Showing 27001 words to 30000 words out of 52525 words

Chapter 10 - CIMA ZAUNE Complete by Maman Afrah.txt

30 Aug 2025

1754

yi ihu don a kawo mata ɗauki amma tana tsoron ya fille mata kai da addar don ta ji Amina ta ce idan aljannunsa suka zo ƴan gidan ma kowa ta kansa yake har kakar tasa kuwa.


Matsowa ya yi Dada ta sauke idanunta a kan fuskarsa da akalla za ta yi wata baya ga ruwa ba sai wani tashin wari yake, matsowa ya yi yana kallon saman banɗakin yana surutai abin da ya kara ɗagawa Dada hanlali kenan yanzu ne take tabbatar da cewa aljannu dubun ne a bayin kamar yadda ya faɗa, a haka ya karaso dab da Dada yana nuna mata addar nan da take ganin kamar kai ai fille mata da ita, nuna ta da addar da yake take yanke wata tusa marar sauti ta kwace mata hakan ya tabbatar mata da alwalar da ta yi karye.

"Taho amarya ki bar guduna kar aljannu su ɗauki mini ke" Ya ce yana wani girgiza jiki Dada sai gangaroear hawayen da bata san da zamansu a kwarmin idanunta ba ta yi.

Tana ji ta gani ya zo ya mika hannu ya kamo hannunta babu musu ta bi umarnin da zuciyarta take bata na kin bijire masa kar ta yi wasa da numfashinta ya aikata barzahu da addar nan.

Bata tantance ba sai ji ta yi ya fisgeta kaɗan su wuntsila daga ita har shi ɗin. Sai da ya kawo ta gabansa tana danne kukan da yake neman kwace mata gudun yin laifi. Ga yunwa ga fargaba yana kawo ta gabansa baya san lokacin da ta durkusa ta ce
.

"Ina wuni Babana y...

"Ni ba babanki bane"

"Tun da an gama bikin ka bar ni in tafi sallah zan yi"

"Ai biki a gaba za a fara mana ni da ke ne amarya da ango ni ba babanki bane tashi kar ki ɓata kayanki masu kyau" Ya furta cikin wata murya mai kamar tsawa ya mata kana kallonsa ka san yau a cikin hauka yake tuburan. Babu shiri Dada ta mike tsaye a zuciyarta tana ja wa Sagiru Allah ya isa don shi ya ja mata kowace masifa da take ciki da a ce yana gidan kerarre ai da tuni suna can suna jiran a yi magriba su yi asuwaki da naman kaza. Tana mikewa ya juya a hankali ya tafi bakin kofar bayin ya tsaya dama ba wata kofar kirki bace a jiki shi ya sa ma ya shigo Dadar tana ciki.


Bake-Bake ya yi a bakin kofar ya bata baya sai kuma ya tattale kafafunsa, ganin hakan Dada ta fara shirin arcewa don bata son wani tsautsayi ya ritsa da ita, tun da in ba tsautsayi ba ta yaya za a ce kana keɓance da mutum da ba cikakken hankali gare shi ba kuma yana ɗauke da makami. Wata dibara ce ta faɗo mata don ita har ga Allah bata shirya mutuwa yanzu ba duk da dama mutuwa ba shirya mata ake ba zuwa kawai take yi bagatatan.

Auna tsakanin kafafunsa take wanda ya tattale, take auna kofar don so take ya shammacesa ta bi ta tsakiyar kafafun ta tsira in ya so in ta fita ta yi ta kanta don ta san yanzu ko ihu ta yi babu mai ceton ta. Ganin hankalinsa yana ga surutai mararsa kai da kafa ya sa ta lallaɓa ta shige kofar kafafun nasa, sai da kanta da kafadarta suka fita ta farw hango tsakar gidan kamar an yi shara babu kowa wannan ya kara tabbatar mata da akwai gagarumar matsala matsawar bata kuɓuta ba. Sani kuwa jin an shiga tsakanin kafafunsa sai nasa sauran hankalinsa ya bashi ya matse kafafun, Dada tana ji aka matse saitin cikinta wanda yake kiran ciromawa ba ma ciroma ba.

