Showing 39001 words to 42000 words out of 52525 words

Chapter 14 - CIMA ZAUNE Complete by Maman Afrah.txt

30 Aug 2025

1752

akuyar kamar jira take ta kara kukanta shi dai da ya bi layin ma yanzu ana ta cewa ga mahaukaci nan ya dawo shi da. Wani layi ya bi yana ta surfa gudu duk inda ya bi sai ya ga mutane suna darewa kowa sai ya kama gabansa bai yi burki a ko ina ba sai a gidan su abokinsa da yake ɗakin abokin nasa a zaure yake don haka yana zuwa ya bankama cikin ɗakin. Abokinsa kuwa da tun gudowarsa gida ya taho yana ta hailala da salatin annabi S.A.W akan wannan al'ajabi da ya faru tun da da kunnuwansa ya ji maganar akuya kuma ya san a rina wai an saci zanin mahaukaciya.

Da yake dama tun da ya dawo a tsorace yake ko cikin gida bai shiga ba ya zauna a ɗakin yana rarraba idanu. Jin bankamowar da aka yi a guje ya tashi ya nufi banɗaki ya rufe don shi bai ma taɓa kawowar ba wai Sagiru ne abu ɗaya kawai ya sani shi ne a cikin tsoro, fargaba da kuma ruɗani. Yana shirin shigewa Sagiru ya yi taku ɗaya biyu sai kuwa ya kamo rigarsa ta baya. Jin an damki rigarsa ta baya sai ya fara kuka marar a
sauti kiii Sagiru ya juyo da shi suka fuskanci juna, a take ya fara karkarwa kamar masassara ganin Sagiru muraran goye da akuyae don yanzu babu zanin da aka goya shi ɗin ma ba ya jikin goyon kawai kankamar da aka yi wa jikin ne ta masa.


"Baabaa don Allah ka mini rai wallahi tsoron su nake ni yanzu har kai ɗin ma tsoro kake ba ni"


"Wallahi baka isa ba ai kai ka ce in sato mana akuyar mu ci kasuwarmu kuma yanzu za ka gujeni?"

Kuka kawai abokin nasa yake hawaye shaɓe-shaɓe shi a dole ma gani yake Sagirun ma duk caɓali ne a jikinsa da na akuyar hakan ya sa yake tsoronsa har hannu biyu ya haɗe yana rokonsa. Su duka kuka suke wiiwii babu mai lallashin wani ga akuya a gefe guda ita ma tana meeeee wanda kukan nata yake kara tsorata su.

"Ku wa mutane shiru" Suka ji ta faɗa. Ɗiffff suka yi tamkar ruwa ya ci su. Babar abokin ce ra taho saboda tana jiyo tashin kuka kuma ba na yara ba.

",Kai lafiyarku daga shan ruwan mutane za ki zo ku dame su?" Su ka ji muryarta tana kafe bayan Sagiru da idanu ganin akuya a bayansa. Haba Sagiru yana juyowa bai ma san lokacin da ya saki rigar abokin nashi ba ya juya ya je gabanta ya durkuwa yana kuka shaɓe-shaɓe da ta rasa ma dalilin kukan


"Kai bana son shashanci ni da na ce ku wa mutane shiru amma sai ka kara kaimi wajen kukan.

"Ki mini rai ki tofawa akuyar nan ko kulhuwallahu kafa uku ce ta sauka daga bayana" Sagiru ya ce cikin gunjin kuka


Masoya daga yanzu har december ana iya mini LIKE na gasa a youtube na littafina MALAMIN BOGI domin taimaka mini in ci wannan gasa ta marubuta

MAMAN AFRAH
09025576222
[8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
*IMZEED VENTURE*
Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna aiyar da gwanjo me kamar sabo!
Tuntuɓemu 07077532253
Wtsapp/IG/TiktocTikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-8yWWJj3GGri&_r=1


