Showing 21001 words to 24000 words out of 52525 words

Chapter 8 - CIMA ZAUNE Complete by Maman Afrah.txt

30 Aug 2025

1756

ya ce

"Ko tare za mu koma?"

"Ina ɗin?" Dada ta tambaya cike da mamaki.

"To ai na ga kun ki fita ko dai kuɗinku kuke lalewa wanda kika kara mini wato ɗari biyu?".

"Kai bana son iya shege kuɗin me zan lale a zama a cikin adaidaita sahu ni in banda larura ma auren namiji da ƴaƴa ai ba zan shiga adaidaita sahu ba sai dai a kai ni duk inda zan je a mota"

"Yanzu dai ga shi adaidaitar ya miki ranar da motar bata miki b...

"Kai yaro kar ka mini rashin kunya in za ka kai mu inda za mu je to idan kuma ba za ka je ba mu nemi wani ya kaimu don kuɗi ba matsalar mu bace yadda nake surikar mai sadaka da makeken gida ai sai dai tayar mota ta yi kuka"

"Wai ina kike so na kai ku ne? Na kawo ku har kofar gida amma sai maganar a kai ku kike haba don Allah kuna ɓata mini lokaci ni da na fito nem...

"Ban gane ba to ko dai saɓo kake son yi ai ko ni da nake kauye gidan da nake zaune ya fi wannan sau goma idan baka san gidan ba ai sai ka mini bayani amma ba borin kunya ba kana neman ka naɗe tabarmar kunya da hauka" Ta katse shi cikin ɓacin rai.

"Ni kam na ɗebo ruwan dafa kaina ni dai wannan gida aka kwatanto mini in kawo ku".

"To tun da uwarka ta haifeka ka taɓa jin mai suna Alhaji ya shiga irin wannan gidan, ai sai dai talaka talakan ma fukara'u"

"Ni ku fita mini a adaidaita" Ya ce cikin kufula don ya ga sun ki fita wato ba niyya ango ya kwana da wando.

"Kai ku fito daga kwaraɓaɓɓan gwangwanin nan, ina dalili za a ke gaya mana magana a kan adaidaita ai ba girma na bane ku fito mu tare wata kila da tambaya ma je gidan Alhaji Sagiru tun da matambayi ba ya ɓata" Dada ta ce daidai lokacin da ta fito rike da igiyar akuyarta akuyar sai faman meee take, haka suka shiga fito da himilin kayansu su Hassu ma suna ta masa fitsara da tsaurin idanu. Yana shirim jan adaidaita sahun sai ga Sagiru ya fito daga cikin gidan yana sakin wata doguwar hamma. Da mamaki su Dada suke bi sa da kallo don ya musu kama da wani wanda suka sani. Sanye yake da wani yafi ruwan omo(Blue) Yadin ya ci gidansu duk ya yi gashi har da inda ya ɓarke daga kafaɗa.

Shi dai Sagiru bai gansu ba da yake yunwa ce take addabarsa.

"Lah Dada wallahi mijin anty Amina ne" Hasuu ta ce da ɗan karfi wanda ya sanya Sagiru maido da hankalinsa kanta.

A daidai nan ne mai adaidaita sahun ya tafi a ransa yana raya yauma tublar sara,il.

Baki sake Dada take kallonsa don ta tabbatar ba wai kama yake da Sagirun da suke nema ba anya ba kama bace suke yi da wancan? To idan ma kama suke yi ai gwara mu sani. Sagiru kuwa har sai da ya zaro idanu ganin Dada da jikokinta yana jin kunyar kayan da yake jikinsa.

