Showing 21001 words to 24000 words out of 116597 words
Chapter 8 - MUWADDAT Complete Document book by Aisha Bagudu .txt
masa hari..
itama bangaren muwaddat haka take fama da muguwar sha'awar idan abun ya tasar mata haka zatayi ta nukurkusun ciwon mara.
lokacin data kammala secondry school dinta alokacin aure taso ayi mata ,amman iyayenta suka sai mata form din jamb ,tayi kuka tayi bakiciki wannan karatu dan haka data je rubuta jarabawarta taki rubuta abun kirki , aiko lokacin da result ya fito iyakacinta poly , ummi tayi bakinciki mara misaltuwa tayita mata fad'a kmr zata bugeta ..
a koda yaushe suna waya da muhammed auwal har ma da chartting tun bata sakewa dashi har tazo idan ma bai kirata ba ita zata kirasa wata irin shakuwa ce atsakaninsu ta dawo mai ban mamaki kowanensu ya girma da burin son mallakar ,mai yanayi da tsari irin na danuwansa.....
yadda muhammed auwal ke mugun son muwaddat haka faiza kanwarta da suke uwa daya uba daya take mutuwar son shi sai dai shi ko kallo bata, ishe shi ba, duka guda nawa take ?
" alokacin duk shekarunta basu haura shabiyu ba shi dayake dil da manya mata mai zaiyi da kamar yarinya kamar faiza?
" mai zata yi masa yaji dadi dan haka ko sau daya bai ta'ba tunanin zai saurareta ba ...
duk karshen shekarar duniya bunayya zai kawo musu ziyara, duk kuma saboda muwaddat yake zuwa amman har wannan lokacin bai fito ya bayyana mata komai ba za dai suyi wasa da dariya har ma da kokuwa idan takama ,wanda a haka yake samu ya karewa halitar jikinta kallo son ranshi... ..
mmn sudais
2/4/20, 8:39 PM - imusamuhd(professor): ππππππ
MUWADDAT
ππππ
ππππππ
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
_AUNTY SALAMATU AYYUBA_
_(UMMIN KADUNA )_
~BEST AUNTY FOREVE AND EVER~
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
page 10
....Cikin dry abi yace "o ,kishi kumallon mata yanzu har cikinki ya duri ruwa ,shi yasa ma yar fara'ar da kika shigo daita ta d'auke ,kin wani tamke fuska daga jin zance kishiya "
"cikin dariya ummi tace "Allah sarki su kishi manya ,dadin abun ban ta 'bata fad'a akan zance kishiya ba ,kuma ni ko kishiyar za'a min me zai tada min hankali ?
"tazo ga gurin zama nan ni wallahi har na gaji da zancenta kullun, ayita kawai mu huta..
"Ai kuwa Ki sha kuruminki wannan karon zan bugi kirji na k'aro aure sa'ar baby suyi zamansu lfy ko baby ?
sai lokacin muwaddah ta saka baki "Dan Allah abi ka daina zance kishiya nan kar ka fad'awar da ummina gaba ,kasan dai yanzu ba kowace ke da imani ba, kowace k'ok'ari take idan tashigo tayi iko ,mu kuwa babu matar da zata shigo gidanmu tayi mana iko aciki..
"Abi yace shikenan tun da kin bi bayan uwarki wato ke ma ba kya son na k'ara aure kin fi son uwarki ta zauna babu kishiya ko ?
"Uhmm abi ba haka bane ,gani nayi da kunya yanzu ace zaka k'ara aure.."kin ci gidanku ke da kunyar ,ba sai na bari sai na aurar dake da bunayya ba ,sannan sai na auro sabuwar amaryata mai kalar 'yan birni ,in zaki zo sai kice wa mijinki zanje gidanmu ana bikin babana ..
Suka fashe da dry gabadayansu muwaddah tace "Dan Allah abi karkace zaka yi aure ,wallahi in ka auro budurwa gori za'a dinga yi mana nida bunayya ,ace babanmu ya auro k'aramar yarinya..