Tana cikin haka sai ji ta yi ya zauna a bayan nata.


"Kai jama'a yanzu katon gardin nan ne a bayana bayan ina da igiyoyin aure a kaina kai ai in aka ce maka babu hankali to sai ta Allah" Ta ce a zuciyarta tana dukufa wajen addu'a a zuciyarta Allah ya sa ya ɗaga ɓata baya don tana ganin idan aka jima bayanta zai haɗe da cikinta ko dai ta sume don wahala. Kamar an tsikare shi ya tashi daga bayanta ita ma sai gata a tsaye tana rarraba idanu. Bata ankara ba sai ta ga ɗakko hular kansa ya saka mata.

"Kar ki cire"

"To" Ta ce tana kara gyaɗa kai. Riga ɗaya ya cire ta atamfa ya ɗora mata a kafaɗa, ya kara ciro wata ya ɗora mata a kanta wato a kan hular kamar dai mayafi haka ya mata. Babu yadda ta iya tana gani ya ɗauki addar ya kama hannunta suka fito daga bayin yadda aka damke hannu Dada kaɗai ya isa ya nuna maka ba mai hankali bane ya yi rikon.


Sai da suka zo tsakiyar gidan ya ɗaga addar nan ya karta a kasa, lokacin kowa ya lura da abin da yake faruwa don haka wanda suke cikin ɗaki suka banko suka saka sakata kakar Sani wato Inna da ta je baiwa dabbobi ruwa kamar an ce ta juyo lokacin ya yi daidai da karta addar da ya yi ai tana ganinsa da tsohuwar da suka zo jiya da rana wato bakin Amina amarya mai daddawa kamar yadda suke mata lakabi ai bata san lokacin da ta mika hannu ba a maimakon ta ɗauki daron robarta wanda bata so a barshi su fasa mata. Karamin ɗan tinkiyar da aka haifa ta sunguma cikin rashin sani ta arce ɗaki a guje shi ma ɗan tinkiyan sai ya shiga mutsu-mutsu yana son kwacewa amma Inna ta ce da wa Allah ya haɗa ta in ba da shi ba ta kankame shi a gefen hamatarta sai gudu ta shige ɗaki ta banko tana mayar da numfashi don ta san yau yadda kan nasa ya motsa har ta ɗau adda to sai mai sauran kwana don ta san in ya yi wa Dada da arziki yi wa namanta filla-filla ba gutsin-gutsin ba.


Tunkiyar da Kakar Sanin ta ɗauke mata ɗiyarta ita ma ta hangame baki tana kuka ganin an tafi mata da ɗa sai fisga take tana son sincewa daga jigon da aka ɗaure ta.

Ɗaya ɗakin dama na wasu yarbawa ne amma musulmai me mata da miji ne da ɗan su guda ɗaya. Tun da mai mijin ya leko zai fito ya hangi Sani da adda yana kartawa a tsakiyar gidan a guje ya koma ɗakin matar tashi da take kan sallaya tana lazimi bacci ya ɗauketa take gyangyaɗi a zaune bata zata ba bata tsammata ba sai ji ta yi an yi ciki da ita wato shi mijin tsabar bai gaji sa duniya bama dama ko zancen mutuwa ba ya kaunar a yi bare kuma yau ya ga mutuwa kusa don haka bai ma kula da matar ba ya yi tuntuɓe da ita ya rafku da kasa bai bari ya ji ciwon faɗuwar bama ya mike da rarrfe ya shiga can cikin ɗakin yana shiga ya banke kofar ya haura kan yamushashshiyar katifarsa ya yi runda ciki yana mayar da numfashi. Matar da ta ga hakan sai ta doka tsaki ta zata tsoron nasa ne da yake da shi baki ta taɓe ta tashi ta naɗe sallayar za ta fito ya ɗora musu ɗan abin dw za su ci, fitowa ta yi gadan gadan ta nufi inda murhun nasu karan karta addar a karo na babu adadi shi ya sa ta ɗago don ganewa idonta aikuwa ta sauke a kan Ɗan Inna yana rike da hannun wata mata da kana ganin kayan da aka libga mata a jiki ka san shirin mahaukaci ne siyam-siyam ta juya a kan sawunta gabanta yama faɗuwa don hatta takalminta a can wajen murhun ta baro su, ta bankamu ɗakin ta rufo kofar don ta tabbata matsawar ta je wajen mijinta ya buɗe mata bedroom to hakika ɓatawa kanta lokaci saboda tsoron bala'i ne da shi.