Wani yamushashshan yadi ne ya gama jin wuyar duniya amma a haka yake lallaɓa shi ga kuma uwa uba kayan ma kamar ko wanki basu da shi in ma suna da wankin to wannan ba karin farko bane da alama an saka maimaici ne wannan. Dada wani irin bugawa zuciyarta take lokaci guda yawun bakinta ya kafe a take wata iska ta busar da laɓɓanta da suke da ɗan damshi so take ta yi magana amma ta kasa harshenta da laɓɓan bakin sun gagara bata haɗin kai ta furta komai dakyar ta yi yaki da hannunta ta ɗaga yatsanta manuniya ta nuna Sagiru a lokaci guda fargaba da wani abu wanda take ganin yana kama da da na sani suka ziyarci kwanya da zuciyarta. Tuno da irin tijarar da ta yi wa mijinta a bainan nasi a kan sai ya barta ta taho har ma da ƴan gari da take ta famkamar gidan siriki ita da ta ɗakko wata guda har da ɗoriya za ta yi azumin ramadan kai a takaice ma dai sai an ganta yanzu kuwa ai karya da ciwo ta ce za ta koma gida tabbas ko daga bacci ta tashi wannan wanda take gani a gabanta ba wai kama yake da Alhaji Sagiru mijin ƴarta ba tabbas ko tantama bata yi shi ne domin kuwa shi ma yana ganinsu duk ya sha jinin jikinsa dama masu iya magana sun ce marar gaskiya ko a cikin ruwa yake sai ya yi gumi.

"Sa,Sa,Sa" Dada take ta ambaton Sa a nufinta so take ta furta Sagiru wannan karon da alama ta janye sunan Alhajin daga jikin sunan nasa wanda saboda sa rai har ma take lakabawa ƴarta Hajiya.

"Sagiru" Ta samu nasarar warto kalmar sunan daga bakinta.

"Dada babu Alhajin yau" Hassu ta tambayeta cike da shekiyanci duk da ita ma ta girgiza da lamarin amma tana so ta ga yadda diramar za ta kaya.

"Na yi kutubol da sunan Alhajin Sagiru zan ce kema shegiyar yarinya mai bakin kamar an ɗaga shantu sama" Ta faɗa a fusace tana jin kamar ta kama Sagiru da Hassu ya yi ta duka ko ta huce daga takaicin da take jin zuciyarta a ciki.

"Ta bi sunan Alhajin da gudu ba takalmi" Usai ta ce tana danne dariyarta saboda yadda Dada gabaɗaya ta shiga tashin hankali abin tamkar ka zauna kake kallon fuskarta kana sha dariya.


"Sannunku da zuwa Dada" Sagiru ya yi karfin halin furtawa a kokarinsa na ganin ya naɗe tabarmar kunya da hauka.

Wannan furucin ne ya tabbatarwa da Dada zarginta ya zama gaskiya tabbas Sagiru ne ba mai kama da shi bane kuma ba gizo yake mata ba. A maimakon ta amsa sai ta ɗaga kai tana karewa gidan kallo gidan da ya dace ya amsa sunan mutuwa kusa yadda ya kusa ruftawa ka san dab yake da ya rushe musamman in lokacin damuna ya zo, da a ce bata ga kayan jikinsa ba da sai ta ce ko taimako ya kawowa mutanen gidan amma ganin suturar jikinta ya tabbatar mata da cewa daga gidan yake.


'Kika sani ko yana cikin masu kuɗin da basa sin a san suna yin alkairi ko ɓadda kama ya yi ya kawowa mutanen gidan sadaka' Wani sashi na zuciyarta ya kai mata wannan tunanin. Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke har ta ji ɗan dama-dama a ranta wannan tunanin tana fatan ya zama gaskiya hakan ya sa ta ɗan tattaro karfin da ya rage a sauran jikinta wanda bai salwanta ba sanadin tashin hankalin da take ciki ta ce

"Ina Aminar kuwa?"

"Tana ciki" Ya ce yana nuni da cikin gidan duk ya wani haɗa uban gumi saboda kunya.

'Watakila tare suka zo kawo taimakon ita ta tsaya bata fito ba' Zuciyarta ta sake raya mata hakan.

"Yanzu za ta fito itama?"