MUHIMMIYAR SANARWA* 👇👇👇

*Assalamu alaikum duk me karatun littafin CI MA ZAUNE ya tsaya ya karanta wannan saƙon ya fahimta. Littafin nan 500 ne za a gama free pages a page 18 sai dai akwai zaɓi biyu ga mai son karantawa har ƙarshe. Ko mutum ya biya ,500 ko kuma ya mini magana in bashi link ɗina ya mini LIKE na gasa idan ya yi zai sa mutane biyu su mini a tura min screen shrt ta PC sai in saka mutum a paid grp ya karanta idan kuma knsan kn yi mini dama to za ki sa mutane biyu su mini sai in saka ki a paid grp amma sai kin fara mini magana a PC na miki bayani. Wanda kuma 500 zai saka zai biya ta asusun faiza abubakar 9030283375 opay shaidar biya ta 09025576222* *Wanda za su yi like ma ta wannn no za su min magana*

CI-MA- ZAUNE


NA

MAMAN AFRAH

🅿️1️⃣5️⃣

"Akuyar waye?" Ta ce cike da masifa dama masifaffiya ce. Wani yawu ya haɗiye mukut jin furucinta ya san yana faɗa mata satowa aka yi satar ma a gida a gidan ma ta sirikarsa to babu shakka sai an ka ruwa rana.


"A gidansa ya ɗakko ta ta sirikarsa ce shi ne ya makale ta ki barin bayan nasa kuma wallahi har magana ta yi" Ya ji muryar abokin nasa ya jika masa aiki tun da ya feɗe biri har wutsiya.

"Ka ce dai sato ta aka yi ba wai ɗakkowa ba, to ba kulhuwallahu kafa uku ba ko tabbatyada ba zan karanta ba, dama ai duk wanda ya sayi rariya ya san za ta zubda ruwa" Ta ce tana juyawa za ta fita daga ɗakin Sagiru ya kamo kafarta yana kuka yana rokonta.

"Yawwa kin birgeni" Ta ji akuyar ta yi magana, kwuiiitt ta saki wata tusar marar kara ta tsoro a zuciyarta tana raya ashe da gaske suke da suka ce tana magana tabbas wannan ba akuya bace akwai lauje cikin naɗi tsoro ta ji ya kama ta don haka ta shiga kiciniyar kwace rikon kafarta da Sagiru ya mata.

"Ka sakar mini kafa tun da ku bakwa jin magana yanzu da auranka amma don zubarwa iyali kunya kake sata? Yanzu ga shi a garin dogon hannun naku kun ɗakko abin da ya fi karfinku ka ga kuwa ko kuka ya kama ba ni ba" Ta ce tana aika musu sakon harara.

"Ni don Allah ki cire mini ita na miki alkawarin na daina"

"Yo ka cigaba da yi ma mana tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa ya kan duka" Ta ce. Dakyar ta samu nasarar fincike kafar tata tana huci saboda ba karamib artabu suka sha ita da Sagiru ba kafin ya sakar mata kafar.

Kafa ya mike kawai yake sharɓar kukan takaici ganin babu tsumi babu dubara, akuya kuwa in ta gurguri jikinsa sai ta saka ta yi kuka. Hannu biyu ya ɗora a kan yana jinjina wannan masifa da ya kefa kansa a ciki.

Ganin hakan sai ya taso ya baro ɗakin abokin ya nufi cikin gidan, da kuka ya shiga tamkar wani karamin yaro har ya zo ya zauna a kasa kusa da mamar abokin nasa ya zauna hannu bibiyu ya haɗe yana rokonta a kan ta taimaka ta yi wa akuyar rukiyya tun da ba dabba bace ya samu ta ɓanɓaru daga jikinsa.

"Yau na ga abin da ya fi karfina in ji bazawarar da ta rasa miji, lokacin da kuka shirya abin ku ma san ma an y? Sai yanzu ne za taso da wasu siraran kafafuwanka ka ce na yi wa akuya rukiyya to ban iya ba" Ta ce tana masifa tana shan lemon fata da kankana.

