Showing 6001 words to 9000 words out of 52525 words

Chapter 3 - CIMA ZAUNE Complete by Maman Afrah.txt

30 Aug 2025

1764

ƙofar bai bi ba bare ya rufe.

MAMAN AFRAH
09025576222
[8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
*IMZEED VENTURE*
Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna aiyar da gwanjo me kamar sabo!
Tuntuɓemu 07077532253
Wtsapp/IG/TiktocTikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-8yWWJj3GGri&_r=1



*CI-MA-ZAUNE*


*NA*


*MAMAN AFRAH*

*Daga marubuciyar*
*Malamin bogi, Ƙazamin miji, Bonono, Ruɓaɓɓiyar igiya, Ƴan adaidaita sahu, jalli joga, Ƙara'in inna delu, Beelal da sauran su* *09025576222*



🅿️3️⃣

Tun kafin ya shigo cikin gidan yake rafkawa Amina kira, Amina tana banɗaki ta jiyo muryarsa yana ƙwala mata wani irin kira mai kamar ba lafiya ba. Fitowa ta yi ta nufi hanyar turakarsa a ɗarare don ya hana ta zuwar masa ɗaki, ta kusa ƙarasawa ta ji ya ƙara ƙwala mata wani kiran sai lokacin ta gane daga ɗakinta kiran yake fitowa da sauri ta nufi ɗakin tana fatan ba wani gagarumin laifin ta yi ba. Tana shiga ɗakin ta yi same shi zaune yaraf a tsakar ɗaki ya miƙe ƙafafu wannan tumbi nasa ya yi yaraf a kan cinyoyinsa. Makaki ne ya rufe ta ganin yadda yake wurjanjan ga shi a jiƙe jagaf kuma ko alamar nutsuwa babu a tare da shi sai wani raba idanu yake tamkar an kama kwarto a ɗakin sabuwar amarya.


"Amina maza rufe ƙofar ɗakin nan" Ya faɗa har lokacin babu nutsuwa a tare da shi. Ita ma abin ya ɗaure mata kai har ta manta yaushe rabon da ya mata magana cikin taushin murya, da sauri ta rufe ƙofar tana mamakin abin da ya sanya shi a halin da yake ciki.

"Amina ɗauke ni ki ɗora ni a kan gado" Ya ce bayan ta rufe ɗakin ƙare masa kallo ta shiga yi tana tunanin ta inda za ta fara.

"Wallahi ba zan iya ɗaga ka ba" Ta furta a tsorace amma abin mamaki bai mata jaraba ba, haka suka kwana a zaune bacci sai gyangyaɗi saboda ya ce ba zai yarda ya kwanta ba dalilin da ya sa ma ya zo ɗakin nata tun da an ce yanzu tare zai ke sabgogi aljannu suna tare da shi, shi ya sa ya ƙi dosar turakarsa, a nan ɗin ma an gudu ba a tsira bane saboda daga bacci ya fara ɗaukansa masu baƙaƙen kaya da ƙaho biyu yake gani wannan dalilin ne ya sa baccin nasa ya kasance rabi da rabi. A ƙarshe ma sai yake zazzabura yana surutai hakan ya sa Amina ta fara tunanin ko jifa aka masa don abin da yake yi ya nuna kamar ba ya cikin hayyacinsa komai ya yi a firgice yake yi.

Da asuba da ta masa maganar ya je ɗakinsa ya canja kayan duk da dai sun sha amma kuma har lokacin da damshin lema amma sai ya ƙi don ko da daren ma da ta tambaye shi mai ya jiƙa masa kayan sai ya ce wai ruwan sama aka yi ita kuwa ganin ba damuna bace sai ta ƙyale shi. Bayan ta idar da sallah tana lazimi sai ta ji wani ɗoyi ya cika ɗakin kafin ta gama addu'a sai take jin sautin darrr, bayan ta shafa addu'ar da mamaki ta juyo tana son gano ta inda ɗoyi ya baibaye ɗakin.

