Showing 99001 words to 102000 words out of 192750 words

Chapter 34 - ZAFIN KAI COMPELET BOOK BY Mamuhgee.txt

12 Dec 2024

7155

rashin kyautawan fitowa dasu sbd ta manta dashi a gidan.


Dan Tari ta saki tana zaunawa ahankali ta dauki cup din Daya ajiye takai bakinta tafara Shan tea din tana Amsa maganar Zeenah sama Sama.


Zeenah da Batasan meya faruba tea din ta hado tazo ta zauna tana daga wayarta ta saka kiransa sukai magana ya sanar mata ya fita yanada meeting me mahimmanci sosai da wasu abokan business nasa Wanda Bana kaantes ba.


Tana sauraron wayar da Zeenah keyi dashi Yana magana a natse ba Wani sauri ko rawan murya bare hayaniya.


Zeenah kuwa suna gamawa tace yau ita bazata fita ba zata Jira gida tayi musu girki tinda ita Bena yau dole zata fita akwai itama aikin dazata leqa.


Suna gamawa sukai wanka kowannensu ya shirya suka fito tare Zeenah zata ajiyeta ta tafi da motan siyayyan abubuwan da zata buqata na girkin.




Zeenah kasuwa ta wuce bayan ta ajiye Bena tayi siyayyan fresh veggies da dasu frozen chicken da duk Abinda take buqata duk a supermarket ta dawo gida.


Koda ta dawo me musu Aiki kullum tazo harta gyake koina harma da dakin DD da babu Wanda ya taba shiga sai ranar aka gyarasa gashi yafi dakinsu girma sosai sbd yanason daki me space sosai bama ya iya zama a dakin da babu space me yawa.


Koina na gidan qamshi yakeyi Dan haka ta dakatar da Sima din ta Tayata aikin girkin.






****Se 6 na yamma Bena ta dawo har lokacin Zeenah ce kawai a gidan tana daki tana karatu a laptop.


Ko zama Bena batayiba Saida tai sallan laasar kafin ta tube tanason tayi wanka Amma ta bari sai after magrib.


Abinci ta fito taci kadan sbd yajin da yayi sosai itama Kuma Bata son yaji sosai.


Pepsi Tasha Daya ta qarasa koshi ta dawo dakin lokacin ake sallan magrib.
Suna gama sallah suka bige da waya da Umme da Amnah.




Shikuwa sai dayayi sallan magrib ya dawo
Kai tsaye bedroom dinsa ya nufa wanka yafara ya samu nutsuwa sosai yajisa fresh kafin ya kunna wayarsa Daya kashe Shima ummen yafara kira yayi magana da Amnah yakira dd babba ma sukai magana kafin yayi sallan ishai
Ya sake magana da Naseer dake hotel kafin ya kashe wayarsa gaba daya ya fito sanye da gajeran Nike da armless da slippers na Salvatore F ya fito fatan jikinsa kaman baby ya nufi dining daidai Zeenah na fitowa da farin ciki ta qarasa ta gurinsa tana masa sannu da zuwa sbd Basu hadun ba tin jiyan dayazo sai alokacin.


Tare suka qarasa dining da kanta ta zuba masa abinci ta dauko masa ruwa mara sanyi Takoma Palo ta zauna tana daukan laptop din Bena dake Palon zata duba Wani Abu.


Abincin ya kalla yaga brown vegetable basmati ce da qananun Naman Kaza aciki,
Ya Dan sake kallan abincin sbd bayason abinci me nauyi sosai da dare Shima Amma haka ya Dan daure yaci sbd Yana Jin yunwa.


Emilian spoon din dake aje ya dauka ahankali yasaka yafara cin abincin a natse.


Da farko baiji yajin sosai ba Saida yaci gaba daci yaji Wani azababben yajin daya sakasa sarkewa gumi na tsatsafo masa a farar fatarsa.


Ruwa ya dauka ya Sha fuskarsa na yin ja take sbd masifar da Bai taba ji ba a rayuwarsa sbd tinda Allah ya haliccesa Bai taba cin yaji haka ba
Baima San yaya masifansa yake ba.


Ruwan Daya Sha ya qarasa tsananta masa yajin dayakeyi har cikin kunnuwansa da cikin Kansa take Wani irin Tari ya sarkesa Yana Jin Kansa na Neman juyewa.


