Showing 51001 words to 54000 words out of 116597 words

Chapter 18 - MUWADDAT Complete Document book by Aisha Bagudu .txt

24 Nov 2024

6309

saurin katsesa " ni ban fahimci komai akan zancenka ba "ya gyara tsayuwa yana rungume hannuwansa akirji ga kuma ritsetsen cikinsa "eh to daman dai na dad'e ina sonki kuma aurenki nake son yi idan kin amince"


idanunta ta rausaya cikin nasa dariya na neman kufce mata a yadda take kallonsa da ritsetsen tunbinsa, da jajayen kwalala idanuwansa kmr na agolan nafawa, hancinsa a zube kmr faranti yasa dryar ta k'arasa kwacewa dry tana rufe bakin da hannuwanta .


take alhji nuhu yashiga kallon jikinsa yana dubanta, gabadaya ya rasa driyar me take masa ,ita kuwa sai dariya take gabadaya bata ta'ba ganin abinda ya sata dariya ba irin maganar alhj nuhu ,ta kalli wannan ritsetsen cikin nasa tana sake kwashewa da dariya gabad'aya mutun babu fasali Amman yace wai ita yake so..
alhji nuhu na dubanta yace "nasan kina dariya ne saboda kina ganin kmr nayi miki tsufa ko ?
Ya fadi hk saboda shi in da tuninasa yaje kenan , ya numfasa kana yacigaba da mgn "ita soyayya da kike ganinta muwaddat babu ruwanta da wannan, ni dai ina sonki tsakani ga Allah idan har kin yarda kin amince zan gabatar da kai....
A matukar tsawace tace "dakata dan Allah baba zance komai me ni ban ma San abinda zan kiraka dashi ba ?


"duk wanda kika fad'a bazai dameni ba matukar zaki soni ki aureni .
ta sake kwashewa da wata dry adaidai wannan lokacin motar M.A ta karyo kwanar unguwar ,
ahankali yake driving ciki hadaddiyar motarsa baka wuluk kirar tucsion 4wd, tunda ya karyo idanunsa ya sauka akansu tana dry shima alhj nuhu na murmusawa , annurin fuskarsa ta d'auke, zuciyarsa tashiga dokawa, muwaddah ta kasa tsaida dryar har zuwa sanda M.A ya k'araso kofar gidan wanda zuciyarsa bata daina bugawa ba ,ita kuma ganinsa bai sa ta daina driyar da take ba .




parking yayi ya fito batare daya tsaya rufe motar ba ya zuba duka hannuwansa acikin aljihun wandonsa yasoma takowa ahankali zuwa inda suke, sai lokacin gabanta yashiga dukan uku uku saboda irin kallon kaskancin daya aiko musu dashi dip dariya dake bayyane akan fuskarta ta 'bace ,yana gama k'arasowa alhj nuhu ya juya da niyyar barin gurin tunda yana da labarin yadda M.A yake korar mata samari, har yayi taku biyu M.A yace "no baba ka dawo muyi magana ta kunne da kunne da kai alhji nuhu ya d'an dawo ya tsaya yaji me zaice .
M.A ya dubesa a wulakance yace "wannan shine karo na farko dana ganka tsaye da wannan ?
"me kawoka gurinta?
muwaddat tayi saurin dubansa "itace ma wanna kmr wanda bai san sunanta ba..
shi kuwa alhji nuhu tsuru yayi da ido yana kallon kwayar idanu M.A dake cike da tsantsar kishi kafin daga bisani yace "wai da sonta nake amman dai karka damu zan yiwa shi mahaifin naku magana "you are very stupid kai da mganar da zaka yi masa "ni kace wa stupid?
"ance maka stupid more than donkeys, banda buduwar zuciya irin taka shekararka nawa shekararta nawa a duniya da zakace kana sonta kuma har da aure?


