Showing 12001 words to 15000 words out of 116597 words

Chapter 5 - MUWADDAT Complete Document book by Aisha Bagudu .txt

24 Nov 2024

6280

na zama acikin kwalkwaluwar yara sosai ..
*************
tsawon shekaru uku kenan da auren mukarama da ishaq Amman har yau Allah bai albarkacesu da samun haihuwa ba sai murza marcinsu suke tamkar sabbin aure, sunyi zaryar asibitin har sun gaji Wanda zuwa lokacin har hajara ta sake haihuwar wani nmj Wanda yaci sunan mahaifinta, sai dai yaron bai Jima ba yace ga garinku ..


Rashin haihuwarsu ta damu mukarama matuka saboda da har daginsa sun fara korafi akan rashin haihuwarta, dan duk lokacin da zatayi waya da daya daga cikin yan dakinsu sai sun tambayeta "kina da ciki ko har yanzu kina nan kina ci kina kasheyewa, wannan abu na masefar 'bata mata rai ,taga haihuwar nan Allah ke badawa ,ya bawa wanda yaso ya hana wanda yaso, sai a wannan alokacin ta lura da akwai wad'an basu son aurenta sosai da ishaq wanda ita batasan dalilin haka ba .


a wani zuwa da ishaq yayi Nigeria ya barta a spain saboda yanayin karatunta,anan suka had'u da babbar yayarsu,aiko ta tasa shi agaba da maseefa agaban mahaifiyarsu, akan lailai sai dai ya k'ara aure, su bazasu iya zama da juya ba macen da bata haihuwa, domin dai danginsu duk masu haihuwa ne, yazo cikin dangi ya k'ara aure , ta inda take shiga bata nan take fita ba, abinda ya 'bata masa rai ,bai wuce rashin takamata burkin da hajiyarsa takiyi ,wanda hakan ya nuna masa da had'in bakinta itama tana son ya k'ara aure, cikin sanyin jiki ishaq ya baro d'akin mahaifiyarsa gabad'aya zuciyarsa ta cika da kunci ,yana son matarsa, sannan baya jin zai iya had'ata da kowa, yasan yana son haihuwa amman tunda Allah bai bashi bashi da yadda zai yi.


har zuwa sanda mukarama ta kammala karatunta na likintacin Amman haihuwa shiru babu labari ,yanzu da kanta take bawa kanta kulawa da d'aura kanta akan magani ,Amman har lokacin shr kake ji ,wannan rashin haihuwa ya sake janyo mata mugun kiyayye mai karfi a gurin dagin mijinta Wanda har aka soma masa tayin yammata daban daban , Amman furrr ishaq yace "shi bashi da ra'ayin mata biyu mace daya ta isheshi rayuwar duniya kuma itace mukarama, haka suka buga suka gaji suka hakura .


Mukarama ta dage da addua tana kaiwa Allah kukanta domin shine maji rokon bayinsa magani kuwa sunyi har daga Nigeria mahaifiyar ishaq take aiko musu dashi ,mukarama bata baccin daren , duk daren duniya zaka iske ko a zaune tana lazimi ko tana nafilfili, matukar ba tana tare da mijinta bane , duk karshen wata sai sunyi gwajin fitsari ko tana da ciki saboda period dinta dake canza yanayi, idan wannan watan yazo on 20 wani watan on 25 zaizo , wani watan ma sai ta shanye batayi ba sai daga baya ya zo .


Allah maji rokon bawa , kwatsam sai ga mukarama da ciki har na tsawon wata biyu , murna agurin wad'an bayin Allah ba'a magana , gabadaya gigicewa sukayi har da kuka ishaq yayi Dan farinciki, ,ranar haka ya dinga rabon kudi da sadaka, ma'aikatarsa kuwa kowa ya gansa yasan yana cikin farinciki, taka nas alhj Mahmood ya d'auka iyalinsa suka zo domin taya amininsa da kuma tilon k'anwarsa murna ,cikin mukarama na girma ahankali ahankali har ya shiga wata hud'u inda tasoma jin motsin abinda ke kwance acikin cikinta .


