Showing 3001 words to 6000 words out of 52525 words

Chapter 2 - CIMA ZAUNE Complete by Maman Afrah.txt

30 Aug 2025

1762

ma ya ce na'am ran Dada har zafi yake ba don tsoron habaicin kishiyoyi ba da a yanzu zai sakar mata ƴarta. A bakin ƙofa ya tsaya bayan ya buɗe labulen ua tsaya getsetse a kan Dada da take zaune a kan kujera yana riƙe da ƙugu. Wani takaici ne ya dirar mata tana jin tamkar ta hau cikin nasa da duka ko ta rage damuwa.

"Ya aka yi ne"

"Au Allah gaskiya ne Sabo ni za ka nunawa salalan tsiya? Ni za ka sincewa zani a kasuwa na ɗauki ƴar budurwa gagal a leda na baka amma ko wata ba a rufa ba gaisuwa ma ban isa ka gaishe ni ba?"

"Yo ai mun gama bajat ni da ke kuɗi dai kika aura mata kuma na sha baku shi kafin na aure ta kun gama cin rabonku yanzu kuma sai yadda hali ya yi sai abin da kuka gani" Ya ce yana saka hannu a aljihu ya ɗauki naira ashirin ya ajiyewa Dada a kusa da ita wai ta sayi goro ya juya ya fita Amina tana jin daɗi da bai ga miyar da Dada ta zubar ba bare ya mata faɗa.

Lallaɓowa Amina ta yi ta zauna ta doka uban tagumi.

"Oh ni Saude in da ranka ka sha kallo, ashe mutumin nan lumbu-lumbu ne wutar ƙaiƙayi ita bata ci ba ta haɗe ko ina da hayaƙi, yanzu lalacewar son kuɗin nawa har ya kai a ɗauki murtala (20) A ce na sayi goro wato ga wacce talauci ya gama baibayewa, ni Saude ina zan kai wannan bala'in wannan abin kunya da mai ya yi kama har nake kasa fitowa daga ɗaki, ni ban san ba ma ko dai su Ladiyo suna da labarin halin da kike ciki nake musu kallon biri suna mini kallon ayaba" Ta ce tana doka wani uban tagumi ga yunwa tana ƙwaƙular ƴaƴan hanjinta.

"Ki yi haƙuri Dada wannan ce ƙaddara ta"

"Ah ah zan yi duk yadda zan yi ko mai gari sai na kai masa ƙara ya raba wannan auren" Da wannan ta baro gidan riƙe da ledar vivan da ta saka zanin Amina da ko wanki bashi da shi don ta yi basaja kar a ce bata kawo komai ba, a yi gulmarta ko a yaɓa mata magana kasancewar zama da kishiyoyi komai kake yi a ido yake.

A inda ta wuce su Sabo yanzu ma suna zaune ko kallo basu ishe ta ba yunwar cikinta ma ta ishe ta, lokacin ana sallar la'asar ta shiga gida ita da ta ce sai dare sai ga shi rana ma ko sanyi bata yi ba ta dawo bare a yi zancen dare. Rai ta haɗe ta shigo tana muzurai.

"Ga Dada ga Dada yau akwai wankin baki auren mai kuɗi akwai riba" Hassu da Usai suka haɗa baki lokacin da suka fito daga ɗaki suna murnar dawowar Dada. Dada jin furucin su sai ta shiga dariyar yaƙe sai dai ta kada mayar da martani don yanzu gani take kamar Ladiyo da Mero sun san abin da yake faruwa. Ƙafa Usai ta saka ta yi ball da kwanon teba da aka musu da miyar ɗanyar kuɓewa dama tun da aka zuba musu ta yi balla da shi wai ba za su ci ba su yau sai abincin gidan Alhaji Sabo, ganin dawowar Dada shi ne ta ƙara ball da shi.

Zaunawa Dada ta yi jugum da ita, su kuma har rige-rigen buɗe ledar suke sai dai ganin zani marar wanki ya karya musu lago suka hau bin Dada da kallon tuhuma sai lokacin ma suka lura da damuwar da take ciki.