" to wannan yazama karo na farko da karshe da zan sake ganin kafarka a kofar gidan nan da sunan kazo zan.. "bunayya ..... muwaddat ta kira sunansa cikin rawar murya ya kake k'ok'arin yin abinda bai dace ba nifa ba son nake ba "shiiiiiii bana son jin komai ya katseta "ina sane sarai ba sai kin fad'a min ba kya son wannan mutumin mai tubi kmr tulun giyya ba.....


alhj nuhu ya fusata sosai cike da kunfar baki yace "kai a she baka da kunya, ina ganinka kmr yaro kirki a she d'an iska ne ban sani ba?
"kwarai kuwa na wuce haka akan wannan ya nuna masa inda muwaddat take tsaye da yatsan hannusa "ai kuwa zaka gane baka da wayo ,ba dai ni kayiwa wannan iskanci ba ?


"Ai sanin babu abinda zaka yi yasa nayi maka , abinda nake so da kai ,ka rike girmanka ka daina d'aura idanunka akan abinda bazaka iya dashi ba, koda kuwa ya zama mallakinka ...




fuuuuu alhj nuhu ya juya ya nufi cikin gidansa yana suritai "aikin banza kawai kananan yara daku sai iskancin banza da wofi ko an ce maka tashen balaga hauka ne, idan kaima sonta kake ai sai ka fito a gabza da kai , ba ka tsaya rainawa mutane wayo ba ,yana mgn yana k'ara sauri dan kar M.A ya jiyosa ya tara musa jama'a a da ya lura yaron bashi da kunya"


M.A ya kalli muwaddat yace " ke kuma ya nuna ta da yatsansa "sai wani bud'e masa baki kiyi kina washe masa hakora "a'a to makeke son nayi ni wallahi dariya yabani "babu wani idan kina sonshi ne tun wuri ki cire hkn aranki ,dan ki sani an haifeki ne saboda ni, nima kuma haka, dan haka wallahi zamuyi mugun samun matsala dake idan kina tsayuwa da irin wannan tsofofin da duk basir yagama rakikesu, babu fa abinda zakiji airinsu alhj nuhu da alhj jibirl ,ki tsaya irinmu mune zamu baki abinda zai sa kiji kwanciyar hankali, amman idan kinji kina son shi shikenan tunbisa ma kawai ya isheki juyawa tayi a matukar fusace tashiga gida tana jan tsaki .

Zaune ta iske ummi da binta mai aiki a palour cikin hiran jin dad'i
da nishad'i ta zauna tana huci "ummi tace lafiya ke kuma kika shigo kina nimfarfashi?
kasa magana tayi, binta data ga hk tayi murmushi "yar gidan umminta wa ta'bo mana ke?
Ko rufe baki batayi ba M.A ya shigo cikin miskilanci yace "ni ne kuma nasan babu abinda za'a iya min ya k'arasa mgnr tare da zama gefen
ummin yana
tab'e fuska yana ta huci.


binta ta kwashe da dry "lallai kam babu abinda za'a yi, domin kuwa babu mai shiga tsakaninku, Allah dai ya huci zuciyoyinku.. M.A
ya kalli muwaddat dake gefe ummi rik'e da kuncinta tana dubansa daga kallon datake masa ya fahimci yadda ranta ya 'baci ,shima tsumammun idanunsa ya tsura mata cikin had'e fuska yace, ummi
"Wlh ni baby kunya take bani ,da irin mutanen da suke zuwa gurinta da sunan so ummi tayi murmushi me kuma ya faruwa su wad'ane mutane zaka fara ko?


"babu wani zan fara ummi wai yanzu ina dawowa na ganta tsaye da wancan shashan tsohon yana tsarata abun gwanar kunya ita kuma sai washe masa baki take ..
Ya maida idanunsa akanta yace " yanzu dan Allah bby kirarsa bata razanaki ba "wallahi ni da mace nake irin su alhj nuhu, alhji jibirl basu taba samu kofar da zan tsaya dasu ba.. ummi tayi dry "kai dai babu ruwanka da samarinta..
Ita kuwa muwaddat harara ta watsa masa cikin 'bacin tace "ina ruwanka to?
" ai gara auren irinsu da auren yara kanana ....."wallahi karya ne bama zaa taba hadawa ba ki dai canza tunani wallahi wadan tsafafin babu abinda zasu miki ..
ta juya ta kalli ummi..


" ummi kiyiwa yaron nan magana ya fita daga harakata da lamarin gabadaya, nifa shiyasa wani lokacin har banason ya dawo kasar nan, gara muyita gaisa a waya dashi .