"To ai ni din ma bawani tsufa nayi ba, Dana aske yar furfurar nan zakiga 'yammata na rububina, suka sake kyalkyalewa da dry muwaddat na dry tace ,"kai abi wata yarinya ce a yanxu zata yarda ta auri tsoho in ba mara wayo ba ,ta k'arasa mgnr tana sake bushewa da dry .
ummi tace" in kai yarka ta hanaka auren yara ,kai tsofafi sazo neman aure gurinka ,abi yace "kmr ya ya ?
"Oh baka da labarin abokinka alhj jabril yana son muwaddat "
abi yayi 'yar dariya ana wata ga wata kenan ga auwal ga abokinsa ,Amman zahiri cewa yayi "shikenan nazama Surukin tsoho a she har gaytumai ke kawowa diyata Hari...
Muwaddat ta turo baki cike da shagwaba kmr zatayi kuka "Dan Allah abi ka bari ,kuma karkacewa ummi komai ,ni dai wallahi babu ruwana me zanci da wannan tsohon "
"me yasame shi shikenan sai muyi musaya Dan nima na gano iri a gidansa, kun ga kuwa ta kwana gidan sauki saboda shi bai da yawon surutu daman kince kin fi son auren nmj mai shiru shiru , yana zuwa zan sheida masa na bashi ..
Muwaddat ta shagwa'be fuska ummi tace "zancen wasa ya wuce bazan laminci ka rikita min 'ya ba shima abokin naka tuni nayi masa Burki na zuwan da yayi kwanakin ban mishi ta dadi ba ,tunda na gane yana son baby nace "masa kar ma ya fara domin yasan bazan iya basa bby ba, Dan ba baby ba ko wace ta girme mata gareni yayi mata tsufa ballanatana ita yarinya.
ina gaya masa sai ya kama driya har da cewa haba ummi ya zaki min hk km, ke din da nake sa rai zaki goyi bayan abun, nace "yaje can ya nemi umminsa ni bazan zama surukar tsofafi ba ..
Abi ya fashe da dry Amman dai gsky kinji kunya tun da kika tsaya kina sai'nsa da suruki "ai abokinka shi yayi babbar abun kunya banda budurwa zuciya ina shi ina muwaddat ?" har da zai bud'e baki yace yana sonta ko an gaya masa neman kai muke yi daita ..
"Yarinyata idan ta kammala karatunta sai ta zaba ta durje tukunna yara matasa masu sabon jini bashi ba ,ko kai ina tunanin ya girmeka kullun yana cikin kankare fuska Dan kar tsufansa ya bayyana ,abinda bai sani ba gyara fuska daban tsufa da ban ..
Abi yayi dry "to ai diyar taki ce ta cika farin jini dayawa yanzu ma wani case din muka gama ana da bunayya wai..... muwaddat tayi saurin cewa "Dan Allah abi kar kace komai "ki barshi yace ,duk masu sonki sa gama shiermensu diyata ta mai rabo ce ....
Aransa yace Allah yasa rabon Auwal ce Dan haka kawai yaji al'amarin ya kwanta masa, bai sani ba ko dan yadda auwal din yake acikin zuciyarsa ne, shi kansa zai so yayi auren wuri domin yaga 'yan jikokinsa tunda shi kad'ai Allah ya nufesa da samun , ,Amman karatunsa na bukatar natsuwa da ajiye hankali guri daya, yanzu yana yin aure hankalinsa dole ya rabu gida biyu duk ma ba haka guda nawa bunayya yake ....?
Hira ta kwance atsakaninsu wani lokacin muwaddat tabi bayan ummi ,wani sain tabi bayan abi , sosai sukayi hirarsu data zame musu jiki a duk sanda suka had'e, rayuwarsu abun sha'awa, duk wannan hirar da'ake hankalin muwaddat ya rabu gida biyu ,wani bangare na zuciyarta na gurin M. A daya bar parlour'n cikin fushi ,wani kuma na gurin hirarsu abi , Dan Sam batason abi yayi su'butar Baki ya gayawa ummi abinda ake ciki , tunda tasan itama ba wani amincewa zatayi da abun ba .