Ganin mummunan halinda ya shiga Yana Tari ya saka Zeenah tasowa da sauri ta dauki ruwa ta miqa masa ya dakatar da ita da hannuwansa Yana sake Tari idanuwansa na sauyawa gabaki Daya,


Idan akace asalin Dan gidan hutu ajebo to DD shine kalman in form of mutum,
Baisan yaji ba,Bai taba cinsa ba,baisan gigicewansa ba tinda duka abincinsa simple abubuwa marasa yaji yakeci,
gidansu Sam baa cin yaji bare shi Da Rabin rayuwarsa a turai ne
Dan haka gabaki Daya ya birkice musu Yana Neman rasa numfashinsa.


Hankali tashe Zeenah ta dauko masa ruwan sanyi tana miqa masa Amma Sam bazai iya Sha ba.


Abinci Ta dauki spoon taci kadan take ta saki ihu itama tana Shan ruwa da sauri ta kallesa tana rasa ya zatayi sbd Sima mayya dai kashesa zatai da yajin ta zuba a abincin Wanda Zeenah Bataci ba sai lokacin,
Batasan Hakan yake ba da bama zata aje masa ba sbd sanin ko kashesa wannan yajin zai iya Yi.


Ihun Kiran sunansa da Zeenah keyi yasaka Bena fito da sauri Bata tsaya saka sauran bottoms na saman guntuwan rigarta ta bacci ba Datake sakawa.


Cikeda mamaki da tsoro take kallansu
Idanuwansa da fuskarsa sunyi jajir ya sauya take sbd azaban da be taba ji ba.


Jikin Zeenah na rawa ta sake dauko ruwa me sanyi sosai ta zuba a cup zata Basa Bena data fahimci meyake kokarin illatasa ta nufi kitchen da sauri itama hannuwanta na rawa ta dauko Nutella ta Bude Bata tsaya saka spoon ba tsaban rudewa ta saka finger dinta Daya ta lakato me yawa ta nufi bakinsa dashi ta saka masa Bai Bai gama shigewa bakinsa ba ya riqe hannun nata ya janyota gabaki Daya ta fado Kansa ya Dora bakinsa da Nutella din akan bakinta ya hade Yana tsotsan Nutella din idanuwansa a rufe jikinsa na Dan rawan masifan Dayake Neman yanka harshensa.
##MAMUH#
#HOT
#DBENA
#ROMANCE
[8/30, 9:48 AM] MG: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
55
A kan qafafunsa ya zaunar da ita hannunsa Daya na zagayo qugunta hannun Daya na riqe da kanta ya ringa tsotsan Nutella din tareda yawun bakinta Dan shi tsaban azaba bayajin ma yanada sauran yawun bakin dazai iya Shan Nutella din.


A yanda yake Janyo yawunta Yana juyasu da harshensa tareda Nutella din acikin bakinsu su dukan yasaka Bena samun attack sbd mutuwan zaune tayi a jikin nasa tareda rufe idanuwanta tana Neman somewa.


Halinda take ciki Bai bari ta qarar da feeling ko Daya ba na yanayin data samu kanta ayau hannun namiji Rana ta farko a rayuwarta.


Shi Kansa idanuwansa a rufe suke Yana sake Dan matseta jikinsa da hannun dake zagayen da ita ahankali,


Tsantsin kayan baccin jikinta da yanda yake matse da ita da lallaunsa hannunsa ya saka rigarta janyewa daga qasa cikinta da cibiyanta na bayyana batareda dukkaninsu sun saniba.


Baitaba sanin azaban yaji haka yake ba a rayuwansa,
Bai taba sanin yaji Yana kisa ba sai a ranar sbd shi dai yasan zaa iya kashesa da yaji Kai tsaye.


Ahankali tafin hannunsa ya sauka kan fatar cikinta Daya bayyana a take taja Wani wahalallan numfashin Daya sake sumar da ita jikinsa tana sake rintse idanuwanta,
Shi kuwa hannun nasa na sauka fatanta sake zagayeta yayi da duka hannuwansa Yana qarasa shanye Abinda yake Sha kafin ya sauke numfashi ahankali tareda zare harshensa daga cikin bakinta Yana sake sauke numfashi Mara qarfi tukuna batareda ya saketa ba ya Bude idanuwansa dasukai jajir ahankali ya Kalli idanuwanta dake rintse gam Wanda data Bude idanuwanta ta ga idanuwansa a wannan halin zata iya somewan gasken wannan Karan Dan haka kaman ta sani ta kasa Bude idanuwanta saima sake rintse su tayi jikinta na rawa hakama kirjinta na Hawa da saukan bugawar da zuciyanta keyi sosai.


Iskan bakinsa dayafi komai azabtar dashi ya sakar mata a fuska ahankali Wanda ya sakata sake rintse idanuwanta ahankali tana qanqame rigarsa.