"karya ne yarinya..wannan mgnrki karya ce wallahi ,ni nasan kusan kin fi kowa jin dadi dawowata ,saboda abinda ido da ido zai gane bazai kai kunne da kunne ba ko ba hka ?


Muwaddat tace "ba'asani ba ,ni dai ka daina shiga rayuwata da samarina ta k'arasa mgnr cikin tsigar wasa, duk Wanda yazo gurina sai ka korensa ko ni Sa'ar wasanka ce"?


bata kai ga rufe baki ya taso cikin fushi ya tsaya gabanta yana nunata jikinsa har rawa yake yace "an koresu din sai kiyi abinda zakiyi ,wallahi sau d'ari zan ganki da irinsu alhj nuhu sai na koresu yana gama fad'ar hk ya juya fuuuuuuu ya bar parlour'n..




ummi tabi bayansa da kallo tare da cewa "binta taya ganin karfin hali ,Anya kuwa bunayya na cin hankalinsa?
" ji yadda yake wani hakikancewa kmr wani ubanta ko mijinta .?
ummin na gama fad'ar hk ta mike zata bi bayansa muwaddat tayi saurin riko hannuta "haba ummi wasani fa, nifa da wasa nakeyi wallahi har ga Allah banji haushinsa ba....


ajiyar zuciya ummi ta sauke sannan ta koma zauninta tace "duk da hk dai rainin hankalinsa na neman wuce iyaka "hakuri zakiyi hjy tunda ita muwaddat din tace wasa ne, kin kuma san da wannan yar tsamar atsakaninsu daka ce ma shine yayanta da auren zumunci za'a yi inji cewar binta tana murmushin.
ummi tayi sauri "tace a'a ban ciki da wani auren zumunci yaje can ya nemo Matarsa itama haka, ina dalili, daga yanxu kar ki sake yarda ya dinga kore miki samari...


suna cikin magana abi ya daga labule yashigo da sallama, muwaddat ta mike ta amshi jakar hannunsa da ledar hannunsa, ta mikawa binta dake tsaye ledar tayi masa sannu da zuwa ta nufi d'akinsa itama binta tayi masa sannu da zuwa tayi ta kama gabanta..


Abi ya k'araso ya zauna kusa da ummi "hubbey fad'an me naji kina yi haka kuma ke dawa?
"sannu da zuwa, ni da wa inda ba da wannan d'an naka ba?
abi yayi murmushin me kuma auwaluluna yayi?
nan tashiga zayyano masa abinda yayi ...
"to ayi masa afuwa a yafe masa shima watakila yana da dalilinsa na yin hakan, yanxu dai ina bukatar ki saki fuskarki domin itace karfin gwiwata ummi tayi murmushi "kai ko, duk lokacin da ake serious issue sai kasan yadda ka shashantar dashi..
muwaddat ta dawo parlour'n rike da tire mai d'auke da ruwa da lemu mai sanyi ta tsiya acikin glass cup ta mikawa abi "yauwa muwaddat sannu da kokari ya gida?
"lafiya lau abi ya aiki ?
"alhamdullahi ta juya ta nufi kitchen.. ya d'an kurbi ruwan lemu yana duban ummi "har yanxu banga fuskarki ta dawo min tmkr yadda nake so ba ,idan tacigaba da zama haka zanje na tsilla wankana na tafi zance .


"daman yau nayi babban kamu har cikin ma'aikata ,yar yariya fara sol dagowa wacce zata gyara min tsufana "suka sa dariya atare ummi tace "ya rabbi..ni dai tashi muje daga ciki.. ta mike tayi hanyar d'akinsa ya biyo bayanta muje din tare da cewa "kinsa surajo mai aiki a kafanina .. ?
"wani surajo vice chiaman na kamfaninka?
"shi kuwa da sauri tace "me yayi Allah dai yasa ba sallamarsa zakayi ba?


"ina ai surajo yafi karfin da kamfani zata koresa saboda himma da hazakarsa tare da rikon amanarsa, bari dai nayi wanka na fito, "okay tashiga taimaka masa ya cire kayansa yashiga bayi ta rufo masa kofar ,ta karasa gaban wordrobe dinsa ta bud'e ta fito masa da jallabiya black colour...




