Showing 108001 words to 111000 words out of 116597 words

Chapter 37 - MUWADDAT Complete Document book by Aisha Bagudu .txt

24 Nov 2024

6297

a matukar sanyaye ya koma gida, zuciyarsa a cunkushe , gabad'aya ya rasa abinda ke masa dadi arayuwarsa ,ji yayi tamkar zai rasa tilon d'ansa ne a wannan karon sakamakon bugawar da zuciyarsa ke yi , shiru yayi yana kai kawo acikin d'akinsa yana dogon tunanin akan lamarin bunayya "Ina sonka ya kai d'ana .....
"Ina son ka rayu cikin farinciki ....
"Bazanaso ganinka cikin tashin hankali da damuwa ba ..
"Tabbass lokaci yayi da zan yi komai akan son zuciyarmu , matukar ina raye duk runtse duk wuya muwaddat ba zata su'buce mana ba.. .........


Cikin wannan halin ummi tashigo d'akin ta riske shi , ai ganinsa tsaye cikin wannan tashin hankalin , yasa ta k'araso da sauri tana kallonsa a firgice.
" hubbey me yayi zafi haka ?
"meke damunka ? Tayi Masa tambyr ajere, hankalinta a matukar tashe ta kamo hannuwansa duka cikin nata suka zauna atare agefen gadonsa tana kai hannunta fuskarshi "ka sanar dani damuwarka mijina.....


Muryarsa a raunane yace "bunayya ........
sai Kuma yayi shiru ya kasa k'arasa maganar "me kuma ya samu bunayya da yanzu kuka rabu dashi ?
"Hubbey bunayya na cikin tashin hankali ,bunayya ya bar kasar nan da muradin mallakar muwaddat arayuwanshi "bunayya na matukar son muwaddat fiyye da tunaninmu...
" yakamata ki duba wannan a'lamarin plz..bugu da K'ari Ina jin tsoron abinda zai faru dashi ,ya tafi cikin tsananin tashin hankalin da bazan iya misalta miki ba , bunayya ya tafi ya bar zuciyata cikin damuwa, Ina ji tmkr na dawo da d'ana gareni nayi masa abinda yake muradi .....


Naunayen ajiyar zuciya ummi ta sauke "yanzu akan wannan mgnr kawai zaka saka zuciyarka cikin damuwar ?
"Ba akan wannan maganar kawai bane ..."
"Wannan maganar ta wuce akirata da kawai ,idan kawai ce agurinki ni agurina ba kawai bace ..
" Domin bunayya ya cancaci fiyye da haka agurina ...
shine komai na rayuwata, shine duniyarta , yau idan bana raye shine majibancin alamarana , ta yaya kike tunanin bazan damu da damuwarsa ba ..?
"Dole na damu damuwarsa , idan son samu ne ma muyi masa abinda ya bukata daga garemu ..
Ummi taja dagon numfashi ta fesar ahankali tace "yanzu nufinka ayi masa aure ko me kake nufi ?


"Exactly abinda nake nufi kenan ,tunda ya nuna yana son aure , ni Kuma inshallahu zan yi masa ,idan ma baki bada had'in kan da zai auri muwaddat ba, zan aura masa diya ko ta uban waye tunda nasan d'ana bashi da wata mummunar kama ko mugun halin da za'aki bashi aure.... ya k'arasa mgnr cikin fushi yana zare yatsunsa cikin nata , abinda bata ta'ba gani ba kenan a tun tsawon rayuwar aurensu .....


"Wai fushin ishaq yayi daita akan d'ansa ko me ?
" 'lallai wannan abun mai girma ne a zuciyarsa ..
Shiru tayi tana dubansa tana nazarinsa ahankali ," tunda shi yayi fushi a halin yanzu, ita bai kamata tayi ba, dan haka cike da mutuwar jiki ta sake kamo hannuwansa tace "kayi hakuri dan Allah , na fuskanci kmr ranka ya 'baci sosai akan matsalar nan ,kada zuciyarka tayi wani tunani akaina ni.. ....
"Kema me ..? Ya katseta ta hanyar fad'ar haka yana huci .
"Ta Yaya kike expecting zuciyata bazatayi tunani akanki ba ?
"Idan zaki amince ki amince ki Sanya hannu ayi komai, Banga dalilin da zai saka ki dinga yi masa kallon yaro ba alhalin yaro ya nuna mana cewar shi ba yaro bane ..
"Akwai wad'an da Basu kai bunayya a komai ba,Kuma anyi musu aure har ma su haihu bare shi..."


