Showing 141001 words to 144000 words out of 192750 words

Chapter 48 - ZAFIN KAI COMPELET BOOK BY Mamuhgee.txt

12 Dec 2024

7156

barin aurenta da DD dole sai Anji cewan uwa Daya Uba Daya suke,
To idan akaji Hakan aka Kuma San Hakan kenan Safnah ba jinin bulama bace daganan Kuma sunyi Tara babu,
Ba auren DD kaante ba zamansu qarqashin bulama sbd zai San safnan ba yarsa bace,
To daga Nan menene makomarsu????


Wannan shine zancen da momy keyi tana kaida kawo cikin palon kaman zata zauce sbd tinani na lissafi.


Kallan Safnah tayi da jajajen idanuwanta tareda zaunawa suka fuskanci juna murya a qage tace


"Meya yakai Bena gidan bayan kince shi Daya ne a gidan Kuma babu Wanda yasan ya Dawo?


Ya akai ita ta sani?
Garin Yaya?
Meyasa Zaki bari duk tsanani duk rintsi Hakan ta faru?


Safnah data koma kaman kurba bayan rawa babu Abinda hannuwanta keyi da qafa
Ta Kalli momy da jajayen idanuwanta da sukai jajir tanason tayi magana ta kasa sai alokacin Wani irin kukan baqin cikin gaske me tsananin nauyi da azaba ya kufce mat ta fasa shi tana zube qasa kan tiles daga kujerar Datake Kai.


Duk da dare ne Safnah kasa riqe kanta tayi ta ringa Kuka Mai tsananin radadi da baqin ciki tana Jin kaman zata mutu sbd baqin ciki.


Kukanta ya saka momy sake shiga baqin ciki da takaici me tsanani itama zuciyarta na sake bushewa da fatan mutuwar DD da Bena tana cikin wannan daren.


Bata rarrashi Safnah ba sbd itama Daman tata zuciyar quna take tana sake shiga lissafi da zurfafa tinani sbd rashin mutuwar su DD Wani binciken zai tsananta akan qwayar Dake jikinsa wadda lefin kama mutum da ita kawai shekara 50 gidan yari ne bare a kama ka da ita kana amfani.


Dole idan DD ya rayu zaa San akwai wannan kwayar a jikinsa Dan haka taji tana sake jiquwa cikin zufa da tsananta fatan mutuwar su DD din tana wannan daren.




******Zeenah data kasa bacci sbd sake Kiran Bena data samun tabbaci a bakin Nafisat cewan yaran Daddyn Amnah ne yazo ya dauketa
Hakan na nufin DD ya dawo kenan tabbas to Amma ko yayane ya kamata Ce Bena ta kirasu Dan bata taba iya bacci batai magana da Amnah ba hakama Shima DD din Amma dukkaninsu babu Wanda ya kira.


Umme dataji Bena din na highbridge ta tabbatarda DD ya dawo Bai fadawa kowa bane Dan haka tace a kyalesu su huta Dan Allah kafin ya dawo Kaantes.


Kowa ya shige,Zeenah na bedroom dinta tana Aiki a laptop har kusan 12 na dare kafin ta daure ta kashe tareda daukan wayarta ta sake saka kiran Bena.


Rashin daga wayar Bena din ya sakata Dan shiga mamaki sbd tasan Bena ko acikin baccin tsakan dare sosai daga wayarta takeyi bare yanzu datasan Daren baiyi sosai irin hakanan ba.


Kwantawa tayi gadonta kafin ta a sake saka Kiran Bena din wayar taci gaba da ringing baa dagawa.


Canjawa tayi ta kira wayar DD shikuma wayarsa a kashe ma gaba Daya,


Bata hakura ba sbd ita tinda Bena ta samu accident din baya Shima kusan haka tayita kiranta Bata dauka karshe suka sameta a accident Dan haka Bata wasa Sam da kiranta taji Bata dauka to hankalinta baya kwanciya barema Amnah da tin yamma tayi Wani sukuku jikinta yayi zafi babu Kuma alaman ciwo a jikinta fatanta Allah yasa ba Wani Abu yarinyar taji a jikinta zai samu mummynta ba Dan haka sai kawai ta nema numbern Naseer ta saka kiransa tana kallan time lokacin 1 daidai.


Shima baiyi bacci ba sbd Yana Aiki Daman wasu lokacin yana Kaiwa har fiyeda 1 dinma baiyi bacci ba.


Kiran Zeenah kaante na shigowa wayarsa da Dan mamaki ya Kalli sunan ya Dan Maida idansa kan time ya kalla yaga karfe dayan dare.