Free page


*Domin bukatar karanta labarin muwaddat zaki biya 300 naira ta wannan account number din 2175076611 zenith bank Aisht Abdullahi,idan kinbiya zaki turawa wannan number 08032384602 domin tabbatarwa ,idan kuma katin mtn ne ta wannan number zaki tura 08059623096*


Mmn sudais ce
2/4/20, 8:39 PM - imusamuhd(professor): 💗💗💗💗💗💗
MUWADDAT
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗






~NA~






*AYSHA A BAGUDO*








~DEDICATED TO~


_AUNTY SALAMATU AYYUBA_
_(UMMIN KADUNA )_


~BEST AUNTY FOREVER AND EVER~




warning!!!


don't read this novel if you know you are not married... ❌❌❌coz this book contains only for mature people , if you read it, is for your own risk .....




WATTPAD @HAUESH


bismillahirrahmanirrahim

page 20


....Tun bayan fitar bunayya daga d'akin abi,abi ya kasa samun natsuwar zuciya a game da al'amarin tillon d'ansa,
" a zahirin gaskiya yana jin tamkar ya biye masa ne, yayi masa abinda ya bukata, amman lokacin daya tuna shekarunsa a duniya a halin yanzu sai yaga gabadaya lamarinsa na tattare da kuruciya da sharrin soyayyar farko ne , Wanda mafi akasari akan samun haka acikin wannan duniya .


soyayyar kuruciya mafi yawa matasa na tsintar kansu ciki wannan shaukin mai wuyar misaltuwa Wanda da wuya akai ga cimma burinta,
Dan haka ya ajiye maganarsa amatsayin yarinta da kuruciya ne kawai ke dawainiyya da d'an nasa ,bancin hk ta yaya kamar bunayya zai ce ayi masa aure a wannan lokacin
"auren ma da wace ta girmesa?
tattara zance yayi ya ajiyesa amazaunin wasan yara da kuruciya , ya cigaba da abinda ke gabansa .


Shi kuwa bunayya Ko daya dawo d'akinsa ya kasa samun sukuni, gabad'aya ya rasa abinda ke damunsa, zuciyarsa banda tafarfasa babu abinda take, ya kasa zaune, ya kasa tsaye, sai zariya yake acikin d'akin rike da kugunsa yayinda hannusa daya ke dafe da goshinsa ,gabad'aya hankalinsa baya gangar jikinsa, 'kwa'kwaluwarsa ke hasko masa wai ga muwaddat dinsa can tare da ala'meen tana masa murmushin nan nata da yafi so da kauna akan komai acikin duniyar nan ,take wani zazzafan kishi ya turnuke zuciyarsa dama gangar jikinsa, ahankali ya runtse idanunsa yana girgiza kai, kirjinsa na wani irin dokawa da sauri " Impossible ya furta a bayyane had'e da bud'e idanunsa ya cigaba da zagaye d'akin ..


"Anya kuwa zan iya d'aukar lokaci batare da na kai kaina gareta ba ?
Anya ba wani abu al'amen yake nufi dashi ba ?
"to wai ma me taje yi d'akinsa a daidai wannan lokacin?
"Ko ba'a gaya masa ba yasan ala'meen son muwaddat dinsa yake, tun da shi ba makaho bane ,dan idanuwansa sun fara hango masa mugun nufinsa akanta ..
Abinda yakamata kawai kaje ka d'aukota ka dawo daita gida shine kawai besty solution da kwanciyar hankalinka gareka ,zuciyarsa ta umarcesa da fad'ar Hakan ,take kuwa ya amince da shawarar zuciyarsa ,ya kudirci aniyar ko bai je gobe ba kamar yadda ya furta mata ba, to kuwa cikin satin sai ya dangana da ilori ,duk ma abinda zai faru sai dai ya faru amman sai ya d'auko abarsa kafarta kafarsa ya k'arasa maganar yana
fad'awa Kan makeken gadonsa da karfi ya kwanta ruf da ciki , yana furzar da iska mai zafi had'e da shafa sumar kansa ,sannan ya kai hannunsa ya janyo wayarsa shiru yayi sakamakon ganin har lokacin wayar tana kan layi ba'a tsinketa ba.


ya sauke naunayen ajiyar zuciya yana duban screen din wayar sannan ya kai wayar kunnensa ,sautin muryar kukanta ya jiyo can kasa tamkar ta baby yana shiga cikin dodon kunnenshi, zuciyarsa ta cigaba da bugawar da take da karfin gaske, wani irin rad'ad'i ya dinga jin yana sauka akan tsokar dake makale da kirjinsa , runtse idanunsa yayi sosai had'e da Jan dogon tsaki sannan ya katse kiran gabadaya ya Mike ya shiga bathroom...