Shi Kansa bai gama dawowa cikin cikakken hayyacinsa ba idanuwansa ya Dan rintse ya sake budewa har lokacin fuskarsu na hade duk da ya saki bakinta Amma lips nasu suna shafan juna shiyasa direct numfashin juna sike shaqa babu Wanda ya motsa.


Jin shiru yasaka Bena hadiye Wani yawu zuwa maqoshinta daqyar kafin ta Bude idanuwanta dasuka Dan sauya itama
Acikin idanuwansa dasukai ja nata idanuwan suka fada sbd fuskansu dake hade.


Kokarin Maida idanuwanta ta sake rufewa tayi Amma motsinta ya saka lips dinsu sake shafan juna atake a ja numfashi daqyar kirjinta yayi sama ya qara mannuwa da nasa take ya rintse idanuwansa ahankali tareda janye fuskarsa daga tata ahankali Yana Bude idanuwa ya janye hannuwansa dake zagaye da ita manne jikinsa.


Kafin yayi kokarin miqar da ita daga jikinsa ta rigasa fizgo kuzarinta ta miqe da sauri hannuwanta dake Dan rawa sune rufe gaban rigarta da sauran bottoms din suka qarasa cirewa Allah yasa rigar Bata janye daga saman ba iya cikinta da cibiyanta kawai ya Gani ya dauke Kai tareda miqewa yabar gurin Kai tsaye batareda ya waiwayo ba.


Yana barin gurin qafafuwanta suka sake ta kasa tsayuwa ta dafa dining din rawar hannuwanta na qaruwa.


Rintse idanuwanta tayi tana kokarin daidaito numfashinta Dayake Neman fasa mata kirji ta ringa danne numfashin har Saida bugun zuciyarta ya dan dawo daidai.


Itama bedroom dinsu ta nufa da Dan sauri tana Hana qafafunta sanyi.


Tana shiga dakin ta rufe kofar tana juyowa sukai Ido biyu da Zeenah dake zaune tana da waya a hannunta da alama wayar takeson Yi kokuma ta gama.


Dauke Kai tayi tana saka botiran rigarta tareda kokarin daidaita kanta ta fuske zata shige toilet Zeenah da ko ajikinta Abinda tagani din Kuma tana ganin Hakan ta tahowarta daki ta basu guri sbd ganin kalan french kiss da Bata taba ganiba tace


"Kiyi wanka kawai daga can sbd Nutella din is All over your face."


Kasa tsayawa tayi ta fada toilet din tareda rufewa ta jingina jikin kofa tana Dafe goshinta.


Mirror ta kalla taga yanda zagayen bakinta yayi kasa kasa da Nutella din hakama Shima ya Dan San mata yajin bakinsa a nata bakin sbd tana Dan Jin yajin kadan.


Batayi wankan ba sbd fitowanta kenan ta fita palon Dan haka fuskarta kawai ta wanke da kyau ta fito bayan ta goge fuskar da towel qarami me taushi Bata iya tsayawa ko fira da Zeenah ba ta Haye gado ta Kwanta ta shige bargo tareda rufe idanuwanta tana yiwa Zeenah din saida safe.


Zeenah kuwa Sam ita Bata Wani damu ko Jin kunyar Hakan ha tinda ai Hakan is more than okay ma garesu sbd su din maaurata ne,
Ita Bata San suna buqatan Hakan ba sai yanzu data wannan incident din ya faru sai take tinawa da aure ne fa akan Bena din na yayanta gashi Young billionaire me class da zafin Kai da yawa mata shine namiji Dari bisa dari dasuke buqatan samu Dan haka gaskia ya kamata Bena tayiwa kanta fighting matsayinta tin kan baturiyar matarsa Daya ta dawo gata jininsu ce bazasu gujeta ba duk yanda suke tsananin kaunar Bena din kuwa.




Washe gari tinda safe Zeenah ta fice gidan lokacin Bena Bata farka ba haka Shima Bai fito ba.


Sai 9:30 Bena ta farka tayo brush ta fito tana kokarin saka kira a wayanta ta nufi kitchen ta dafa white Instant noodles da half done eggs guda biyu tana zaunawa Yana fitowa cikin free size kayan baccinsa farare Kal masu santsi gaban rigar a Bude gabaki Daya fatan cikinsa Wani daukan Ido takeyi sbd lafiya,hutu da murdewan Naman cikinsa maana abs nasa.


Ruwan tea din Dayake bakinta ta hadiye ahankali tareda Dan dauke idanuwanta daga tinkaro dining din da yayi.


Yana qarasowa fuskarsa babu walwala ko sakewa ya Dan kalleta kadan ya Bude baki a natse yace Yana buqatan coffee kawai.