Daukan wayar yayi cikin kasa boye mamakinsa da tinanin dole akwai Abinda ya faru sbd babu ta yanda Zeenah da ko da Rana Basa waya bare da irin wannan lokacin,Yana dauka Kai tsaye yace


"Hello Allah yasa lafiya dai"


Ajiyan zuciya ta sauke itama Bata Wani tsaya Jan wata gaisuwar ba ko batawa juna lokaci ta tambayesa Abinda yasakata Kiran nasa tace


"Bena fa tinda ka dauketa ka tafi da ita baa samunta har yanzu idan aka kira Bata dauka shikuma D tasa ma Bata shiga."


Shiru yayi tareda sake kallan time yace


Shi D Daman wayarsa a kashe suke tin kafin na baro ya buqaci Hakan na kashe masa su,
Ita Kuma Bena din banajin zata qi daga wayar ba dalili gaskia.


"Abinda nake tinani kenan Nima shiyasa na kira, please ko zaka kira ka bincika ko securities na bakin gate din highbridge din zaka tintinba."


Dan ajiyan zuciya ya sauke sbd Shima gameda lamarin da duk ya shafi DD baya wasa dashi Dan haka idan har Zeenah tafara tinanin ko ba lafiya ba dole zaije ya duba sbd DD shine top priority nasa a yanzu.


Sallama sukai ya kashe wayar tareda sake kallan lokaci ya sauke laptop dake qafafunsa ya ajiye gefe ya miqe tsaye ya nufi bedroom dinsa Kai tsaye ya dauko key ko kayansa Bai Wani tsaya canjawaba sbd gajeran wando ne me tsayi da Fadi sosai sai short sleeve shirt takarmi kawai ya zira ya fice.


Gidansa bayada Wani Nisa Sosai da highbridge sbd DD Dan haka Yana fitowa yahau titi ba Daman banka gudu tsakar dare ne a kamasa a dauka me lefi ne kafin a gama gano gaskiyarsa an Bata masa lokaci Dan haka ya taho a natse Yana Yi Yana duba time har ya iso highbridge din.


Take aka Bude masa gate ya shige sbd sanin shi waye sun masa farin sani ire irensu basuda shamaki da shiga highbridge a ko yaushe suka zo.


Duka duka su Safnah Basu rufa 45 min da fita highbridge dinba ya shigo
Kai tsaye gidan ya nufa yana Isa yayi parking ya fito Kai tsaye ya dosa kofa ta saka password Yana sake saka Kiran wayar Bena datake shiga.


Wani mummunan haqayi da qauri ne ya cike palon Wanda ya sakasa shiga mamaki da tsoro da gudu ya nufi hanyar kitchen din wuta yakeci sosai ga ruwa na zuba na kashe wutan sosai Amma Basa Kaiwa koina da wutar take tsabar rudewa ma shi saiya kasa tsayawa kashe wutar ya fito da sauri Yana sake saka Kiran Bena yaji vibrating din wayar palon Yana dubawa yaga wayar ma dap take da mutuwa Dan haka ya kashe wayarsa tareda nufar hanyar bedroom din DD Kai tsaye ya Isa da sauri cikin tashin hankali,
Kama kofar yayi zai saka password ya Bude sai ya dakata tinawa da D din ba shi kadai bane a ciki kaman yanda ya Saba akwai yiyuwar Bena ma tana ciki tinda tana gida.


Sakin hannun kofan yayi tareda fara bugawa da karfi sbd yasan ba lallai akejin bugun kofarba.


Yanda yake buga kofan babu alaman motsinsu aciki ya sake saka hankalinsa mummunan tashi Yana kokarin juyawa ya koma kitchen ko wutar ya qarasa kashewa Kiran Zeenah ya shigo wayarsa a rikice ya dauka ya sanar da ita tabbas ba lafiya ba ya tararda gidan wuta tana kokarin kamawa daga kitchen hakama suna ciki Yanata kiransu ba response.


"Ganinan zuwa Nima" Zeenah kawai ta fada masa tana kashe wayar.


Bata bari kowa ya saniba itama ta zari key dinta ta fito daga kaantes ta nufo highbridge itakam a mugun speed sbd Bata damu da Wanda zai kamata ba tana nuna Id dinta sukaga kaantes zaa saketa batareda Bata lokaci ba.