"shikenan naji but ka kwantar da hankalinka dan Allah, ka saurareni "nima bawai bana son yayi auren bane, zan fi kowa son haka atsakaninsu ,"wallahi tallahi ina son bunayya da muwaddat amman ka duba lamarin nan hubbey ka gani ,mai bunayya zai iya yi muwaddah a fanni auratayya bare aje ga zaman kewar rayuwar zaman aure ?
" Bana tunanin zai iya mata wani....
"ki bashi ita mana ki gani ko zai iya ko bazai iya ba..
"idan zaki canza tunaninki ki canza ni dai na rigada na gama maganata , zan tuntu'bi muwaddat akan shi matukar ta nuna tana son shi ,zan aika masa da ita can sun karata .. ya k'arasa mgnr Yana Mikewa tsaye cikin tashin hankali....
Itama ta mike tsaye tana cigaba da dubanshi "zaka aika masa da ita fa kace ?
Yace "yes of course"
" Sai kace wata kaza "to ai baby bata so shi bare ka aika masa ita wata uwa duniya.. ,"kama cire wannan son zuciyar naka akan d'anka , dan zance da nake maka ma yanzu tuni muwaddat sun gama magana da al'ameen akan zai turo iyayensa ...


abi yayi shiru zuciyarsa na dokawa "sun gama magana da wa kenan ..?
"da al'ameen mana..ta bashi amsa tana tsare shi da idanuwanta. "yakamata mu cire son zuciya acikin lamarin nan , a zahirin gsky idan zamu bada auren muwaddat mu bawa Wanda ya girmemeta, ba wanda ta girma ba, tunda shi aure ba wasan yara bane ....
Ahankali yasoma taku had'e da Juya mata baya ya cikin kunar rai, yana fuskarta window d'akin..
Itama ummi cikin fushi ta bar d'akin ta nufi d'akinta ....


Ummi na barin d'akin ,abi ya d'auki wayarsa yasoma neman layin uncle umar kaninsa ,Kira d'aya biyu , uncle umar ya d'auka had'e da yi masa sallama"assalamu alaikum"
daga can bangaren abi naji ya d'auka ya amsa masa da "waalaikum Salam, kana yace "umar sabuwar matsala fa taso a gidana gabad'aya ban San yadda zanyi ba " nan abi yashiga zayyanowa uncle umar komai tun daga zuwan bunayya har zuwa yau din nan daya bar kasar .
Uncle umar yace "karka damu Yaya wannan bawata matsala bace , komai zai zo da sauki inshallahu ,ka bari zan Kira ita ummi na fahimtar daita nasan zata fahimta ,"wace irin fahimtarwa zakayi mata ?
" Zaka mata bayani komai ne, sbd lamarin fa yasoma fin karfina ?
"to me ka gani a fad'a mata ne ?
"zan so haka gsky dan...
"No Yaya kusan fa ummi ta fika gsky ta wannan bangaren, karka biye bunayya plz ,da akwai kuruciya acikin lamarinsa, idan ma hakan ce zata kasance abarshi zuwa gaba plz ,tautauna suka cigaba da yi akan lamarin kafin daga baya
sukayi , sallama .




Bunayya na sauka a kasar london muwaddat ya soma kira amman number's dinra shiru basa shiga, dan haka ya kira na ummi,batare da 'Bata lokaci ba , ta d'auka suka gaishe muryarta a kausashe mai nuna al'amun tana cikin damuwa yace ,"umminah me ya sameki naji muryarki somehow like kina cikin damuwa ?
"Babu komai ya ka Isa ?
Muryarsa a sanyaye ya sheida mata ya sauka lafiya ta gayawa abi.. .. sukayi sallama, ranar dai duka ahlin gidan yini sukayi cikin damuwa ,most especial abi wanda ya fi ummi d'aukar zafi, dan ko lokacin dataje d'akinsa yaki sakar mata fuska, bare wani rawar jiki daya sabayi akanta amman dayake tasan ta kan kayanta haka ta dinga binsa da rarrashi da dadin baki da komai har dai ta d'an shawo kansa suka daidaita ..


