Showing 108001 words to 111000 words out of 192750 words

Chapter 37 - ZAFIN KAI COMPELET BOOK BY Mamuhgee.txt

12 Dec 2024

7137

market Abba hamisu plaza block A shop no 8
or dorayi sabon titi before gidan man b i
Wa.me/+2348067376035




*****
Dukkaninsu ranar sai yamma suka dawo kowa a gajiye Dan haka ordern abinci sukai Koda aka kawo sunyi wanka da salloli abincin kawai sukaci Bena ta fara Wani aikin a laptop Zeenah ma kusan aikin tafara duk da Rabi wayoyi ne takeyi.


Sai dare sosai Bena ta gama taje ta kwanta kanta na tsananin ciwo.


Washe gari da kanta taje airport ta dauko Fahad daga airport Dayake sun latti Kai tsaye gurin meeting din suka wuce.


Duk yanda Bena take tinanin lamarin ya wuce Nan sbd Manyan mutane ne da iyakacinta jinsu da ganinsu a media.


Su uku ne kawai mata Kuma ita Daya ce yarinya Mai sauran lokaci Amma sauran matan duka manyan mata ne da shekarunsu suka Dan ja sai wadda batai shekarun nasu ba ita Kuma zata girmeta sosai.
Hakama a kawai fararen fata har guda hudu Suma Wanda dagani daga wata qasar suka zo.


Asalin turanci da wayewa tareda zurfafa a harkan businesses da juya kudi ne yake tashi a gurin.


Da farko da zatai presenting nata bayanin rudewa taso Yi Amma qarfin gwiwan da dd babba yake Bata kullum tareda Dora duka hopes dinsa a kanta akan cewan zata zamewa business din kaante lucky charm inshallah akan sa'a da nasarorinsu zata ninka musu yake fata.


Hakan ne ya sakata sauke numfashi tareda ajiyan zuciya cikin nutsuwa da nata fresh ilimin da fasaha ta fara Koro bayanai da nata turancin da itama ta qware cikinsa.


Kai tsaye suka fara accepting ideas nata tareda sabuwar fasahar data kawo harma da fashewan wata sabuwar hanyar da kusan zasuce ta course din datai ne Kuma tabbas kwalliya ta biya kudin sabulu.


Wannan shine Karo na uku a rayuwar Kaantes da suka samu nasarar janyo manyan Tycoons, billionaires da Wainda baa taba tsammani ba shigo da mutum 9 a lokaci daya su zama shareholders a cikin kaantes.


Dd babba ne da Kansa mutum na farko Daya taba Hakan sai DD da Kansa Daya shigo musu da wasu shareholders daga nasa business din sai Kuma Bena yanzu,
Bilal na ya taba wannan nasarar Amma nasa mutum 8 ne Dan haka ana gama Fahad ne yayi presenting sauran bayanin in documents aka qarasa meeting din suka fito manyan motaci da securities sai tsaro na musamman ake Bawa gurin har kowannensu ya fice daga gurin.


Lokacinda dd babba ya fara samun labarin daga media ne da Akai musu hotuna bayan fitowarsu tini aka fara yada zancen na kaantes sun sake samun damar qwamushe manyan Tycoons a matsayin yan saka hannun jarinsu.


Farin ciki yayi mara sosai hakama dad kaante farin ciki ne fal a ransa sbd dole zaa ce matar 'dansa ce.


Dinner sukai having ita da Fahad da Zeenah ta farin cikin a Wani muhaukacin luxury restaurant suna can dai 12 Saura suka baro suka ajiye Fahad tsadaddan hotel din Daya sauka suka wuce gida.


Wanka kawai Bena tayi Dayake sunyi sallah ta fada gado ko wayarta Bata iya kunnawa ba tin bayan wayarta da dd babba da Annenta dasuka gaisa.


Washe gari Bata iya fita ba sbd bacci da gajiyan dararrakun datai ta Hana kanta bacci sbd wannan aikin Dan haka Zeenah ce taje takai Fahad airport daga can ta wuce Aiki.


