Showing 18001 words to 21000 words out of 52525 words
sautin gamawa ya fito da yake Hassu da Usai ne masu bugawar. Yan zuwa ya buɗe yana bin su da kallon mamakin ganinsu don shi iya tsawon rayuwarsa a gidan bai taɓa ganin baki irin wannan ba har da akuya saboda haka sai ya yi tunanin neman abinci suka zo. Hassu da Usai tamkar su bangajeshi ganin ya yi kememe a jikin kofar ko hanyar wucewa bai yi ba.
"Bayin Allah ba sai kun damu da bugawa ba shi
"Ni Saude na ga annabi in na yi hali na gari"
"Hajiyar tana sama sai dai kwa sake sawowa t...
"Allah ɗan Allah baku mu samu, ka san da wa kake magana kuwa? To ka tausasa kalamanka in ba haka ba za ka yi da ma sani za ka yi sanadiyyar suɓucewar aikin gadin naka"Baki sake yake kallonta ga wannan jikokin nata kowacce ta yi ɗamara da tamkar wanda za su je gasar dambe.
"Baiwar Allah abin ba na zafi bane cewa na yi tana sama...
'Saman uban wa ? in ce dai saman bene take ba to ni nan na baka izini ka hau ka ce uwarta mahaifiya ce ta zo fa kanta ba sako ba" Ta ce tana zazzare ido, mamaki ya kama mai gadin don ya san mahaifiyar matar amma ya ji ita tana ikirarin ita ce mahaifiyarta.
"Allah baki hakuri" Ya ce cikin sanyin murya.
"Da in banda iskanci mutum uwarsa ta zo amma sai ta zauna zaman jiran iso" A daidai wannan lokacin Alhajin ya fito daga ciki sai ya ce direban ya zo za au fita tafiyar gaggawa da sauri mai gadin ya zo.
"Dada hango mutumin zai shiga mota bayan an wangale get ɗin, ganin Alhajin ya sa ta bankamo cikin gidan ita da jikokinta.
"Baiwar Allah lafiya?"
"Dama amaryar da aka kawo nan gidan ne muka zo ganin gida...
"La baiwar Allah ai ba nan bane ganin Alhajin" ya juya yana waya mai gadin ya yi saurin faɗa jikinsa ya hau tsuma yana karkarwa don muddin aka ce ga abin da ya faru wato an kawo musu amarya gida da basa nan shikenan da kashin ya bushe.
'Ai gidan gaba da mu ne ma" Ya ce yana tsoron kar wani ya ji maganarsa ga tunanin Ɗan Ibra kar ya zo a daidai wannan lokacin a samu matsala.
Baki galala Dada take bin su Hassu da kallo jin katoɓarar da suka yi ita dama ganin gidan ya tsorata ta faɗa ne kawai bata yi ba dama da a ce wannan gidan ne na Amina to da hatta su Ladiyo sai sun zama kamar bayinta da ɗaga kan da za take yi sai ya shallake tunanin mutane. Alhajin bai bi ta kan su Dada ba bayan an buɗe masa motar ya shiga direba yana shirin jan motar ya saka hannu a aljihu ya ɗakko kuɗin da a su kai dubu goma ya jefowa mai gadin yana masa nuni da ya ba su Dada don shi a nasa tunanin naiman taimako suke, yana gama jefowa motar ta tashi suka fice. Mai gadin ne ya ɗakko kuɗaɗen nan ƴan ɗari biyar -biyar sababbi ya nufo Dada yana yi yana waiwayan bayansa kar Hajiya ko wani daga cikin ƴan aikin su ji su kai mata rahoto, saboda ya san tabbas tsakin kuka a masaki ba zai rasa magani ba muddin wannan magana ta fita sunansa korarre tun da da haɗin bakinsa aka yi komai.
