Showing 9001 words to 12000 words out of 52525 words
gari ta ji labarin tafiyar su Sagirun tun daga ranar Dada ta daina baccin dare kwana take tana sallah tana addu'ar Allah ya dawo da Sagiru ya auri Amina. Kwatsam bayan sati guda sai ga Sagiru da Ɗan Ibra a wata motar da ban har kofar gidan Dada. Bayan an musu iso Dada ta sa suka shio har ɗaki bakin nan nata kuwa ya ki rufuwa ganin Sagiru har tsakar ɗakinta ya sha galleliyar shadda tana sheki ga wata katuwar leda da aka ciko mata da kayan marmari. Jin fata da addu'ar ta sun karɓu wato Sagiru ya zo da maganar auren Amina lamarin da ya saka Dada sakin wata uwar guɗa da ta karaɗe gidan, wanda hakan ya kara janyo hankulan kishiyoyinta, sai bayan ta yi guɗar kunya ta kama ta ta shiga sunkuyar da kai. Amina kuwa tamkar an tsoma ɓera a ruwan zafi haka ta koma jikinta sanyi kalau don ita yanzu auren ma kansa ba ya gabanta bare wani auren masu kuɗi tana dai ganin yadda ta koma a gidan Alhaji Sabo. Dakyar Dada ta tilasta mata musu rakiya zuwa zaure kasancewar ma Malam ba ya gida bai ma san wainar da ake toyawa ba.
Bayan sun fita Dada ta ɗakko lemon fata huɗu ayaba huɗu ta fito tsakiyar gidan ta shiga yin guɗa sai da ta yi kwarara sau uku sannan ta sauke idanunta a kan fuskokin kishiyoyinta wanda suka fito daga ɗakunan su suna ganin ikon Allah kunnuwan su cike da son sanin dalilin guɗar tata.
"Allah sarki duniya gidan kashe ahu, tabbas duk wanda ya ce tukunyar wani ba za ta yi zafi ba to tasa ko ɗumi ba za ta yi ba. Sannan daren tuwo ba yana nufi za a kwana da yunwa ba" Dada ta ce tana sakin wata dariyar.
"Wai Saude a kan mai za ki zo kike yadawa mutane magana da habaice-habaice? Kina guɗa kamar wanda ake saka amarya a lalle" Ladiyo da ta cika ta yi faful saboda bakin ciki ta faɗa saboda ta san dai zancen gizo ba ya wuce na koki kuma dai ruwa ba ya tsami banza tun da har ta ji Dada Saude tana wannan murna ta da walakin goro a miya.
.
"Kema dai kya faɗa don abin ba na wasa bane wai ɓera ya gutsurewa amarya hanci tana bacci" Mero ta faɗa tana kama haɓa.
"Kai duniya rawar ƴanmata na gaba ya koma baya, ai gani ya kori ji" Dada ta ce yana mikaws kowacce lemo biyu ayaba biyu.
"Aunty Amina ce ta samu miji ɗan birni mai mota shi ne ya ka... Kafin Hassu ta kai karshen maganar da take yi cikin tsiwa lemo da ayabar da Dada ta ba Ladiyo ya suɓuce ya zube saboda jin ba a rabu da bukar ba an haifi habu suna murna auren Aminar da Alhaji Sabo ya mutu sun samu abin faɗa da yada magana a tsakar gida har suna musu wakar kwaɗayi mabuɗin wahala, kan kwaɗayi kuda ya wahala ashe dai taki suke karawa shuka.
Baki sake suke kallon Dada da take sakin murmushin kun dai gani ai.
"In ka ga tsohuwa tana rawa a kasuwa tabbas ta daɗe tana yi" Dada ta ce tana juyawa ta koma ɗaki ta bar su da sakakken baki.
