Showing 45001 words to 48000 words out of 52525 words

Chapter 16 - CIMA ZAUNE Complete by Maman Afrah.txt

30 Aug 2025

1753

jelarta sai ta ɗan karkata gefe shi ne ta saki tusar da ita ce ummul aba'isin gudun famfalakin da su malam da da matarsa da Baba suka yi. A ɓangaren su Sagirun ma hakan ce ta faru don gabaɗaya sun manta cewa akuya ce take tusa kuma sun manta ta ce musu tusar ƴan shayi ce take yi, don haka lokacin da karan ya ziyarci kunnuwan su sai suka ɗauka karan tashin boom ɗin ne don haka babu wata-wata suka yanki cikin gidan malam ɗin da yake basu ma lura da kofar ɗakin zauren ta malam ba wacce yake ganin baki ko kuma don suna cikin halin tsoro ne basa cikin nutsuwar su oho, suna shigowa zimbet suka nufi kofar da za ta sada su da tsakar gidan, duk da kasancewar kofar an karo ta an ɗan rufe ta haka suka bankama ciki a guje. A ɗakin malam ma kuwa zaune yake a tsakiyar ɗakinsa wannan babbar riga ta baje a kasa naɗin hiramin kansa da hular sun kalli arewa maso gabas sai mayar da numfashi yake.

Baba kuwa lungun kujera ta shige da yake akwai kujeru biyu a ɗakin, ita kuma matar malam tana shigoea ta diri tukunyar a tsakiyar ɗakin malam ɗin daga can gefen inda yake zaune ta koma can wajen tulin kayan wankinsa ta kwasa ta yaɓa a kanta a nata tunanin ko da ƴan bindigar sun zo ba za su ganta ba.


Jin karan banko kofar gidan ya saka cikin malam murɗawa babu ɓata lokaci ya saki wata sassanyar tusa marar kara mai bala'in wari saboda tsurewar da ya yi, a ɓangaren Baba ma kuwa jin karan ba karamin saka ta cikin ruɗu ya yi ba, don ita a halin da take ciki yanzu ta ma manta da wasu su Sagiru da ta bari a bakin kofa bare har ta tuna cewar akuyar da suke tafe da ita tana tusa mai kamar karan booom. Matar malam kuwa jin karan banko kofar sai ta kara cusa kanta cikin kayan wankin malam ɗin da ban da wani uban warin dauɗa babu komai a ciki.


A tsakar gida kuwa lokacin da su Sagiru suka shigo sai suka fara rarraba idon inda za su ga maɓoya duk abin da suke akuya tana kallonsu kuma tana sane da su so take kawai ta ga gudun ruwansu. Har lokacin suna manne da juna kamar yadda akuya ta haɗa su da kafafunta suka zama tif da taya da juna. Basu yi wa idanunsu masauki a ko ina ba sai a kofar turakar malam da take a rufe don matar malam tana shiga malam ya banke sai dai ya sha'afa bai saka sakata ba.

Suna zuwa suka daki jikin kofar da kafafunsu, malam da yake zaune a tsakiyar ɗakin yana lazimi da baki hannunsa da yake kai komo ya ma manta da sharɓeɓan carbinsa mai ƴaƴa dubu da yake rataye a wuyan nasa, jin karan banko kofar ya tashi da sauri yana son ya samu maɓoya saurin tashin da ya yi a firgice sai ya yi tuntuɓe da kwarya da take ajiye a ɗakin yana yin tuntuɓen ya koma babu shiri tamkar an jefa shi ya yi zaman ƴan bori a kan sabuwar kwaryar ji kake fushhhhh kwarya ta daddare. Shi malam ba damuwarsa bace faɗuwar burinsa kawai ya tserewa karan booom da kuma alburushin bindiga.


Su kuma ganin sun yi bugu ɗaya kofar bata buɗu ba sai suka sake bugawa, sai kuwa ta buɗe, malam jin karan gwaruwar buɗewar kofar sai ya tabbatar kwanan su ya kare tun da ga ƴan bindiga a garinsu a kuma unguwarsu a gidansa, a gidan nasa ma a ɗakinsa. Da sauri ya buɗe tukunyar nan mai zazzafan ruwan miya ya cinbula kansa a ciki, zafin ruwan da ya ziyarci fuskarsa da zafin yajin da ya shaka a hancinsa shi ya sanya ya ɗago kan babu shiri yana sakin atishawa a kai- a kai, duk da haka bai daddara ba ya ɗaga tukunyar ya kelayar da ruwan miyar a tsakar ɗakin ya ɗaya tukunyar ya kifa a kansa da yake tana da girma sai ta rufe masa har fuskarsa jin karan shigowar mutane sa kuma yadda suka rufe kofar ga sanya ya fara ja da baya.