"Amma ku dai an yi shashashu wallahi ya za ku kawo mu gidan da ba gidan Amina ba? Ni dama na aan a rina wai an saci zanin mahaukaciya ta yaya gari birni kamar Gumel a ce kun iya gane gida sai ka ce a wani karamin kauye to wallahi da sake yadda muka kwaso kayan nan himili guda yaushe za muke yawo da su?" Dada ta faɗa cike da takaici tana kallon yadda yaran suke kara karewa gidan kallo don tabbas sun san basu yi ɓatan kai ba nan ne gidan amma kuma abin mamaki kwalli a kunne gashi dai abu yana neman ya sauya salo wai gemu a kafaɗa.
"Wallahi Dada nan gidan muka kawo Aunty Amin... Kafin Usai ta kai karshen maganar mai gadin ya karaso da kuɗin a hannu yana wani warwara su don su kuɗin ya ɗauke musu hankali su yi shiru da maganar gudun tonuwar asirin su har ya samu ya musu maganar da za su fahimta ba tare da wani ya ji ko ya gani ba. Kyarrr idanun Dada a kan sabbin kuɗin da suke filfil a mike ita kuwa mai idanun cin naira.
"Ga wannan kuɗin in ji Alhaji ya ce a baku" Ya faɗa yana mika wa Dada duka kuɗin duk son kuɗinsa sai da ya danne ganin asirinsu zu tonu ya rasa ɗan aikin da yake takama da shi.
"Yo mu da ba bara muke ba kuma ba neman taimako ba" Dada ta ce lokacin da ta damke duka kuɗin a tafin hannunta.
"Anya ma zan yarda in koma kauye, yo ni ba don Allah ya mini gyaɗar dogo ba Amina mai kuɗi ta aura ai da na ga wurin zuwa don wallahi sai in kauro Gumel ɗin da zama in lankwashe kafa in karkace baki in ke ta annabi Allahzi wahidin, kawai daga ganinmu ko ratrabo masa matsaloli bamu yi ba ya cake kuɗaɗe sabbi dal ƴan ɗari biyar biyar ya bamu?' Dada ta jefawa kanta tambayar tana kara damke kuɗin gudun akasin lissafi.
"Bawan Allah mai ka ce? Mu fa gidan ɗiyata muke nema to da yake ni ban san gidan ba wannan yaran ne masu kai tun na haihuwa aka zo da su amma suka kawo mu nan ashe dai gidan kama ya musu da na Aminar"
."Ikon Allah" Ya ce yana ɗan wayancewa so yake ya samu bakin zaren yadda zai faɗa musu".
"Sunan mijin nata Alhaji Sagiru ita kuma Hajiya Amina"Cewar Dada tana ɗan kafe motoci guda biyu da idanu wanda suke a fake a harabar gidan wanda indai ba gizo idanun nata suke mata ba, kamar motocin da Sagiru da Ɗan Ibra suke zuwa garinsu in ma ba ta yi mantuwa ba ɗayar ita ce wacce ta fara ganin su a ciki ransr da suka zo garin har suka rage musu hanya sai dai tuno ba su kaɗai aka kerawa motar ba sai ta kawar da tunanin.
"Taɓɗi! Wai Alhaji Sagiru mutumin da ko hanyar filin jirgi bana jin ya taɓa sani shi ne har aka lakaba masa Alhaji, hatta ita ma matar dalilin kasancewarta matar Alhaji ita ma ta zama Hajiya tabbas yau akwai cakwakiya musamman yadda kuka lodo kayan nan kuka taho alamu sun nuna ba tafiya ,a ku yi a kwana kusa ba bana jin ko abincin da za ku ci yau akwai shi a gidan Sagiru, don tun da ya yi auren nv ya daina wanki da guga ya zama CI-MA-ZAUNE babu aikin sile barr na sisi sai dai ya zauna a can majalissar ya tashi ya koma wancan' Mai gadin ya ce a zuciyarsa yana gyara murya domin yin bayani a gefe ɗaya kuma yana danne dariyarsa don har ya hango diramar da za a kwasa da tsohuwar nan idan ta je ta ga mazaunin ƴarta.
