lafiya".

."Amin yaya"

Ka'idar su idan suka yi Bismillah suka fara cin abinci ba sa magana har sai an kammala.

"Ummi wannan wane turaren wuta ne aka kunna a falon nan mai wani irin daɗin kamshi?" Ya tambaya yana wani lumshi idanu tare da kara baza hanci yana shakr kamshin turaren wutar da ta saka a bunner.


"Yanzun nan Abbanka ma ya gama tambaya ita ma Ruma ta tambaya sai na ce su bari sai ka zo in muku bayanin tare don na san kaima kana zuwa sai ka tambaya" Cewar Ummi tana dariya.

"To muna sauraren ki kar ki makarar da mu wajen aiki" Abba ya ce tana dariyar shi ma saboda rayuwa ce suke cikin farinciki.

"Waɗannan kayayyakin gabaɗaya wajen MAMAN AFRAH na yi oder, kowa na sauya masa bedsheet jiya to wajanta na siya, zannuwan gado ne masu matukar inganci da kwari basa koɗewa basa gashi, ni ma wajen aminiyata na gani na tambaya ta bani no ta. Tana sayar sa zannuwan gado masu bargo, da masu labulaye, da masu filo huɗu da mai filo biyu, tana siyar da turarukan wuta da turare na jiki da na kaya da humra freshner, tama sayar da set na kayan gyaran gashi mai cire dandruf ya sa gashi baki da sheki ga abin wankin banɗaki da na mopping da turaran wanka, atamfifi lesuna dogayen riguna shaddodi har da ɗinkakkun kayan yara masu kyau da inganci abin jin daɗin har sari take bayarwa duk yawan da mutum yake so tana aika masa ko a ina yake"


"Kai irin wannan lissafi Hajiyata kamar wanda kike mata talla sai yabawa kike" Abba ya ce yana dariya.

"Ba yabawa bane Abban yara kayanta ne wallahi babu ha'inci ba cin amana komai ka saya sai ka yaba".

"Au ni Ummi ki bani lambar wayarta tun da gobe za a tashi da azumi wajen ta zan saya kayan rabon salla da zan yi" SURAJ ya ce yana fito da wayarsa daga aljihu".

"Aikuwa ni ma wajen ta zan saya" Abba ya ce yana tashi tsaye don tafiya wajen aiki.


"Ummi bani lambar".

"Ni na tafi sai na dawo idan na dawo za mu zauna sai mu ji yadda za a yi ki mana oder" Cewar Abba.

"A dawo lafiya Allah tsare" Suka haɗa baki wajen faɗa".

"090? Ka rubuta?"

"Eh Ummi".

"09013181851 za ka iya kiranta kuma za ka iya mata magana don da lambar take wtsapp sai ta baka samfura ka gani ka zaɓa"

"Ashe ma har tana tura samfura"..
.

"Eh mana kawai dai bata son wanda ba siya zai yi ba ya mata magana"

."Bari na karanto ki duba mini ko daidai na saka 09013181851".

"Yawwa daidai ce"

"Sai na dawo" Ya ce yana ɗaukan jakarsa.

."A dawo lafiya Allah bada sa'a". Cewar Ummi.

"A dawo lafiya yaya"..

"Amin ya rabbi" Ya amsa musu yana fita.

Alhaji Matawalle da Hajiya Zaituna da ƴaƴan su biyu SURAJ da Ruma suna zaune a Garin Gumel a unguwar wazirawa.


Juyi Dada ta yi idanunta a rufe tana sakin wata hamma, idanun ta buɗe jin karan kiran sallah da sauri ta tashi zaune tana kankame robar dankali tare da kunun ta mayar gefe guda ta ajiye ba tare da ta buɗe su ba tsaye ta mike tana kunna fitilar ta fita ruwa ta ɗauka a buta ta nufi bayin tana jin faɗuwar gaba gudun kar abin da ya faru da ita jiya da la'asar ya sake faruwa da ita na Sani da ya bita.

Da sauri ta kama ruwa ta fito da sauri ta yi alwala ta nufi ɗaki jin koea na gidan ya tashi ta koma ɗaki

"Ke Amina, Hassu, Usai ku tashi mana ko ruwa kwa sha tun da ku kun cinye dankali da kunun naku ai ni kam bana iya ɗoren nan ba shi ya sa na ajiye kayana, ku yi sauri kar a kira sallar ku makara" Ta ce tana zaunawa ta mike kafa ta janyo ƴar robar dankali da kuma kunun nata duk kauɗin nan da take yi Sagiru yana jin ta.