tun daga lokacin da cikin ya cika wata hudu bata sake jin motsi komai acikinta ba ,hankalinta a tashe suka nufi wani babban asibiti dake Spain, ana likitan daya dubata yake tabbatar musu da cewar ba ciki gareta ba ,mutuwar zaune sukayi agurin suna duban doctor kafin daga baya ishaq yasoma zubawa doctor ruwan bala'I "Dan mai zakace matata bata d'auke da ciki alhalin watanin baya anan hospital din aka tabbatar mana da tana dauke da ciki ?
,da kyar mukarama tasamu ta shawo kansa tana zubar da hawaye yace "tashi tashi mubar Gurin nan tun jinina bai hau ba,jiki a sanyaye ya tasata gaba suka dawo gida ranar daga ita har shi kasa runtsawa sukayi tana kuka yana rarrashi .


Abu Kamar wasa zance cikin mukarama yazama tahiri,bayan sun dawo Nigeria anan aka fahimci ai cikin na nan kwantawa yayi, a inda aka tura su neman magani anan aka tabbatar musu da kwantar da ciki akayi kuma aciki daginsa mace ce tayi aikin da kitsen rakumi matukar wannan matar bata bar duniya babu yadda za'a yi mukarama ta haifi cikin jikinta sai wani ikon Allah .


aiko anga tashin hankali ranar agurin ishaq, domin taka nas yayi tattaki Tun daga lagos har kano ya zabgawa daginsa rashin mutunci son rashi gabadaya matan dagin ya hada bai bar kowa ba sai matar d'an'uwansa dake zaune a London , tare da sharadin kada yaga kafar kowace shegiya daga cikin family dinsa tazo gidansa da sunan ziyara .


, lokacin da suka cika shekara bakwa cikin ta takwas da aure a wannan shekarar hajara ta haifo diya mace kuma duk wannan lokacin cikin mukarama na nan sai dai baya motsi ...


Farinciki agurin wannan family bai muslatatuwa, domin kuwa kowa ya kasa boye murnarsa hatta ishaq Ba'abarsa abaya ba , ita kuwa mukarama tunda tazo ganin bby taki komawa gidan mijinta, saboda wani azababben soyayyar bbyn daya shigeta, jin yarinyar take tamkar itace ta kowata duniya ,ana jibi suna alhj Mahmoud yashigo d'akin hajara bai isketa ba tana bayi tana wanka sai mukarama ya iske zaune rungume da bby tana goge hawaye.


da sauri ya k'araso gareta hankalinsa a matukar tashe yana tmbyrta abinda ke sata kuka yace "ya ke ya'ruwata mai ya sakaki kuka haka ?
"Hakika idan akwai abinda na tsana bai wuce ganin hawayenki ba ,banason ganinki cikin damuwa da tashin hankali ,ki fad'a min damuwarki matukar ina da yadda zanyi a yanzu zan biya miki ita .




Tayi shiru taki mgn tana rungume da jariri tana kuka tana jijigata saboda kukan da takeyi kar ya tasheta a bacci "ki gaugata sanar min mukarama duk duniya baki da wanda yafini,ki fad'a min damuwarki, nine mutun na farko daya kamata yasani karki 'boye min komai "ko ishaq din ne yayi miki wani abu ?
tayi saurin girgiza masa kai "to gaya min damuwarki da kyar tasoma mgn " yaya kamin alfarma ,ka tausayawa rayuwata ka ceto rayuwata daga shingi ,Nasan abinda zan tmby yana da wuyar aikatawa Amman dai dole na sanar maka tunda ka bukaci hkn "ki fad'a komaye shi matukar bai fi karfina ba zan miki "
Cikin sheshekar kuka " tace "yaya wannan jaririya nake son ka mallakamin ita halak malak ta karasa mgnr tana kuka.....
babu abinda ya zowa zuciyar alhj Mahmud sai maganar innarsu "ka rike mukarama amana, karka barta tayi maraici,kar abun duniya ya shiga tsakaninku, abunka nata haka itama abunta naka ne, ku rike junanku amana...


hakan nan yaji hawaye ya cicciko a idanunsa ,shi ko ko zata tambayesa ya hanata wannan jaririyar ko ita kad'ai yasoma samu a duniya ai zai mallaka mata bare yana da wani kwan a duniya, ahankali taji sautin muryarsa ta ratsa cikin dodon kunneta "Dan wannan kike hasarar hawayenki mukarama ?
ta kasa d'agowa haka hawaye yaki tsayuwa a idanunta.