"Lemo da ayabar taki sun faɗa, ungo ki yanka a je a tsotsa a bakin salati a saka albarka"Usai da ta ɗauki lemo da ayabar ta mikawa Ladiyo ta faɗa cike da shekiyanci saboda ta san ji suke kamar su haɗiye zuciya su mutu. Karɓa Ladiyon ta yi tana jin tamkar ta rusa ihu, ganin Usai ta shege ɗakin ya sanya Ladiyo ta nufi nata ɗakin bugujun-bugujum ko ta kan Mero bata bi ba, ita ma Mero nata ɗakin ta nufa zuciyarta yana suya don su ma zuwa yanzu nasu ƴaƴan sun fara kawo musu korafin zamantakewar da suke da mazajansu duk da dai ba yabo ba fallasa domin zaman aure dama ɗan hakuri ne amma dai lamari ne mai girma a ce Amina za ta yi aure a birni to tabbas sun san da sauran rina a kaba don sai sun kaɗe har ganyen su a wajan Dada saboda ba gori ba har goriba sai sun fuskanta.
Amina kuwa tun da ta fita zauren baya ce musu komai ba sai wasa da take yi da yatsunta kasancewarta dama nutsatstsiya kuma mai kawaici, Sagiru kuwa gabaɗaya baki ya ki rufuwa sai kallonta yake tana washe bakinsa ganin kyakkyawar mace wacce yake da burin ya aura kwana kusa duk da bai ajiye ba bai kuma ba kowa ajiya ba amma ko ta halin kaka ya yi alkawarin ba zai bari wannan garaɓasar ta wuce shi ba. Ɗan Ibra ne yake hirar yana neman amincewarta tun da dai bazawara ce ba wani dogon lokaci za a ɗauka ba, ita kuma ganin ko tana so ko bata so tun da Dada tana so to ta san babu gudu babu ja da baya dama shi Malam ba a ma zancen shi saboda shi ma sai yadda Dada ta yi da shi ko da ya mata magana bai isa ba. Bayan sun gama jawaban su a kan nan da sati biyu suke so a gama komai za su aiko magabata sai kuma a kawo kayan lefe a ɗaura aure don ya ce lefe zai yi mata irin na budurwa. Da za su tafi ya ɗaukko rafar ƴan goma -goma ya bata dakyar ta karɓa shi ma don ta san matsawar ta ki karɓa sai ta gwammace kiɗa da karatu a wajan Dada.
"Kai gaskiya na tsinci dami a kale" Sagiru ya ce yana kyalkyalewa da dariya lokacin da suka kama hanya domin komawa birnin Gumel suna tafiya a mota.
"Ka yi dai a hankali wallahi wannan uwar tata masifaffiya ce don duk ranar da ta gano fakiri ne kai to kuwa ka kaɗe har ganyenka"
."Yo ai ba za ta gano ba domin lokacin da za ta gano tuni na kurewa tayar motarta gudu, don ba tsimi babu dubara tun da ni ne dai zan saki yarinya to kuwa ba zn sake ta ba, don sai in nuna mata ni ma ɗan zamani ne yadda take tsohuwar zamani dama ai wayon a ci ne ya sa aka kori kare daga bakin ɗinya" Ya kara faɗa yana waya dariyar.
"Ai ni sai kashina ma ya fi naka bushewa saboda ni na kai ka garin...
