Showing 102001 words to 105000 words out of 192750 words

Chapter 35 - ZAFIN KAI COMPELET BOOK BY Mamuhgee.txt

12 Dec 2024

7169

din.


Numfashi ta Dan sauke ahankali tareda ajiye wayar ta yaye bargon jikinta ta ziro qafafunta qasa ta Sauko tareda zira slippers dinta na masu laushi gashin dayake jikinsu.


Fitowa tayi ta nufi kitchen ta kunna wuta ta nufi fridge ta Bude tareda dauko ruwan me sanyi sosai guda Daya ta dauko Daya marasa sanyi tareda glass cup ta jerasu a trey ta kashe wuta ta fito.


Bedroom dinsa ta nufa Kai tsaye tareda tsaya bakin kofar tayi knocking ahankali hannuwanta na Dan rawa hakama zuciyanta.


Shiru babu alaman yajita Amma batai saurin sake knocking din ba ta Dan Jira Wani mintin Daya kafin ta sake Dan buga kofan a hankali.


Ahankali ya Bude idanuwansa a Dan galabaice ya Kalli kofan cikin qaramin sautin da baiyi tinanin taji ba yace


"Shigo"


Numfashi taja kirjinta na sake bugawa kafin ta Dora hannunta a handle na kofan ta Bude ahankali tareda turawa Wani sanyi da qamshinsa Dayake kame da dakin suka sauka fuskanta da hancinta taji kirjinta na tsananta duka
Ta Maida kofan ta rufe ahankali ta juyo babu haske sosai a dakin da yawa Amma tana iya ganin komai.


Ahankali yakai hannu ya qarawa wutan dakin haske sai alokacin tagansa zaune jingine da gadon jikinsa ba kaya
Kiris ya rage ta Sako ruwan hannunta Amma ta qanqame trey din tana dago qafafuwanta da qyar ta nufosa kanta a qasa.


Ahankali ya Bude idanuwansa Shima sai alokacin yaga itace ba Zeenah ba Dan haka ya Maida idanuwansa ya Dan rufe tareda miqa hannu cikin nutsuwa yace ta Basa ruwan.


Ajiye kayan tayi akan Wani luxury table dake tsakiyar makeken dakin tukuna ta dauko robar ruwan me sanyi ta miqa masa.


Yana karba ya Bude ruwan Kai tsaye tareda dorawa bakinsa yafara Sha a hankali.


Juyawa tayi zata fice Bata Isa kofa ba ruwan ya dawo masa ta hanyar Amai me qarfin gaske sbd ruwan sanyin Kansa ba abin shansa bane.


Toilet ya nufa Kai tsaye tanajin Yana zuba aman take ta fahimci baida lafiya Dan haka sai ta kasa ficewa ta juyo ahankali ta Kalli ruwan daya aje din ko rufewa baiyiba ta dawo ahankali ta dauka ta rufe ruwan ta Maida kan trey ta dauke pillow dake jikinsa ya fado qasa gurin saukowansa ta durqusa ta dauka tareda mayarwa kan gadon tana gama sauya masa Wani soft luxury beddings Yana fitowa daga toilet daure da towel jikinsa na tsiyayan ruwa da gumin Dayake Yi har lokacin na zafin cikinsa.


Kallanta yayi ahankali tareda qarasawa kan gadon ya zauna ahankali batareda ya kalleta ba yace ta dauko Wani ruwan me sanyi.


Kallansa tayi cikin sanyi zatai magana Amma ta kasa ta juya take ta dauko Wani ruwan me sanyi Koda ta dawo ya kwanta jikinsa na fidda Wani tiririn zafi.


Ajiye ruwan tayi tareda kallansa taga idanuwansa rufe Dan haka batada zabin Daya wuce juyawa taje ta tada Zeenah ko zasu kira masa likita ne.


Tana fita dakin dakinsu ta koma tayita kokarin tada Zeenah Amma Zeenah din tace Mata kanta na ciwo Bata buqatan tashi yanzu.