Juyawa yayi ba ya koma Palo kan kejeran Datake ta zamansa ce duk Yana gidan ya zauna a natse tareda crossing legs a hankali kafin ya dauki remote ya kunna TV yayi qasa da murya sosai Dan bayason murya sosai ko a qasa qasan Yana Dan ji,.aje remote din yayi ya dauki wayarsa ya Nemo numbern Naseer ya kirasa
Cikin tausasshiyar murya mara qarfi sosai Kai tsaye Yana dauka yace


"Ina buqatan doctor I think papper ya tabamin kirji ko zuciya,just find a doctor Dayake kusa ka kawomin."


Kashe wayan yayi ya ajiye daidai lokacin ta qaraso dauke da coffee din ta ajiye masa kan table tareda Dan kallansa kadan tace


"Good morning"


Juyowa yayi ya zuba mata idanuwansa da sukai laushi da rashin kuzari sbd zazzabin Daya kwana dashi na azaban jiyan.


Dauke kallan nasa yayi akanta ahankali kafin ya amsa cikin qaramin sautin da nutsuwa tukuna ya dauki cup din yakai bakinsa cikin nutsuwa.


Juyawa tayi tabar gurin itama ta koma dining acan ta zauna tana qarasa Shan tea dinta sbd Instant Noodles din Kuma ta fita ranta bazata iya ci ba ya huce.


Tattara dining din tayi Takoma kitchen tana ajiye kayan Sima na knocking.


Fitowa tayi tana kallan time tasan Sima dince Dan haka Kai tsaye ta Bude mata ta shigo.


Tana ganin DD a palon tayi saurin yin qasa da Kai tana masa barka da safiya ta silale ta wuce kitchen.


Bena Kuma cup Daya gama dashi ta dauka ta Kai kitchen Takoma daki ta shiga wanka sbd yau itama zata fita.


Tana fitowa wanka ta shirya karfe goma Sha Daya da mintina ta fito cikin classy Alexander McQueen long pencil skirt golden yellow da farar laced shiffon long sleeve cikinta a shafe kaman wadda batacin abinci hakama shape dinta daidai yafito sosai a shigar bawai matsewaba,
Silk scarf ne a kanta me Dan girma ta zagaye kanta dashi daga handbag sai wayarta a hannunta ta fito key din motan ma Yana Palo tana fitowa ta dauka ta fice sbd baya palon ma ya shige Shima sbd motsin Sima me Aiki Yana damunsa.


Bayan fitarta a harabar gidan ta hadu da Naseer zai shigo kasa kallan juna sukai sbd yanda tasa zuciyar ke bugawa da sonta har lokacin ita Kuma batasan metakeji ba Amma dai bazata iya kallansa ba sbd tinawa da kalman so ya taba shiga tsakaninsa da kanta.
Buga mota tayi ta fice daga gidan gabaki Daya tana saukar da numfashi.




Daga gurin aikinta karfe 5 na yamma ta baro ta biya ta dauki Zeenah daga Nan suka wuce shopping Wanda kusan Zeenah ce duk tayi sayayya ita Bata buqatan komai kawai pyjamas ta sake Dan Siyawa kanta da Amnah sai undies da Bata gajiya da siyansu designers masu shegiyan tsada.


Sai gab da magrib suka dawo gida Koda suka shigo Yana Palo zaune cikin black Armani's marasa nauyi Yana waya a hankali har lokacin Bai dawo daidainsa ba Dan ciwon ciki Kuma yajin jiya ya sakar masa Dan haka wunin ranar koina ma Bai fita ba Yana gidan.


Itace ta fara gaidasa cikin sanyi da nutsuwa kafin ta wuce ciki batareda taji ya amsaba sbd muryansa da bayason dagawa.


Zeenah kuwa zaunawa tayi gefensa tana gaidasa cikin kulawa da tambayan jikinsa.


Idanuwansa masu haske ya Dan waiwayo ya zuba mata kafin ya dauke Kai cikin nutsuwan harshe ya amsa mata Yana cewa


"A wannan time kuke dawowa from work normally or...."


Fasa qarasawa yayi kawai sbd baimasan meye dalilin tambayar tasa ba.


Itama Zeenah data so fahimtar tambayar dabai qarasa din ba sai tace


"Muna buqatan abubuwa da Dan yawa shine muka biya muka Siya bayan munbar office."


Bai kalleta ba ya gyada Kai ahankali kawai.


Miqewa tayi ta nufi bedroom din itama ta shige lokacin har Bena ta tube tashige toilet.