"Dada Antyn ce bata da lafiya?" Hassu ta tambaya ita ma Usai kallon Dadar take don jin amsar tambayar.

"Yo ina fa yaran nan tana lafiya sai dai bata cikin jin daɗin da muka tsammata" Ta ce tana kwashe komai ta faɗa musu cikin raɗa don kar a musu laɓe a ji abin da suke cewa.

"Dama haka yake matsiyaci ne" Suka haɗa baki wajen faɗa.

"Hmmm! Wai ni Sabo zai kalla ya ba naira ashirin sai ka ce almajira, tabbas ba wahalalle sai kwaɗayayye, tun da an ci moriyar ganga sai ayada korenta.

"Ki ƙyale shi Dada za mu nuna masa kurensa" Bata ce musu komai ba don ta san za su iya.

"Yunwa ce take addabata wallahi kamar in ci babu" Dada ta ce tana kallon su.

"Aikuwa Usai ta cewa Ladiyo ba za ki ci teba ba kar ma a yi rabo da ke, mu ma namu da aka bamu gashi can a ƙofar ɗaki da muka yi ƙwallo da shi"

"Na shiga uku ni Saude shikenan ni da ku mun yi haihuwar guzuma ƴa kwance uwa kwance" Ta ce tun da kowa yunwa yake ji kuma ga shi sun yi sagegeduwa ba wan ba ƙanin karatun ɗan koli, wato basu ci na gidan Aminar na gashi na gidan ma ya gagare su kuma babu damar a tambayi Ladiyo abincin Dadar ta ce bata kasa da ita ba ko ma ta musu gori. Haka suka zauna sai dare da aka gama tuwo kowa ya zuba yana muzurai don ma kar a yada musu magana.

*DARE*

Wajen ƙarfe goma sha ɗaya na dare lokacin dawu ya fara ɗaukewa, Hassu da Usai ne suka zo wurin ƙatuwar kwatar kwalbati inda suka san nan ne wurin wucewar Alhaji Sabo idan ya dawo daga majalissar gabas inda yake zuwa kullum hira da dare. Gadar da aka yi a kwalbatin guda ɗaya ta katako wacce sai ta nan Alhajin zai bi, gatari suka saka suka daddatsa ta yadda ba za a gane ba, sai da suka gama suka gyaggyara katakon yadda ba a a gane ba. Kan bishiya da take kusa da wurin suka haye suna jiran dawowarsa. Ba ɗau lokaci ba kuwa sai ga shi ya taho da tulelan cikinsa yana tafiya cikin yana rinjayarsa, riƙe yake da wani kafcecen rake yana tafiya yana gaftara abinsa, kwalbatin cike yake da ruwa taf. Sun kallonsa kowacce ta saka hannu ta rufe bakinta don ma kar a samu matsala dariya ta ƙwace musu, yana zuwa hankali kwance yana cikin giyar rake ya hau gadar da yana takawa gaba ɗaya ya rufta ciki, da yake dama sun gama ragargaza gadar kuma ga nauyinsa sai ya zama yana takawa ta rabe gida biyu shi kuma sai gashi yana iyo a tsakiyar tafkeken kwalbatin, wutsil-wutsil yake yana neman ɗauki amma babu kowa a wajen ga shi don ƙarfin hali zungureran raken sa yana riƙe a hannunsa. Su Hassu suna ganin duk abin da yake faruwa da a ce ya ɗaga kai saman bishiya zai iya hango su amma ta ceton ransa yake domin ya faɗa a bazata ga shi kwalbatin da mugun zurfi da faɗi sai wasu shegun ƙurunƙusan duwatsu a ciki wanda tun lokacin da Alhajin faɗa bayansa ya bugu da jikin wani abu da bai san mene ne ba.