Jin haka sai batama tsaya fada mata DD din ne baida lafiya ba ta juyo ta dawo Palo tana kallan kofar bedroom dinsa batasan mekuma zatai ba.


Samun kanta tayi da zaunawa a palon tareda shiga tinani har bacci ya ringa Dan fizgarta kadan.


Tashi tayi zata koma dakinsu taji Bude kofan bedroom dinsa ahankali ta juyo daidai yanason fitowa ganinta yasakasa komawa Yana cewa ta qaro ruwan sanyi.


Wannan Karan Daya ta qaro ta koma dakin tana shiga ta taddasa kaman yanda ta taddasa farko zaune tsakiyan gadan ya jingina bayansa da kan gadan.


Qarasowa tayi Bata ajiye ruwan ba ahankali ta Bude baki cikin sanyi tace


"Shan ruwan sanyin zai kawo wata illar"


Bude idanuwansa dasukai jajir yayi ya kalleta cikin gajeran sauti yace a cikinsa yake buqatan ruwan ta zuba masa ahankali.


Bazata iya zuba masa ruwan Kai tsaye ba dan haka ta fita taje ta dauko sabon Dan qaramin towel me qaranci sosai ta jiqasa da ruwan sanyin sosai ta hadiye Wani numfashi daqyar kirjinta na dokawa ta hau gadon ahankali matsawa inda yake hannuwanta na Dan rawa ta Dora towel din kan fatar cikinsa da babu kaya jikinsa ruwan sanyin ya sauka cikinsa tareda gangarawa jikinsa ahankali ya bude idanuwansa take numfashinsa na Neman daukewa.


Saukan mayun idanuwansa akanta yasa Bena hannunta ya tsananta rawar data saka tafin hannunta sauka kan qasan cikinsa ta shafi cibiyansa a take dukkaninsu suka Kalli juna.


Saurin janye hannunta tayi tana goga masa sanyin a Dan rude shikuma ahankali relief ya fara saukan masa sbd zafi ne sosai cikinsa keyi Amma sanyin ya taimaka masa.


Saida ta sake saka wasu ruwan sanyin jikin towel din ta sake rage masa zafin cikin tsawon lokaci kafin ya samu dawowa hayyacinsa ahankali ya dago ya kalleta itama Jin idansa akanta ya sakata dagowa idanuwansu suka shiga na juna a hankali tayi saurin janye nata har lokacin tana Jin nasa akanta.


Rudewa tafara Yi da Jin idanuwansa akanta ba tsammani tsaban rudewa ta sake Sakin towel din tattausan tafin hannunta ya sauka kan fatarsa wannan Karan riqe hannunta yayi da hannunsa tareda dagowa Yana sake kallanta tsikan jikinsa gabaki Daya suna miqewa.


Hannunta Daya riqe yasata rasa balance nata a zaune sbd a hannun ne qarfinta na zaman yake Dan haka ba tsammani ta fada jikinsa ahankali kirjinta da nasa suna mannuwa da juna wannan Karan rintse idanuwansa yayi ahankali sanyin AC da rigar baccinta ta kama Yana sauka kan fatar jikinsa Yana sake sanyaya masa jikin Dan haka batai tsammani ba taji hannuwansa ya zagayota kirjinta na qarasa mannewa da nasa ita kanta Saida ta rintse idanuwan.


Babu komai akanta Dan haka qamshin Olay dake cikin gashinta yafara shiga hancinsa tareda asalin nata qamshin Daya sani suka ringa shiga hancinsa Kai tsaye suna Neman dawo da zazzabinsa Daya sauka.


Ahankali ta daga hannuwanta ta sauke kan bayansa zata janye jikinta Amma ta kasa Hakan sbd mutuwar da jikinsu yayi su dukan.