Itama sai 11 ta farka tayi breakfast ta shirya ta wuce aikin.


Bayan komawar Fahad take akai celebrating wanann babban sabuwar nasarar data qara daga daraja da girma tareda habbakar arzikin kaantes da bayama faduwa,
Bena Bata Nan Amma haka aka ringa kiranta anai mata barka tareda mata adduar fatan nasara me dorewa.


Dawowanta kawai ake Jira ta fara aikinta me matsayi babba a Kaantes
Shi Kansa Fahad yanajin Dadin Aiki da ita sosai hakama dad kaante yanzu yasan zai samu Wanda zai maye masa gurbin Bilal a bangaren Aiki Mai cikeda nasarori sbd tin bayan rasuwar Bilal basu samu Wanda ya cike musu gurbinsa ba a fagen nasara shi DD Yana nasa business din daban baya cikin family business bare ya kawo musu tarin nasa nasarorin da Allah yayi masa baiwa.


******Bayan sati uku da wannan samun Abinda akeso din suka kammala service nasu Akai duk abubuwan da zaayi suka fara Shirin dawowa.


Yau gabaki Daya baa gida suka wuni ba sai yamma suka dawo kowannensu a gajiye Dan haka wanka sukai da sallah sai alokacin sukaji sun sake.


Snacks sukaci sbd ba sosai suke Jin yunwa ba
Suna zaune a Palo suna fira suna taba wayoyinsu wayan video call din Amnah ya shigo wayan Bena.


Cikin farin ciki ta dauka fuskarta cike da murmushi saidai cak ta tsaya tana Neman rudewa da Abinda tayi niyar fada sbd ganin Amnah din jikin daddynta sanye da jersey pyjamas na Ralph Lauren navy blue fuskansa da skin dinsa sun qara haske sosai kaman Wanda tinda yakoma baya fita hutawa yakeyi,
Qafansa Daya na kan Daya Amnah na jikinsa kwance riqe da iPad din.


Neman gagara iya magana takeyi Amma Amnah ta kira sunanta tana cewa


"Mummy bakice komai ba fa"


Dan numfashi ta sauke a boye tareda Dan sake murmushi Mai sanyi tana cewa


"Kema baki gaida mummy ba shiyasa"


Dariya Amnah din tayi irin ta Yara tace


"Ok ok sorry" datse Kiran tayi ta sake saka Wani Bena din na dauka tace


"Mummy Ina Wuni?"


Wani murmushin me sanyi Bena ta sake tana amsawa cikin kulawa zatai magana Amnah ta Riga da cewa


"Mummy kema baki gaida Daddy ba"


Tsit Bena tayi tareda kasa kallan screen din wayarta sbd Jin mayun idanuwansa akanta duk da Bai furta komaiba tinda Kiran na Amnah da mummynta ne babu shigarsa aciki.


Maganar Amnah din ta sakasa juyowa ya Kalli Bena din itama Jin idanuwansa ya sakata Dan hadiye numfashi ahankali ta dago ta kallesa kadan cikin sanyi tace


"Ina wuni?barka da dare"


Ahankali ya Bude baki ya amsa yana Dan dauke idanuwansa daga kan iPad din sbd singlet ce jikin Bena din blush pink ta kwanta jikinta sbd taushi da tsadanta Kuma da alama babu bra jikinta iya singlet dince kawai sbd yanda kirjinta shape dinsu yake nunawa sosai sabanin idan akwai bra bazasu nuna sosai din ba.


Ita kanta batai tsammanin Yana tareda Amnah ba da bazata daga Kiran ba saita sakawa jikinta Wani abin.


Surutu Amnah ke mata tana amsawa a Dan kunyace sama sama sbd duk ta motsa babu Abinda yake sake bayyana kaman shape din kirjinta dasuke sakasa dauke nasa idanuwan Shima.


