Showing 12001 words to 15000 words out of 52525 words
nemo masa auren Amina da kuɗin da zai yi kowace hidima saboda iyayansa sun mutu a wani kauye yake a hannun kawunsa wanda gagararsa ta sanya kawun ya kai shi Gumel makarantar allo a can ɗin ma ya gagari malamin maganar da ake yi yanzu ya bar makarantar ma gabaɗaya tun da daɗewa.
Sagiru tsawon sati guda yana aikin wahalar wanki sai da ya tara kuɗi yadda yake so sannan ya je ya ɗauki hayar mutane maza uku mata biyu wanda suka je cikin shigar alfarmar kayan sa shi ma arowa aka yi, su kan mazan hayarsu aka yi don aikin su kenan su je nemowa mutane aure a biya su. Sun je maganar auren inda Malam ya amince ba don komai ba don Dada ko bincike ta hana a yi tana ganin idan aka yi bincike tamkar za a binciko abin da zai hana auren wanda bata fatan hakan shi ya sa ta yadda da maganar kazantar da ba a gani ba tsafta ce. Daga Malam ya yi maganar bincike sai ta ce ai a gidan da Ɗan Ibra yake aiki yake kuma aure taya shi ake yi. An yanke maganar aure sati guda saboda kayan lefe suka taho set guda na akwati ga kaya tsala-tsalan leshina da atamfofi tsabar murna Dada sai da ta zuba ruwa a kasa ta sha saboda kayan lefen da ta gani na gani na faɗa.
Sai ana saura kwana uku ɗaurin aure sannan Sagiru da Ɗan Ibra wannan karon har da wani abokin su suka je, Amina duk da ba wani karewa Sagiru kallo take yi ba amma a ranar ta ga ya sauya sosai ya yi baki ya rame ko Dada ta lura da hakan amma a ranta sai ta raya ko rashin lafiya ya yi basu san cewa tsabar wanki da gugar tara kuɗin hayar kayayyakin da za a fita kunyarsu bane.
Ranar ɗaurin aure motoci biyu su Sagiru sula ciko da mazan da suka je neman auren sauran kuwa wasu abokan su ne aka ɗaura aure, aka yi hidima amm sai ango ya ce sai washe gari za a ɗauki amarya har ma Ɗan Ibra yana jaddadawa Dada cewa ba wani gayya za a yi ba kuma ana zuwa za a dawo da wanda suka je kai amarya. Dada dai duk da bata san dalili ba amma ta yi mamakin wannan magana sai dai saboda gudun ƴan tsurku sai ta ja bakinta ta tsukw don ya ce musu ma iyayensa suna kasar waje amma wani satin za su dawo wanda suka zo nema masa auren kannen babansa ne.
Washe gari gida ya kacame da murna ana ta shirye-shiryen tafiya kai amarya, don mutanen da suka taru sun fi karfin mota biyar ma kowa yana son zuwa birni kai amarya Hassu da Usai an caɓa gayu Dada kuwa ji take ba don ita uwar amarya bace da babu abin da zai hana ta tafiya.
Mero da Ladiyo Usai Hassu sai wasu mata guda uku su kaɗai ne za su je kai amaryar, su Ladiyo ma Dada ta zaɓe su ne don su je su ga abin da zai hana su baccin saboda bakinciki. La'asar sakaliya suka iso da motocin guda biyu wanda babu ango sai abokin ango Ɗan Ibra da wani wanda yake tuka wata motar haka aka yi tururuwa a kofar gidan har aka shishshiga motar da amarya da take sanye da jar atamfa an lulluɓe ta da mayafi.