Zama ta yi tana mayar da numfashi.

A can kuwa ɗan daban nan wanda ɗakunan suke jere da na Amina.

"Gafara dai masu gida" Ya shigo yana wani tafiya yana kanbo shi ala dole niga don karfi yake ji tamkar ma azumin ba ya bashi wahala. Yana tafiya yana wani ciccije wa bai tashi yin arba da oga Sani ba sai da ya zo tsakiyar gidan wato yana dab da shiga ɗakinsa amma bai je kofar ba. Karan karta addar ne ya ankarar da shi wannan karon ya sakalo hannunsa a kugun Dada wacce ta takure waje ɗaya ko motsin kirki bata yi wai ita amarya amaryar ma ta mahaukaci.


"Innahu min sulaimanu wa innahu bismillahir ramanir rahim" Ya ce a zuciyarsa ganin mahaulacin gidansu ya yi kamu.

'Wa kake nema?" Ya jefa masa tambayar.
.
"Wallahi ni ba gandai bane ina azumi' Baffalo niga ya ce a ruɗe don shi bai san bama a kan me ake tambayar shi dai abu guda ya sani yana so ya bada amsa daidai gudun kar kwaɓarsa ta yi ruwa ya shiga amsawa ne don mugun tsoron Sani yake yi kamar mai bare ynzu ga shi da makami kuma ya san duk wanda ya duka ya daki banza don ba wanda zai yi shari'a sam da mahaukaci domin kowa ya san kansa ba nashi bane.

A duke Baffalo ya shiga yin baya-baya ɗamamman cikinsa da yake kamar zai haɗe da baya ya shiga karta masa, so yake Allah ya taimake shi kar Sani ya dakatar da shi yana dab da zai shige ya ji ya ce

"Za ka taka almutsutsai" Da sauri ya iyo cikin gidan a tsorace don duk duniya babu abin da yake tsoro irin aljani musamman da ake musu kirari da su suke ganinmu bamu muke ganin su ba. Ya san kuwa Sani yana da aljannu manya ma kuwa don idan aka zo masa rukiyya yana jin yadda ake artabu da su. Tsayawa ya yi yana zare ido yana jiran umarni don ba ya so ya shige ɗaki a ce suna ciki.

"Wayyo Dada" Usai da Hassu suka haɗa baki wajen faɗa. Amina kuwa sai sharɓar kuka take yi ganin mahaifiyarta tana tare da mahaukaci ga kuma adda a hannunsa ta san matsawar ta masa musu to komai yana iya faruwa.



Masoyana a shiga youtube a yi searching littafina malamin bogi a danna mini like masu tambayar basu gane ba idan kun shiga wajen hannun nan kawai za ku taɓa shiknn👍 ina gdy sosai maman afrah🥰
[8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
*IMZEED VENTURE*
Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna aiyar da gwanjo me kamar sabo!
Tuntuɓemu 07077532253
Wtsapp/IG/TiktocTikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-8yWWJj3GGri&_r=1


*Don Allah da son annabi S.A.W ku shiga link ɗin nan ku danna min like pls*
👇👇👇👇👇
https://youtu.be/_zBSgYkvrzY?si=yglDNBJ5uwIMjHGT



CI-MA-ZAUNE



NA


MAMAN AFRAH



🅿️1️⃣1️⃣



"Kake yi wa amaryata kiɗan indiya tana rawa" Sani ya ce yana buga masa wani tsohon kwanon silbar da yake gabansa. Da sauri Baffalo ya tsugunna ya ɗauki silbar tare da ɗaukan wani tsohon ludai da icce karami ya shiga kiɗan jikinsa yana tsuma.