Cikin surutun Amnah tace


"Mummy kina dawowa karki koma gida gurinsu dd babba da Umme ki dawo Nan ki zauna damu da daddy na kullum mu zauna tare."


Shiru Bena tayi tareda dagowa kadan ta Dan kallesa shi kuwa idanuwansa ya zuba mata Yana Jin Abinda Amnah ta fada Yana jiran amsarta.


"Kinji mummy?"


Murmushi ta sake tace


"Akwai school gobe ki kwanta idan nadawo sai muyi maganar,
Ki kula kinji Rabin ran mummynta,
I love you, goodnight."


Dagowa tayi ta kallesa idanuwansa na kanta har lokacin Yana sake rudar da ita a hankali ta Bude baki ta furta "goodnight" ta kashe wayar ta ajiye tana sauke ajiyar zuciya a hankali.


Tana kashe wayar Wani murmushin gefen baki ya sake ahankali sbd ganin yanda ta rude da maganar Amnah.


Shi Kansa baisan Amnah zata furta Hakan ba Dan haka zancen ya Dan sakashi murmushin ganin tashin hankalin da zancen kawai ya sakata,
Daga lokacin Amnah zata buqaci Hakan daga garesa babu Wanda ya Isa ya hanasa Bata Abinda takeson Dan haka kawai Mummyn nata tayi fatan kada Angel dinsa tace masa tanason su dawo gidansa a ranar ko kwana daya Bena ba zatai a Lagos ba ko kaantes.


*****Bayan kwana biyu da maganarta da wannan suka tattaro suka dawo gida yayi daidai da saka lokacin bikin Daddyn Amnah din da matarsa wata biyu masu zuwa kaman yanda mahaifiyarta ta buqata Dan samun Daman shirinsu Daya kamacesu.


Bayan dawowarta ta tarar da sabuwar rayuwar Datake jiranta ta daukaka da cigaban da Bata taba tsammata ba,


Dd babba ya zama Wani irin gata da zuciyarta Dan kuwa yanda take jinsa a duniyarta kaf yanzu daga Anne sai Amnah dashi ne wainda takejin zata iya komai akansu hakama bazata iyaba idan babu su din.


Shi Kansa dd babba Bai taba tinanin akwai ranar da zai kaunaci Wani qauna me qarfi ba irin wadda yakewa Bena bayan Dawood a cikin jikokinsa.


Cikin tarin nasara ta karbi babban matsayinta na fara Aiki a Kaantes tareda sabuwar tsadaddiyar motar data saka lissafin Ababa kuncewa Dan haka ya fara birkice mata akan ko kudi kokuma Annenta Takoma inda ta fito.


Zeenah ma ta fara Aiki da babban matsayi ita Kuma a DDs sunan babban kamfanin DD kenan.


Fara aikinta yazo mata da nasarori Dan kuwa Aiki takeyi da gaske cikin qwarewa da wayewa tareda nutsuwa,


Acikin qanqanin lokaci ta qara daga darajar kaantes Dan haka ta tabbata Nasarar kaantes da dd babba yake kiranta.


Dad kaante sosai yake Yaba mata Shima sbd shigewarta kaantes ana samun yanda akeso daman babban burin kaantes su zama sune a sama babu tamkarsu bare Daman babu me ja dasu sai DDs Shima Bada baqin cikin da Company din sbd tamkar nasu ne tinda na DD dinsu ne.


****Tinda ta dawo aka saka lokacin tarewan matarsa Bata bari ko a hanya suna haduwa kullum office take fita tayi busy sosai gidansu ma so biyu Ababa ya bari taga Annenta Shima Sai data Basa 100k a duk kowane ganin.


Amnah tinda aka saka ranar bikin koyaushe cikin rigima take tsakanin iyayen nata gashi ko haduwa Basuyi ba har lokacin bare Wata maganar ma ta shigo.