"La'ilaha illallahu muhammadur rasulullahi S.A.W" Dada ta ɗauki salati da mugun karfi duk ta karaɗe ɗakin tana tafa hannuwa karan salallamin da take yi ne ya tashi duk kan ƴan wanda suka yi tunanin ma ko wani gagarumin abu ne ya faru.

"Dada mai ya faru?" Amina ta tambaye ta a firgice ko wartsakewa daga baccin bata yi ba.

Masoyan rubutuna a shiga youtube a mini like a kan littafin malamin bogi ina gdy ss
[8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
*IMZEED VENTURE*
Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna aiyar da gwanjo me kamar sabo!
Tuntuɓemu 07077532253
Wtsapp/IG/TiktocTikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-8yWWJj3GGri&_r=1

*Ku shiga link ɗin nan ku danna min like pls*👇
https://youtu.be/y_DlU3d7lzs?si=LPgsMFnnVlyjZMsW


lCI-MA-ZAUNE


NA

MAMAN AFRAH


🅿️1️⃣3️⃣


"Ya ɗin nan mai ya faru Amina wane ɗan gwafar uban ne ya shanye mini kunu da dankalin da na ajiye zan yi sahur?" Ta ce tana dangwarar da robar can gefe robar ta suka gangara suna gwaruwa da juna.

"Dankali da kunu kuma Dada?" Hassu da Usai suka faɗa cikin mamaki ita ma dai Aminar mamakin take don ta san daga ita har su Usai babu wanda zai ɗauka mata amma abin mamakin da tambayar waye zai shigo ɗakin har ya je ya ɗauki dankalin da kunun a gaban Dada?.

Fitowar Sagiru daga ɗaki yana sakin ƴar gyaran murya da yin hamma lokacin da ya zo tsakiyar falon.

"Ke Amina mene ne dalilin da za ku fara yi wa mutane hayaniya da asubar farin nan duk kun hana ni bacci bayan idan na tashi ba wani abun sahur za ku bani ba ai sai ku barni in koshi da baccin " Ya ce cikin ɗan faɗa-faɗa mai kama da na mai burin kunya zai naɗe tabarmar kunya da hauka. Cije baki Dada ta yi tana jin mugun haushin Sagiru ga haushin marin da ya yi wa Amina jiya ga shi kuma yanzu yana musu wata magana ta rainin hankali wanda ta ma kasa gane dalilin yin hakan sai take ganin kamar ma mantawa da ita yake yi in yana abu kamar yana mantawa sirikarsa ce ita.

"Wai ni kai Sagiru mantawa kake akwai uwar Amina a ɗakin, sai ka ce wasu mararsa galihu a ce mu da bakinmu da Allah ya tsaga mana ba za mu yi magana ba"

"Ni fa ba haka na ce ba kawai dai gani na yi ba wani abu bane da za a dinga ka ce na ce"

"Saboda ba abincin uwaka bane ko? An zambaɗa mini zabgegiyar sata an sace mini kunu da dankalin sahur amma ni da ƴata da jikokina mu jajantawa juna ba".

"Yanzu Dada dama a kan dankali sa kunu ne ake wannan hayaniyar.?"

"An yi, na ce an yi tun da dai ba wani ne zai kawo mini ba ai a gidan nan da satar kunu da zinare duk ɗaya ne" Dada ta ce cikin hargowa don gabaɗaya ya kawo ta wuya ji take kamar ta danne wuyan shege ta yi da jibga har sai ya daina numfashi don yanzu zarginta ya bata cewa shi ne kaɗai zai iya sace mata abin sahur ɗin tun da jiya ya ce a bashi na buɗa baki an hana shi, shi ne ya sace na sahur ɗin don ta san su Hassu da Usai ba za su ɗauka ba bare kuma Amina.
.

"Kowa ya fito kafin mu bu ɗaki-ɗaki nu fito da mutane" Suka tsinkayi muryar Sani yana faɗa a tsakar gida, wani irin kartawa cikin Dada ya yi Hassu da Usai suka fara makyarkyata.

"Wayyo mun shiga miliyan" Sagiru ya ce a tsorace yana yin hanyar ɗakin da ya fito a maimakon ya yi waje. Dif-dif-dif suka ji karan gudu daga kowane ɓangare da alama mutanen gidan ne suka fara fitowa daga ɗakunan don su amsa kiran Oga Sani.