"Taimako jama'a taimako" Ya yi furucin a wahalce don dakyar yake iya jan numfashi a cikin tukunyar.

"Allah ka mana rahma ka haɗamu da mala,ikun rahma" Ya ce a fili don ya san tun da ƴan bindiga suka shigo ɗakin da yake kwanansa ya kare, ganin ruɗun da suka tsinci mutumin nam yana ciki sai suka gane ashe dai kowa ya ji abin da suka ji. Akuya kuwa duk abin da ake tana kallon su.

'"Ku taimaka ku bamu mafaka"Sagiru da abokinsa suka haɗa baki wajen faɗa. Gaban malam ne ya faɗi a take kwanyarsa ta shiga laluɓe yana tunanin ya za a yi ƴan bindigar suke neman wajen ɓuya. Matar malam ma da take kwance dukunkune a cikin kayan wanki tana shakar warin dauɗa ita ma mamaki da al'ajbi ne ya kamata saɓanin Baba da jin muryrsu raɗau sai tashi tsaye tana faɗin.


MUHIMMIYAR SANARWA* 👇👇👇

*Assalamu alaikum duk me karatun littafin CI MA ZAUNE ya tsaya ya karanta wannan saƙon ya fahimta. Littafin nan 500 ne za a gama free pages a page 18 sai dai akwai zaɓi biyu ga mai son karantawa har ƙarshe. Ko mutum ya biya ,500 ko kuma ya mini magana in bashi link ɗina ya mini LIKE na gasa idan ya yi zai sa mutane biyu su mini a tura min screen shrt ta PC sai in saka mutum a paid grp ya karanta idan kuma knsan kn yi mini dama to za ki sa mutane biyu su mini sai in saka ki a paid grp amma sai kin fara mini magana a PC na miki bayani. Wanda kuma 500 zai saka zai biya ta asusun faiza abubakar 9030283375 opay shaidar biya ta 09025576222* *Wanda za su yi like ma ta wannn no za su min magana*
[8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
*IMZEED VENTURE*
Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna aiyar da gwanjo me kamar sabo!
Tuntuɓemu 07077532253
Wtsapp/IG/TiktocTikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-8yWWJj3GGri&_r=1

*CI -MA-ZAUNE*

NA

MAMAN AFRAH
PAGE 1️⃣7️⃣


MUHIMMIYAR SANARWA* 👇👇👇

*Assalamu alaikum duk me karatun littafin CI MA ZAUNE ya tsaya ya karanta wannan saƙon ya fahimta. Littafin nan 500 ne za a gama free pages a page 18 sai dai akwai zaɓi biyu ga mai son karantawa har ƙarshe. Ko mutum ya biya ,500 ko kuma ya mini magana in bashi link ɗina ya mini LIKE na gasa idan ya yi zai sa mutane biyu su mini a tura min screen shrt ta PC sai in saka mutum a paid grp ya karanta idan kuma knsan kn yi mini dama to za ki sa mutane biyu su mini sai in saka ki a paid grp amma sai kin fara mini magana a PC na miki bayani. Wanda kuma 500 zai saka zai biya ta asusun faiza abubakar 9030283375 opay shaidar biya ta 09025576222* *Wanda za su yi like ma ta wannn no za su min magana*


CI-MA-ZAUNE


NA


MAMAN AFRAH


🅿️1️⃣7️⃣



"Sagiru" Baba ta furta don ita gabaɗaya ma ruɗanin da suka shiga ya sa ta manta cewa tare suka zo kuma sai yanzu ne kwanyarta ta shiga tuno mata karan tusar akuyar ne musamman da suka yi ido huɗu da akuyar sai ta ga akuyar tana harararta har da murguɗa baki wanda hakan ya sa ta kauda kanta da sauri.

"Baba karan boom" Ahmadu ya ce yana tsilla idanu.

"Karan fitar iskar ƴar shayi ce(Ƴar kaciya) " Baba ta ce kamar za ta yi kuka don abin takaici yake bata wai akuya da shayi. Malam kuwa jin suna surutu ya yi saurin cisge tukunyar kansa don ya ganewa idanunsa wace irin tusar ƴan shayi ce don yanzu ya ji cewa ba abin da yake zato bfe wato ƴan bindiga tun da ga shi su ma a firgicen suke. Ita ma matar malam da sauri ta fito daga cikin kayan wankin da warinsu suka cika mata hanci. Kallon -kallo aka shiga yi kowa malam yake kallo yadda ya yi wani wurjanjan da shi gabadaya a firgice yake tamkar an jijjiga ɓera a buta.

"Malam waɗannan ne bakin da muka zo da su" Baba ta ce don kawo karshen wannan daru da ake.