Shiru sukai kowannensu idanuwansa a rufe numfashinsu ne Kawai ke sauka jikin junansu,nasa yana sauka cikin wuyanta ahankali da nutsuwa ita Kuma nata na sauka kan kirjinsa da babu kaya tana tayar da tsigan jikinsa da duk saukan dumin numfashin nata.


Shi bacci yafara daukewa ahakan cikin sanyi da gabalaitan da yayi daga jiya zuwa yau din,
Ita kuma sai daga baya nata baccin ya dauketa tana jira ya saketa ta tafi sai kasalanta ta saka baccin dake idonta tun farko dawowa ya dauketa.




Da Asuba Zeenah na tashi sallah taga babu Bena,
Fitowa Palo tayi nanma Bata ganta ba Takoma daki ta duba wayarta taga wayarta ajiye.


Toilet ta shiga nanma bata Nan Dan haka tayo alwala ta fito Bata tada sallah ba Saida ta sake fitowa ta nufi dakin yayan nata zata sanar dashi Bena fa bata gidan tana Kaiwa kofar bedroom din ta dakata sbd tinanin ko Bena din tana ciki,to Amma Tayaya?yaushe?


Danne zuciyarta tayi ta Hana kanta bugawa Takoma daki ta tayarda sallah tayi tagama har lokacin tana cikin yar shakku da fargaban inda Bena din zata tafi cikin dare tinda tare sukai bacci Tama rigata yin bacci Kuma ita Tama kasa Tina Bena din ta tayar da ita da daddare.


Har kusan 7 na safe babu Bena ba labarinta Dan haka 7 din na wucewa ta tashi ta fito tareda musu ordern breakfast daga Wani one of the best restaurants dake Lagos.


Bena kuwa cikin kasala ta motsa ahankali tareda Bude idanuwanta dake da sauran bacci har lokacin ta samu idonta cikin nasa yana Mata Wani irin Kallon data kusan somewa sbd tsayawar bugun zuciyanta.


Tashi tayi da Dan sauri daga jikinsa Datake kwance kaman baby.


Shikuwa har lokacin kallanta yakeyi da idanuwansa dasuka koma yanda suke suke gigitata mutane da kwarjininsa kyansu tareda haskensu.
#MAMUH#
#DBENA
#KAANTES
[8/31, 9:28 AM] MG: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
57
Kasa kallan fuskarsa tayi ta sauko gadon ahankali tareda zira slippers nata masu laushi qafarta tana kokarin juyawa ta fice batareda ta iya ko furta kalma Daya ba
Tana Kaiwa kofa ahankali taji muryarsa me taushi da nutsuwa a sakalance yace


"Idan kinyi sallah I need coffee irin na jiya."


Gyada Kai tayi ahankali batareda ta juyo ba ta Bude dakin ta fice tana gyara rigarta datake qamshin jikinsa gabaki Daya....


Daidai fitowan Zeenah daga kitchen ta tsaya tana kallan Bena din dake gyaran rigan baccinta tana fitowa daga hanyar bedroom din DD.


Kunyace me tsananin gaske take son kama dabaibaiye Bena din Amma taqi yarda da Hakan sbd wahala zatasha gurin Zeenah da tsokana Dan haka ta fuske ta nufi bedroom nasu tana qin sauraran Zeenan data biyota tana Kiran sunanta da sauri.


Tana shiga daki toilet ta wuce Kai tsaye ta rufo sai alokacin ta saki ajiyan zuciya Mai sanyi tana rintse idanuwanta.


Yanayin lattin sallan da sukai yasakata kasa tsayawa tinani da daidaita nutsuwanta tayo brush da alwala ta fito ta saka kayan sallah ta tayar.


Bayan ta idar tayi istighfar da adduointa ta miqe ta sauya kaya sbd duk motsinta qamshinsa takeji ajikinta Yana tashi Yana dawo mata da dumin fatarsa a jikinta.


Fararen Dior sweatshirt da slim trouser ta saka ta fito da qaraman hulan da Bata gama rufe gashin kanta ba ta nufi kitchen.