"Ka bar wannan maganar mu ji da badakalar da take gabanmu, ta samo aron kayan lefe da gidan haya da kuma iyayen aro"
"Ka bar komai a hannuna yanzu dai bari mu karasa ka je ka cirewa wannan masifaffan mutumin wannan shaddar ka kara goge masa kar ya zo karɓa gobe ya yi kuli-kulin rakiya da kai"
"Wallahi kuwa ni ma tunanin da nake yi kenan, wannan hular ma da na aro nake so in je in mayar ka san shi ma ya ce mini in ta kai bayan magriba sai na kara masa ɗari huɗu, ni kuma wancan sabbin kuɗin da na bayar ma raina ciwo yake ko gajiyar wankin da na yi aka bani ban huce gajiyar ba amma na ɗauki kuɗin sukutum na bata"
"Dalla malam rufewa mutane baki, rafar ƴan goma-goman kake yi wa ido to ai sai ka sauka ka koma ka karɓo kayanka ka ga in tsohuwar nan bata tsige ka daga mai aurenta ba, ni kuma fa da na saka mana mai a mota wannan man mai tsada, ga haɗarin da na saka kaina na ɗaukan motocin Alhaji don baya kasar wallahi ka kula a yi auren nan kafin su Alhaji su dawo Nigeri'a don in suka dawo baka da mota mai kyan da za ka cigaba da karya da ita a kauyan amma in aka gama komai ka ai ko sun dawo ta famjama-fanjam"
"Haka ne wallahi kai dai da Allah ya taimake ka, ya manta da mukullin motar a wajanka da ka kai su filin jirgi ai da yanzu wata maganar ake ba wannan ba" Suna ta tattaunawa har suka shigo garin Gumel ɗin.
Washe gari Malam Saminu da yake islamiyar su Amina dama tun kan ta yi aure yake sonta amma tun da Dada ta kyalla ido ta hana shi sakat saboda bashi da masu gidan rana har ya gaji ya hakura ba don ya so ba. Yanzu kuma tun da aurenta ya mutu ganin ta gama idda yake dibdibtu, yau ma da la'asar sakaliya ya shirya tsaf domin zuwa wajan Amina sanye yake da yadi yalo wanda ko aiki babu a jiki yadin ko inda guga ta bi bai biyo ta wajan ba sai dai babu cukurkuɗewa. Rike yake da karamar bakar leda da ya sako yalo da goba da mangwaro wanda ya siyo a kasuwar da yaje ci jiya sai kifi naɗe a takarda shi ma a ledar yake. A zauren gidan ya tsaya daga gefe bayan ya aika yaro ya masa iso, yaron yana sanar da sakon Dada ta yi karaf ta ce ya ce masa tana zuwa, yaron yana fita Dada ta ɗauki mayafi ta nufi zauren don ita Aminar ma tana ɗaki bata san wainar da ake toyawa ba. Lokacin da ta iso zauren Malam Saminu hankalinsa yana a ledar da ya zo da ita ya buɗe yana lekawa sai murmushi yake ganin zai farantawa abar kaunarsa Amina musamman da ya ji an ce tana zuwa wato Dada bata hana ta zuwa ba hakan ya sa a ransa ya fara jin cewa sannu -sannu ba za ta hana zuwa ba sai dai a daɗe ba a je ba wato ko ba daɗe ko ba jima zai auri Amina domin in da rai tabbas da rabo.
Tsaye ta yi a gabansa tana kallonsa shekeke kamar wanda ta ga kashi, sai lokacin ma ya san da wanzuwarta a wajen hakan ya sa gabansa bugawa da karfi don ya san in ba tijara ba babu abin da zai kawo ta. Cikin rawar jiki ya tsugunna yana mika gaisuwar da a maimakon ya ce ina wuni kasancewar da yammaci ne sai ambaton ina kwana yake yana karawa kamar dai wanda aka ce ina kwanan sau ɗaya bata gamsar ba duk da babu ko ɗaya da Dadar ta amsa kuma bata da niyyar amsawa sai kallon da wa kuka zo take masa.
"Kai hamago! An ce maka yau tun da garin Allah ya waye babu wanda ya gaishe ni ne da ka hamgame baki kake mini gaisuwa babu kakkautawa kamar dai wanda na roke ka?"
"Allah huci zuciyarki Dada" Ya ce cikin sanyin murya yana mikewa daga tsugunnon da ya yi.