Kuka ya zauna yana mata wiwi har ta gaji da magiyar ta sakala mayafinta ta ce ya tashi ta raka shi gidan malamin da take rukiyya.

"Na gode sosai Allah ya saka da alheri


'Ka bari dai ka ga yadda halin zai yi a toh don wannam badakalar ba ta wasa bace" A baya ya bita yana jin damuwarssa ta ragu. Suna zuwa ɗakin zauren ta kalla kamar yadda ta yi zato hka ce ta faru domin kuwa kwance yake ya libgawa kansa bargo baka jin karan komai sai salatin annabi. Ganin ya rufa har kansa sai ta lallaɓa ta shiga ɗakin ta haɗa hannu biyu da damke kafaɗarsa. A take komai ya kwance masa maganar da yake faman yi ta salatin annabi S.A.W ta kwace ya ma rasa ina zai sa kansa wata irin jijjiga jikinsa yake tsabar tsoro sai makyarkyata yake yana neman yadda zai yi ya buɗe fuskarsa sai dai yana tsoron mai zai gani don a nasa tunanin akuyar nan ce ta bayan abokinsa Sagiru ta zo ta makale masa shi ma musamman da ya san tare suka haɗa baki aka sato akuyar sai ya yi zaton tasa ukubar za a gana masa.


"Sama dai iccen maraya sama dai iccen kosai, ba don rashin uba ba, da ban shuka ka ba" Ya ci ya fisgo wata waka da ya san tun suna yara ana musu ita a cikin wata tatsuniya. Don yanzu shi a yadda yake a ruɗan nan ba ya jin ma bakinsa da kwakwalwarsa za su bambance masa tsakanin waka da karatu saboda bashi da nutsuwa ko miskala zarratin. Babar tasa kuwa jin abin da yake faɗa ya so bata dariya kai hatta Sagiru da yake cikin halin kakanikayi sai da dariya marar sauti ta kwace masa yake ganin yanzu an dafa sa ma yana shiriftu saboda tsoro to ina da shi akuyar ta makalewa kuma yana ji take magana watakila ya suma. Dama ta gaji da shaye-shyen nan da yake kullum tana masa faɗa amma ba ya ji ga shi daga shaye-shaye ya afka sata kuma daidai gwargwado tana masa nasiha amma kuma mu'amala da abokan banza ba ya sa mutum ya sauya halin don haka yanzu ta kudurta a ranta za ta tsoratar da shi watakila ya rage abin da yake ko da bai daina duka ba. Ganin ya zube yaraf ya kwanta wanda da a zaune yake sai ta kai hannunta ɗaya wajen kafaɗarsa ta kai ɗayan saitin kafafunsa ta fara kokarin kamar za ta masa ɗaukan jarirai. Jin ana kokarin ɗaga shi gabaɗaya sai ya ya saddakar tashi ta kare don sai ya fara tunanin kenan lamarin Sagiru da da dama -dama wai kibiya a ido tun da shi Sagirun basu ɗauke shi ba kawai akuya aka lika masa taki fita shi kuma ga shi zunzurutun tashin hankali ya mamaye shi tun da suna kokarin ɗaga shi kuma ya sam suna ɗaukan nasa daga na kuma sai inda hali ya yi watakila ma su tafi da shi duniyar su ta aljannu shi ma ya kwatse da su ya zama aljani.
Ai wannan tunanin sai ya sa jikinsa ya fara tsuma ya ji ba zai iya zama a duniyar da ba ta bil adama ba wato ta aljannu a take ya fara kokarin kwace kansa amma kash! Abin ya fassakara domin ita Babar tasa sai ta kara kaimi wajen kankame saitin wuyansa da kuma kafafunsa.
"Maza ya jibu alaika, mene ne ya wajaba a gareka, an ta'amalahu, ka aikata shi, kablal salati kafin ka yi sallah" Wannan karatun tun na islamiya da suke zuwa kafin su gagara su daina zuwa islamiyar ma baki ɗaya shi ne ya samu nasarar cafkowa daga bakinsa da yake kokarin gagararsa furta komai saboda karkarwar da yake har hakoransa suna gwaruwa da juna saboda yadda suke haɗuwa kamar wanda zazzafan zazzaɓi ya rufe a lokacin muku-mukun sanyi. Sagiru tsabar dariya har sai da ya zube a kasa don bai taɓa tunanin tsoron da abokin nasa yake da shi ba ya kai haka ba, shi tsabar diramar da yake gani ana tafkawa tsakanin uwa da ɗanta har ya manta da nasa tashin hankalin da yake ciki wanda yake goye da akuya tana makale tana gwagwiyar bayansa.