Bena ta zabi janye kanta da boyewa ne sbd nauyin da zuciyarta bazata iya dauka ba,
Ta sani ita din matar biyan buqatan karban Amnah ce tin farko,
Babu komai ko wata darajan Datake dashi bayan wannan Dan haka barin zuciyarta ta kaita inda be kamata ba wuya zatasha a tsakaninsa da matarsa shiyasa ta zabi janyewa ta fuskanci rayuwarta da aikinta da Allah ya daukakata akansa.


**Daga office Kai tsaye shahararren DDs company ta biya Dan daukan Zeenah su koma gida tare sbd yau driver yakaita Bata fita da mota ba Kuma yanzu Bata buqatan yazo ya dauketa shiyasa takira Bena akan idan ta tashi ta biyo ta dauketa su wuce gida tare.


Suna baro DDs wayar Zeenah tayi ringing tana dubawa taga D dinne Dan haka a tsanake ta dauka.


"Idan ki tashi Aiki kizo ki tafi da Amnah gida kaina na ciwo zan huta"


Kashe wayar yayi ita Kuma ta juyo ta Kalli Bena dake driving tana waya a natse.


Kallan da Zeenah ke mata ya sakata sallama ta kashe wayar tana cewa


"Yaya dai?


D yace na biya na dauki Amnah bayajin Dadi.


Ajiyar zuciya Bena ta sauke ahankali sbd itama Daman tayi kewan 'yarta kwana Biyun Dan haka tayi parking Zeenah datasan gidan nasa ta karbi tuqin zuciyarta na Dan tsinkewa sbd batasan haduwa dashi.


Littafin ZAFIN KAI na kudi ne akwai regular akwai vip pay at 09033181070


#MAMUH#
#DBENA
#SAFNAH
#ABABA
#KAANTES
#ABABAS
#BOOM
[9/2, 10:24 AM] MG: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
61


*_HAMMAK KITCHEN UTENSILS_*


*_INA MAABOTA GAYU DA SON BURGE BAQI DA ME GIDA?_*
*_SHIN KUNSAN HAMMAK KITCHEN UTENSILS SUNA DA QAYATACCIN KAYAN KITCHEN MASU KUDI DA MASU ARHA NA WAJE DANA GIDA NIGERIA_*


*_BA IYA ZUWA SHAGO KADAI KU SIYO BA HARDA AIKAWA SUNAYI KOINA HAKAMA SUNA ADASHEN KAYAN KITCHEN MANYA DA QANANA,MASU SAUKI DA MASU TSADA,NA WAJE DANA GIDA NIGERIA,_*


*_ZAKIYI ZUBINKI A HANKALI KI KWASHI DUK ABINDA KIKESO A AIKA MIKI ABINKI CIKIN SAUKI DA AMANA DAN HAKA SISTERS KARKU BARI AYI BAKU MUN SANI MUN SHEDAR HAMMAK KITCHEN UTENSILS SUNE THE BEST👍_*


@hammakkitchenutensil
Tarauni market Abba hamisu plaza block A shop no 8
or dorayi sabon titi before gidan man b i
Wa.me/+2348067376035






******
Tinda suka kama hanyar zuwa gidan nasa tayi shiru Bata sake magana ba saidai idan Zeenah tayi mata ta Dan amsa ahankali tana Hana zuciyarsa bugawa ba daidaiba.


Tsaro da tsarin anguwar ya saka Bena mamakin wainda suke rayuwa a cikinta,
Main gate na shiga gidajensu DD din sai ka nuna Id card naka anshigar da sunanka,
Sunan kaantes dake qarshen sunayensu ya saka securities fahimtar gidan DD kaante suka zo Dan haka aka Bude musu suka wuce.


Daga ka shigo baka horn har saika fita Dan haka ahankali suke tafiya da motan har suka Isa gate na gidan DD Shima akwai security Daya agurin ya Bude musu gate suka shigo madaidaiciyan harabar gidan sukai parking.


