Showing 105001 words to 108000 words out of 192750 words

Chapter 36 - ZAFIN KAI COMPELET BOOK BY Mamuhgee.txt

12 Dec 2024

7151

wash dinsa ya cika mata iskar Datake shaqa a tsakiyansa gashi duk numfashinta Daya saiya daga kirjinta ya sake gogan nasa dakyau
Jin Yana Neman rasa Kansa gabaki Daya ya sakashi qarasa zagayota da hannuwansa ya manneta sosai da kirjinsa ta Yana rintse Ido ta yanda bazata ringa numfashi tana gogansa ba zafin jikinsa na tsanantuwa.


Tafin hannunta Daya ta dago ta Dora tsakiyan bayansa zata Zame dayan hannun na qugunsa Dafe da towel din datake tsananin tsoron ya Fadi.


Saukan tafin hannunta bayansa da babu kaya ajiki ya sanyashi qara cusa Kai cikin wuyanta ya sake Bude baki da muryan data sata qanqamesa da duka hannuwanta biyu cikin kunnenta yace


"Don't do that again"


Batasan lokacinda ta lumshe idanuwanta ta ba tana langabar da kanta gefe sbd dayan gefen Dayake shinshina wuyanta zuwa kirjinta idanuwansa a rufe.


Yanda yake shinshinata Yana hada fatarsa da tata yasa dukkaninsu mantawa da su waye su din dakuma inda suke tsaye suna aikin.


Rigarta data yaye hannunsa ya sauka kan cikinta ta ja numfashinta Daya so barinta da qarfi tareda Bude idanuwanta ahankali daidai Shima ya Bude nasa idanuwan suka Kalli juna tayi qasa da nata idanuwan tana shikuma ahankali ya sake Kai bakinsa kunnenta cikin sauti mara fita sosai yace


"Wannan ruwan ya huce Ina buqatan Wanda yafi zama colder"


Yana fadan Hakan ya zare hannunsa daga fatar cikinta ahankali tana rintse idanuwanta sbd yanda yake dauke hannun.


Juyawa tayi da sauri kaman zata Fadi tabar gurin tana Isa kitchen hannuwanta na Dan rawa ta dauko ruwan sanyin sosai ko nata Bata tsaya dauka ba ta fito baya palon Dan haka dakinsa ta Isa Kai tsaye tayi knocking ta shiga baya dakin Yana toilet ta ajiye ruwan da sauri ta fito ta koma dakinsu ta fada toilet itama.


Fuskarta dake Dan tsatsafo gumi ta wanke tana sauke numfashi ahankali ahankali har ta samu ta Dan dawo daidai ta fito jiki ba qwari tahau gadon ta kwanta ruwan ma Bata daukoba hakanan taji ta Dena Jin kishirwan Dan bazata iya sake fita ba.


Ta Dan jima kafin bacci ya dauketa Bata farka ba sai Asuba.


Tare sukai sallah da Zeenah suna gamawa Zeenah ta koma ta kwanta ita Kuma akwai aikin kamfanin kaantes da zatai Wanda Fahad ya tura mata Dan haka shi ta fito Palo ta zauna tahau Yi cikin pink kaya masu Dan kauri sbd sanyi da safa a qafanta.


Har kusan 7 na safe tana Aikin tana Kiran Fahad din a Wani abin.


8:30 Zeenah ta tashi ta fito ganin Bena na aikin ya sakata Yi musu breakfast da kanta gasashen chocolate and coconut bread da fries tayi musu se hot milk tea.


Shima yau yanada meeting na qarshe da zaiyi Dan haka 9 ya fito sanye cikin native wear yau dinma na blue cashmere da wula kaman Wanda yau ne daurin aurensa da matar Dayake so Dan Kansa da raayinsa bana wainda yake aure na umarni da cika burin iyayeba.


Waya takeyi da Fahad Koda ya fito shigar jikinta ta kayan loro Piana ya kalla kaman Amnah Takoma ga tea da Zeenah da miqo mata da chocolate coconut bread takeci ahankali tana cigaba da amsa wayar idanuwanta na kan laptop dake kan qafafunta.