"Daina ba kan ki wahala Amina ni ne nake sakin iska tamkar keken da tayarsa ta caku da ƙusa, ni ba bodari ba amma tusar nan nayi-nayi na na danne ta na matse abata amma abin ya ci tura! Ki yi dabara ki kai ni banɗaki mana" Ya ce yana kallonta. Gaba ɗata yadda ya haɗe ɗakin da wari tamkar mushe ya mutu a ɗakin, ji take warin har maƙoshin ta tamkar ta yi amai. A lan rusheshen cikinsa ta yi wa idanunta masauki wanda yake tatul.

"Wallahi ba zan iya ɗaukan ka ba" Ta ce cikin sanyin murya tana so ta ce mai ya sa ya ƙi tashi amma tana tsoron ya mata jaraba.

Kashin da bai yi ba sai sakin tusa a kai-a kai haka ta daure ta zauna da shi har gari ya waye sannan yana mata faɗa ya ce ta je gidansa ta kira uwar gidan da mai ɗakin tsakar tun da su suka san darakarsa ba za su ƙi taimaka masa ya tashi ba. Tun da matan nasa suka zo suka ce ba za su iya ɗaga shi ba a nan yake ce musu faɗuwa ya yi sai mai baro aka kira zai kai shi gidan mai gyara don mai gyran tsoho ne kuma ba ya zuwa ya gyara ko waye sai dai a je gidansa. Ga shi ya ce kar a taɓa masa mota saboda tsabar son abin duniya.


*HASSU DA USAI*

Da lallaɓe suka koma gida suka rufe ƙofar suka shige ɗakin Dada, ita ma Dada tana jiran dawowar su don haka ko da suka labarta mata abin da ya faru har da rawa ta taka.

"Shegen mutumi da ciki kamar motar lodin shanu, shi don haɗama duk yadda tukumbu(Tinubu) ya shashshafa mutane duk suka ƙare kamar hatsin guzuri kowa ka gani a rame a ƙanjame amma shi jikinsa kaf babu ƙashi sai tsoka luƙum-luƙum ga cikin nan nasa ina ga ma ko kayan cikinsa linki biyu ne to na ga dai da alama girman cikin nasa ya yi yawa" Ta ce tana taɓe baki. Haka suka ringa labarin Alhaji suna shan dariya tare da gwadawa Dada acting ɗin da ya sha yi, a haka har bacci ya yi awon gaba da su.

Da safe Hassu ta fita sayan ƙosai ta zo da labarin wai Alhaji sabo ya karye a kwankwaso. Wannan labari ya yi musu daɗi musamman Dada saboda ta ce ta samu kangarar raba aurensa da Amina. Bayan sun karya ta saɓi mayafi sai gidan Amina, a nan ta samu matan nasa sun yi faɗa uwar gidan ta kai ƙaran amaryar wajen Mai Gari da yake gidan Mai garin babu nisa da gidan Aljahi Sabo. Dada ko gidan Amina bata shiga ba sai kawai aka ɗunguma zuwa wajen Mai gari don tana ganin faɗuwa ce ta zo daidai da zama ita ma tana da magana da Mai garin.

"Wallahi Mai gari ita ce bata da gaskiya ni na fara ɗaukan wando da ƴar cikin shi ne ita kuma ta ɗauki babbar rigar a kan na ce sai ta bani shi ne muka kaure rigima" Cewar matar Alhaji Sabo mai ɗakin tsakiyar.

"Ke mai ya haɗa ku" Mai gari ya jefawa uwar gidan tambaya.

"Kawai don ta ga shaddar tana da kyau kuma tana da tsada ai tun da ni ce uwar gida sai ta bar mini tun da ta samu kusan kala ashirin" Uwar gidan ta ce tana damƙe bakkon (Ghana most go) Da take kusa da ita wanda a kan ta kayan sakawar Alhajin ne da suke ɗauka tun da basho da lafiya shi ne kowacce ta kwashi rabonta.