"To da mai zai samu zuciyata da za ta yi zafi, ni nan da kake gani ɓacin raina sai dai a kan naira wato kuɗi saboda kuɗi su ne ake cewa suna son maso wani wato ina son su su kuma suna son wasu. Wa ya gayyaceka gidan nan sau nawa na faɗa maka Amina ba sa'arka bace in banda sakarci jiran jirgi a tashar mota ta yaya za ka ɗakko wasu koɗaɗɗun kafafunka tsiri-tsiri kamar itace ka zo gidan nan, dube ka don Allah mai na sama ya ci bare ya ba na kasa kai nan wai wanka ne ka ɗauka na zuwa wajan zawara a ganinka ka kure adaka shi ne ka ɗauki wani yadi tsarrr da shi ruwan ɗorawa sai ka ce gaskami wai nan hira ka zo babu wani kamshin turare sai uban karnin kifi da ka cikawa mutame zaure da shi kalli takalmin kafarka kamar wanda aka bar maka gado duk ya suɗe ya katale, to wallahi tun muna shaida juna ka ja guntun mutuncinka ka koma inda ka fito in ba haka ba zan saɓar maka gwara ka koma ka samu ustaziya a cikin ɗaliban islamiyae taka ku rufawa kan ku asiri ku yi auren ustazai amma Amina dai ta fi karfin samun ka don matar manya ce, shi ya sa ma yanzu nake tura ta makarantar toka (Makarantar allo) Saboda kar ma take zuwa makarantarka ka sace mata zuciya"
Tun da ta fara faɗar maganganu na cin fuska da wulakanci Malam Saminu ya sunkuyar da kai yana jin ciwon abin da take masa tabbas ba don albasa bata yi halin ruwa ba da babu dalilin da zai sa yake son Amina sai dai kasancewar tana da nutsuwa shi ya sa ma amma dama yadda Dada take bata ganin kan tsohuwar kowa da gashi da ba zai zo wajenta bama.
"Za ka wuce da wani kalar yadinka yana ɗaukan ido wal-wal-wal ko kuwa sai na koma ciki na ɗakko katon faskaren icce na gurɗa maka kafa?" Ta ce tana aika masa harara. Sumi-sumi ya juya rike da ledarsa ya fita zuciyarsa tana masa zafi ita kuma ta koma cikin gidan tana faman kumfar baki, sai da ta je ta gargaɗi Aminar ma sannan hankalinta ya kwanta.
Da daddare Dada tana zaune a turakar Malam tana shan rake tana ɗora ɓawon a murfin kwano sai da ta gutsiri raken ta tauna tana wani gyaɗa kai sannan ta ce
"Malam nawa na kaina"
."Faɗi bukatarki".
"Kamar yaya?"
"To ai na san ruwa ba ya tsami banza"
"Yanzu kenan ba zan faɗa maka abu ba sai ina bukatar wani abu?".
"Kamar haka hasashe ma ya nuna mini"
"Haba kai kuwa mai ya yi zafi hakan shi ba wuta ba"
"To yanzu ya kike so na yi Saude kin uzzura sai da yarinyar nan Amina ta auri Alhaji Sabo haka na yarda ba da son raina ba amma kuma auren bai je ko ina ba kika yi uwa kika yi makarɓiya kika kashe mata auren ta dawo ta zauna kin mayar da ita karamar bazawara, kuma yau ɗin nan zan shigo na ga malamin islamiyar su ya fito daga zauren gidan nan fuskarsa alamar damuwa ta bayyana karara har kusan bangaje ni ya yi saboda bai ma lura da ni ba, ki ban tambaya ba na san hakan ba ya rasa nasaba da ke"
"To ya kake so a yi ne haka kawai sai in bar ƴata ta yi auren talauci, kuma da kake maganar kashe aure kana nufin in barta ta zauna a gidan mai karyayyan kwankwaso to ba zai iyu ba kuma shi wancan mai yadi ruwan ɗorawar ai bai dace ya auri Amina ba mutumin da sai in kirga maka layan sawarsa kaf ina ga basu fi kala biyar ba daga wani yadi kore sharrrr sai wannan mai kalar ɗorawar sai wani jaaa da wani mai dishi-dishi...