Abin da ya so ba ruɗawa Dada ciki shi ne yadda Ɗan Ibra ya jata gefe yake mata batun tafiya da kayan lefen da babu abin da suka taɓa a ciki sai su Hassu da suka ɗauki kayan kwalliya, amma abin da ya sa ta ji ɗan daɗi jin wai angon ne ya ce a tahowa amarya da kayan saboda a gobe zai kwashe ya kai a ɗinko mata domin take shiga ta alfarma kar danginsa su rainata kuma zai kai ta ta sake zaɓo wasu. Wannan maganat ce ta sanya Dada jin salama tana ganin idan har za a ke kai Amina tana zaɓo kaya a shgo to kuwa ta san ita ma akwai nata rabon. Don haka bata ɗauki komai ba ta basu suka loda a boot ɗin mota suka tafi mutane suna ɗaga musu hannu suna ganin Aminar ta yi babbar sa'ar auren ɗan masu kuɗin wasu , zawarawan ma da ƴanmata suna jin ina ma su ne.
A kofar wani tangameman gida motocin suka tsaya, Ladiyo da Mero tsabar bakin ciki kamar su haɗiyi zuciya su mutu. Don Ladiyo da yake bakinta a buɗe yake babu abin da yake kwaranyowa daba bakin sai yawu saboda haɗuwar gidan sai da wata da take kusa da ita ta ankarar da ita zubar yawun sannan ta ga har gaban hijabin nata ya jike cike da wayincewa ta shiga rufe bakin tana lulluɓe wajen da yawun ya jika. Get ɗin aka buɗe a nan ne kallo ya koma cikin gidan ƴan cikin mota sai kus-kus ake yi ganin gidan kamar gidan sarki ko wani gwabna, dama basu ɗakko kayan jere ba saboda an ce ba sai ta je da komai ba. Unguwar ma da alama ta manyan mutane ce shiru babu hayaniya ana gama shiga cikin gidan kowa allah-allah yake ya fito ya kashe kwarkwatar idanunsa. Mero tana tafiya bata ma san ta samu wuri ta tsaya ba tana kallon haɗuwar gidan ga wasu shukokin fuɗawa duk sai ta kasa cigaba da tafiya tana jin ina ma ƴarta ce ta samu wannan ɗanɗasheshen gida. Ladiyo tintiɓen da ta yi ne da wani dutsi ya ankarar da ita katoɓarar da ta yi na raja'a a kan kallon benen da take yi.
."Mero wallahi har da gidan sama" Ladiyo ta ce tana nunawa Mero.
.."Gidan sama ko gidan bene ai wallahi mun kaɗe har ganyenmu don kaju da gori dai a wajen Saude sai dai mu tashe kummuwanmu"Ta ce tana taɓe baki. Gyaɗa kai kawai Meron ta yi don ta ma kasa magana.
Ɗan Ibra kuwa katafaren falon Hajiya mai ɗakinsa gidan da yake direbanci nan ya nuna musu a matsayin falon amarya suka shiga cike da murna. Basu san cewa Ɗan Ibra ne ya yi dibarar buɗe ɗakin ta karfin tsiya tun da yana ganin basa kasar kuma sun rasa gida mai kyau inda za su yi karyar da shi.
Har bedroom suka shiga da ita aka zaunarta a bakin gado, kowa cewa yake aljannar duniya.
Wasu ko zama basu yi ba aka fara cewa su fito a mayar da su lokacin ana kiran sallar magriba amma aka hana su yin sallah wai masu motar sauri suke nan kuwa Ɗan Ibra da gangan ya ce haka saboda yana tsoro mutanen unguwar wani ya ankara da abin da ake yi ya faɗawa iyayen gidan nasa, dama saboda ban ruwan shukoki da kuma zubawa kifayen da ake kiwo a gidan abinci aka bashi mukullin gidan dama kuma akwai mai gadi.
Sun tafi sai amarya kaɗai a bakin gado ta buɗe mayafin tana karewa ɗakin kallo sai sannan ta gane ashe dai haɗuwar gidan ta kai haɗuwa shi ya sa ta ji Hassu da Usai suna ta cewa yau har sai sun rasa mai za su cewa Dada saboda bada labarin tsaruwa da haɗuwar gidan ɓata baki ne sai Dada ta zo da kanta domin gani ya kori ji.