Muwaddat kuwa har lokacin tana zaune tana kukan bakinciki abinda bunayya yayi mata , kukan ma ba wai akaron kanta taso yinsa ba, ji tayi kawai hawaye na fita daga cikin kwarnin idanunta, tayiwa kanta alkwarin duk runtse babu abinda zai sake shiga tsakaninta dashi, idan mutuwa zatayi da soyayyarsa , sai dai sonsa ya kasheta ,amman babu ita babu shi har abada ko komawa tayi lagos bazata shiga tsabgarsa ba .
tana cikin wannan kukan mumy tashigo d'akin ganin har 11:00 na dare bata fito taci abinci ba .
Tana ganin shigowar mumy tasoma k'ok'arin had'iye kukanta had'e da share hawayenta da sauri ,yayinda ita kuma mumy tana ganin haka ta maida kofar da sauri ta rufe ta k'arasa shigowa d'akin tana kiran sunanta "muwaddat meke faruwa ?
" lafiyarki ?
"kukan me kike?
"Waye ya mutu ko waye bashi da lafiya ?
Tayi mata tambayar gabadaya ajere tana zama kusa daita.


kai kawai muwaddat tashiga girgiza mata al'amun babu komai "ke ki bud'e baki ki min magana, ba wai ki dinga karkad'awa mutane kai ba "me ya faru ,me yasameki ?


Muryata cike da kuka da in ina tace " ba..Babu komai fa" "babu komai zaki zauna kina kuka kamar wace aka aikowa sakon mutuwa, ki gaya min abinda ke damunki ?
Wasu sabbin hawayen suka sake gangaro wa bisa kuncinta , tasa bayan hannunta ta goge tana sake girgiza mata kai .
Hankalin mumy ya sake tashe matuka, tace "wato kina boye min Abu ko ?
Cikin rawar murya tace "Sam Sam ba haka bane mumy ,"kina boye min mana mumuy ta fad'i tana mai mikewa tsaye da sauri tayi hanyar fita domin kiran dady, muwaddat tayi saurin riko tafin hannuta "mumy karki yi fushi dani Dan Allah ,babu fa abinda ke damuna kawai dai ina cike da kewar ummina ne ........
ta tsinci kanta da fad'ar haka wasu siraren hawaye na gangaro mata .




Naunayen ajiyar zuciya mumy ta sauke sannan ta koma ta zauna tana dubanta had'e da nazarinta "har ga Allah ta yarda da maganar diyarta, saboda tasan yadda shakuwar dake tsakaninsu da uwarta tafi karfin haka ,domin kuwa daya baya iya d'aukan dogon lokaci batare daya ba ,yanzu haka kullun garin Allah ya waye akalla basuyi waya ba sai sun yi sau Goma hatta bacci suke tashinta wani lokacin ko abinci zata ci sai takirata tana cin suna waya haka zalika abi ,Yayinda komai akayi ta bangaren kowanensu ,yanxu ne zasu bugawa juna suna cike da tsantsar farinciki suna labartawa juna "
Ahankali mumy ta bud'e bakinta "to kuma shine zaki zauna kina kuka?
" idan kin gaji da zama damu kamata yayi kiyiwa umminki magana tasa azo a tafi dake .. .. ba wai ki zauna a d'aki kina kuka irin hk ba "
Amman yanzu ki bari zuwa wani sati sai ki koma, saboda ina son kije kalgo ki ga inna kafin ki koma, ki d'an yi kwana biyu agurinta ,dan koda yaushe idan munje sai tayi maganarki ,Dan haka zan saka ala'meen ya kaici gobe tunda weekend ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login