"To shi Alhaji Sabon da yak rashin lafiya ba mutuwa ya yi ba, amma kuke raba kayansa bayan yana can yana shan azaba a wajen gyara amma ba za a tausaya masa ba sai faɗa har gaban Mai gari" Mai gari ya ce yana kallonsa.

"Yo ai da shi da gawa babu maraba, auren sa ne na gama" Uwar gidan ta ce.

"Ko ni ba zan zauna da shi ba "Mai ɗakin tsakiya ta ce

"Ko ni Amina ta gama zama da gurgun mage, yarinya samtaleliya ba za ta ƙare a zaman jinyar wannan mutumi da ba san ranar warkewarsa ba, haka kawai take cicciɓarsa tana kai wa bayi a je allon bayanta ko ƙirjinta ya lotse in shiga uku, bayan ita kaɗai ta rage mini sai marayun ƴan biyun can Allah na tuba idan Amina ta zauna tana taimaka masa yana tashi tsaf kafaɗunta za su bar gangar jikinta, wato hannayenta ya baro jikin daga kafaɗar haka kawai a tashi zaune tsaye wai sarki ya ji naɗin sarautar dogarinsa" Ta ce har ca share guntun hawaye.

"Haba ku kuwa larura fa tana kan kowa, ku ma yanzu Allah zai iya jarrab...

"Bakin ka ya sari gatarin aikin gona kar ka mini baki ni dai don baki ba ɗan uwa bane... Hango Alhaji Sabo an turo shi a cikin baro yana ciki yamutse a zaune kamar kayan wankin da aka daɗe ba a wanke ba, shi ba a zaune ba shi ba a kwance ba ya ringisa gaba kamar dai wanda ya sunkuya, hakan ne ya katse maganar da Dada take yi sai kowa hankalinsa ya koma gare su.


"Bawan Allah gashi nan ma yau ko motar ma ƙin shiga ya yi ya gwammace a kai shi a baro(kura) Mai gari ya ce yana kallon sa.

"Haba ai yanzu zama a gidan Sabo ya zama larura auren namiji da ƴaƴa ko kaɗan duk wanda ya zauna to ya tabbatar wahala ce" Dada ta ce tana taɓe baki.

"Sannu Dada ke ma kin zo dubiyar, ashe kun ji tsautsayin da ya rufta da ni" Alhaji ya faɗa yana sakin wani ɗan nishi tamkar wanda ya daɗe yana jinya a gadon asibiti.

"Waye zai zo dubiyar taka? Ni? Taɓ ala suturi buƙwi in ji kishiyar mai doro rabani da tsautsayin takaba auren shiɗaɗɗe, ai babu mai rabon shan duka sai mai waiwaye idan yana tafiya ni nan zuwa na yi ka sakar mini ƴata tun da ba tare muka yi naƙudarta da kai ba"

"Haba Dada a lokacin da mutum yake cikin buƙatuwar mai tallafa masa ai ba a yi zacen saki ba duk da dai ba ita kaɗai bace matar tawa amma kowa yana da amfani sai suke baki-baki kowa ranar bakinta sai ta tallafe ni karaya ce a kwankwaso zan iya warkewa...

Tun da ya fara maganar Dada take aika masa saƙon harara, har ta ji ba za ta jure saurarensa ba ta katse shi da faɗin


"Ƴata ba wahalalliya bace da a ce kai tsohon arziƙi ne sai ta zauna amma dai ba za ta zauna yanzu da mai karyayyan kwankwaso ba, haka kawai da yarintar ta kuma da kake maganar matanka gasu nan ai sai mu gani in tusa tana hura wuta tun da gasu nan har sun fara rabon gadon kayan sawarka har suna faɗa a kan riga" Cewar Dada tana aika masa kallon iska tana yawo da mai kayan kara. Sakin baki ya yai yana bin matan nasa da kallon mamaki jin furucin Dada ganin ƙamshin gaskiya ya sa wasu zafafan hawaye suɓuce masa suka shiga zarya, yana ganin ga ƙosho ga kwanan yunwa domib alamu sun nuna babu wata mace da za ta zauna a dashi.