'Oh ni Aminono wannan wane irin miji na aura mai bala'in kuɗi haka, wannan ai sai a ɗauka yankan kai yake' Ta ce a zuciyarta tana mamakin hatta gadon ma abin kallo ne. Kasancewarta mai yawan ibada bata wasa da sallah bata bari lokacin sallah ya wuce da gangan, hakan ya sa ta tashi don yin alwalar sallar magriba, duk da tana tsoron yin kauyanci, ganin kofar da Hassu ta buɗe wanda ta ji suna ta kyalkyala dariya ita da Usai wai banɗakin ƴan gayu har da famfo a ciki. Wannan ya sa ta ɗan tura bayin tana kare masa kallo ga fitilun wutar lantarki ko ina haske ral kamar safiya. Alwalar ta yi da ruwan famfom ta fito tana waiwayen inda za ta ga sallaya ganin jakar kayanta a ajiye tare da akwatinan lefen ta je ta zige jakar za ta duba ko Dada ta saka mata sallaya don ko haɗa kayan ma Dadar ce ta yi wai na za ta kwashi tsummokara ba kafin ta fara dubawa ta hangi sallaya guda biyu a gefen karamar loka kusa da gado jakar ta zige ta je ta ɗakko sallayar sai kamshi yake fita daga jikin sallayar, bayan ta shimfiɗa ta gabatar da sallar magriba ta sake tashi ta kabbara nafila tana cikin sallah ta ga shigowar mutum kamar ma babu nutsuwa a tare da shi, kiii ya fara jidar akwaitinan yana fita da su, lokacin da ya dawo ya ɗauko sauran ta idar da sallar nan ta ga Sagiru ne bai ko kalleta ba ya ɗauka ya fita abin da ya fi bata mamaki ma yadda yake a firgice kuma sanye da wasu kaya ba irin wanda ya saba zuwa garinsu da su a jikinsa ba wato wannan kayan yadi me mai saukin kuɗi kamar ma ya ji jiki. Mamaki kwalli a kunne tana cikin wannan tunanin ya dawo, bata san cewa tun kayan ɗaurin auren da ya aro ganin kuɗaɗen hannunsa sun kare shi ya sa bai kara aro wasu kaya ba. Ga shi kwana biyu ma ba a kawo wanki da guga ba bare har ya samu na sakawa aro.
"Ki taso mu tafi" Shi ne abin da ya ce yana rike da jakar kayanta da mamaki take kallonsa tana ta wasi-wasi a zuciyarta a kan ko dai dama ba gidan da za a kawota bane suka yi ɓatan hanya amma da ta tuna har da Ɗan Ibra aka je ɗakkota sai abin ya kara ɗaure mata kai tun da dai ta san duk tsiya Ɗan Ibra ba zai kasa sanin gidan ba.
Bata ce masa komai ba ganin ko fuska bai bata ba, hakan ta bi bayansa suka fito sai lokacin ta kuma ganin gidan ashe ba karamin girma gare shi ba.
"Ka ga ango da amaryarsa" Mai gadin ya ce cikin zolaya.
"Bari ina zuwa ka ce wa Ɗan Ibra idan sun dawo mun tafi zan dawo amma"
"To ango kamar ka faɗa a kunnensa" Cewar mai gadin yana dariya.
"Amarsu ta ango" Furucin mai gadin ya dawo da ni daga tunanim inda za mu je wanda na ji yana cewa ma wai zai dawo wato ni ba da ni za a dawo bama a can za a barni ko mai yake nufi oho.
"Ina wuni" Na iya furtawa cikin sanyin jiki.