Mage da suka taho da ita Usai ta ɗaukota tare da saita Alhaji Sabo da yake iyo yana facal-facaltun yadda zai fito ta jefa masa ai kuwa ta sauka a saitin wuyansa, maƙalƙale masa wuyan ta yi tana ta faman karta faratan ta a wuyan ga wani kuka da take yi wanda yake zuwar wa Alhajin a kamar sautin kukan kare wannan magen ita ta saka Alhaji ya fara tsorata da lamarin ganin ya kasa fita daga kwalbatin da bai kai ya kawo ba kuma ga wata mage da bai san daga inda take ba ta mayar da wuyansa tamkar jikin bishiya. Wannan dalilin ya sanya ya fara tunanin magen ko dai ƴar ruwa ce a gefe guda kuma yana tunanin ko dai igiyar ruwa ce ta ja shi tun da ga shi ma yana jin bayansa tamkar an sara ƙashin bayan, tun da tun bayan da ya bugu da bayan ya kasa kataɓus.

Yunƙurawa ya yi a karo na ba adadi yana ƙoƙarin fitowa amma abin ya ci tura! Magen kuwa tamkar wanda aka haɗa ta da abokin dambe haka take kokawa da Alhaji, ƙeyarsa ta baro ta dawo daga gaba ta maƙalƙale wuyansa ga farcenta da ta maƙaleshi da shi ji yake tamkar an caccake shi da allura duk faratan sun nutse a cikin ƙosasshiyar tsokar wuyan nasa. Tamkar wanda aka faɗa wa magen ta sako bakinta ta kama gemun Alhaji da yake reto kamar jelar ɗan akuya wanda yake jiƙe da ruwa sharkaf ruwan sai ɗisa yake tana damƙa da haƙoranta masu tsini don sai da ta haɗo har fatar jikin haɓar ta gatsa sai ta riƙe gemun a bakin tamkar za ta cisge shi daga haɓar.

"Wayyo Allahna! Ya furta a galabaice yana sakin ɗan ƙara. Ana cikin haka Hassu ta yi wani tsalle ta diro daga saman bishiyar , faɗowarta ke da wuya sai Usai ma ta biyo bayanta sai a lokacin na ƙare musu kallo ta cikin haken farin wata, sanye suke da baƙaƙen dogayen riguna kan su babu ɗankwali sun barbaza gashin kan su sai kuma suka samu ƙahon kan saniya suka saka shi a gefe da gefen kansu wato wajen kunnuwan su, suka yi dibara suka ɗaure da siraran tsimma sai ƙahon ya zauna daram tamkar dama a haka suke amma kana ganin su za su baka tsoro don basu da maraba da aljannu.

Alhaji Sabo wanda a kan idanunsa Hassu ta faɗo ƙasa kuma maimakon ta zo a tsaye sai ta zo a tsigunne, shi dai da yake yana cikin tashin hankali ne bai san daga saman bishiya ta diro ba duk a tunaninsa ta saman iska ta diro. Bai gama mamakin kasancewar hakan ba sai Usai ma ta diro a take ya ki duk damuwar faɗawa ruwa da yake ciki da kuma azabtar da gemun haɓarsa da mage take yi sun zama nafila yanzu ne yake ganin tashin hankali na farilla saboda ganin idanunsa a kan ƙahon su ya sauke idanun.

Ƙuuuuuiiiit Wata tusa da ta kuɓuce masa ta samu damar fitowa da yake yana cikin ruwan shi kaɗai ya ji sautin fitowarta amma hakan shi ba damuwarsa bane ko da a ce kashi ne zai ƙwace masa a kan tashin hankalin da yake ciki tun da babu alamar wani mau taimakonsa zai zo abin ka da ƙauye kowa ya shige gidan baka jin komai sai kukan karnuka.


Yana ji yana gani su Hassu suka fara tashi tsaye daga tsugunnon da suka yi, cikin wata tafiya mai kama da ta mutanen ɓoye suka fara doso wurin da yake.