Qamshin Caron poivre Daya fara gauraya palon a hankali ya sakata kasa dagowa tana hadiye tea din bakinta a hankali sbd Jin idanuwansa sun sauka akanta.


Zeenah ce ta washe baki cikin kulawa tayi masa Good morning ya Tako ahankali Yana amsawa.


Bena na ganin ya tinkaro tayi saurin ajiye cup din hannunta ahankali tareda Dan dagowa tana kasa kallansa tace "good morning" ahankali itama.


Yana isowa Bai amsaba cup din data ajiye na tea dinta ya dauka ahankali yakai bakinsa yasha kadan ya sake Sha har so uku kafin ya ajiye ya amsa gaisuwan Shima ahankali ya juya ya fice Zeenah data kasa gasgata Abinda yayi din ta miqe ta biyo bayansa suka fice tare suna magana.


Suna ficewa Bena ta dago ahankali ta zubawa cup din idanuwanta tanajin jikinta na mutuwa takai hannu ahankali ta dauki cup din itama takai bakinta taci gaba da Shan tea din zuciyarta na sanyi.


Koda Zeenah ta dawo Bena har lokacin Bata gama Shan tea din ba sbd gabaki Daya kuzarinta takejin kaman ta rasa.


Zeenah na zuwa taso maganar Abinda DD din yayi Amma Bena ta fuske tana basarwa.


Qarasa aikinta tayi guraren 11 tukuna ta miqe Takoma daki tayi wanka ta kwanta bacci sbd tana buqatansa Kona mintina arbain ne.


Sai Data tashi bacci tayi girkin Rana Takoma tayi sallah tukuna tayi wanka ta fita itama.


Dukkaninsu su ukun kusan lokaci Daya suka dawo Zeenah ce tafara dawowa kafin shi tukuna ita daga baya.


Kowannensu wanka yayi yayi sallar laasar suka fito dining gabaki dayansu suka ci abinci babu Wanda ya iya kallan Wani tsakanin shi da ita har aka gama kowa ya tashi.


Bayan magrib shi da Zeenah suka fita Basu dawo gidan ba sai after 12 lokacin tayi bacci Dan haka Saida safe na tasan time dasuka dawo.


Dayake ya gama Abinda ya kawosa sai ya fara Shirin kowama A Daren ranar da zai tafi ya bawa Zeenah card dinsa Daya suka fita shopping sukaiwa kudi wulaqanci haka yasa akaiwa Amnah siyayyan abubuwan da ma wasu tanadasu sunfi nawa duk baa fara amfani dasu ban.


Bayan sun dawo sunyi wanka sun huta sunci abinci suna gamawa Amnah ta kira daddynta tace sai taga mummynta sunata Kiran wayarta Bata dauka dayake tabar wayar daki.


Dan dagowa yayi da idanuwansa yayiwa Bena dake Jin Abinda Amnah ke fada Kallo Daya itama shi ta saci Kallo daidai time din.


Idanuwansa rudata sukeyi Dan haka ta janye kallanta tareda qarasa shanye ruwan dake glass cup din hannunta ta jiye.


Kallan Daya sake mata ya sata tasowa suka dawo Palo suna zaunawa kan kujera Daya tana kokarin Hana bugawan kirjinta fita sbd Amnah dake kallansu hakama Zeenah.


Qaqalo murmushi tayi cikin kulawa sosai da kauna tace


"Baby me kike Jira bakiyi bacci ba haryanzu? Akwai school gobe fa"


Dariya Amnah tayi tana cewa


"Bazan iya bacci da wuri ba yau sbd murna my daddy is coming back tomorrow, right daddy?


Wani qayataccen murmushin da Bena Bata taba ganinsa yayi ba ya sake a natse
Saura kiris ta kasa dauke kallanta daga Kansa ta samu ta dauke idanuwanta ta maidawa kan Amnah.


Cikin nutsuwa da kulawa hankali kwance yace


"Gobe Inshallah Daddynki ne zai dauko angel dinsa from school."