Cikin haka abi ya Mike yace zaije ya kwanta ya d'an huta ,yaso kwarai ummi ta biyosa ko d'an tausa tayi masa Amman yaga ta sharesa tacigaba da kallon tashar zeeyword dan haka ya kama gabansa yana tsokanarta.
byn tafiyarsa ummi ta dubi muwaddat "bby bunayya ko ya karya?ta fad'i hk saboda ganin har lokacin abun Karinsa na ajiye akan k'aramar kujera .
Muryarta a sanyaye tace "Bai karya ba "what har wannan lokacin?
"Ga abincin nan yace bazai ce "
ummi tace akan wani dalili kenan da bazai ci ba ?ni fa banason zama da yunwa ya dawo kenan za'a yi ta fama dashi akan abinci ..
"Nima dai bansan dalili ba ya dai ce bai ci , ummi tayi shiru kawai Amman gabadaya hankalinta ya karkata garesa,ganin zaman bazai fisheta ba ta yunkura ta Mike tsaye "bari naje na dubo shi ...
Koda ummi ta isa bangarensa ta iske shi tare da abokinsa nabeel Suna hira ummi cikin fara'a tace "a'a nabeel yaushe kazo gidan ?
Nabeel ya sunkuyar da kai yana shafa keyarsa alamun jin kunya "wallahi banjima da zuwa ba mun sameku lafiya ?
"Lafiya lau yaya gurin mamanka da kanenka fatan duk suna lafiya ,nima InshaAllahu zanyi k'ok'arin nashigo unguwar taku mu sada zumunci tunda kai kaki kawosu "nabeel yayi murmushi " kiyi hakuri ummi InshaAllahu kafin ma kizo zan kawosu "shikenan Allah ya taimaka yayi albarka "ameen ummi "
"Bunayya ummi ta kirasa ya d'ago ahankali yana shagwa'be mata fuska "me za'a dafo maka naji ance ko breakfast bakayi ba ?
"Yatsina fuska yayi yana D'an tunani abinda zai ce kafin daga baya yace anything ..cowslow ummi "to shikenan Amman ka dinga cin abinci mai Dan nauyi ,ni sai naga kmr ma bakajin dadi ,ko wani guri na maka ciwo ne ?
"Fuskarsa ya shafa da hannuwansa duka kana ya bud'e baki da kyar yace "Gani nan dai ummi ni kaina na rasa abinda ke damuna ta k'araso har inda yake zaune ta kai hannunta ta ta'ba gefen wuyansa "jikinka yayi zafi bunayya bari zan bawa baby magani ta kawo maka yanzu "yauwa ummi kice mata tazo min da coffee , ta juyo ta koma bangarenta sai lokacin tasamu natsuwar zuciya ta bawa masu aikinta umarnin su shirya masa lafiyayen abinci da cow slow, sannan ta aika muwaddat da magani.
bakinta d'auke da sallama tashigo d'akin ta nufi Kan karamin table din dake gabansa ta'ajiye tiren hannunta dake d'auke da flask da cups guda biyu ko kallon inda suke batayi ba shi kuwa tunda tashigo d'akin ya kafeta da tsumammun idanunsa yana kallonta har ta bar d'akin sannan ya maida hankalinsa kan nabel .
Nabeel ya numfasa sannan yace "ina fatan dai zuwa yanzu kasamu narasar shawo hankalin yarinyarka tare da bayyana mata sirrin dake ranka ?
M.A ya girgiza kai al'amun a'a Dan bayason nabeel din ya gane bai samu kar'buwa agurin muwaddat ."kana nufin baka fad'a ba ?
Ya sake d'aga masa kai "kai ko dai kana jin tsoron tinkararta ne hade da jin tsoron karka tace bata sonka ?
Murmushin gefen baki M.A yayi irin nasu na wayyayu "haba nabeel yakamata zuwa yanzu kasan halina kasan who's Muhammed Auwal? "Ka ta'ba ganin na furtawa wata mace kalmar so balle har tace bata sona ?
Yadda ban ta'ba furta hkn ga kowace mace ba haka nasan bazan kasa yin nasara da zuciyar muwaddat ba,zuciyar da nasa tana cikin shaukin kaunata, kawai dai zan barta zuwa wani lokaci kafin mu koma ..