"A'a tana kulla daddawa da kukar kaɗi ne" Ya ce cikin sanyin jiki.


"Shikenan ta faru ta kare an yi wa mai damu ɗaya sata, wato dai a gidan nan suke da zama na shiga uku ni Saude yanzu Aminar ce take kulla kalwa da kukar kaɗi na siyarwa ne ko na mene ne?' Ta jefawa zuciyarta tambaya.

"Shikenan Anty ta koma mai kalwa da kuka" Hassu da Usai suka haɗa baki wajen faɗa.

Tsabar takaici Dada bata kara furta komai ba, domin tana buɗe bakinta watakila kukan takaici ne zai fito don haka ta tafi fuuu kamar za ta tashi sama ta nufi kofar shiga gidan gadan -gadan Sagiru da yake tsaye a kofar gidan da sauri ya matsa ya bata hanya ganin za ta bangaje shi.

Da kallo ya bita idanunsa a kan ƴar kosasshiyar akuyarta wacce koshin nata ta nuna tamkar tana da juna biyu. Hassu da Usai ma baya suka take mata suna aikawa Sagirun sakon harara.

"Salama alaikum" Dada ta buɗe baki take rafka sallama, wata tsohuwa da take wajen jigon dabobi tana basu abinci ta ɗago ta yi wa Dada kallo ɗaya ta kauda kai gefe tana cigaba da abin da take yi ba tare da ta kalli ko iskar da ta ɗakko Dadar ba bare har ta amsa sallamar ta.

"Wai ba kowa a gidan ne ake sallama babu mai amsawa" Hassu ta ce cikin muryar irin ta gagararru mai kuma shige da muryar ƴan daba.

"Wa kuka ajiye don yake amsa muku sallama idan kuma kun matso sai an amsa sai ku biya kuɗin amsawar'' Matar nan ta ce cikin halin ko in kula.

"Ikon Allah na kwance ya faɗi yanzu don tijara dambe sa kishiya sallamar ma sai an biya za a amsa? Ni in ba larura ba ma mai zai kawo ni na sako kafa a wannan gidan mai kamar makabarta ai da ganin gidan nan ya ci sunan tafi da farin likkafaninka saboda ko yaushe zai iya rushewa ya danne mutum" Dada da ranta yake dama a kololuwar ɓaci ta ce

Ko kallon su matar bata yi ba ga gidan da girma sai wasu kashin nakuna kashi-kashi tamkar an yi kashin dankali a kasuwa, hakan ne ya sanya ma suka kasa gane inda za a samu Amina to ga shi sai artabu ake wajen amsa sallama bare a tambayi inda take.

"To Dada amsar sallamar dole ne rabu da ita kawai" Usai ta ce cikin tsiwa.

."Kaka zan yi" Wani katon saurayi da ya fito da wani katon foo na kashi kato yana tsotsar babban ɗan yatsan sa.

"Allah sarki kashin ne to maza je ka banɗakin ka hau foo ɗin in ka gama sai in je in zubar" Tsohuwar nan ta faɗa cikin karya harshe da lallaɓawa.

"Ni dai ke za ki je ki ɗora ni" Ya ce cikin ɓaci

"Yi hakuri ka ji ɗan kirki maza jeka zan siyo maka alewa" Da sauri ya wuce ya shige bayin inda ya bar su Dada da sakakken baki mamaki al'ajabi ya gama baibaye su ita kuma tsohuwar ta ɗauki wata katuwar silba daga gaban wata tinkiya ta juya ta nufi wani ɗaki daga can ɓangaren da wannan saurayin ya fito ta shige ɗaki.


Suna shirin juyawa domin tambayar Sagiru inda Aminar take sai ga wani matashi yana busa sigari yana rike da kare wanda ya saka masa wata sarka a wuya daga ya cire tabar sai ya saki fito tamkar an hura usur.