Ko data iso highbridge securities duk da sunga id card dinta na kaantes daya nuna ita qanwar DD kaante ce Basu barta ya shiga ba sbd lokacin barin masu ziya su shigo ya wuce Daman da 1 ta wuce duk Wanda ba acikin highbridge din yakeba Basa barin ya shiga.


Ranta Baci yake Neman Yi ta kira Naseer dole shi ya kira gate din aka barta ta shigo.


Data shigo ne dole ta Hana kanta gudu da mota Saida ta Isa tayi parking ta fito Kai tsaye tayo cikin
Itama Tari ta fara tsoro na kamata sosai da ganin hayaqin ta nufi kitchen da mugun gudu ta tadda Naseer duk ya jiqe gurin taimakawa ruwan kashe wutar sbd kamar wutar asiri yakasa kasheta duk da Bata cika kitchen dinba iya inda oven din yake ne taqi mutuwa Kila saiya gama cinyewa.


Zeenah fitowa tayi a rikice tayi hanyar bedroom dinsu tana Isa Bata tsaya komaiba ta saka password Kai tsaye ta bude dakin duhu babu haske sosai.


A kan gadonsa ta fara sauke idanuwanta takuma gansu duk su Biyun a kwance kan gadon rufe cikin bargo babu me numfashi a cikinsu.


Ihu taso fadawa cikin tsoro da rawar jiki ganin tashigo babu Wanda ya motsa a cikinsu Dan haka da sauri jikinta duka Yana rawa ta zagaya gurin Bena data lura kaman babu kaya jikinta dukkanin hannuwanta rawa sukeyi ta dauki kayan data Gani qasa ta dawo jiki na rawa ta dagata daqyar ta iya saka mata su duk a rude tana gama saka mata ta qwala Kiran Naseer baiji ba ta fito da gudu ta kirasa yaje dakin ita Kuma ta tsaya Palo tana sake shiga tashin hankali ya taimakawa D Daya Dan motsa alaman Yana yanada sauran Rai ajikinsa ya shirya dole Naseer ne ya dauki Bena yakaita mota ya dawo ya dauko D Shima Wanda yake Bude Amma Basa buduwa sbd a lokacin ne asalin qwayoyin jikinsa na mummunan maye suke Aiki sbd na desire sun sauka tinda ya sauke buqatansa.
#MAMUH
#DBENA
#LOVE
#ROMANCE
#ABABA
#KAANTES
#SAFNAH
#MOMY
[9/7, 1:47 PM] MG: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
76
Hankalin tashe cikin tsoro da firgici Naseer da Zeenah din suka nufi Asibiti dasu ba tareda sun tsaya sanar da securities komai ba kawai dai Naseer yace musu akwai oven ya kama da wuta a gidan please suje su kashe shi asibiti zaije.


Yana fada musu yaja motar ya fice da gudu yau Yana karya doka.


Su Kuma securities din Kai tsaye gidan suka nufa tareda Isa kitchen suka kashe wutar Basu tsaya bincika komaiba sbd batareda wata damuwa ko matsala ko zargin Wani abin ba yafada musu Dan haka Suka dauki Hakan a tsautsayi suka rufe gidan suka koma gate kawai.


Asibitin kaantes ya nufa dasu cikin mugun gudu kankanin lokaci yakaisu Asibitin cikin gaggawa Aka fito aka karbesu su duka biyun aka shige emergency dasu ta sama.


Ana karbansu aka shige dasu Zeenah ta fidda wayarta cikin tashin hankali da tsoron Daya mamaye zuciyarta ta Nemo numbern Umme ta saka kira.


Harta katse Bata daga ba Dan haka sai Bata sake Kiran ba Kuma Bata nema kowa ba suka fara zarya ita da Naseer kowannensu cikin shiga tinanin da jiran tsammanin dayafi komai azaba sbd matsuwa suje menene matsalar.


Yawo suka ringa yi Zeenah ta kasa zama babban tashin hankalinta da tsoranta idan ba Wani mummunan al'amarin ne ya samesu ba,
To Amma da alama dai love sukai making a Karan farko duba da yanayin da aka samesu.


Naseer babu Abinda yake ransa da qwaqwalwansa face Jin D ya farfado lafiya.


Ko su Bena dasuke ciki a kwance Basu Kai su Zeenah din Shan azabar zuciyar ba sbd tashin hankalin Dayake ransu da tsoro yasa idanuwan Zeenah har sun fara dark circles kanta sai sarawa yakeyi.


Karfe biyu da kusan arbain Umme ta farka shiga toilet kaman ance ta duba wayarta taga misscall din Zeenah,


Da mamaki ta Kalli time na Kiran taga kusan 2 na dare akai Kiran.