Coffee ta fara kunna masa kafin ta soya masa chips da farin soyayyan kwai.


A farin kyakyawan trey ta jera masa su harda coffee din ta fito ta ajiye masa a dining tana juyowa Yana fitowa Shikuma cikin black Ralph Lauren sleeveless sweatshirt da quarter trouser.


Fuskarsa pale Amma so fresh Da kallo Daya zakai masa ka Dan fahimci yayi kasalan ciwo.


Dining din ya nufo Kai tsaye idanuwansa akanta
Ita Kuma ta Dan Yi qasa da Kai tana Bude baki da sanyin murya tace masa


"Good morning"


Saida ya zauna ahankali kafin ya dago ya kalleta ya Bude baki a gajarce Shima ya amsa Yana tambayanta Zeenah.


Kafin ta Basa amsa Zeenah din ta fito daga bedroom sbd breakfast datai order da aka kawo.


Da mamaki da shagwaba a fuskanta tace musu tafa Yi ordern breakfast.


Bai kalleta ba Bena din ya Dan kalla Yana daukan cup din coffee yakai bakinsa ya kurba a hankali.


Ganin soyayyan farin egg din ya Basa tabbacin babu pepper a ciki Dan haka yaci breakfast din cikin nutsuwa sbd shi yanzu ko abinci me kala bayasan gani a gabansa.


Junk food ne ma kusan duka Abinda Zeenah tayi order Dan haka anan dining din Suka zauna tareda shi sukai breakfast.


Suna gamawa Dayake sunyi lattin tashi duka gidan saiga Sima tahau aikinta.


Bena Bata fita ba yau Zeenah ce kawai ta fita Dan haka daga ita sai shi suka wuni gidan Amma kaman ma baya gidan Dan tinda ya shige Bai fitoba.


White couscous da kidney sauce Mai hade da veggies tayi masa batareda ta saka yaji ko kadan ba.


Tana gamawa ta wuce daki tayi sallan azahar tareda sake wanka ta saka kayan marasa nauyi ta kwanta Dan baccin ko awa Daya ne ta huta.


Sai 4 ta tashi tayi alwala tayi sallan laasar tana idarwa ta fito tana waya da Amnah cikin kasala sbd baccin Rana kashe mata jiki yakeyi.


Dining ta nufa ta zauna taga baa taba abincin ba ta juya ahankali ta Kalli kofan dakinsa kafin ta dawo da hankinta kan wayar datakeyi a natse tace


"Baby kinyi waya da daddynki yau?"


Eh,yanzuma dashi na gama waya kafin ke."


Numfashi ta sauke ahankali tace


"Ok bacci yakeyi ne ko me?"


Aa Ya tashi bacci fa tin dazu."


"Ok baby ki sake kiransa kice ya fito ga abincinsa a dining"


Shiru Amnah tayi har Mummyn tata ta gam bayani tace


"Mummy kina fushi ne da Daddy?
Shine Zaki saka na kirasa?
Meyayi kike fushi dashi?
Nidai mummy ki shirya da daddynah.


Saurin dakatar da ita Bena tayi tana cewa


"Ya Isa haka naji,jeki gurin Nafisat ko Umme zan kira anjima."


Kashe wayarta tayi tana ajiyewa kan dining din ta miqe ta nufi kitchen Dan dauko drink me Dan sanyi.


Tana fitowa ta taddasa yana zasu ne a natse idanuwansa kan wayarta dake ringing.


Da sauri ta qaraso ta ajiye drink din tana duba wayar sunan Fahad kaante ne Akai.


Daukan wayar tayi daga gabansa batareda ta dauka ba ta ajiyewa dayan gefen tana masa barka da fitowa.


Bai dago ya kalleta ba ya gyada Kai ya Dora da cewa


"Bana buqatan spicy food you Already know so idan akwai pepper karki zuba I will order Wani abin."