********




tunda bunayya ya bar kasar take cikin damuwa da tashin hankali gabad'aya ta fita haiyacinta, kallo d'aya zaka mata kasan bata cikin natsuwarta da kwanciyar hankalinta, komai dai yinsa take dan kar ummi ta harbo jirginta ....


Duk wunin yau babu inda ta leka ko makaranta bataje ba saboda zazzabi daya rufeta, da taimakon ummi ta dawo normal , sai dai ummi haka nan take yiwa muwaddat din wani irin kallo na daban,zuciyarta nayi mata aiyane aiyane akanta ,lokacin datayi tunanin danganata da asibiti domin duba cikakken lafiyarta ,sukayi gari muwaddat din tana murkususun ciwon mara ,d'aga karshe sai ga jini ya barke mata , wannan Abu ya kwantar da hankalinta ummi sosai ta sake bata magani da allura , bayan kwana uku muwaddat ta d'an samu sauki dan haka ta shirya zuwa makaranta ,ummi na ajiyeta tashiga cikin makaranta ta isa deptment dinsu , ko minti goma batayi ba sai gasu fatima da zainab kawayenta suka shigo , da sauri suka k'araso gurinta fatima tace "muwaddat lafiya kwana biyu baki zo makaranta ba?


muwaddat ta yatsina fuska tace "kema kinsan duk abinda ya hanani zuwa makaranta koda rana d'aya ne, abu ne mai mahimmancin gaske , ballantana har kwana uku.
"ikon Allah to me ya faru wallahi hankalinmu yayi mugun tashi har fa muna tunanin zuwa gidanku?


muwaddat ta tsuke k'aramin bakinta tace "rashin lafiya ce amman yanxu naji sauki sosai "suka had'a baki gurin mata "Allah ya sauwake sannan suka shiga duba hand out dinsu..


bayan sati biyu al'ameen ya kirata bayan sun gaisa yayita mata hira, tun tana basar dashi har da tasoma amsa shi sama sama daga karshe yace mata yana son cikin weekend din nan "zaizo ko kar yazo?
tace masa "babu komai kana iya zuwa ,yaji dadi sosai .


muwaddat tana gida kasancewar weekend ce, bata zuwa makaranta tana ta harkokin gabanta sai a lokacin ta fad'awa ummi zuwan al'ameen,ummi tace allah ya kawoshi lafiya ,ai bakiji yadda nake son yaron nan ba, irin mijin da nake miki fatar samu kenan cikakken namiji mai zati da haiba "wannan idan kika aureshi zai ririraki saboda yana da sanyi hali .


jikin muwaddat yayi sanyi ,da jin abinda ummi ta fad'a yayinda lokaci lokaci gabanta na faduwa musamman idan ta tuno bunayya , duk sanda za suyi waya dashi maganarsa bata wuce ta rike shi amana ta jirasa har sanda zai dawo .... .


bayan ta gama breakfast ta shiga bayi tayi wanka, farar hoda kawai ta shafa saboda batason kamshin man shafawarta yanzu , tashiga cikin wata hadaddiyar koriyar doguwar riga gashinta ta jima tana gyara shi saboda tsawonsa da tsantsi ta fashe jikinta da turare mai sanyi kamshi tare da k'ok'arin dasa digon kaunar al'ameen aranta, tunda yana neman ya zame mata karfen kafa, ta fito parlour ta d'auki litaffin karatunta tana dubawa kafin ya k'araso , bata fi minti biyar da zama ba sai ga kiransa yashigo, ta dubi ummi kawai ,itama ummi kallonta tayi tace "halan ya karaso ne ?
"bansani ba"
" to ki d'auka kiji ko ya karaso ne?