Dakatawa tayi daga shiga toilet din ta Kalli dad kaante dake kwance Yana bacci cikin lafiyayyan gadan dakin nasa sai kawai ta saka Kiran Zeenah sbd taji idan ko jikin Amnah ne data ke da alaman zazzabi ya tashi.


Ringing Daya Zeenah a ta cafki Kiran ta daga Umme na Jin muryarta tasan Bata gida Kai tsaye tace


"Zeenah lafiya kuwa?
Ina kike?
Jikin Amnah ne?
Ya Akai??


Katse ummen tayi da sanar da ita Kai tsaye suna Asibiti da DD da Bena.


Tana fadar Hakan Umme ta Bude murya da kyau tace


"Dawood dai kike magana ko kuwa?
Bena ma?meya same su?
Yaushe?
Meyake faruwa ne? innalillahi.


Bude idanuwa Ras dad kaante yayi Jin Abinda ummen ke fada murya a sake.


Tashi zaune yayi bacci na sakinsa babu Wani sauran magagin bacci ya kalleta yana cewa


"Lafiya?
Meya faru?
Su waye a Asibitin??


Hankali tashe Umme ta juyo ta kallesa tace


"Dawood da Bena ne a asibiti basusan inda kansu yake ba."


Agogo ya kalla da sauri kafin ya yaye rufar jikinsa Yana saukowa kan gadon ya qaraso gabanta ya karbi wayar ya saka kunne ya sake tambayar Zeenah da kyau
Ta tabbatar masa da suna Asibiti dasu Dawood din.


Kashe wayar yayi tareda komawa bedside ya dauki tasa wayar ya fito Palo Yana Neman numbern Abbakar.


Umme ma fitowa tayi ta koma bedroom dinta ta canja doguwar rigar baccinta zuwa doguwar Abaya da mayafi me Dan kauri sbd sanyin tsakar Daren da zasu fita.


Ko data fito dad kaante da Kansa zaiyi tuqi Abbakar ma tini ya fito daga Dan sashensa dake bayan na Ubandakinsa dd babba Wanda Shima tini Abbakar ya isar masa da sakon.


Motar dad kaante tini tayi gaba tareda Umme shikuma dd babba Shima cewa yayi Abbakar ya fidda mota Suma suje Yana buqatan zuwa Asibitin jikokinsa biyu mafi soyuwa aransa suna Asibiti kwance Rai hannun Allah ana cewa baa San meyake damunsu ba.


Qanqanin lokaci ya kawosu Asibitin suna isowa kowa Kuma hankalinsa ya Dan sake shiga damuwa sbd Jin harda wuta aka tadda a gidan tana ci da baa je da wuri da kilama mugun labari zaa ji kawai.


A lafiyayyan palon jiran manyansu dake can saman Asibitin suka zazzauna kowa ta girgiza qafa cikin rashin nutsuwan zuciya bayani kawai suke Jira.


Babu Wani bayani daya zo musu sai kusan karfe 4 Dr Ashley tafara fitowa ta Kalli Zeenah kafin ta Kalli Naseer sbd sune suka taso zuwa inda take da sauri, tanason magana tana kokarin daidaita iya Abinda zata iya fadawa familyn kaantes din a gaban Naseer sbd batasan waye shi ba.


Cikin zaquwa Zeenah tace


"Dr Ashley ki fada koma meye ne wannan din kaman familyn kaantes ne sbd Shine kunnuwa da hannuwan DD harma da ganinsa a Alamuransa."


Ajiyan zuciya Dr Ashley ta sake tareda kallans dd babba da ba iya cewa komaiba bayanin Kai yake jira ya gyada mata Kai alaman ta fada kawai suka saurarenta
Ta tausasa murya tafara cewa


"Ita Bena nata ciwon ba komai bane face sex na farkon rayuwarta data samu yau,
Bai Wani je mata da sauki ba ya nuna mata karfi gaskia Dan haka ta jigata ta Kuma tasha wuya sbd na farko ne so rashin saukaka mata muke kyautata zaton ya sakata kasa dauka ta Suma,akwai stitches kadan da Akai mata Dan haka ita inshallah zata farko kowane time sai a fara kulawa da ita da dinkin."


Shiru gurin ya dauka kowa yayi tsit Zeenah da Naseer suka Kalli juna sbd sune a kusa da juna lokaci Daya kansu na Neman juyawa da Jin wai sex din farko ga wadda ke da 'ya.