"Ayya Allah sarki wai dama gidan Alhaji Sagiru kuke nema wanda ya auro matarsa Hajia Amina daga Bausuwa?"
"Yauwa shi fa ai dama na san yaran nan shirme suka mini ba nan ne gidan ba, Allah sarki ashe dai ka san shi yo ai dama mai kuɗin ɗan masu naira kamarsa zai yi wuya a kasa sanin sunansa Allahu akbar! Duniya labari ashe dai Amina ma an fara sanin zamanta a birni wannan ne amfanin auren mai hannu da shuni kaima sai sunanka ya shahara" Dada ta ce tana washe baki.
"Yo dama ai sai dai ba a ambaci sunansa ba, kuma yaran nan da gaskiyarsu, ai nan aka kawo amaryar tasa to basu jima ba a gidan ya bawa wannan Alhajin sadakar gidan ya koma wanda ya fi wannan" Mai gadin ya ce don ganin ya kara rura wutar son samun Dada.
Kurrr take kallon gidan jin wai sadakarwa mijin ƴarta ya yi kenan yana da dukiyar da zai iya sadakar gida kamar wannan ya ba Alhajin da ya ɗakko wannn uban kuɗin ya bata sadaka tabbas ta kusa kaurowa Gumel da zama dole ya nemi kyankyatsetsan gida daga cikin gidajansa ya bata ta zauna a matsayinta na sirikarsa ta barowa su Ladiyo can su karata su da Malam ɗin don ita hatta tsohuwar igiyar aurenta da take reto ta kusa cirewa sai ta tsinke ta don ba zai iyu ba ta cigaba da zama inuwa ɗaya da igiyar auren Malam ba dama tun da ya mata kishiyoyi take jin haushinsa.
"Allah kara buɗi" Ta ce tana kallon kayan da suke ɗakko na sawa tana ji a ranta da a ce ta san har haka mijin Amina ya shahara da kayan nan ba za su taho da su ba, yanzun ma tana tantamar ko dai su watsar da su a bola don abin kunya ne tana sirikar Alhaji Sagiru tana saka wannan kayan.
'Dan na san haka yake da ɗimbin dukiya da ranar da na kai Malam kara wajen mai gari da sai na sa an saka shi ya since mini igiyoyin da suka kullini ni da shi" Ta ce a zuciyarta.
A fili kuma sai ta ce " Yanzu wa zai kai mu gidan ko kana da lambar wayarsa ka kira shi ka ce sirukarsa ce Saude ya aiko mota a ɗauke mu muna gidan da ya bada sadaka" Ta ce tana kallon mai gadin da ta rasa dalili rashin nutsuwarsa sai waige-waige yake na marar gaskiya. Sai da ya yi da gaske ya danne dariyarsa jin har ta hau ta zauna a kan maganar sadakar gida.
"Wane mutum in ji mutuwa bani da lambarsa sai dai na saka ku a adaidaita sahu(Shin kin karanta littafina ƳAN ADAIDAITA SAHU? Idan baki karanta ba ki nema ki karanta ki ji yadda cakwakiyar jika da kakarsa a hayar adaidaita sahu ki mini magana ta no ta 09013181851) "
"To muna godiya ɗan nan ai ba don a ce kana aiki a nan gidan ba da saboda karamcin da ka mana na sama maka aiki a wajen sirikin nawa" Ta ce lokacin da ta jua su Hassu suka bi bayanta su ma baki ya ki rufuwa.
"Ba komai wallahi" Ya ce a fili lokacin da ya biyo bayansu ya janyo get ɗin don ya kwatantawa mai adaidaitar gidan da zai kai su. A zuciyarsa kuma sai ya ce.
'Hmmm shi kansa sirikin naki da za ki sama aikin so yake tun da dai CI-MA ZAUNE ne.