"Ni Sabo na ga ta kaina daga karayar kwankwaso shikenan sai a fara guduna tamkar wanda nake cin mutane?" Ya faɗa yana rushewa da kuka, uwar gidan nasa da mai ɗakin tsakiyar ne suka damki wuyan rigarsa suna jijjiga jiki a kan sai ya sawwaqe musu ga kuma Dada tsaye a gefe guda ita ma tana jiran takardar ƴarta bayan ita Aminar bata san wainar da ake toyawa ba. Dakyar da suɗin goshi Mai gari ya ba wa matan nasa hakuri suka fasa neman sakin bayan ya faɗakar da su cewa babu kyau neman saki, haka suka hakura Dada kuwa ta saka auduga ta toshe kunnuwanta dan daga karshe ma sai ta je ta sako Aminar a gaba tana kuka amma haka Dada ta saka aka saki Amina. Malam sai na mujiya ya zuba musu don a ranar sai da aka kwaso kayan Amina kaf aka kawo gida aka zuba a wani tsohon ɗaki sa ake saka tarkace.




BAYAN AMINA TA GAMA IDDA


Tafe Dada take ita da ƴan biyun ta suna tafiya suna hira daga gidan kawarta da take can karshen gari suke. Wata haɗaɗɗiyar mota ce ta zo gifta su wacce sai sheki take da kallo suka bi motar Dada a zuciyarta tana raya ina ma Amina ta samu miji mai mota kamar wannan da kakarsu ta yanke saka. Har motar ta gifta su sai ta dawo da baya, a saitin su ta tsaya aka zuge gilashin.

"Ɗan Ibra?" Dada Hassu da Usai suka haɗa baki wajen faɗa. Wani murmushi ya sakar musu ya kwama wani uban gilas a fuska.

"Dada ku shigo in rage muku hanya na karasa da ku gida ...

"Ɗan Ibra daga tafiya birni sai in ganka a galleliyar mota to in dai ba yankan kai kake ba ta yaya za ka samu mota ya wannan?" Dada ta ce tana ɗan ja da baya kamar yadda su Hassu suka ja.

"Dada direbanci nake a birnin gidan su yallaɓai Sagiru to yanzu cewa ya yi bai taɓa zuwa kauye ba shi ne na kawo shi ya gani" Ya faɗa yana kallon na gefen mai zaman banza wanda sai lokacin su Dada suka lura da shi, sai wani gyara zama yake yana yatsina.

"Allahu akbar kabiran, Allah sarki Ɗan Ibra ka yafe ni har na ɗauki alhakinka ka san duniya ta ki daɗi ashe da yallaɓai kuke tafiya" Ta ce tana washe baki idanunta kurrr a kan wanda aka kira da yallaɓai Sagiru.

"Ba komai Dada" Cewar Ɗan Ibra. Dada kuwa gaishe da yallaɓan ta yi tana wani bashi girma kamar ta ari baki, inda Hassu da Usai ko kallo bai ishe su ba. Kai kawai ya gyaɗa bai yi magana ba kamar wani mai ciwon hakori.

"Ku shiga mu tafi" Ɗan Ibra da ya fito ya buɗe musu kofar ya ce yana rike da murfin, sai da suka shiga ya rufe ya shiga ya tada motar suka tafi Dada sai jan shi da hira take tana tambayarsa bayan saduwa tana kallon Sagiru tana rayawa a ranta dama ya zama sirikinta ko Allah ya musu gyaɗar dogo su samu hanyar zuwa birni.