ta d'auka had'e da mikewa ta bar gurin dan bazata iya amsa waya a gaban ummi ba,byn minti biyu ta dawo tace "ashe wai har ya karaso ,"to maza shirya ki tafi sai ki kai shi parlour'n baki "

ahankali tabi ta cikin main parlour'n ta shiga parlour'n baki ta bud'e ta waje tare da lekawa farfajiyar gidan , aiko dashi idanunta suka soma cin karo, suka had'a ido dashi yana jingine jikin motarsa ya hard'e kafafunsa, sanye cikin wata had'ad'diyar shadda dinki jamfa idanunsa manne da glss Yana kallonta , kusan minti goma idanunsa na kanta ya kasa d'aukesu " ta d'an lumshe idanunta , ahankali yasoma
ta kowa ta matsa baya kadan domin bashi hanta ,,shi kuma karasa har cikin parlour'n, ta biyoshi abaya tana nuna masa gurin zama ya zauna idanunsa akanta ,ahankali ta motsa labbanta tace "ya gajiyar hanya ?


yayi murmushi yace "ai babu wata gajiya, idan ma akwaita babu ita yanzu tunda na ganki ,
tayi murmushin nan nata mai tafiyar da ruhi, tace "to dame zaka soma abinci ko kayan motsa?
" tukunan dai"


"tsiyaya min lemu kawai ya isheni ,inta kallonki , kallonki kad'ai ya isheni, ta kai hanuta ta tsiyaya masa lemu a glas cup ta mika masa ya amsa yana had'awa da yatsun hannunta ,take jikinta ya kama rawa ganin haka yasa ya amshi cup din ya sha kad'an ,ya ajiye tare da kiran sunanta "muwaddat kina da matsayi mai girma agurina ban ta'ba cewa ina son wata mace arayuwata ba sai ke, dan Allah ki soni koda ba zai kai kwatankwacin wanda nake miki ba ,ina rokon wannan alfarma, babban misali shine yadda na taso tun daga ilori zuwa lagos dan na ganki , ina neman yarda daga gareki zaki aureni ?
mayafin doguwar rigarta tasa ta rufe idanunta dashi amman ta kasa amsa masa ..
dadi ya sake rufeshi domin hango nasarori acikin wannan had'uwar tasu ba kamar sauran lokutan baya ba ,duk inda aka samu kunya to soyayya na nan, koda babu yawa al'ameen bai cika son ganin mace cikin shigarta irin wanda ke jikin muwaddat ba a yanzu, burgeshi da mace tayi shigar riga da siket ko duk wasu kaya da zasu dame mace jiki su fidda surarta a sarari ya kalla yadda yaga dama .


wannan kayan da suke jikin muwaddat bazasu bashi damar ganin komai nata ba sai kyakkyawar fuskarta amman akanta yazamota shigar na matukar burgeshi komai nata yazamo da ban acikin mata kullun zaka ganta cikin abaya take amman hkn bai hana surarta bayyana .


ahankali ya taso daga mazauninsa ya dawo daf daita ya zauna" duk abinda yakamata na fad'a na rigada na fad'a ta bakinki kawai nake jira


tayi shiru na kusan minti biyar daga bisani ta numfasa tace "yaya al'ameen...
ya tsura mata ido yana kallonta cike da fargaban abinda zatace, allah kadai yasan halin da zuciyarsa ta shiga alokacin data ambaci sunansa , ta cigaba da magana cikin sanyi murya "zan fad'a maka wata magana guda daya yayi saurin katseta "dan allah idan kinsan bazata faranta min rai ba, ki bar maganar domin ni yanxu abinda zai sanyaya min rai nake bukata daga gareki idan kina sona kawai kice kina sona muwadda a wuce gurin .


tayi murmushi kawai saboda gani yadda gbdy ya rikice, yace "bakya sona ko muwaddat .. ?