Qarasa zuba masa tayi tareda Dan dagowa Bata Kalli fuskarsa ba tace "Abincin is not spicy ko kadan"


Janyewa tayi daga gurin bayan ya Dan deba spoon Daya yaci kadan yaji ba yajin ko kadan tukuna ya Dan sauke ajiyan zuciya ahankali mara sauti yafara cin abincin a hankali cikin nutsuwa.


Itama abincin takeci ahankali batareda ta dago tana kallansa ba.


Ta rigasa gamawa duk da sanyinta sbd kadan taci ta koshi,
Miqewa tayi ta dauke plate da sauran kayan ta mayar kitchen ta tsaya gyara kitchen din Bata dawoba tanaji wayarta na ringing taqi fitowa sai Daya gama yabar gurin.


Fitowa tayi ta qarasa kwashe kayan ta gyara gurin Shima Takoma kitchen ta qarasa aikin gyara can din ta wanke hannuwanta ta goge da tsafatataccen Daya daga cikin towels qanana dake kitchen din Jere ta fito.


Wayarta dake dining ta dauka tana dubawa duka misscalls fin Fahad kaante ne Dan haka ta wuce daki zata kirasa Zeenah ta dawo Dan haka ta fasa Kiran tana kallanta da murmushi kan fuskarta tai mata Barka da dawowa suka shige daki sbd lokacin Me girma DD din ya samu fita daga gidan.


Suna shiga ta kira Fahad ta zauna kan qaramar couch dake dakin tana wayar cikin nutsuwa da sakewar datai dashi.


Har Zeenah ta shiga ta fito suna wayar sai daga baya ta kashe tana kallan Zeenah dake zaunawa gaban mirror tace


"Yaya dai Zee kaante?"


Gajeran dariya mara sauti Zeenah ta sake tana fara shafawa jikinta body cream me kyau da tsadan gaske tace


"Ki shirya mu fita akwai inda zan kaiki to show you Wani Abu."


Cikin Jin Hakan yayi mata Bena tace ok sbd tana buqatan refreshing kanta itama.


Sai bayan sallan magrib suka fita Wani mahaukacin mall suka tafi me dauke da duk abubuwan dasuke buqata designers na waje masu tsadan gaske suka fara kashe kudi batareda Jin zafinsu ba.


Suna gamawa Wani 5star Res sukai branching suka ci abubuwa kala kala kowannensu Yana waya hankali kwance.


Basu dawo gida ba sai 10 harda mintina lokacin Shima DD ya dawo suna parking motarsa na parking da Dan mamaki ya Kalli Zeenah Data fara fitowa motan kafin Bena da itace tayo driving ta fito daga ita se blue slim jeans da christian Dior free size shirt me tsayi.


Naseer Daya kawo DD a mota Shima fitowa yayi ahankali Yana Satan kallan Bena din wadda ta kasa kallansa DD da idanuwansa ke kanta ta Dan kalla jikinta na sanyi tayi masa sannu da dawowa ko amsata baiyiba ya wuce gaba Naseer na kokarin biyo bayansa ya datakar dashi da cewa yaje saida safe kawai.


Yana shiga palon Zeenah dake bayansa ta shigo ta wuce bedroom dinsu ta shige
Bena na shigowa ta rufe kofar itama ta shige bedroom din.


Wanka sukai dukkaninsu sukai Shirin bacci take Zeenah ta fada gado se bacci Dayake ta rigata wanka.


Sallah ta fara ita kafin tayi wankan ta fito ta saka Riga da wando na bacci masu santsi gajeru ta hau gadon itama zata kashe wuta ta duba Bata shigo da ruwa ba Dan tana Shan ruwan dare sumtimes Dan haka ta sauko da qafafunta ta miqe tareda zira slippers ta fito ta nufi cikin Dan duhu sbd wutan koina a kashe lokacin 12 har ta Dan wuce da mintina.