"Ka ji wani shashanci jiran jirgi a tashar mota yanzu duk ɗakin karɓar bakin da yake zaure bai isheku ba sai kun shigo mini har cikin gida garsama-garsaman samari da ku har cikin turakata" Ya ce cikin wayincewa don gabaɗata bai so ya kunyata ba amma kuma ta faru ta kare wai an yi wa mai dami ɗaya sata, tun da mai afkuwa ta afku ai dai a kiyayi gaba.


"Ka yi hakuri malam" Baba da su Sagiru suka haɗa baki wajen faɗa saboda basa kaunar dalilin da zai sa ya ki raba su da wannan jarababbiyar akuyar.

"To na ji ku je ɗakin zauren ku jira ni kuma a yi a hankali in an je ɗakin kar a zauna a kan tabarmar aljannu wacce suke zaune don zama a tabarmar da aljani yake zaune daidai yake da mazaunan mutum su manne su ki fita har gaba da abada" Ya ce yana muzurai don so yake ya maido da ɗan guntun mutuncin nashi da ya zube saboda a nashi ganin yadda yake malami bai kamata a ce yana gudub famfalaki ba. Sumi-sumi suka juya suka fita daga ɗakin gabansu yana dakan lugude domin jin sabon salo wai kiran salla da usur wato kashedin da aka musu na kar su zauna a tabarmar aljannu.


Ɗakin suka nufa kowa yana togewa musamman Baba da ita rakiya ta iyo amma abu yana neman wuce makaɗi da rawa wato cibi yana neman ya zama kari. Haka dai ta zauna amma Sagiru da Ahmadu da suka je za su zauna sai suka ji an ce


"Za ku zauna a kan kofato" Da sauri suka tashi daga kokarin zaman da suke yi, suka matsa can gefe ita ma Baba jin furucin da akuya ta yi sai ta fara jan mazaunai ta matsa daga wurin.

"Ka taka kan ɗan kundalo" Akuyar ta sake faɗa a karo na biyu wannan ya sa suka ja da baya har sai da suka koma bakin kofa suka tsaya a tsaye tun da zaman ya zama larura auren namiji da ƴaƴa.


Baba kuwa tun da ta zauna ta shiga lazimi saboda ta lura abin ba na kare bane sai lokacin da Allah ya yanke musu.


A can turakar malam kailu kuwa bayan fitar su Ahmadu sai ya shiga yin muzurai matarsa kuwa take masa dariya ganin gabaɗaya rawanin kan nasa ya jike sa ruwan miyar da ya tsoma kansa a ciki ga kuma warwarewa da ya yi ga shi kuma shi malam sai wai ɓata rai yake yana muzurai shi ala dole ba ya so a kawo masa raini, tsaye ya tashi da jagaggaɓar rigarsa da duk ta naɗe ruwan miyar da ya zubar a kasa.

"Wai malam da kake cewa kar zauna a kan tabarmar aljannu idan kuma aljannun suka je ɗakin naka suka shimfiɗa tabar...


"A bakin ki mugun fatanki ya sari bango" Ya ce yana aika mata sakon harara.

"Ana tsoronka ɗan mayya ya ce daga ni har uwata" ,Cewar matar malam tana danne dariyar ta saboda ita kanta ta san cewa mijin nata muna malam ne amma babu wata malunta yana yana cewa yana aiki da aljannu ne kawai amma duk ba gaskiya bane hasali ma mugun matsoraci ne.


Tukunyarta ta ɗauka ta fita shi kuma ya sauya kaya da rawani ya yafo hirami ya riko carbinsa ya fito yana baza babbar riga ya nufi ɗakin zauren.

Da sallama ya shiga Baba da duk jikinta ya yi sanyi ta amsa masa yana wani bokara da wani bada faɗi ya samu wuri ya zauna.

'Hmmm! Allah fitar da A'i daga rogo' Cewar Baba tana kallon yadda rawanin kansa ya zauna daram.

"Mun ci dubu sai ceto maganin biri karen maguzawa iya gani iya kalewa" Malam ya ce yana duba duka kusurwowoyin ɗakin.

"Malam su ne fa za a yi wa aikin" Baba ta ce jin yana tofe ta da yawu.

Bai tanka mata ba ya cigaba da tofe tofensa gabas da yamma kudu da arewa. Sai da ya kammala ya ce.

"Almutsutsai ne kewaye da ɗakin shi ya sa kuma kin ga aikin naku babba ne don haka sai an shiry" Kai kawai Baba ta shiga gyaɗa masa don ita gabaɗaya a tsorace take tamkar ta zura da gudu.