Mai napep ɗin ya taro musu ya faɗa masa sunan unguwar da gidan da zai kai su.
"Na san gidan ma ai wannan gidan ba ɓoyayye bane" Cewar mai napep ɗin.
"Yo dama gidan hamshakin mai dukiya irin wannan ina zai ɓuya ai in ka je ana cewa ba a san gida ba to gidan ya ku bayi ne wato gidan malam shehu wato talaka nan ne za ka ga babu wanda ya sani daga ƴan uwa sai dangi amma gidan masu hannu da shuni ko babu haɗi sai ka ji an ce an sani saboda shahara" Cewar Dada lokacin da take shigewa cikin adaidaita sahun rike da ƴar akuyarta dama su Hassu tuni sun shiga sun zauna suka linga jakununan kayan a baya.
"Yawwa ka kai su za ta baka kuɗin" Cewar mai gadin nan don ba ya so mai adaidaita sahun ya ce wani abu game da maganar da Dada ta yi saboda ya ga ya saki baki cike da mamakin furucinta shi kuma mai gadi ya fi so har sai ta je ta ganewa idanunra domin bahaushe ya ce gani ya kori ji.
"Ungo ɗan nan ka sha ruwa ka ji mu ai yanzu kuɗi ba matsalar mu bace" Cewar Dada tana lissafo dubu ɗaya daga cikin sabbin kuɗin nan ta mikawa mai gadin shi kuma cike da murna ya mika hannu ya karɓa ya juya ya shige gidan ya rufo get ɗin Dada tana ta jero masa godiya kamar ta ari baki shi kuma mai gadin a zuciyarsa yana cewa
'Da kin san inda za ki je da ba za ki yarda ko naira ɗari ki bani ba bare har dubu guda' Mai napep dai ja ya yi suka tafi ga ya kure kiɗa a napep ɗin ji kake dumm-dummm-dumm m su Hassu sai kaɗa kai ake Dada kuwa sai rausayi kai take daga gefen hagu zuwa na dama tana jin duniya ta mata daɗi tabbas yau ta yarda da maganar kyankyaso da yake cewa garin daɗi yana nesa lokacin da ya leka masai.
Suna tafiya mai gadi ya ji horn a kofar gidan da sauri ya taso ya buɗe ya ga Ɗan Ibra ne bayan ya shigo ya faka mai gadi ya ja shi gefe ya shiga labarta masa zuwan su Dada.
"Wallahi Allah me ya maka gyaɗar dogo yanzun nan suka bar nan " Ya ce yana kwashe duk yadda suka yi ya faɗa masa.
"Taɓ lallai Allah tarfawa garina nono yau za a sha artabu kenan don wannan matar idon cin naira ne da ita ta ki jinin talauci amma kuma sai Allah ya yi ta talakar, tabbas iska tana yawo da mai kayan kara lallai yau Sagiru zai gamu da gamonsa duk da shi ma ba kanwar lasa bane"
"Aikuwa na ga take-takenta sai dai Allah daidaita"..
"To amin za a ce don har na hango yadda bakinta zai kasance a buɗe wayam idan ta je ta ga inda ƴarta take zaune" Ɗan Ibra ya ce yana tuntsurewa da dariya
"Ai na faɗa maka Allah ya sa Hajiya ta aike ka da a ce yau kai ne za ku fita da Alhaji da tsuhuwar nan ta ganka ka kaɗe har ganyanka tun da a gaban Alhajin za ta shiga rattabo maka tambayoyi"
"Allah ne ya rufa mini asiri" Ya ce yana juyawa da sauri ya tafi ya isarwa da Hajiya sakon aiken da ta masa
Masoyana masu bibiyar rubutuna ina buƙatar ku danna min like a wannn link ɗin na shiga gasa ne da littafin da like 👍 za a fitar da sakamako wanda ya min ina gdy ss
https://youtu.be/xYBCkQuUxnQ?si=-0h_Dapw86VBXeE1
Ga link ɗin
[8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
*IMZEED VENTURE*
Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna aiyar da gwanjo me kamar sabo!