Fitowa Zeenah tayi tana kallan Bena da batai niyar fitowa ba tace


"Waye zai iya rarraso baby Amnah ta yarda ta bar daddynta idan bake din ba,kinsan sarai bazata yarda tabar daddynta ba saida dubaru.


Ajiyan zuciya ta Dan sauke tareda ajiye wayarta cikin motar ta Bude ta ziro qafafunta ta fito tareda rufe motan suka nufi ciki Kai tsaye bugun zuciyarta na Dan qaruwa tareda Jin rashin sakewa.


Gioconda door din shiga main sitting room na gidan suka Bude Kai tsaye suka shigo sbd sanin password dinsa na shiga da Zeenah tayi.


Zeenah din ce a gaba kafin Bena wadda sanyin AC da qamshinsa da babu inda babusa a gidan nasa ya sata Dan lumshe rintse idanuwanta tana budesu ahankali.


Komai na rayuwarsa daban yake tin daga kan inda yake rayuwarsa da yanda yake gudanar da ita,


Palonsa babu Abinda yakeda wata kalan bayan fari milk da gold.


Bayason kaloli a komai shiyasa ko kayansa daga black sai fari sai Kuma navy blue Shima kalan Dan tanada duhu ne.


Baiji shigowansu ba sbd Yana can master bedroom dinsa a kwance Amnah Kuma tana palon cikin bedroom dinsa tana rubuce rubuce da kallan cartoon.


Waya Zeenah ta Ciro ta kirasa tana nufar kitchen dinsa Dan Shan ruwa.


A natse cikin sanyi ya dauka yaji ta iso yace ta dauko Amnah din kawai su wuce.


Har cikin palonsa ta Isa tareda Bena
Amnah na ganinsa ta taso da gudu ta fada jikin mamanta tana Kiran sunanta cikin farin ciki sosai.


Itama sake murmushi tayi cikin farin ciki tana daukanta jikinta tace


"Ohhh I miss my baby so much, please kizo muje gida daukanki nazo Yi"


Zaunar da Mummyn tata tayi ta hau jikinta tana taba dogon hancinta tace


"Aa mummy bazanje ba kema bazaki tafi ba Daddyna bayada lafiya ki zauna mu kula dashi idan ya warke saimu koma gurin su Umme tare,
Aunt Z Takoma ita Daya"


Dariya Zeenah tayi tana Jan hancin Amnah din itama tace


"Amnah din Aunt z ta girma tasan yakamata a kula da daddynta bayada lfy."


Bena kuwa Wani murmushin ta qaqalo tana cewa


"Daddynki bayason hayaniyan kowa shiyasa zamu tafi gidan idan yaji sauki sai akula dashi din,.oya tashi muje gida Umme na jiranki Kuma ga Arabic uncle dinki nata zuwa bakyanan,kinason karatun Arabi naki ya Dena gudu?


Girgiza Kai tayi tana Bata fuska tace


"Banason ya Dena gudu Amma mummy nidai banason Abar Daddy shi Daya dazu yayi Amai fa Kuma Uncle Naseer ya kawo doctor yayi masa allura,
Cikowa idanuwanta sukai da hawaye taci gaba da cewa


"Nidai mummy to ki tsaya anan naje ayimun karatun Arabic Dina yau da gobe saina dawo ke ki tafi"


Shiru Bena tayi tareda matse fuska tace


"Banason Jin kowane magana tashi mu tafi idan na sake Jin maganar Wani ya tafi Wani ya jira I will slap your mouth."


Fashewa Amnah tayi da kuka Wanda ya saka Zeenah janyota jikinta tana kallan Bena tace


"Meye Hakan?
Gaskia ta fada idan har baida lafiya haka sosai kaman yanda ta fada Wani zai tsaya tareda shi gaskia and it has to be you sbd ita almost 5 days Bata gida karatunta Yana rawa.


Kukan Amnah keyi sosai tareda zarewa daga jikin Zeenah tayi hanyar dakin daddynta da gudu ta shige tana qarawa kukanta qarfi.