Boootttttt, ya saki wata ƙatuwar tusar a cikin ruwan yana ciccira idanu yana fatan kafin su zo ya arce don a zuciyarsa ya fara tunanin cikin ɗayan biyu ko dai sheɗanun aljannu saboda ya ji an ce sheɗan yana da ƙaho, kuma aljannu ma suna da ƙaho, bai manta ba a majalissar su wata rana ana hira ya ji an ce dujal ma yana da ƙaho. Mala'iku ma an ce suna da ƙaho shi dai kokwanto yake don bashi da wani ilimin addini da na zamani bare ya jahilci zallah yanzu bai san takamaimai waɗanne ne suka zo ba.

Alhaji dama mugun matsoraci ne, yana ganin sun ƙaraso wajensa kallo ɗaya ya yi wa fuskarsu wacce take shafe da baƙin gawayi duk shirin nan sun yi shi ne a gidan wata tsohuwa makauniya da yake kusa da wajen da yake ita ba bani take yi ba sai suka yi shirin su a zauren gidan gudun kat su shirya a gida asirin su ya tonu.

"Wayyo ni Sabo ɗan gidan Rakiya yau kuma da wannan muka fara kuturu ya ga mai ƙyasbi, tabbas abin da yawa mutuwa ta shiga kasuwa" Ya ce a zuciyarsa yana jin tamkar ya ɓace ya tabbatar idan dai mala'ikun mutuwa ne to tabbas zai mutu ya tarar da abin da ya shuka na zakunci da yake yi qa al'umma hatta da iyalansa bai bari ba tauye haƙƙoƙin su da yake amma ya saka bokansa ya rufe musu baki basu isa su faɗi aibun sa ba.

Hassu ce ta zo ta gabansa da yake daga gaba ya fi kusa da bakin kwata tana kuma tsoro ta je ta baya ita ma ta wuntsila cikin kwatar a yi haihuwar guzuma ƴa kwance uwa kwance. Hannu ta miƙa saitin kafaɗarsa ta dafa shi har lokacin magen nan tana riƙe da jelar gemunsa a bakinta shi zuwa lokacin ma ya daina jin zafin ja masa gemun da take yi domin kuwa yanzu ya ƙara tabbatar da gaba da gabanta aljani ya taka wuta! Usai ma bata yi ƙasa a gwiwa ba ta tsugunna a gefen ƴar uwarta ta kai nata hannun ta dafa ɗaya kafaɗar tasa. Duk da a cikin ruwa yake kuma fuskarsa a jiƙe da ruwan amma kuma hakan bai hana su ganin yadda gumi yake tsirnano masa dama bahaushe ya ce marar gaskiya ko a cikin ruwa gumi yake. Tun da hannayen su ya sauka a kafaɗar sa jikinsa ya shiga karkarwa kamar wanda zazzafan zazzaɓi ya rufe, yanzu kam ya tabbatar da mala'ikun mutuwa ne.

'Tabbas rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya yau ranar tafiyata lahira ta zo ba tare da na shirya ko ta yi tsammanin zuwanta a kwana kusa ba' Maganar da ya yi a cikin zuciyarsa ta fito fili cikin karkarwar baki. Ta wutsiyar ido Hassu da Usai suka kalli juna yanzu kam tarkon su ya kama tsuntsu!.


Da ƙarfin su suka danna kafaɗar tasa sai da ya shige ruwan gaba ɗaya kansa suka bashi minti biyu sannan suka saka shi ya ɗago daga ciki, sai da suka masa haka sau uku dama su buƙatar maje hajji sallah wato su azabtar da shi kamar yadda yake azabtar da ita saboda suna tsoron su masa kashedi ya yi wani tunanin da ban.

"Sabooooo" Hassu ta faɗa cikin wata muryar tsoratarwa. Hannu ya kai ta cikin ruwan ya shafo cikinsa wanda yake tamkar mai cikin ƴan uku yana jin da a ce babu rusheshen cikin nan da tuni ya fito daga ruwan ya gudu tun kafin ma su zo.