Tsalle tafara tana murna da cewa


"Daddy na matsu gobe yayi,
Mommy please ki dawo tareda Daddy I miss you both inason na zauna tareda mommy na da Daddy na kaman sauran yara kaman,
Kaji daddy? Please bring mommy with you.


Ahankali ya juyo ya Kalli Bena wadda ta kasa cewa komai.


Kallan Dayake mata ya sakata yar rudewa tana Hana kanta bayyanarda rudewan ta Dan basar ta hanyar kallan Amnah din tace


"Baby ni zan dawo daga baya ba na fada Miki nakusa dawowa ba?"


Bata fuska Amnah tayi tareda marairaicewa tana kallansu su duka biyun idanuwanta na cikowa da hawaye tace


"Ba ance matan daddy na ta dawo yau Nigeria ba naji Umme na waya tana fada nidai Daddy mommy na ce kawai zata dawo gida"


Tsit sukai dukkaninsu harda Zeenah data zauna lokacin
Benazir kuwa hannuwanta ne suka Dan dauki rawa tayi saurin boyewa ahankali kada ya Gani zuciyarta na harbawa da qarfi.


Shi kuwa Bena din ya Dan kalla kafin ya Maida kallansa kan Amnah yace


"Ok Angel je ki kwanta da wuri sbd gobe ki samu karfin yiwa Daddy oyoyo,ok?"


Gyada Kai tayi ahankali tareda kallan Bena tace "goodnight mommy"


Ahankali Bena ta furta "goodnight baby.....Bata qarasa kira ya shigo wayarsa dauke da sunan SBB baro baro ajiki.


Miqewa Bena tayi ahankali tareda barin gurin ta koma dining Dan tattarawa taga Zeenah tini ta gyara komai Dan haka Kai tsaye bedroom dinsu ta wuce batareda ta juyo ba bayan tanajin idanuwansa akanta.


Bai dauki wayar ba tana katsewa Kiran ummensa na shigowa a natse ya dauka cikin nutsuwa yace


"Hello Umme barka da dare"


"Barka" ta amsa tareda cewa


"Safnah ta sauka a Lagos yau itama gobe zata qarasa porthacort inaga yakamata ka wuce can daga Nan sbd daddynta ya kira su dd babba maganar saka ranar biki da tarewanta.


Kashe wayarsa yayi bayan yacewa ummen to kawai sbd baisan me zai fada ba akan aurenda har aransa ya manta dashi.


Barin palon yayi Zeenah ma miqewa tayi ta nufi bedroom dinsu tana shiga Kiran Safnah na shigowa wayarta sbd DD Bai dauki nata ba Kuma ance suna tare.
#MAMUH#
#DBENA
#ZAFIN KAI
#ABABA
#KAANTES
[9/1, 1:04 PM] MG: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
59
Akwai wani cuta da ake kira da POLYCYSTIC OVARIAN SYNDROME(PCOS) wanda ake samun shi a mafi akasarin mata.
- [ ] CUTACE DAKE HAIFAR DA RASHIN HAIHUWA A KASHI 70-80% NA MATAN DAKE DAUKE DASHI.
- [ ] CUTACE DAKE HADDASA RIKICEWAR AL’ADA
-FITOWAN GASHI A GEMU DA SAMAN CIKI
-TUMBI
-KIBA
-KURAJE A FUSKA,KIRJI DA BAYA
-YAWAN KWADAYI
-YAWAN KASALA
-RASHIN SAMUN BACCI DA DAI SAURANSU .
-SHIN an tabbatar miki da cewa kinada wannan cuta da akema lakabi da PCOS kuma kin rasa yadda zakiyi?
-SHIN kinyi amfani da duk wani mataki da kikasani amma kin kasa cin karfin CUTAN??
-SHIN kinata kokari kisamu JUNA BIYU amma har yanzu shiru ba labari?.
Toh sha kuruminki,nesa tazo kusa,dan 4WEEKS REVERSE PCOS SYMPTOMS CHALLENGE DINMU zai taimaka miki wurin samun cikan burinki. KUMA ABUN ALBISHIR SHINE,ZAKI IYA SHIGA CHALLENGE DIN A PROMO PRICE NA NAIRA 3000 KACAL wanda zakiyi iya biya ta (VFD MICROFINANCE 1013793139
NASIBA MUHAMMAD AL-AMINA) sai a turo shaidar biya ta wannan lamba
(08109388227)Abunda kawai kike bukata shine JAJIRCEWA da kuma NACEWA.
Zaki iya shiga kungiyar mata masu wannan CUTAN ta WhatsApp a NAIRA 1000 KACAL DOMIN SAMUN INGANTATTUN BAYANAI GAMEDA WANNAN CUTAN.
Ko kuma kiyi subscribing YouTube Channel dinmu ME SUNA LAFIYAR MATA TV domin samun video duk sati akan wannan cutan ta wannan link din ⬇️ YouTube@LafiyarMataTv