"Baby sannunku da zuwa gidan yawa" Ya ce yana yi wa Dada wani kallo tare da busa mata hayakin taba a fuska. Da baki sake suke binsa da kallo don ba maganar babyn ma ba da su Hassu yake ba da Dada take wai ita ce baby. Shi ma wani ɗaki ya shige daga can ɓangaren da suke jere daga inda suke wato na biyun karshe.

Shigowar Sagirun ne ya dakatar da su daga saka da warwarar da suke wato sakar jaki.


"Ga can ɗakin Aminar" Ya ce a wani yatsine lokacin kamar ma bashi ne ya ji kunya a waje ba hankalinsa kwance wannan lokacin har wani fisga yake yi. Yana gama faɗar hakan ya musu nuni da ɗakin ya sanya hannu a aljihun wandonsa yya juya yana wani bobbokara tamkar wani mai doro su duka ukun sai sa suka bi bayansa sa kallo har ya fice daga gidan.

'Na ga annabi in na yi hali na gari ni Saude wane irin miji na aurawa Amina kuma' Ta ce a zuciyarta tana jan igiyar akuyar tata suka nufi ɗakin da ya musu nuni da cewa nan ne ɗakin Aminar lokacin ma ana ta kiran sallar azahar. Hassu da Usai ne suka yi karfin halin yin sallama a kofar ɗakin amma ita Dada kasake ta yi tana bin ɓurjajjan kofar ɗakin da kallo. Amina da ta yi nisa cikin tunani tana rike da ledar da take kulla kukar miya babu zato ba tsammani sallamar su Hassi ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lulu har bata san lokacin da ta yi jifa da ledar hannunta ba ta taso fa nufo su. Da gudu suka yo wajen suka rungumeta Dada kuwa kallon abin take kamar almara yadda Amina ta yi wani mugun baki ta rame tamkar ta shekara tana jinya.Wata kwallar tausayin Aminar ce ta cika mata idanu tana ji a ranta ta ma rasa ma'aunin da za ta ajiye tunanin abin da yake faruwa fatan ta ɗaya Allah sa mafarki take don idan gaskiya ne to tabbas ta kaɗe har ganyenta. Sagaggun kafafunta ta ɗaga itama ta shiga ɗakin jiki sanyi kalau tana shiga ta yi wa idanunta masauki a kan kuka da kalwar da Aminar take kullawa. Wani irin kankance idanu ta yi saboda yadda take jin zuciyarta tana mata zafi.

"Anty kin ganki kuwa" Hassu da Usai suka faɗa suna tattaɓa jikinta. Bata iya ce musu komai ba sai ta kawar da zancen da cewa

"Ku kwashe kayan ku ajiye a can" Ta ce tana musu nuni da kusurwar ɗakin. Dada kuwa har lokacin tana rike da igiyar akuyarta wacce take ta meeee.

"Dada sannunku da zuwa ku zauna ga wuri, wannan akuyar fa ya aka yi kuka taho da ita?" Ta ce tana nunawa Dada buhun da yake shimfiɗe a tsakar ɗakin. Ita Dada tamkar an yi wa bakinta dabaibayi haka take ji ta kasa cewa ko da kanzil dakyar ta yi yaki da bakinta ta ce

"Amina wai mai nake gani haka kamar almara? Wa na aura miki ne amma na san ko karayar arziki ne ya same shi bai ci a ce kun samu kan ku a cikin wannan bakin talaucin ba"
Shiru Aminar ta yi hawaye yana gangaro mata ita ba talaucin ne damuwarta ba ma yadda Sagirun yake CI-MA-ZAUNE babu sana'ar sisi bare kwabo, sai zaman yunwa kawai sai dai ya ɗora rai a ƴar sana'ar da take yi ta siyar da kuka da kalwa ko yanzu ma a cikin kuɗin ne ta bashi ɗari da hamsin wai zai siyo musu rogo wata rana ma sai dai su zauna sa yunwa idan bata da kuɗin ya gwammace ya kwanta yana baccin asara.