Tana fitowa daga wanka sallar magrib tayi ta fito zuwa kitchen sanye da pencil jean Daya lafe a siraran cinyoyinta da hip nata hakama rigar jikinta White vest ce Kuma Bata Dan haka bra din jikinta ta zama strapless bra.


Abincin da Sima tayi ta jera a dining ta fara budewa taga fried spaghetti da veggies,
Daga qamshinta kawai ta tabbatarda zatayi yaji Dan haka kadan ta saka fork ta Dan diba kadan takai bakinta taci.


Ajiyewa tayi tareda daukan ruwan dake kan dining din ta Bude Tasha tana satar kallan inda yake taga ko waiwayowa baiyiba.


Ajiyar zuciya ta sauke tareda kwashe kayan tayi kitchen dasu sbd itama bazata bari yaci abincin ba sbd akwai yaji sosai yauma.


ZAFIN KAI Na kudine akwai regular akwai vip
09033181070
#MAMUH#
#HOT
#DBENA
#ROMANCE
[8/31, 9:28 AM] MG: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
56
Simple chicken macaroni salad ta hada musu da zallan pineapples drink mara sanyi sosai sbd dukkaninsu babu me son Abu me sanyi sosai.


Jerawa tayi a dining ta iso palon cikin nutsuwa ta sanar masa
Juyowa yayi ya Dan kalleta kafin ya saukar da idanuwansa kan dagayen cinyoyinta da jeans din ya lafe.


Dauke idanuwansa yayi tareda Dan kallan time ya Bude baki a hankali yace


"Bana buqatan abinci irin na jiyan"


Numfashi ta Dan sauke ahankali tareda kauke Kai daga kallansa a natse itama tace


"Light Abinda zaka iya ci ne"


Gyada Kai yayi batareda ya juyo ya sake kallanta ba.


Juyawa tayi ta bar gurin zata koma kitchen Zeenah ta fito tareda Janta suka nufi dining din dole ta zauna
Shima tasowa yayi a hankali ya zauna tareda kallan Bena din da kasalallun idanuwansa
kaman mara gaskia haka Ta taso ta zuba masa ta koma ta zauna itama ta zuba suka fara a natse babu me magana.


Kadan yaci yasha drink din sosai kafin ya dauki tissue ya goge bakinsa ya miqe yabar dining din.


Kai tsaye bedroom dinsa ya nufa
Suma suna gamawa suka tattara gurin suka shige.


Sallar ishai tai kafin tayi brush tai Shirin bacci ta kwanta.


Da daddare ciwon ciki sosai ya hanasa bacci bayan zufa babu Abinda yake hadawa duk da ba kaya jikinsa dogon silk wandon pyjamas dinsa ne kawai jikin nasa.


Sosai yakejin azaban ciwon cikin Dan haka ya qarawa AC din dakin qarfi tareda tashi zaune ya jingina Kansa jikin kan gado Yana rufe idanuwansa da suka sauya sbd ciwo a hankali.


Ruwan sanyi yakejin Yana buqata Dan Sha su shiga cikinsa ko zai rage zafin Dayake ji cikinsa.


Hannu yakai ahankali ya dauko wayarsa dake kashe bedside dinsa tareda kunna wutan gefen gadansa.


Kunna wayan yayi Bai tsaya duba time ba ya saka Kiran Zeenah sbd shi ya Saba komai Yi masa akeyi ruwan ba bayajin zai iya miqewa yaje ya dauko gefen cikinsa ya riqe sosai.


Bena ce tafara Jin ringing wayar cikin bacci Dan haka ta Dan Bude idanuwanta dake cike da bacci tafara lalaban wayar ta dago ta duba sunan waye ke kira sbd ta dauka wayarta ce ma.


D" taga an rubuta Kai tsaye ta Gane waye Dan haka baccin ya Dan saketa ta miqa hannunta Daya tana taba Zeenah din wadda Baa tadata idan tana bacci Sam Bata san Hakan.


Ganin Zeenah din taqi tashi ya saka Wani Kiran na Kuma shigowa ta daga wayar a hankali tareda cewa "hello" cikin muryan bacci.


Bai tsaya Jin Ba Zeenah din bace Kai tsaye da muryarsa Shima da bata fita yace


"Ina buqatan cold water yanzu"


Yanada fada ya kashe wayan tareda ajewa Yana rintse Ido zufansa na qaruwa.


Bena kuwa Ras ta Bude idanuwanta gabanta na faduwan.


Tashi tayi zaune ahankali tana kallan wayar hannunta kaman Bata Gane Abinda ya fada ba sbd qasa qasan muryansa Amma Kuma bazatai karyaba taji Abinda ya fada

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login