"Kai ku karaso nan ku saki jikin ku ku kaddara babu akuya a bayanku rukiyya zan yi da kanta za ta san na yi don karo sa mu babu daɗi" Ya ce yana janyo wani kwano mai ruwa a ciki. Sai da ya kawo ruwan gabansa sannan ya kalleta ya ce

"Ladan abin sadaka bama faɗa amma dai kuma a kan abin da za ku bayar za ku ɗoro mini katon turkekken rago kosasshe da bunsurun ɗan akuya" Ya ce cikin halin ko in kula. Gaban Baba ne ya faɗi don ita ɗari biyu ce a leɓen zaninta take so idan ya gama ta bashi sadaka amma yanzu jin gagarumin abin da ya zana wai kuma ba shi kaɗai bane ma abin sadakar shi a matsayij abin da za a ɗora masa a kan abin da za a bayar ne. Ina ta ga wani katon rago da bunsurun ɗan akuya.

Kallon kallo aka shiga yi tsakanin Sagiru da Ahmadu jin furucin malam bayana dama babun da suke ciki ce ta ishe su suka je suka sato akuya to yanzu ina za su samo rago da ɗan akuya.

"In ba zai samu ba kar ma in wahalar da kaina don wannan akuyar sai an sha fama za ta ɓanɓaru daga jikin su in ba za su samu ba a bar su da kayansu amma ku sani sai ranar da ransu ya bar gangar jikinsu za ta fita" Ya katse musu zancen zucin da suke shi ma kuma fa bai zaci abin ya kai yadda yake ba duk a tunaninsa dai kawai akuya ce take da gardama shi ne yake son damfarar waɗannan abubuwan.

"A yi wallahi za mu nemo duk inda suke" Ahmadu ya yi saurin faɗa.

."Ko da na ji ku dawo daga nan" Ya ce yana nuna musu gefensa ita dai akuya tana lakuɓe a bayansu.

Hannu ya saka a ruwan ya kamfato ya watsa musu har akuyar, baki ta buɗe cikin wani karaji ta ce meeeee.

"Ai yau sai kin gwammace kiɗa da karatu za ki san kin zo hannun malam kailu kare kukan ka" Ya ce yana kara ɗakko ruwan ya watsa mata. Akuya bata yi bori da sanyin jiki ba ta saki tusa mai bala'in karan da malam ya ɗaga kwaryar kasar da yake zane a ciki ya sheke a kansa, da ta sake sakin wata a guje ya yi taku biyu ya tsallake Baba da ta dukunkune kanta ta toshe kunnuwanta shi kuwa bai yi masauki a ko ina ba sai a saman buhun hatsin da yake ɗakin, yana ɗare buhun ya mika hannu yana kokarin neman inda zai kama ya fake a jikin saman silin ɗin ɗakin.

Bai yi aune ba sai ganinsa ya yi suuuu yana bin jikin bango tamkar wani kadangare shi dai a saninsa ya shi yake tahowa ba amma sai ya ji tamkar janyo shi ake yi sai da aka kawo shi har kasa sannan ya daina jin ana ja masa kafa a zahiri dai babu kowa ma a kusa da shi amma a baɗini yana jin yadda aka yi ta jan kafarsa. Raba idanu ya shiga yi cikinsa yana karta masa.

"Jama'a kuna jin yadda ake tada boom a garin nan namu na Gumel tabbas yau ƴan bindiga sun kawo ziyara.

Baba da yake akuya ta bata baya sai ta shiga yi wa malam nuni da akuya tana alamanta masa cewa daga gare ta ne karan saboda shi ɗazu a turakarsa da ake cewa karan iskar ƴar shayi ce ai ba wai ya gama fahimtar manufarsu bane shi ya sa ma yanzu ya kasa yaki da zuciyarsa wajen danne tsoron danya dirar masa ta sanadiyyar karan da ya kareɗe kunnuwansa

"Ina miki maganar booom kin nuna mini wannan karamar alhakin da na kusa yin mganinta ki bari karan nan ya lafa sai na gama mata aiki ga wani wari ma da nake ji yana baibaye mini hanci tamkar an ajiye mushe a ɗakin" Ya ce yana kallon su Sagiru da gabaɗaya ido ya raina fata. Dakyar ya samu dawowa daidai ya koma kan buzunsa ya zauna tare da gyara babbar rigarsa da ya gama yakune ta wajen gudun famfalakin karan sai kuma ya daidai naɗin rawanin ya janyo kwaryarsa da ya shekar da kasar ya ajiye a gefe ya janyo farantin mai kasa ya ce

"Innama amruhu iza arada shai'an an yakula lahu kun fayakun" Ya ce yana tofawa a satin fuskar akuyar. Idan har ba gizo idanunsa suke masa ba idan kuma ba wai kwayar idanunsa ce bata gani daidai sai ya ga akuyar murmushi take masa har da hararar kasan ido. Dimmmmm kirjinsa ya buga da karfi ya razana don ya san tabbas akuyar nan va wai akuya ce aljannu suka shige ta ba, ba don ma kar ya faɗi ba daidai ba sai ya ce aljana ce sak babu sirki.

Amma saboda karfin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login