Kara ɗaga kafafun ta yi sama alamar dai ba za ta saurara daga abin da take ba. Da mugun karfi ya buɗe murya ya ce

"Jama'a ku kawo mini ɗauki, mutanen ɓoye sun kawo mini farmaki, don Allah ku zo za su tafi da ni duniyarsu, wayyo uwata wayyo ubana wayyo ni Allah na shiga uku yau na yi angamo" Ya ce yana sakin wani wahalallan marayan kuka da ya karaɗe ɗakin da yake ɗakin ma a zaure yake ihu da karaɗin da yake har kofar gida.
Gudun kar hankulan mutane masu wucewa ya iyo cikin gidan nasu don ya dage da iface-iface na neman taimakon jama'a su kawo masa ɗauki sai ta saki wuyan nasa ta kama uban jikin ta shiga jijjiga shi a take ya saddakar da cewa shi tashi ta kare don jijjigar da take masa sai ya yi zaton kashe shi ne aljannun suke son yi hakan ya sa ya saki iface-iface da kiran jama'a su kawo ɗauki yaje yaki da bakinsa a kan ya samu ya karanto kalmar shahada ko ya dace ya cika da imani.
"Innal mu'uminuna, wal mu'uminati, wal muslimuna, wal musilimati" Wannan kawai yake maimaitawa don ya kasa karanto kalmar shahadar.
"La'a'abidu mata'abiduun" Ya sake warto wata ayar a cikin kuliya ayyuhal kafirun yana kyautata zaton in har yana karanto duk abin da ya zo bakinsa matsawar dai ba ihu bane to da sannu zai samu karanto kalmar shahadar tun da sannu -sannu bata hana zuea sai dai a daɗe ba a zo ba.
"Wattini wazzaituun, walɗurisinin, wa hazal baladul amiin"
"Wayyo Allah na" Ya furta da karfi jin har yanzu kame-kamen ayoyi yake bai kai ga samo nasarar kalmar shahada ba gabaɗaya ruɗu ya hana shi ga shi kuma ya ji sai jijjiga shi ake yi shi kuma yanzu ya daina kiciniyar buɗe bargon daga fuskarsa don ba ya ma kaunar ya yi angamo da fuskar aljani. Wata iriyar jijjiga ta masa da karfi a take ya ji ya yi nasarar warto kalmar shahada da karfi kamar wanda aka fisgo maganar ya ce
"Ashshadu an la'ilaha ilallahu, wa ashshahadu anna muhammadur rasulullahi.... Ya dakata yana sakun wani marayan kuka mai kamar jiniyar sarki ta wuce

"La'ilaha ilallahu muhammadur rasulullahi S.A.W" Ya faɗa wannan karon har da sakin tusa da fitsari na wahala da tsananin tsoro. Da karfi ta fisgi bargon ta yace masa shi duka ya haɗa uban gumi idanunsa a rufe. Shi kuma jin an buɗe shi sai ya kara rufe idanunsa gagam don a nashi zaton ya ɗauka so suke sai sun gama tsorata shi da kamannin su kafin su kashe shi, shi kuma ya san yana ganin halittar su to tabbas zai karasa mutuwa kafin su kashe shi saboda ya san dai ganin siffar aljani dai babu sauki wai ciwon arne Ganin bai buɗe idon ba sai ta ɗaga hannu ta falla masa mari da zafin marin ya sa ya buɗe idanun a gigice ba tare da ya san ya buɗe ba ganin ta tsaye ya sa ya wani taso tsaye da shakarkaɓin wandonsa ya rirrike ta yana fashewa da kuka ya ce

"Wayyo Baba she dai za ki zo ki cece ni dama an ce mutuwa tana tsoron idon mahaifi ashe dai aljannu ma suna tsoron idon mahai...