alhj Mahmud ya numfasa yace "wannan jaririyar fa ditarki ce halak malak ,bata da wata uwa duk duniya daya wuceki ,ni Mahmud na mallaka miki ita halak malak daga yanzu ba diyata bace takice sai dai ziyara Wanda bazan hana hakan faruwa ba...


mukarama batasan lokacin data zube gabansa bisa gwiwowinta tana kuka mai gauraye da murmushin jin dadi ba "nagode yaya ,na gode Allah bar mana zumuncinmu, d'anuwa mai dadi, waye zai maka irin kyautar ban da d'anuwa mai zumunci irinka yaya?
"ki bar kuka haka mukarama babu abinda zan mallaka kice kina so naki baki shi, AYSHA diyarki ce har abada wani farinciki yakamata sakamakon sunan innarta dataji ya furta cikin murna tace "sunan innata yaya?
ya daga mata kai "sunan wa zansa mukarama?
"ai daga sunanta sai naki yakamata nasa, nasa nata sai kiyi adduar nan da kwana arba'in a samu mai sunanki... sukayi murmushi "yaya ka nufin daga arba'in zan zo na tafi da muwaddat?
ya d'aga kai "a'a yaya zan barta har sanda za'a yayeta sai nazo na d'auketa ..
alhj mahmud yace "wannan kuma ya rage naki ,kiyi duk yadda kike so daita diya dai taki ce, fatana dai ki bata karatu kamar yadda nabaki "karkaji komai yaya karatu sai tace tagaji dashi..


hajara dake kokari fitowa daga cikin bayi kunnuwanta suka jiyo mata tautaunawarsu gabanta yayi wani irin muguwar faduwa hakan yasa ta kasa fitowa wasu zafafan hawaye suka gangaro mata ta koma ta jingina bayanta da jikin bango bayi ....




Mmn sudais ce
2/4/20, 8:39 PM - imusamuhd(professor): 💗💗💗💗💗💗
MUWADDAT
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


~NA~


*AYSHA A BAGUDO*




~DEDICATED TO~


_AUNTY SALAMATU lAYYUBA_
_(UMMIN KADUNA )_


~BEST AUNTY FOREVER AND EVER~


alhamdullahi am back again.


warning!!!


don't read this novel if you know you are not married... ❌❌❌coz this book contains only for mature people , if you read it, is for your own risk ......wannan shine.




WATTPAD @HAUESH


bismillahirrahmanirrahim

page 9




.....kafafuwanta suka hard'e saboda irin kallon kurrular da M. A yake binta dashi , amman duk da haka a natse tacigaba taku tana d'aga kafafunta ahankali , duk yadda taso ta kaucewa kallonsa ,hakan ya gagara .


wannan tafiyar da take ahankali tamkar an tsamota cikin ruwa ba k'aramin sake tsuma zuciyarsa tayi ,saboda yadda jikinta ke moving da rawa , tana shiga parlour'n taja ta tsaya rungume da hannuwanta duka akirji tana fesar da numfashi tamkar wacce tayi gudun famfalaki .


ahankali shima ya sanyo jikinsa gbdy cikin parlour'n, had'e da maida kofar ya rufe, har da sanya makuli, ya jingina bayansa da jikin kofar had'e da tsura mata tsumammun idanunsa yana kallonta , suna had'a ido kowanne ya kafe d'an'uwansa da kallo zuciyoyinsu na ayyana abubuwa da dama, bangarensa kuwa yaba kyawun surarta yake yi ganin yadda jikinta yayi matukar amsa doguwar rigar abayar jikinta,ta yane kanta da k'aramin mayafin rigar ,gashi daman irin karuwan jikin nan gareta masu d'aukar hankali.


yadda ya zuba mata idanu ya kasa d'aukewa ,haka itama zuba masa ido tayi tana kallonsa batare da tace masa komai ba, illa kirjinta daya shiga bugawa da karfin gaske saboda ganin ya maida kofar ya rufe har da sanya key ,
shine ya katse shirun ta hanyar yin kasa da muryarsa tamkar mai jin bacci yace "wannan kallon fa kmr zaki cinyeni? ya fad'i hkn yana
furzar da iska...