Tana shiga kitchen ta Bude fridge ta dauko Daya jikinta na qwari sbd baccin Datake ji
Tana rufewa taji motsi bayanta ta juyo da Dan sauri daidai isowansa gurin fridge din Shima ahankali yazo yana buqatan ruwan sanyin a kusa dashi Incase.


Da qarfi kirjinta ya doka da ganinsa sbd Bata taba tinanin Ganin nasa ba a lokacin gashi jikinsa ba kaya daga shi sai towel a qugunsa da kaman be dauru ba ana tabawa zai kunce da alama shi sai a time din yayi wanka.


Dauke kallanta tayi ahankali daga Kansa sbd haske da kyan fatarsa tareda murdewan jikinsa da kullum yana geamin ya yasa bugun zuciyarta Dan tsananta.


Fuskarsa a Dan kame ya dakata Bai iso fridge din ba a hankali yace ta dauko masa biyu ta kawo masa.


Juyawa yayi ya fita
Tana ganin Hakan ta dauko ruwan da sauri ta biyo bayansa Dan Basa basai taje har cikin bedroom dinsa ta Kai masa Dan haka da sauri sauri ta biyo bayansa ta cimmasa a Palo Yana daf da shigewa Jin tahowarta bayansa ya sakashi juyowa ahankali daidai ta iso Bata saka ran juyowan tasa ba kirjinsu yayi Wani irin haduwan da yasakashi loosing balance nasa a take yayi saurin dafa bango da ita a kirjinsa Dan haka itace jikin bangon shikuma yana Dafe da bangon har lokacin kirjinsu a manne.


Matse sosai yake da ita a bangon Yana kokarin dawo da balance dinsu itama Kuma tsananta bugawa kirjinta yayi har yanajin sama da qasan da Kirjinta sukeyi kan nasa kirjin.


Kasa motsi sukai dukkaninsu ta fizgo Wani boyayyan numfashinta dake Neman barin kirjinta da qarfi Wanda Hakan ya sakata kirjinta da babu bra yimasa Wani irin suka take tsikar jikinsa suka miqe ba zato ya Bude idanuwansa dasukai Wani iri take ya zuba mata tareda sake manneta da jikin bangon daqyar ya iya Bude baki cikin Wani Mayen sauti mara tashi ko kadan ya Dora bakinsa kan kunnenta Saida numfashinsa me dumi ya fara saukan mata ya furta


"Stop"


Saukan lips nasa kan fatan kunnenta da saukan muryarsa cikin tareda dumin numfashinsa ya sakata rikicewa gabaki Daya kirjinta ya sake Wani mummunan bugawan ta sake saka tsinin kirjinta suka sokesa
Rintse idanuwansa yayi da qarfi tareda soka Kansa cikin wuyanta yayiwa qamshinta wata irin shaqa hannuwansa na zagaye qugunta take ta saki duka ruwan hannunta tana qanqame towel dinsa dataji Yana Neman kuncewa ya Fadi.
##MAMUH#
#DBENA
#TOO HOT
#MARRIAGE
#SAFNAH B BULAMA
[9/1, 1:04 PM] MG: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
58
Saukan hannunta kan towel dinsa ya sakashi dube idanuwansa dasukai nauyi ahankali yayi mata Wani irin Kallon kasala da Yana sake saka Kansa wuyanta ahankali fatar fuskansa na gogan fatan wuyanta zuwa kirjinta tana sake qanqamesa daga qugu.


Qamshinta Dayake shaqa ya saka idanuwansa qara nauyi Yana son janye kirjinta daga nasa dake Neman kashesa da zafin jiki Amma ya kasa motsawa sbd idan ya motsa a lakacin shi Kansa yasan towel din nasa zai iya kuncewa.


Yanda fuskansa ke gogan wuyanta ya saka jikinta mutuwa tayi shiru tsigan jikinta na tashi itama qamshinsa gabaki Daya na Jo Malone body

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login