"Maza kike mini rawar indiya amaryata" Kai kawai Dada ta shiga gyaɗawa don zuwa yanzu babu karfin gwiwar furta komai musamman da ta lura ashe tamkar dodo haka ƴan gidan suke tsoron Sani saboda haukarsa. Sosai Dada ta shiga yin rawa tana juyi irin ta indiyawan kamar yadda ya bukata domin ta san yadda indiyawa suke rawa saboda ta sha gani a wayar mutane kuma akwai wani mai shago a kauyansu da bashi da aiki sai kunna wakar indiya tana ganin yadda yara suke dandazo daga gefen shagon suna ta kwatanta rawar wakar da ya kunna.

Tsabar tashin hankalin da take ciki na rayuwa ko mutuwa ya sa ko wahalar azumin bata ji, har wani karkaɗa kugun da indiyawan suke take kwatantawa gudun matsala sai kuma ta yi gefe da gefe hatta hannuwa da suke ɗan kare fuskarsu idan suna rawa sai da Dada ta kwatanta tun da ta san gyara ba zai taɓa yin kamar kashi ba. Duk da kasancewar kiɗan ko hanya bai haɗa sa na indiya ba domin baka jin komai sai kwalkwalkwal da Baffalo ya dage yana yi.

"Kai ana wani abu a wajen nan wai rawar indiya gaskiya kin cuci indiyawa" Bayerabiyar nan ta faɗa cikin hausar ta da bata fita duka, don duk abin da ake tana gani ta wata karamar tular jikin kofar ɗakin.


"Gaskiya ɗan Inna kana shuka tsiya ai sabga da mahaukaci ma sai dole in ba haka ba ka samu sa'ar kakarka ka ce wai ita ce amaryarka in ban da babu hankali" Cewar Kakar Sani da komai yake wakana a kan idanunta. Matsawa Sani ya yi ya kama Dada suke ta gewaya wa shi ala dole rawa suke shi da amaryarsa sai da ya gaji da kansa ya saka ta.

"Me kike a nan wajen bar nan" Ya ce cikin tsawa da sauri Dada ta nufi kofar ɗakin Amina har tana haɗawa da gudu don gabaɗaya ma ta manta da batun banɗaki bare ta tuna alwalar sallar la'asar ta je yi a bayin. Sai da ta buga sannan Amina ta yi karfin halin buɗe mata duk da kuwa a kan idanunsu aka yi komai amma tsoron kar ya biyo Dadar ɗakin ya sa suka ɗan dakata sai da ta zo ta buga.

"Wash Allah nah" Dada da ta yi zaman dirshan a tsakiyar ɗakin ta ce tana mayar da numfashi da yake duk rigunan da ya yaɓa mata sun faɗi a garin rawar indiya hula ce kaɗai a kanta ita ma cisgewa ta yi ta jefar.


"Allah ya isa tsakanina da Sagiru yaron nan ya ɗauki alhakina da ya sa na baro kauye na taho domin zaton Amina a gidan naira take, yanzu babu damar komawa kauye a saka ni a wakar na yi karya ga shi a tara ko wuri ɗauka ba sai yau za a kai azumi ɗaya" Ta ce tana rushewa da kuka domin gabaɗaya ta tsorata da lamarin mahaukacin bare kuma a ce ana zaune gida ɗaya da mahaukaci wannan kam ya zama tsautsayi zagin mahaifi.