rausayar da kwayar idanunta tayi cikin nasa kana ta bud'e bakinta da kyar tace "gani nayi ka rufe kofa alhalin hakan bai kamata ba "


"uhmmm agurinki ne bai kamata ba ,amman agurina hakan shi yakamata, domin ni maji'bacin rayuwarki da al'amuranki ne, idan babu ni babu ke, haka zalika idan babu ke babu muhammed auwal ....
ya karasa fad'ar hk yana zagayowa ya rungumeta ta baya ya matseta gam ajikinsa kamar zai maida ita cikin jikinsa .


ta saki k'ara mara sauti tana k'ok'arin zamewa daga jikinsa saboda yanayin data tsinci kaina ciki mai wuyar misaltuwa,
amman ta k'asa saboda sake rungumeta da yayi ajikinsa da iyakacin karfinsa ,yana busa mata iskar bakinsa mai tsuma zuciyarta "yau gani agabanki ,ki taimakeni ki furta min kalmar kina sona kmr yadda nake sonki fiyye da komai a duniya ,ki amince da kina sona ,ki daina kallon rashin dacewar kasancewarmu cikin inuwa daya,
ina sonki muwaddat kuma a shirye nake dana mallakeki amatsayin matata ta sunnah , ki amince min plz, a yanzu hk burina bai wuce na nasarwa ummi da abi ba saboda nasan kema kina sona ...


tayi saurin zaro idanu waje tana girgiza masa kai, ahankali ta juyo suna fuskantar juna had'e da shakar numfashin junansu, da kyar tasamu ta fixgo magana "bunayya ka ..ka daina tunanin ina sonka, irin soyayyar da kake tunani ba irinta nake ma ba, tabbas ina sonka muhammed auwal amman soyayya irinta 'yan'uwanaka, ka ajiye soyayyar da kake cewa ina maka a wannan muhalin "


"abinda na tsani ji kenan arayuwata ,irin wannan soyayar sam bana bukatarta atsakaninmu "baby i love you, you won't understand how am feeling about you , ya fad'a yana sake had'eta da jikinsa, "wallahi na yarda ke aunty'na ce amman hkn nan na tsinci zuciyata da tsananin kaunarki " nasan kema kina sona muwaddat kmr yadda nake sonki dan Allah karki cutar da zukatanmu, idan baki aureni ba komai zai iya faruwa dani "


"babu abinda zai faru da kai......sannan kar ka sake ka furtawa kowa wannan kalmar, asalima kasan burin iyayenmu akanmu na ganin mun samu ingantaccen ilimi mai zurfi kafin aure....


yawo yashiga yi da duka hannuwansa a sansar jikinta yana romancing dinta cikin salon wayonsa , wanda hakan yasa ta dinga jin jikinta na macewa da amsar salon dayake mata ,lokaci daya kirjinta yashiga dokawa da sauri sauri, dan wani irin tsoro ne ya ziyarceta , cike da sanyi jiki ya kamo hannuta ya nufi kan kujerar kushin, ya zauna tare da zaunar daita akan cinyarsa jikinsa na wani irin rawa "shikenan shikenan!! nasan da wannan burin nasu akanmu , zan hakura har xuwa sanda muka gama karatunmu,idan mun gama zaki aureni zuwa lokacin ?


tayi shiru ta tsaida kwayar idanunta cikin nasa tana kallonsa kirjinta na dokawa da sauri , "ki daina min irin wannan kallon, yana matukar kashe min jiki, a duk sanda kika yi min " ki bani amsa kawai, zaki aureni idan kin gama karatunki nima na gama nawa ?


haka kawai ta tsinci kanta da girgiza masa kai ala'mun a'a had'e da kawar da fuskarta gefe guda tana kallon d'akin "ba zaki auri muhammed auwal ba?
ta d'aga masa kai ala'mun eh "to yaya kike son yayi da rayuwarsa me tattare da shaukin soyayyarki....?


"hakuri ta furta hkn tana 'ko'karin mikewa tsaye daga kan cinyarsa yayi saurin kamota ya maidaita jikinsa "ki zauna bamu gama magana ba tukunnan "me yasa bazaki aureni ba?