Nabeel yayi shiru yana kallonsa ,shi kuwa M.A banda shafa qirjinsa dake kwance da suman gashi babu abinda yake yana sakin murmushi saboda fuskar muwaddat dake yawo acikin kwayar idanunsa.
'"Dan Allah friend kayi k'ok'ari ka fahimtar daita yadda kake matsanancin sonta kafin mu koma dan gsky banason ganinka cikin tunanin ,"karka damu zan yi k'ok'arin yin haka ,wannan ba wata matsala bace ,daga nan suka zarce da hirar makaranta, nabeel shine babban aminin M.A ,a London suka had'u a Jimi'a,tare sukayi karatu dashi ,dalibi ne mai kwazo kamar yadda M.A yake da tarin ilimi , couse dinsu daya ,suna karanta orthopaedic sugyre shima nabeel asalin Dan Nigeria ne karatu ne ya kai shi kasar har suka had'u da M.A ,nabeel na d'aya daga cikin mutane da suke mugun shiri da M.A babu abinda nabeel bai sani ba a game da soyayyar M.A da muwaddat ...
********
Misalin karfe biyar na yammacin ranar yashigo parlour'n ummi da akwati daya , yayinda direban ummi ke rike da daya ,
akwati guda yayiwa ummi tsarabar , Wanda kusan duk dogoyen riguna ne da takalma , da turarruka designer masu kamshi gaske ,da mayuka masu kyau da tsada, dayar akwatin kuma na abi ne shake da kaya ..
Gabadaya ummi ta duba taga babu abinda ya danganci na muwaddat aciki har sun soma hira ta kasa hakuri tace "ni kuwa naga tsarabar kowa agidan nan banga na auntynka ba ?
Iska ya furza sannan yace" wace haka kuma ?
"Kaci gidanku da wace haka ,aunty muwaddat nake nufi ina nata tsarabar ?
"Kai ummi dan Allah ki daina min irin haka wallahi bakin san yadda nake ji ba idan kikace muwaddat aunty nace ..
"To sannu gyambo sarkin son girma ,ko ma mai zakaji sai dai kaji amman muwaddat na nan matsayin auntynka ,kuma kabani amsar tambayata ina tsabarta take Dan nasan da kabata Zata nuna min ?
Ya had'e rai sosai kmr Wanda aka aikowa da sakon mutuwa yace "yana part Dina ki gaya mata tazo ta d'auka idan tana bukata .
" wani irin magana ce hk kmr kai da sa'arka ,kasani fa ko awa daya baby ta baka a duniya ta girmeka balle shekara har hudu "
"Ta girmeni a shekaru ni kuma ai na girmeta aciki da jiki , dan idan ba'a an fad'a ba babu me cewa ta girmeni ,ni Dan Allah ummi ki daina cewa haka Dan allah ,idan kina fad'ar haka kina da kusar min da burina akanta ," wani buri ne shi wannan?
Ya. tsotsa bayan keyarsa tare dana waskewa "ki ce mata tazo ta d'auki akwatinta, ko kuma ni kike son na kawo mata tasamu damar raina ni?
"Duk ma yadda kagani ,tunda dai ma zaka bata ai shikenan Allah yayi maka albarka "ameen yaso kwarai yayi mata zancesa da muwaddat sai kuma ya share ya dan Jima zaune hira ko zai ga fitowar muwadda bai ganta ba Dan haka ..
Ya baron parlour'n yana fitowa daga cikin part din ummi sai ga me gadi da saurinsa "yana ganinsa ya ja ya tsaya yana gaida shi, shima ya gaisheshi cike da girmamawa saboda yana ganin girman mutumin sosai "mai gadi yace ranka ya dade wani ne ke sallama da muwaddat a waje...
"Wani ya furta a d'an razane Gabansa na dukan uku uku cikin rawar murya yace "waye shi ?"gsky nima bansani ba amman yau shine zuwansa na biyar baya samu ganinta..