"Lafiya amarya ta ango an iso lafiya ko" Ya furta yana ƴar dariya ni kam ban samu zarafin bashi amsa ba, gabaɗaya alhinin fitarmu da kuma inda za mu je ya tsaye mini a rai kafin in gama tantancewa sai jin hannun Sagiru na yi a cikin nawa ba shiri ya shiga jana kiiii muka fita fitowarmu daga get ɗin ya yi daidai da wata adaidaita sahu da na hanga za ta sha kwanwa wanda hasken kwayayan da suka haske unguwar tarrr ya mini nuni da akwatinan aurena wanda Sagiru ya fito da su. Na zama kamar wani mutuntume na kasa gane mamaki zan yi ko al'ajabi ko kuwa wasi-wasi a kan wannan ɗanyan lamari marar alkibla.
"Hau mu tafi" Na tsinkayi muryrsa ina ɗagowa na sauke idanuna a kan wani tsohom machine, baki sake nake kallon machine ɗin amma sai na yi kokarin kawar da mamakin da nake na ɗaga kafa na hau bayansa domin ya saka jakar kayan a gaba haka ya tada machine ɗin da yake wani kara
"Ko dai gida zai mayar da ni ya fasa aure? Ko kuwa karayar arziki?" Na shiga jefawa kaina tambayoyi da bani da mai bani amsar su. Yadda ya tada machine ɗin duk sai da hayaki ya buɗaɗe su.
Hanyar da mai napep ya bi da ban shi gabas ya yi mu kuwa yamma muka bi, tun da muka fara tafiya bai tanka ba ni ma hakan.
A daidai wani gidan kasa ya tsaya zato na sako zai karɓa sai na ji ya ce na sakko babu musu na sauka. Ganin ya faka machine ɗin ya ɗauki jakar ya ce in taho bayansa na bi ina ganin yadda ginin gaban gidan ya rufto kamar ma ya kusa zubowa. Ni dai ban ce komai ba ko gidan mu da yake kauye bai yi wannan tsufan ba. Muna shiga gidan na ga ɗakuna reras, da yake gidan yana da girma kuma da yake yanayin sanyi ne kowa yana ɗaki sai dai ina jiyo tashin maganganu, ɗakin da yake karshe da suke ɓangaren farko guda uku ya shiga na karshe ni ma shigar na yi don zatona zai yi sallama da neman iso amma abin ya ci tura saboda ɗakin kawai ya shiga kamar ma dai ya samu kufai. Ciki da falo ne na kasa falon ko arzikin tabarma babu duk ɗakin ya ɓurɓurje.
"Wannan shi ne inda na kama mana haya a nan za mu zauna can inda aka kai ki gidan uban gidan Ɗan Ibra ne bari zan je na dawo" Ya ce lokacin da yake shimfiɗa mini wani tsohon buhu kato. Laɓɓana ma na kasa haɗawa bare na samu kwarfin gwiwar bashi amsa ba komai ne ya cika kwanyata ba sai hango yadda Dada za ta yi a lokacin da ta samu wannan labari.
MAMAN AFRAH
09025576222
[8/24, 4:02 PM] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
*IMZEED VENTURE*
Kayan kicin da na yara, muna yin adashe sannan muna aiyar da gwanjo me kamar sabo!
Tuntuɓemu 07077532253
Wtsapp/IG/TiktocTikTok https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-8yWWJj3GGri&_r=1
MASOYANA INA MUKU FATAN ALKAIRI DON ALLAH KU SHIGA WANANN LINK ƊIN KU MINI LIKE (👍) WANDA YA MIN ALLAH KA BIYA MASA BUƘATARSA KA YAYE MASA DAMUWARSA👏
👇👇👇👇👇👇
https://youtu.be/xYBCkQuUxnQ?si=-0h_Dapw86VBXeE1
: CI -MA-ZAUNE
NA
MAMAN AFRAH.