"saboda kai kanina ne ,ta tsinci kanta da bashi amsa da abinda ba shine a cikin ranta ba, taso ta amincewa soyayyarsa a wannan lokacin amman gabad'aya tarasa dalilin dayasa ta kasa furta hakan a zahiri ,sai ma hango kankantarsa data yi yanxu idan ya aureta me zai ce mata?
tayiwa kanta tmbyr tana sake yunkura zata mike, wannan karon bai ce mata komai ba, haka zalika bai yi yunkurin tsaidaita ba, saboda takaicin maganarta.


shiru tayi tare da tsura masa idanunta tana aika masa da wani irin kallon mai tadda sha'awa, kallonta kawai yayi ya lumshe idanunshi dan a yadda yake jin kansa, idan yacigaba da kallonta komai zai iya faruwa.


ta yatsin fuskarta tace "ina tsarabar da kazo min daita ?
"ka bani zan wuce kar ummi taga na jima ,ya nuna mata hanyar d'akinsa kawai da yatsan hannusa batare da yace mata komai ba, saboda bazai iya magana ba, koda ma yace zai yi sam sam muryarsa ba zata fito ba, gumi ne kawai yashiga tsa tsafo masa ta koina ajikinsa , gabadaya kwakwaluwarsa ta d'auki caji sakamakon d'acin kalmarta garesa .




yana kallon yadda tashiga jujjuya jikinta tana takawa ahankali, yayinda koina ajikinta yake motsawa a duk taku daya daza tayi most especial hips dinta, cikin rausaya tashige cikin d'akin tana cewa " wlh bunayya ka maseefar raina ni ...




yayi saurin d'auke idanunsa akan bombom dinta tare da sauke naunayen ajiyar zuciya yana lasar lip's dinsa saboda wani abu daya ji ya tsagar masa tun daga kwal'kwaluwar kansa har zuwa tsakiyar kafafunsa .


ahankali ya runtse idanunsa har sanda ta fito ta tsaya a gabansa idanunsa a runtse suke, amman agaresa tar yake kallonta most especial kirjinta ....
"bunayya ta kira sunansa cikin sanyayiyar muryarta me dadin sauraro da kashe jikin duk wanda yashiga kunnuwansa "banga komai ba, ni zan wuce idan zaka fito gobe kafito min dasu..


ta juya da niyyar barin d'akin ya riko damtsen hannunta sai gata agabansa tana yatsina fuska.
ya Bud'e idanunsa dake runtse tar akanta yana kallonta yana girgiza kai can km yasoma k'ok'arin bud'e bakinsa,"i love you aysha......... .dan Allah ki soni mana kmr yadda nake sonki .


bakinta na rawa tace" nagaya maka karka sake furta wannan kalmar ,gara ka canza wata, amman ban da wannan, sannan ka sakar min hannuna na wuce kana 'bata min lokaci ..


"to bby nah me kike son na fad'a to byn wannan kalmar ?
"ai duk abinda zan fad'a bai wuce wannan kalmar mahimmanci ba agurin , kawai ke dai, kin ki fahimtata ne kawai, sannan bakya fahimtar yadda na kamu da matsanancin sonki, Allah aysha ina sonki fiyye da komai, ina daya daga cikin wanda so yayiwa mugun kamu ,yake matukar yi musu rad'ad'i a zuciya, shiyasa ban so bayyana miki hkn ba , dan kina yi min abinda kika ga dama , kina careless da maganata, sam baki bata mahimancin daya dace"


"Ai maganartaka ce Sam sam bata da amfani ,Dan tsabar rashin kunya ka dubi tsabar idanuna ka dinga gaya min kana so na ...


"to meye acikin dan nace ina sonki muwaddat ?
Ya katseta ta hanyar fad'ar hk yana tsareta da tsumammun idanunsa "meye dan na bayyana miki sirrin dake raina ?
,"ni kad'ai nasan yadda nake ji akanki aysha ina sonki kinsan da haka ,wannan tishi ne kawai da zuciyata ke sake miki ..
"Azahiri ina hango rainin da kika min sai dai kisani al'amari na aure Sam babu raini acikinsa domin ni cikakken nmj ne Dana tattara duk wani muradin diya mace ,babu abinda bazan iya miki ba .....


Zaro

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login