Tuntuɓemu 07077532253
Wtsapp/IG/TiktocTikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-8yWWJj3GGri&_r=1
*Ku shiga link ɗin nan ku danna min like pls*
👇👇👇👇👇
https://youtu.be/Qne4qxr3CGw?si=scht05CDUP-pKVpB
*CI-MA-ZAUNE*
*NA*
*MAMAN AFRAH*
*Daga marubuciyar Malamin bogi, Ƙazamin miji, Bonono, Ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, Jalli joga, Beelal, Ungozoma da sauran su* *09025576222*
🅿️8️⃣
*DADA*
Tun da suka shawo kwanar da za ta sada su da gidan ta fara yi wa idanunta masauki a wani tamfatsetsan gidan wanda take kyautata zaton a nan za a sauke su. Sai dai hasashen ta bai zama gaskiya ba don suna zuwa ko kallon gidan nai napep ɗin bai yi ba ya wuce.
.
"Yaro ka ce ka san gidan Alhaji Sagirun ko?" Dada da ta ɗaga murya tana tambayar mai napep ɗin ta faɗa cike da mamakin ganin ya wuce gidan da tale zato nan zai kai su.
"Wane Alhaji Sagiru kuma? "
"Kamar ya wane Alhaji Sagiru kuma to gidanku za ka kai mu? Ko kana ganin bamu yi kama da wanda za su je gidan ba gani kake bamu da dangantaka ko? To ni nan ni ce mahaifiyar Hajiya Amina matarsa ka ga kuwa ai mu ne kirjin shiga gida" Ta ce tana hayayyako masa don ta ga abin nasa kamar raini ne yake son nuna wa bayan an faɗa masa inda zai kai su ya ce ya san wurin gidan ba ɓoyayye bane amma kuma yanzu yana raina mata hankali yana rainawa kansa ajawali.
"Ke kika san su ma ni ina na san su, abu ɗaya na sani dai ya ce mini tsamiyar osi zan kai ku gidan yawa shi ne na ce na san gidan saboda gidan ba ɓoyayye bane"
"Au to dama shi Alhaji Sagirun har wani mutane ya tara suka cika masa gida ko dai ƴan aiki ne har ake wa gidan lakabi da gidan yawa? Son hayaniya take hana Amina hutawa to da sake uban miji zai auri matar ɗansa" Ta ce tana ji a ranta duk sai ta sa an sallame su sai dai a bar kaɗan don ba zai iyu ita da ta baro kauye don ta zo ta huta kuma sai ta zo ake hayaniya ana hana su rawar gaban hantsi. Shi dai mai napep bai sake cewa komai ba dama karan ya ɗan rage yana gama baya amsa kuwa ya kara kure karan kiɗan.
"Dada ki rabu da shi kawai ina jin babu ce take damunsa" Usai ta ce tana kallon Dada.
"Yauwa ƴar nan ashe kin gano shi ina jin fa yadda ya ganmu yamutsai ɗin nan zatonsa almajirce za mu je gidan" Ta ce tana ɗakko dubu ɗaya cikin sabbin kuɗin ta mika masa.
"Ga dubu nan ka rike canjin tun da ɗari takwas ka ce" Ta faɗa tana mika masa hannu ya miko ya karɓa yana ta godiya
"Ahaf ai kin ji zancen yanzu ba gashi ya ware ya karɓe kuɗi ba, ya saki fuska ai na faɗa muku kuɗi masu gidan rana mutum da kuɗi abokin tafiyar kowa"
Sun ɗan kara tafiya kenan sai kuwa mai napep ɗin ya tsaya a kofar wani kwaraɓaɓɓan gidan kasa, su Dada basu kawo komai ba don duk zaton su ko wani abu zai karɓa. Shi ma ganin basu da niyyar fita sai