Umme ma duk rudanin Datake ciki Bai hanata kallan Dr Ashley da sauri ba kafin ta juyo ta Kalli dad kaante da shi Kuma dd babba ya kalla Wanda Kallo Daya zakai masa kaga babu alaman shock ko mamaki a tareda shi
Basu gama fitowa daga mamakin maganar ba da dauke wuta dd babba ya sake buga kansun da kallan Dr Ashley Kai tsaye yace


"Mun San wannan tinda ita an samu shawo kan tata matsalar Allah ya Yi mata albarka ya Basu zuria dayyaba me albarka da zanyi alfahari dasu,
Shi Dawood din nawa meye matsalarsa???


Shiru Dr Ashley ta Dan Yi Suma suka dawo da kallansu kanta batareda mamakin dd babba yagama sakinsu ba.


Shirunta ya sakasu Jin suna sake shiga damuwa da fargaba.


Numfashi ta sauke jikinta na Dan sanyi ta Bude baki a natse tace


"DD nasa matsalar kusan ba guda Daya bane gaskia,
Na farko dai Muna kyautata zaton Shima sauke desire me qarfin gaske ne a Karan farko Daya San mace ya sakasa somewa..


Dan shiru tayi ta Dan tauna Abinda zata fada kafin ta sake kallansu taci gaba da cewa


"To Amma Muna zargin akwai mugayen qwayoyin drugs a tareda shi,
Babban tsoronmu akwai kwayan da muke zargi wadda idan akwaita a jini take shiga Nan take Dan haka Kila sai anfitar dashi babu kayan awonta anan,
Muna Koda siyo kayan awonta mukai anan Muna Yi masa aka Gane zaa soke lasisin wannan Asibitin tamu gabaki Daya,
Acan zaa dubata a jikinsa akwai kaman antidote nata da akesha shi kadai yake koneta a jikin mutum idan ba haka ba zai ringa yi ne Yana taso masa wannan qwayar.


Tsit sukai gurin gabaki Daya sbd babu Wanda ma ya Gane taqamaimai me take nufi sbd rashin yarda da Abinda kunnuwan nasu ke ji musu.


Meya hada DD da qwayoyin drugs Kuma?
Bai taba muamalantar su ba rayuwarsa,
Sam shi qyanqyamin irin wainnan abubuwan ma yakeyi sbd lafiyarsa,
Yaji ma kaman zai kashesa yake masa bare qwaya,ta Ina wannan zancen ya fito?


Dd babba Daya kasa yarda ko fahimtar Dr Ashley din sosai ya Dan gyara zama ya kalleta yace


"Yanzu dai baa tabbatar ba tinani kukeyi right??


Yes Sir" ta fada a natse tana fatan suka tinaninsu kada ya zama gaskia.


Gyada Kai yayi a natse yace


"A bari ya farfado zamuji meya samesa da sauran abubuwan da maganar gwajin ya biyo daga baya."


Gyada Kai tayi itama tana sake Basu tabbacin inshallah zai farfado lafiya for now dai.


Juyawa tayi tayi sauka zuwa office dinta su Kuma suka kwasa zuwa dakin DD din Zeenah da dd babba Kuma Bena suka nufi dakinta.


Sosai ta wahala Dan haka fuskarta tayi fayau kaman wadda ta wuni a ciwo bacci yakeyi na wahala da azaba ga zazzabin gaske a jikinta Daya dauki dumi sosai.


Shiru sukai kowa da Abinda yake ransa yana tinani.


Zeenah kasa Dora zancen cikin Kansa a takeyi wai Bena Bata taba sanin kowane namiji ba sai yau,
To ya Akai ta samu cikin Amnah har ta haifeta?


Bangaren su umme ma tinanin suka shiga da damuwa duk da kaf acikinsu babu Wanda ya kama maganar wai qwayoyin maye a jikin DD sbd sunsan ba Abu me yiyuwa bane Dan haka Basu damu da wannan ba sai fatan su farfado kawai su samu lafiya daga shi har Bena din wadda itama Umme tinani ne kala kala cikin kanta game da cewan Bena Bata taba sanin kowane namiji ba sai yau da DD ya sameta a macenta.


To meye Hakan yake nufi?
Idan ana fada musu wannan zancen kenan so ake a fada musu ba Bena ce ta Haifa Amnah ba kokuwa?


Duka kowa Tara tambayoyinsa yayi cikin zuciyarsa da Kansa ya danne har asamu lafiyar su Bena din a koma gida aji gaskiyar kowa daga bakinsa, dashi da ake cewan akwai maye a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login