"Ɗan kwal uba wuce ku kama hanya mu tafi gidan malam Kailu ai thn da baku da hankali baku san annabi ya faku ba to kuwa dama ai kun ringa ganin abin da ya fi wannan ma ai duk wanda ya ja ruwa shi ruwa ya kan duka" Ta cw cikin hargowa tare da ture shi daga jikinta don bata so ma ya gane ita ce ta masa duk abubuwan da ya ji ta fi so a tafi a hakan har su je gidan malamin yana ruɗe hakan zai sa watakila in za Allah ya nufe shi ya yi taubatun nasuha wato tuba na ha abada ya daina sata da shaye-shayen.

Sagiru da sai yanzu da Babar abokin nasa ta fara faɗa ya dawo daga duniyar dariyar ketar da yake ta faman sha, hakan ya sa ya mike tsaye yana tsayawa dakyau don gabaɗaya dariyar ma ta ki sakin sa sai yanzu yake kara tabbatar da yanayin tsoro mai haɗe da tsurewa ba karamin abin dariya bane idan ana gani ga shi, har ya sa ya manta da nasa tashin hankalin.

"To, to, to, to, to" Yake ta faman maimaitawa don shi yanzu gabaɗaya ma a ruɗen yake ba wai ya gama dawowa daidai bane, sai wani kallon ɗakin nasa yake yana jin wai wannan ɗakin ne aljannu suka shigo har suka yi ta jijjiga jikinsa, da wannan tunanin ya fito daga ɗakin Babar tasa tana biyo bayansa bai damu ma da wandonsa da yake jike sharkaf ba don shi yanzu a halin da ya shiga ya samu damar kuɓutowa gani yake ko tsirara aka ce ya fita zai fita saboda yadda ya tsallake rijiya da baya.

Yana fitowa kallo ɗaya ya yi wa Sagiru ya ɗauke kai tare da yin gaba ba tare da ya masa magana ba, na farko haushinsa yake ji saboda yana ganin duk wannan halin da ya shiga da sa hannun Sagirun tun da shi ya ɗakko akuya mai aljannu na biyu kuma yanzu da ya fito ya masa kallo ɗaya ya lura akwai alamar dariya shimfiɗe a fuskarsa, wannan ya tabbatar masa da cewa shi yake yi wa dariyar keta, ga shi ma shi yanzu daɗin daɗawa mugun tsoron Sagirun yake ji yanzu saboda akuyar da take makale a bayansa don har ita bai ɗaukewa zargin da ita aka jijjiga shi ba.

Abokin Sagirun ne a gaba sai Sagirun sai kuma Babar ita ce a karshe tana fitowa ta banko gidan.

"Ka yi ta kan ka, don daga gidan Malam Kailu babu inda zan kara raka ka matukar ba a dace a haka ba don daga can ma sai dai ka wuce gidanka ku je can a dage da fatiha da salatin annabi da rokon Allah har zuwa ranar da Allah zai sa ta yarda ta ɓamɓaru daga jikin ka, tun da kai har kana da bakin dariya baka duba bala'in da kake ciki a ce akuya da ranta makale da jikin ka har tana magana amma har kake da bakin dariya bayan ga bayanka nan duk ta kwarzane ta gwigwiyar da take amma ko don bahaushe ya ce bakin dariya shi ne na kuka" Ta ce tana wuce shi ta wuce ɗan nata ya zamana ita a gaba sai ɗan nata sai kuma Sagirun da jikinsa ya yj sanyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login