Numfashi me zafi Bena ta sauke ranta na Dan Baci da yanda suka lalata 'yar tasu Amma Kuma bazasu iya hanata Abinda takeso ba koyaushe daga su iyayenta musamman Daddyn nata har kakanninta su Umme shi dad kaante ma Badan daddynta da baya iya kwana biyu baizo ya tafi da itaba Shima kullum itace abokiyan firarsa idan Yana gida kokuma tana gurin dd babba Shima ta ishesa da surutunta.


Kasa cewa komai Bena tayi ta waiwayo ta Kalli Zeenah wadda itama ita ta kalla tace


"Kinsan bazan shiga bedroom dinsa ba dauko ta right??
Kece matarsa kece Zaki iya shiga so please je ki fito da ita mu tafi inada abin Yi gida da sauri."


Kallan hanyar dakin tayi ta Dan sauke Kai taja numfashi tareda dagowa ta sake kallan Zeenah tace "ko Zaki kira wayansa ne"


Zeenah na ganin Hakan ta miqe ta nufi Kofa zata fice Bena tayi saurin riqota zatai magana suka Jiyo takunsa ahankali tareda Amnah ya fito daga bedroom din zuwa palon.


Zeenah ce ta fara juyowa tana kallansa cikin kulawa tai masa ya jiki kafin ta sake magana ya katsesu da cewan


"Meyake faruwa anan?"
"Amnah na Kuka me ya faru?"


Sai alokacin Bena ta juyo a hankali cikin nutsuwa ta Dan dago ta kallesa daga ita har shi lokaci Daya zuciyoyinsu sukai nauyi ya dauke Kai Yana sake maimaita tambayansa.


Cikin sanyi Bena tace masa "Ina wuni"


Amsawa yayi a gajarce Yana kallan Amnah Dake jikinsa ta lafe yace


"Angel kije gida zanzo gobe na dawo dake,ok??


Maqale kafada tayi tareda sake kwantawa jikinsa cikin kunnensa qasa qasa tace


"Daddy kace mummy ta tsaya anan to"


Idanuwansa ya jefawa Bena wadda tana ganin Hakan tasan me Amnah ta fada ta Maida kallanta kan Amnah zatai magana ya gyadawa Amnah Kai ahankali tareda miqawa Zeenah ita yace "kuje gobe zanzo na tafi da ita."


Bena na ganin Hakan tayi saurin yin gaba zata wuce Amnah tayi saurin juyowa ta Kalli daddynta
Hannu Daya ya saka ya zagayo shafaffen cikin Bena yayo baya da ita ta jingina da kirjinsa.


Wani murmushin Dadi Amnah ta sake suna ficewa tace


"Mummy ki kula da daddy fa kafin nadawo gobe"


Suna ficewa ta Zame da sauri tana waiwayowa ta kallesa tace "zan bisu"


Bai kalleta ba ya juya ya koma bedroom dinsa Yana cewa


"Ki Jira sai goben da Amnah tace"


Da sauri tabi bayansa zatai magana sbd suna wucewa batada yanda zaayi ta fita anguwan sbd securities bazasu bari ba
Bata ankara ba ta bisa har cikin bedroom dinsa tana masa magana suna Kaiwa tsakiyan dakin ya juyo daidai ita Kuma ta zo daf dashi suka tsaya da sauri tana kallan Dan mitsitsin space din Daya rage kirjinsu ya hade.


Shima mayun idanuwansa ya Kai ya Kalli space din Wanda ko fadin batir bazai shiga ba hakama dasun hade din akwai yiyuwan zazzabinsa ya qaru.


Wani siririn yawu ta hadiye tana dago da idanuwanta sama ta kallesa tareda Dan yin baya ahankali ta janye bayan sun shagi numfashin juna.


Juyawa tayi ya fice daga dakin ta koma Palo ya zauna sai alokacin ta Tina da wayarta na mota da handbag dinta Dan haka dai tana tsaka me wuya.


Zaune take shiru a palon daga ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login