"gaskiyar magana yaya al'ameen zance ace ba'a sonka ma bai taso ba ,baka d'aya daga cikin mazan da diya mace zata ki ko wace ce ita kuwa "to meyasa kike kunbiya kunbiya akaina ?


tace ba kunbiya kunbiya bane yaya al'ameen ina da dalilina mai karfi ya saukar da kwayar idanunsa kasa yana jan numfashi da kyar "wani irin so yake mata mai zafi hk? Ya tambayi kansa.


cikin haka wayarta tashiga Kara ,ahankali ya kai ganinsa kanta daga inda yake yana iya hangon mai kiranta amman sunan kanina daya gani ne a rubuce yasa shi sauke naunauyen ajiyar zuciya "muwaddat ki bari muyi magana kune da kune umminki da kanta ta kirani ta bani umarni zuwa, nasan tayi magana dake kafin naxo idan kinsa bakya sona ki fad'a min sai na hakura saboda banason takurawa rayuwatarki.


"ita ba wai kalmar so bane bazata iya fad'a ba, shi din ne ba zata iya fad'awa ba, gara kawai ta amince da zata aureshi akan ya tutseyeta akan tana son shi ko bata sonshi, bunayya nata faman kiranta amman taki d'aukar wayar daga karshe ma ta jawo wayar ta kasheta gabad'aya, ya sake numfasawa "to zaki aure ne na turo magabatana a saida mamaga mai karfi ..?
ya furta mata wannan kalmar yana tsareta da idanunsa, ahankali ta daga masa kai "yayi murmushi kawai "shikenan nagode yasan tabbas batason shi amman bazata iya furta masa hakan ba, koma dai yaya ne ,tunda ta amince bazai yi sanya agwiwa ba, ahankali yashiga janta da how, wata maganar ta bashi amsa wata tayi shiru da zai tafi ya tursasata sai tayi masa rakiya gurin motarsa tana tsaye ya bud'e motar ya fito da manya fararen lododi guda biyu duk shake da kayan ciye ciye, duk abinda yasan tana so sai daya siyo mata har ma da wanda bai sani ba, kudi ne dai bai bata ba, dan yasan koda ya bata bazata amsa ba..


har dare muwaddat ta kasa kunna wayarta saboda matsanacin tsoron tuhumar da bunayya zai yi ,yanzu idan ta kunna ya kirata mai za tace masa?


shi kuwa har wannan lokacin nemanta yake a ways bai samu ba, gashi yana son ya kira ummi yaji ko lfy sbd zuciyarsa bata ta'ba shiga damuwa ba irin wannan lokacin, amman Yana fargaban kiran ummi , yana kwance bisa lafiyayen gadonsa rike da waya , ac dake manne da gadonsa yana aiki kmr me ,Amman sam damuwar da yake ciki yasa bai jin aikinta ajikinsa , ya kai hannu ya danna wani abu ajikin gadon domin k'ara karfin ac d'akin, babu abinda yake kaunar ji a halin dayake ciki kmr muryar muwaddat , domin jin muryarta kad'ai ya shafe duk muryar wata diya mace a zuciyarsa ,abin mamaki wai yau shine saboda jin murya mace ya shiga halin tashin hankali da matsanancin damuwa," a she haka yammata da suke rud'ewa akansa da son jin muryarsa suke ji idan bai d'auki wayarsu ba?


a wasu lokunta ma yana sane yake kin d'aukar wayar ko ya kashe ko yasasu a derveting, , ya kasa runtse idanunsa gashi dai bacci yake ji amman ina bacci yace bai san haka ba, ranar kwana zaune yayi yana neman layinta .


bangaren muwaddat tunda tayi sallar asuba ta koma ta kwanta ,sai gurin karfe goma ummi tazo ta tasheta taci abinci , byn ta tashi tayi wanka taci abinci ,sai ta kunna wayarta ta koma ta kwanta .


wuraren karfi 12:00 taji wayar ta dameta da k'ara cikin magagin bacci ta dauko batare da ta duba ba tace "waye............?
shiru yayi kirjinsa na wani irin bugawa da matsanancin karfi yana jin da zai iya ,da kuka kawai zai sakar mata ko ya huta da radadin dayake ji"
jin shiru yasa ta cire wayar a kunneta ta duba, sunan data gani yasa ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login