"Saboooo mutuwarka tana tafe ko da wane lokaci sannan kuma kana cikin haɗarin bibiyarka da aljannu za suke yi don sanin mai za kake aikatawa har zuwa ranar cikin wa'adinka" Usai ta dawo da shi daga tunanin da yake kai ya shiga gyaɗawa tamkar wani ƙadangare, yana ganin allura ta tono garma tun da har rayuwarsa za ya zama da bibiyar aljannu dama an ce na shiga ban ɗauka ba bata fitar da ɓarawo.

Sai da suka gama bashi wuju-wuju sun tabbatar da cewanya karɓi hukunci sannan suka ce minti biyu suka bashi ya fita daga kwalbatin in ba haka ba mutuwa za ta riske shi. Facal-facal yake a ruwan tamkar agwagwa tana wanka a kwata yana ta neman hanyar fitowa don tun da suka ɗauke hannun su daga kafaɗarsa yake jin ko makka suka bashi umarnin zuwa a ƙafa babu abin da zai hana shi zuwa saboda zaman hannunsu a kafaɗarsa ko yi masa magana da kuma nutson da suka masa a ruwa ba ƙaramin halin tsoro bane. Taimakon da Allah ya masa yana ɗaga ƙafarsa ya sauke a kan wani dutse mai ɗan tudu wanda shi ne ya taimaka masa ya yunƙuro, hannu biyu ya ɗoro a saman ya ɗare sai kuwa ya wuntsila sai ga shi a reran cikin nan kamar an ɗora ƙwarya mirginawa biyu ya yi sai ga shi a zaune amma ya rasa mai ya samu bayansa ya kasa tashi amma yana tunanin hakan ba ya rasa nasaba da buguwar da ya yi lokacin da ya faɗa kwalbatin.

Ganin tashin ba zai samu ba sai kawai ya shiga jan mazaunai yana nufar hanyar da za ta sada shi da gidansa da yake ranar ma a bakin Amina yake don haka can ya nufa yana tafiya hawaye suna masa sintiri kamar an kunna lalataccen famfo. Su Usai suna kallonsa yadda yake jan mazaunan ma cikin sassarfa ga wannan ciki nasa kaya guda shi kaɗai zai baka dariya saboda su ko tausayinsa ma basu ji ba tun da shi ma ba ya tausayin kowa.

Sai da suka daina hango shi sannan suka cire ƙahon a kwalbatin ma suka jefa suka cire dogayen rigunan suka saka a leda dama a kan wani kayan suka ɗora, kuma sun cire ne saboda tsaro ba don tsoro ba don sun san za su iya haɗuwa da wani a hanya ko dai su a gida a gano su don sun san tabbas gobe Alhaji zai iya bada labari kuma wanda ya gan su za a iya hango jirgin su kuma hukunci zai biyo baya.


*Alhaji Sabo*


Tun da ya kama hanyar nan ko waiwaye ba ya yi ba ma ya fatan abin da zai sa ya waiwayo ya ƙara arba da masu baƙaƙen kayan nan da har sula sallame shi bai gama gane wane rukunin jinsi bane, shin mala'iku ne ko kuma aljannu. Yadda yake gurzar mazaunansa a tantagayyar hanya ce ga ƙurunƙusan duwatsu, yana dab da shiga ƙofa ya ji magen nan da take maƙale shi kwata-kwata ma ya manta da ita don tun da ya ga masu baƙaƙen kaya wanda ya yi wa laƙabi da mutuwa kusa sai ya manta ma da wanzuwarta dama an ce gaba da gabanta aljani ya taka wuta!. A ƙufule ya kai hannu ya warto ta har lokacin tana riƙe da gemun a bakinta, wani irin matse cikinta ya yi aikuwa ta saki gemun tana sakin kuka ta ce miyau, sai da ya wujijjigata yadda ya san ya rama abin da ta masa ya yi wurgi da ita ta kuwa ruga da gudu, shi kuma ya ƙara ƙaimi wajen gudun jan mazaunansa, ya shige gida sai lokacin ya tuna takalminsa da rakensa mai zaƙi da ya baro a kwalbati.

"Ana ta kai wa yake ta kaya" Ya furta a wahalce yana kusa kai cikin gidan ko ta kan rufe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login