A daidai kofar gidan suka tsaya da motar su Dada da Ɗan Ibra ya buɗewa suka fito Dadar tana ta faman zabgar godiya tamkar ta ari baki. Har Ɗan Ibra zai ja mota Dada ta ce

"Ɗan Ibra ko ruwa baku sha ba da kun shiga kun sha ruwa"

"Haba Dada ai sai dai ni in sha hakan ma don ana cewa kowa ya bar gida, gida ya bar shi amma yallaɓai sai ruwa gora yake sha ɗan kamfani" Gyaɗa kai kawai Dada ta shiga yi kamar kadangaruwa jin wani babban al'amari wai ruwa ma sai na kamfani hakan ya kara tabbatar mata da wuya wai gurguwa da auren nesa wato burinta ya kai ga cika saboda yanzu komai ya zama akwai ya babu kakar wajen uba. Su Hassu tuni sun shige gida tana shirin juyawa ita ma sai ga Amina za ta shiga gida.

"Ɗan Ibra" Dada ta shiga kwalla masa kira don tuni ya fara jan motar ta fara tafiya. Birki ya ja kafin ya dawo da baya Dada har ta karasa a gefe guda tana kiran Amina.

"Dama cewa na yi ga Amina ku gaisa" Ta ce tana kamo hannun Aminar ta kawo ta windown motar saitin da Sagiru yake. Gaishe da su Amina ta yi cikin girmamawa tana jin babu daɗi a zuciyarta yadda Dadar ta kawo ta sai ka ce wanda suka ajiyeta wai ta gaishe su.

"Ai Amina da budurwa marabar su kaɗan ne wallahi, yo sakin wawa ce wawan ma mai runtumemen ciki silgar didi in ji ƴan birni (Sugar daddy )" Dada ta ce tana kallon Sagiru.

"Haba Dada kin manta abokina ya nemi Amina amma da yake ba rabonsa bace bai aure ta ba ai ba zan iya neman budurwar da abokina ya nema ba dama ya ce mini aurenta ya mutu" Ɗan Ibra ya ce yana kallon Dada.

'Ka ji wani sakarci jiran jirgi a tashar mota haba Ɗan Ibra kowa rai ya yi wa daɗi ba ya mai shi va, ana maganar inda za a samu mai maiko amma kana maganar ka, kaima da gaka nan jiya iyau baka gaba baka baya kullum kana kwan gaba kwan baya sharar mai son jiki, kowa ya ganka ya ga wanda tikumbu ya shafa taɓ lallai da sauran aiki wai tukumbu ya ga talaka da tumbi' Dada ta ce a zuciyarta a fili kuma ta ce.

"Dama mai gidan naka" Sagiru da yake wani ɗauke kai kamar ya ga kashi ya mata wani kallo da ya sa ta fara inda-inda.

"Taɓ lallai Dada da ake miki kirari da Dada idon cin naira ashe dai haka ne daga ganin sarkin fawa sai miya ta yi zaki ba tare da an saka nama ba?' Ya ce w zuciyarsa a fili kuma ya buɗe baki zai yi magana Sagiru ya katse shi da cewa

"Mu tafi" Umarninsa ya bi suka bar Dada tsaye da sakakken baki don Amina tuni ta shige gida.



MAMANA AFRAH
09025576222
[8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J?mode=ac_t



*CI-MA-ZAUNE*


*NA*


*MAMAN AFRAH*
Daga marubuciyar
*MALAMIN BOGI*
*ƘAZAMIN MIJI*
*BONONO*
*RUƁAƁƁIYAR IGIYA* *ƳAN ADAIDAITA SAHU* *ƘARA'IN INNA DELU* *JALLI JOGA BEELAL* *ƳAR ZAMAN WANKA*
Da sauran su *09025576222*
🅿️4️⃣


Dada abin duniya ya haɗe mata goma da ashirin gabaɗaya ta ɗora rai a kan Sagirun da Ɗan Ibra yake direbanci a gidan su bare kuma mutumin da yake zaune a birni ai duk ranar da Amina ta aure shi kakarsu ta yanke saka. Sau uku tana fita dab da magriba ko Allah zai nuna mata motar su Ɗan Ibra don ta gwammace ko sadaka ne ta ba Sagirun Aminar saboda kawai ta aure ɗan birni kuma ɗan masu kuɗi.

A cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login