Batare daya sake cewa komai ba kawai yasoma tafiya yana yiwa mai gadi al'amar ya koma bakin aikinsa, shi kuma ya fito harabar gidan inda ya iske wata lafiyayiyar Mota kiran TOYOTA COROLLA LE fara sol, ya isa har jikin mota hannuwansa duka zube cikin aljihun wandosa ,cike da jin kai ya ciro hannunsa daya ya kwankwasa glass din motar Wanda ke ciki motar yayi warning glass tunaninsa ko itace Amman sai yaga sabanin haka ..
Ai take Fara'ar fuskarsa ta d'auke ,ya tsurawa M.A ido kawai yana kallonsa saboda tsabar kama da sukayi da sahebar ransa ,cike da karfin hali M.A yace "malam lafiya tsayuwar me kake yi anan sannan wa kake nema ?
barrister Abdul yace" ammm uhmm muwaddat nake nema Dan Allah ko tana ciki ?
M.A ya sake had'e rai sosai kmr an aiko masa da sakon mutuwa yace "tana ciki me zata maka ?
"No daman bawani Abu bane kawai dai nazo ne dan ..."dan Allah malam dakata ya katse masa hanzari cikin zafin zuciya " daga yau karka sake zuwa kofar gidan nan da sunan kazo gurinta Dan muwaddat matar aure ce ..."
"matar aure fa barristers ya furta hankalinsa a matukar tashe ?
M.A yayi masa banza yana watsa masa wata uwar harara datasa hantar cikin barrister kad'awa cikin tsoro yace "dan girman Allah kuyi hakuri wallahi ban sani ba, watakilla shiyasa taki saurarata tun farko, cikin rawa jiki yasoma k'ok'arin tada motarsa .
shi dai M.A bai sake cewa komai ba ,ya juya ya koma ciki gidan yana bawa mai gadin umarni kar ya sake zuwa kiranta ,a duk sanda Wani yazo nemanta yace matar aure ce ..
mai gadi yace "babu ma mai zuwa gurinta ,ai hajiya akwai kamun kai ," kai dai kawai kabi abinda nace maka "to angama.
M.A ya nufi part dinsa ya bar mai gadi da mamaki wannan al'amari ,ya dad'e yana tunanin wannan matakin da M.A ya d'auka, Amman dayake yasan hatta ita kanta hjyr gidan batason ana zuwa gurin muwaddat din ,yasa ya amshi dokar da mahimmanci.
Anwar na shiga part dinsa yashiga sintiri gabadaya ya rasa wa zai tunkara da matsalarsa kusan minti goma yana zariya sannan yasamu guri ya kwanta akan gadonsa ya janyo wayarsa yashiga what's app aiko yaci sa'ar tana on line bai tsaya wata wata ba ya hau tura mata sakon kuka ππππππππππππ..
Cikin minti daya kacal ta turo masa da martani sakonsa, har biyu ,Amman ta goge
" me yasa kika goge abinda kika turo? Ya sake turo mata had'e da kuka.
"Nothing ta turo masa ."
Ya sake turo mata uhmmmmm wallahi mun 'bata dake ..π
πΌββ
Ita kuma ta turo masa alamar dariya π
π
daga k'arshe ta rubuta masa "kace mun 'bata ko ,to ai kayiwa kanka wallahi ?
Jikinsa na rawa ya rubuto mata "yi hakuri mun shirya ai bamu fad'a da juna .."
"No bana son shiri da kai yanzu , sai na tsula maka tsiya.
",uhmmm plz kiyi hakuri kinji tawan bazan iya dogon fushi dake ba.
"tawan ta turo masa da alamar π€π€mamaki ..
Shima ya turo mata "to ta waye idan ba tawa ba?
" ke din tawace muddin rai babu Wanda ya isa ya rabamu..
Ta turo masa alamar π€Ίπ€Ίπ€Ίπ€Ίzata zanesa sannan ta sauka .shi kuwa yana ganin ta sauka yaja tsaki ya kwanta ,bai farka ba sai can yamma yana tashi ya tashi da zazzabi sosai sai dayayi kansa allura ya janyo wayarsa yashiga what's app yashiga turawa muwaddat sako .
"Muwaddat zazzabi nakeji yau "what when kasoma jin zazzabi ina ke maka ciwo?
Voice ya turo mata dashi "muwaddat sanyi nake ji, zazzabi ne yake son