🅿️6️⃣
*DADA SAUDE*
Tun daga lokacin da su Hassu suka zo suka bawa Dada labarin kyau da tsaruwar gidan da aka kai Amina gabaɗaya ta ji kanta ya mata girma ta ji a yadda take ji tana iya fito na fito ko da da shugaban kasa ne, saboda kuɗin da sirikinta yake da shi musamman yadda ƴan rura wuta wato wasu daga cikin wanda aka kai amaryar da su suke kara kambaba hauhawar girman kan nata.
"Allah kai damo da harawa ɗiyan nan dama rabo ne ya kashe auren Amina da Sabo gashi yarinya ta yi goshi a bazawara ma ta samu miji a birni son kowa kin wanda bai samu ba a birnin ma ɗan masu hannu da shuni ai ni wallahi Amina ta yi goshi yarinyar nan farin jini gare ta"
"Ai Dada da a ce kin ga yadda Ladiyo da Mero suka saki baki suna kallon gida aljannar duniya da abin sai ya baki dariya" Usai ta ce tana dariya.
"Ni yadda suke kallon ɗakin da gadon ne ma ya bani dariyar, Mero cewa take Ladiyo kina ganin abin da nake gani kayayyaki kamar a kasashen turawa" Hassu ta ce tana kyalkyalar dariya su duka dariyar suke yi kafin daga bisani Dada ta ce
"Ai mu yanzu gidanmu ya zama biyu birni da kauye, idan aka shafi kwanaki sai ku je can ku huta ɗan abin kasafin da kuka samo sai ta harhaɗo muku ku kawo mini "
"Wallahi Dada ai kakarmu ta yanke saka" Suka haɗa baki wajen faɗa.
Tun daga wannan rana Dada ta kasa zaune ta kasa tsaye don bata da burin da ya wuce ta je ta ganewa idanunta gidan Amina gori habaice-habaice shi take yi wa su Ladiyo su kuwa ganin irin daular da ƴarta take ciki su suka ja bakinsu suka yi shiru domin sun san faɗan da ya fi karfinka wasa kake mayar da shi tun da dai sun san irin ɗimbin daular da ƴartata take ciki. Wat ranar asabar ta kasa hakuri domin bata da burin da ya wuce ta je ta kwana biyu a gidan Amina tun da dai Allah ya horewa mijinta tana so taje ta ɗan kwana biyu a gidan Aminar ko ta ɗan lasa zumar arzikin da suke ciki a bakinta. Saboda ɗorawa rai ma watarana sai ta yi ta jin lamin duk abin da ta ci saboda ta ɗorawa kanta son cin abu mai daɗi idan ta je birni. Shagon mai caji ta nufa wanda a wayarsa Sagiru yake kiran Amina kafin a yi auren suna waya.
"Dada Saude ko dai caji kika kawo" Ya tambaya cike da zolaya.
"Yaro man kaza ko don an ce ta yaro kyau take bata karko, ka jira kwanaki kalilan zan yi waya ƴar dangwale ma kuwa(Torch secreen) Yanzu ma dai zuwa na yi ka kira mini mijin Aminar in ji lafiyarta ka san idan aka ce ɗanka yana gidan daula"
"Allah dai ya ja da kwananki Dada yo kaf kauyan nan akwai wanda zai ce bai san cewa Amina gidan daula ta yi aure ba ai tuni zance ya gama karaɗe ko ina labarin da ake kenan"
"Yawwa ko da na ji" Ta ce ranta fari kal jin wai kaf gari an san Amina a gidan mai kuɗi ta yi aure. Wajen sau uku yana kiran wayar tana shiga amma ba a ɗauka.
.
"Wayar tana ta shiga ba a ɗauka ba"
"Ka san gidan ƴan gayu yanzu haka bacci suke yi mu da muke kauye ai mu ne aka bari da tashin sassafe kuma talaka ai ko don fita neman abin sanyawa a bakin salati ya fito da safe wanda yake da kuɗi kuwa ai ya huta sai ya sha baccinsa ya tashi lokacin da ya ga dama" Ta ce