"Ba magana ba nake miki Amina" Dada ta zafice ta cikin takaici.

"Dada CI-MA-ZAUNE ne kika aura mini bashi da sana'ar komai almajirci ya zo nan garin bashi da kowa ma a nan, gidan wannan ma gidan haya ne tun a ranar da ka kawo ni ya fita da kayan lefen ya ɗakko ni ya dawo da ni wannan gidan" Ta shiga basu labarin komai salati Dada ta shiga rafkawa tana yi tana maimaitawa daga ta kai karshen salatin sai ta sake kamo wani.

"Na shiga uku ni Saude yanzu fakiri ne dama na aura miki na je na addabi jama'ar kauye da kuri da tinkaho ina ɗagawa kishiyoyi kai ni ga mai ƴa tana auran mai kuɗi har da kai Malam wajen mai gari kara a kan ya barni in taho mu yi azumi a gidan hutu har da akuyata na taho ita ma ta murmure ashe dai gabaɗaya namijin hotiho ne ina zan kai wannan abin maganar ni Saude " Ta kai karshen maganar tana zaunawa daɓas a kasa tare da sakin igiyar akuyar hannunta da take ta faman meeee sai Usai ce ta rike igiyar Dada kuwa wani uban tagumi ta buga tamkar an aiko mata gagarumar mutuwa.

*Masoyana ina neman arziƙin ku shiga youtube ku danna min like👍 a kan labarin MALAMIN BOGI gasa ce na shiga da littafin kuma da like za a tantance ina gdy ss* *Ko kuma ku shiga link ɗin can na saman page na youtube direct zai kai ku sai ku min like*

MAMAN AFRAH
09025576222
[8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
*IMZEED VENTURE*
Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna aiyar da gwanjo me kamar sabo!
Tuntuɓemu 07077532253
Wtsapp/IG/TiktocTikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-8yWWJj3GGri&_r=1


*Ku shiga link ɗin nan ku danna min like pls*
👇👇👇👇👇

https://youtu.be/eEW4fiSAxOg?si=koWZsBTo1F3rQZb8

*CI-MA-ZAUNE*


*NA*

*MAMAN AFRAH*
*Marubuciyar*
*Malamim bogi* , *Ƙazamin miji, Bonono* , *Ruɓaɓɓiyar igiya, Ƴan adaidaita sahu, Jalli joga, Ƙara,in inna delu, Beela, Ƴar zaman wanka da sauran su*
*09025576222*

🅿️9️⃣


Gabaɗaya sun shiga jimamin abin da ya faru don ita Dada ko magana ma bata yi saboda takaci tana ganin duk laifinta ne da ta aurawa Amina wannan mijin amma dama cikin rashin sani ne da ta san haka yake da ta gwammace Aminar ta yi ta zama da Alhaji Sabo duk da yana da larura dai amma ba a rasa abinci ba duk kaskancin abincin kuwa yanzu ta yarda da ake cewa kwaɗayi mabuɗin wahala kwaɗayi kuda ya wahala tun da gashi basu da tsuntsu basu da tarko. Babban ɓacin ranta ma yadda ta kwaso su Hassu har da akuya suka taho gashi yanzu sun gama yaɗawa cewa su tafi birni a can za su yi azumi duka kai cewa ma suke sai an gansu idan kuwa suka koma lallai har sai an saka su a waka kai sai fita ma ta gagare su a kauyan domin gori dai har da goriba sai an musu. Dada ban da yunwa da take addabarta babu abin da suke ji Amina ce ta kama akuyar ta je ta ɗaure ta a wajen da ake ɗaure dabbobin gidan sai da ma suka mata jigo don gudun gutsiri tsoma. Sagiru dai tun da ya fita bai dawo gidan ba tun suna sa ran zai dawo ya kawo ɗan abin saukar baki kai ko da ma rogon da ya tafi siya ne amma shiru tamkar malam ya ci shirwa sai Dada

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login