"Dada baki ji yadda kirjina yake bugawa ba in na ga yana wasa addar nan a kasa ba" Usai ta ce cikin tausayin kakarta.

"Ni wallahi baki ji yadda nake shiga tashin hankali ba"

"Ku ɗin ma kenan da baku bane a hannunsa ni ai gabaɗaya ma na saddakar cewa kai zai fille mini domin kuwa babu tabbas a al'amarin wanda bashi da cikakken hankali.


"Wallahi Dada kwanaki da ya damki wuyan kakar tasa sosai ta ringa makyarkyata mun ɗauka ma ta mutu Allah ne ua sa da kwananta a gaba shi ya sa ita ma bata yadda ta tsaya gabansa in haukar ta motsa don wani lokacin sai ki ga kamar mai lafiya" Amina ta ce cikin tausayawa mahaifiyarta.

"Ai da ni da ita ba maraba tun da ni ma ɗan uwan hakan ne tun da har gwara ita hannu ne ni kuwa adda ce kin ga kuwa ai babu gwara amma ni shegen yaron nan Sagiru ne duk ya jaza mini da a ce na san talauci ya masa katutu da ba zan tarki zuwa bama to rashin sani ya fi dare duhu" Ta ce tana buga uban tagumi da ta tuna ko abin da za su kai bakinsu babu idan an sha ruwa.


Bayan ya yi jifa da addar hannunsa ya juya ya shige ɗakin kakarsa wanda suka raba ɗakin shi a bedroom ita a falo, yana shiga ta shiga makyarkyatar tsoronsa sai da ta ga ya fashe da dariya ya zauna sannan ta ki hankalinta ya kwanta dakyar ita ma don bashi da iyaye sun mutu kuma babansa shi kaɗai ne ta haifa a duniya shi ya sa take zaune da shi amma in ba haka ba babu abin da zai haɗa ta zama ɗaki ɗaya da mai taɓin hankali. Kowa ganin Sanin ya shige ɗakin kakarsa sai aka fara lallaɓowa ana fitowa don samun abin da za a kai baki idan an sha ruwa. Baffalo kuwa tun da Sani ya yi wurgi da addar nan yana ganin ya shige ɗaki ya yi wurgi da ludai da iccen da yake kiɗa don ko bayan an dakatar da Dada an sallameta bai daina kiɗan ba tun da ba a ce ya bari ba gudun kar ya yi laifi sai ya cigaba da kiɗan, don haka a sukwane ya yi hanyar waye ba tare da ta shiga ɗakinsa ya ɗauki kuɗin da ya zo ɗauka ba wanda zai je siyan kankana da lemo.


"Hassu ke da Usai ku tashi ku siyo mana abin da za mu yi buɗa baki kun ga an kusa yin magriba " Cewar Dada.

"Dada a wannan makotan namu na dama matar tana siyar da dankalin hausa kima tana siyar da man gyaɗa ko shi za su siyo a soya" Amina ta ce cikin sanyin murya don tana ganin ita ya kamata ta tanadar musu abin buɗa bakin sai dai bata da halin yin hakan.

"Ku sayo dankalin na ɗari biyar man na ɗari uku" Ta ce tana mika musu ɗari takwas. Karɓa suka yi suka tafi.

"Ai ba don wancan mutumin arzikin ya bani kuɗin nan ba ban san yadda zan yi ba wallahi ga shi dai su nake gurgura" Cewar Dada tana kwantawa a kan buhun nan da yake shimfiɗe a falon shiru Amina ta yi saboda ta kasa cewa komai ma duk da dai Dadar ce silar faruwar komai amma kuma kaddarar ce a haka.

Da ɗan damar dankalin haka su Hassu suka fere suka soya, sai kuma wani garin kunu da wata yarinya ta kawo talla Dadar ta saya da tsamiya suka dama kunun suka saka hasfatin don Dada ta ce wallahi ba za ta sayi suga ba. Har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login