"Ya isa don Allah ni ban saka ki lissafa masa kayan sawa ba, shin yadika za ta aura?"
"Ko bata auri yadika ba na san dai sai yana ɗinkawa zai ɗinka mata ko barw ni ma sirikarsa in samu yake bani tirmin zani ka ga kuwa ai bamu ga ta zama ba wai an saci ɗan ɓarawo don shi kansa bai mora ba bare a samu mamora don wallahi kana kallonsa ka san Tukumbu (Tinubu) Ya bi ta gabansa ya wuce ma'ana tsananin talauci ya masa katutu wato Tukumbiyya (Tinubiyya" Ta mamaye shi
0902557622
[8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
*IMZEED VENTURE*
Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna aiyar da gwanjo me kamar sabo!
Tuntuɓemu 07077532253
Wtsapp/IG/TiktocTikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-8yWWJj3GGri&_r=1
*CI-MA ZAUNE*
*NA*
*MAMAN AFRAH*
Daga marubuciyar
*Malamin bogi* *Ƙazamin miji, Bonono, Ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, Jalli joga, Beelal, Ƴar zaman* *wanka, Ungozoma da sauran su.* *09025576222*
🅿️5️⃣
Kallonta kawai ya yi ba tare da ya ce uffan ba.
"Yo ni da a ce ma na kashe mata aure, ka san an ce rabo shi yake kashe rabo wato yanzu ba ga shi ta yi babban kamu ba kamun ma a birni ni wallahi wannan gutsiri tsomar na guda shi ya sa yaron nan Sagiru ɗan birni abokin Ɗan Inba da ya zo haka ya kawo abin arziki bakko guda amma saboda kar na faɗa maka ka dinga kawo kauli da ba'adi shi ya sa na yi gum da bakina"
"To da kika yi gum ɗin ma ai na ji komai a gari'.
"A gari ko dai a gida ka ce dai waɗannan munafukan matan naka sun labarta maka, to duk mai bakin ciki sai dai ya mutu don na fahimci so suke ka hana a yi to kuwa na gani nan bari farar tumfafiya iya gani iya kalewa, dama ai duk wanda yake da kishiyoyi sai ya ga hassada ko da ba masa kiri-kiri ba to za a masa a bayan idanunsa" Ta ce tana gutsirar rakenta hankali kwance.
"Duk tsiya kuma tun da ni ne ubanta dole sai da izinina ba'
"Kuma dai ai ka san budurwa ake yi wa dole zawara kuwa gashin kanta take ci don haka Amina sai ta zaɓa ta darje" Ta ce tana mikewa tsaye .
"Allah bamu alheri bari na je na irga ƴan matsabban kuɗaɗena na kwanta bacci ka san an ce mai kuɗi bai kwana da haushin kowa ba, saboda haka ma idan mutum yana lissafa kuɗi ba ruwansa da damuwa to sun yi hannun riga ɓacin rai" Ta ce tana saka kai ta fice ko abin da ta tara ɓawon raken bata ɗauke ba.
Tun da Sagiru suka koma Gumel bai samu kara zuwa ba, sai dai yana bugowa wani mai cajin wayar garin su Amina ya ce ya kai mata su yi magana, don ya ce ya yi tafiya ba ya kasar ma domin ko da ya ce a ba Dada wayar ma sai da ya kara jaddada mata sun tafi kasar waje shi da iyayansa su siyo kayan lefe wannan maganar ce ta kara saka kan Dada da na su Hassu da Usai fashewa suna jin ba ya su domin Amina za ta yi auren kece raini basu san cewa Sagiru yana can ya dukufa ba dare ba rana yana wanki da guga domin ya tara kuɗin da zai ari iyayan karya su je