"A fito a yi sahur" Suka kara ji ya faɗa.

"Yo ai shikenan ta kwana gidan sauki kun ji mun samu abincin sahur" Dada ta ce tana tsitstsilla idanu.

"Dada tun da kika ji wannan kiran ba na lafiya bane watakila ma aljannun jikinsa ne suke buɗe masa idanu yake ganinsu suna sahur

"Yo kuma dai in kin ji kira ai samu ne" Hassu ta ce

"A kiran mahaukaci ai sai dai a ce in an ji kira wahala ce" Amina ta ce cikin sanyij murya.

Daga can ɗakin Baffalo suka fara jim ya yi gyaram murya da karfi ya fara rafka kiran sallah, da yake ɗakinsa yana jere da na Amina.

"Duk wanda bai fito ba yanzu aljannu za su bi ɗaki -ɗaki su goyo shi su fito d... Ruuuu aka fara ƴar tsere Sagiru ne ya fito daga ɗaki a guje rigar a wuyansa ya sakala kan bai saka hannayen ba ya ji wannan maganar ta Sani, hakan ya sa ya taho ba tare da ya tsaya saka hannuwan rigar ba, don ba zai juri ganin aljannu sun goyo shi a bayansu ba, domin daga lokacin da suka goyo shi to watakila kwanansa ya kare.

Dada da take zaune kafafu a mike jin furucin a take ta shiga dafa kasan da hannu biyu ta mike tana saurin taro zaninta da yake neman kuncewa gudun kar ta yi tsirara a gaban siriki ta rike zanin da sauri ba tare da ta ɗaura ba ta nufi hanyar fita jin ana zancen aljannu za su goyo wanda bai zo ba. A kofar ɗakin har kusan karo suka yi da Sagiru da zai fita shi riga makale a wuya ita zani rike a hannu.

Amina ce ta mara musu baya Hassu ganin Usai a gabanta ita ce a karshen baya ta riko rigar Usai kiiiii suka fito wajen tamkar yara masu wasan motar kara.

Baffalo kuwa dama jin Sani yana kiran a zo sahur jikinsa ya bashi wata ukubar ce saboda ya san ruwa ba ya tashi banza dama gama sahur ɗinsa kenan ya ji wannan kiran hakan ya sa ya shiga rafka kiran salla da karfi wanda ya cika gidan a tashi dibarar don a ce sallah yake amma jin ana batun aljannu za su goyo wanda bai zo ba hakan ya sanya shi ya yayumo sallayarsa da wani dogon carbinsa ya fito gajeran wando ne ma a jikinsa.

Kowa ya fito an hallara a tsakar gidan da ya samu wadatuwar hasken farin wata.

"Ku je ku ci abinci jama'a" Sani ya ce yana bushewa da wata dariyar su ta mahaukata, gabaɗaya sai aka fara kallon-kallo ganin abin da yake kira da suna abinci. Foo ɗin da yake kashi ne shake da kashin sa a ciki ya ajiye a tsakiyar gidan wai shi ne yake cewa abincin da za a yi sahur.

"Ni dai Sagiru ka cuce ni da ka sa na rabo kauyanmu ina can cikin rufin asirina ka sa na kwaso yara na taho don son in murmure amma ga shi sai gashin kuma nake sha, kuma babu damar na koma kauye a dame ni da gori watakila ma shan ruwa ya gagare ni" Cewar Dada a zuciyarta ganin wai kashi za su ci yau kuma.

"Duk wanda bai ci ba aljannu ne za su masa ɗura... Kafin ya gama faɗa su duka suka fara rige-rigen zuwa gaban foo ɗin suna jin takaici.

"Wannan gidan haya ko gidan jaraba haka kawai an zo an haɗa mahaukaci da masu hankali a gida ɗaya saboda son kuɗi a bai wa mai hankali haya a ba mahaukaci ... Muryar Kakar Sani ta katsewa Baffalo tunani

"Ka yi hakuri ɗan Inna ba a cin kashi"

"Kowa sai ya ci kashi har da ke ma" Ya ce yana nuna ta da yatsa tare da bushewa da dariya.

Su duka a gaban foo ɗin suka yi kawanya wani wari duk ya cika wurin. Gabaɗaya babu wanda ba ya hawaye yarbawan nan ma su duka kuka suke marar sauti amma kaf an rasa wanda zai fara cin kashi.


"Ai dama tsohuwar nan mai gararambar tsiya ka sa ta cinye na san duk tsiya idan ta cinye kashin nan dole ta kama gabanta ta koma inda ta fito dan jaraba ko gama wankar amarcin ban yi ba sun zo su tare mini a ɗaki" Sagiru ya ce yana aika mata da wata muguwar harara a fakaice.

"Kashi ne sarki kowa zai ke zagaya shi yana rawa yana masa waka" Sani ya ce yana tsalle. Tun kan ya rufe bakinsa an hau layi an yi kawanya an fara rawa Dada ce a gaba sai Sagiru sai Baffalo sai sauran suka take musu baya, ana ta wake kashi ana rawa kwata-kwata Dada ta manta da wani siriki Sagiru haka shi ma ya manta da ita. Har sai da gari ya yi haske sannan suka watse zuwa yin alwala suka yi sallar shi kwa gogan Sani bacci ne ya yi awon gaba da shi a zaune.

Sallah kowa ya yi azumin kuwa waɗanda basu yi sahur ba ɗore suka yi bare su Dada dama da basu da abin sahur ɗin. Duk da haka dai zuciyarta bata daina bata cewa Sagiru ne ya sace mata abin sahur ba.

Yau abin mamaki Sagiru tun da yamma ta dawo rike sa wata bakar leda da babu wanda ya san mene ne a ciki, da farko ma Dada ta ɗauka kayan buɗa baki ne ya kawo amma ganin bai ba Amina ba kuma ya shige ɗaki Dada har da ce mata ta yi saurin zuwa yau ya yi abin kirki dama yau garin tuwo ne Dadar ta bada aka siyo ake tuwo da miyar busasshiyar kuɓewa, sai dusa da aka aunowa akuyar kwano ɗaya, aka tsakura mata sauran tana ɗaki a ajiye ta fi rabin kwano tun da bata kwata aka bata ba.

"Ya na ganki kin dawo hannunki yana dukan cinya?" Dada ta tambaye ta rai a ɓace sai muzurai take.


"Kayan sakawarsa ne a ciki ba abin ci bane" Ta ce cikin sanyin jiki don ganin ran Dadar ɓaci.

Har aka kusa shan ruwa amma Sagiru bai it
fito ba daga ɗakin ba.

"Dada ina ga fa don a yi kashin abinci da shi ya dawo gida" Usai ta ce cikin raɗa .


"Ai bar ɓata bakin ki yarinya don faɗa ma ɓata baki ne don kuwa ya yi tsarara kamar shayi ko a daginsa ba zan bashi ba" Ta ce cikin faɗa.

Ana fara kiran magriba Amina ta ɗauki ruwa ta kai masa amma abin mamakin sai ta same shi a tsaye yans ta kewaya ɗakin da alama dai ko wani abu ne yake damunsa. Tana shigowa ya yi saurin zaunawa yana damke bakar ledar da ya shigo da ita sosai rashin gaskiya muraran ya bayyana a tare da shi.

."Amin mai ya sa bakya sallama wai haba sai ku shigo ɗaki babu neman izini " Ya ce yana muzurai.


"Na yi sallama sai dai ko kai ne dai baka ji ba"

"Kar ma ki ajiye mini bakin ruwa don ba sha zan yi ba ku bakwa bawa mutum abinci sai wani ruwa a ce ka kai azumi guda amma a haɗa ka da ruwa salon cikin ka ya kulle" Ya ce yana kauda kai gefe.

Wani kululun bakin ciki ne ya tsaye mata jin furucinsa wato ita yake so take ciyar da shi bayan ɗawainiyar hakkinta a kansa take ko kuma abincin da mahaifiyarta take tsakura mata yake so ta bashi ita ta hakura. Juyawa ta yi da ruwan za ta fice.


"Ai sai ki zo ki ajiye"
Ba tare da ta ce masa komai ba ta zo ta ajiye ta juya ta fita tana fitowa falon ta ga su Dada suna shigowa ita ma wuri ta samu ta zauna. Suna cin tuwon ya fito daga ɗakin rike da bakar ledar Dada ce ta bi ledar da kallon tana jan dogon tsaki a zuciyarta.

'Aikin ɓur in ji tusa, wallahi an

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login