**********
Zaunawa Zeenah tayi kan couch Ahankali tana Dan kallan Bena datake zaune kan gado tana duba wayarta Dan kawar da Abinda takejin Yana Neman saka zuciyarta nauyi.


Wayar safnah Zeenah ta dauka ahankali tareda miqewa ta nufi Kofa sbd taji bazata iya daga wayan Safnah din gaban Bena ba.
Palo ta dawo ta zauna ahankali tareda daga wayan.


Cikin sautin nutsuwa da bayyanarda damuwa da rashin hakuri Safnah tace


"Ina buqatan address na gidan D zanzo Ina buqatan ganinsa I've been calling Him Amma baya dagawa."


Cikin nutsuwa Zeenah tace


"Bamu gaisa ba ai tukuna ko?"


Qaramin tsoki Safnah ta sake a boye kafin a fili ta Dan sauke numfashi Mai sanyi tana sassauta dacin zuciyarta tace


"Sorry Sis na manta ne sbd hankalina Yana kan D gaba Daya Ina san ganinsa sosai kafin na bar Lagos din gobe,ya kike?
Ya service?
Nima inshallah next year Dani zaayi."


"Fine Alhmdllh,barka da dawowa to." Zeenah ta fada tana Jin zuciyarta batajin Safnah da yayanta tafi jinta a 'yar uwarta kawai.


Sake tambayarta address Safnah tayi Zeenah din datasan bazai yiyuba ta Bata address na Nan gidan bayan Bena na gidan Dan haka ta Zame taqi fada mata qarshe ma ta sanar da ita gobe zai tafi so babu buqatan sanin address Kuma 'dayan matarsa na gidan.


Kalaman Zeenah sun sosa zuciyar Safnah sosai Dan haka cikin baqin ciki da radadin zuciya ta daure sukai sallama kawai tayi jifa da wayarta tana Jin kanta na daukan zafin wai matar D din na gidansa tareda shi.


Tsoki taja Mai qarfi tareda daukan wayarta ta fasa kwana garin take tasa Akai mata booking ticket na tafiya cikin Daren.




*Bena kuwa bayan ficewan Zeenah daga dakin numfashi ta sauke ahankali sbd ta Dade da mantawa ba ita kadai bace matarda aka aurowa DD ba,
So Daya taji zancen ta sani Kuma tin daga ita har waccan din babu wadda ke gabansa yasaka ita kanta mantawa takeyi da akwai aurensa akanta bare wadda Baa Gani.


Dawowan matar tasa na nufin zai zama magidancin gidansa Dan haka dole tana buqatan kame kanta tinda waccan yar uwarsa ce ta jini ita kuwa tasani darajan Amnah takeci wadda itama duk ranarda ya gano ba itace ta haifeta ba tsanarta zaiyi ita.


Tashi tayi tashiga toilet tayo Abinda zatai ta fito ta shirya cikin kayan bacci masu Dan kauri sbd sanyi tayi kwanciyarta tareda rufe idanuwanta ahankali tana jiran bacci.


Zeenah kuwa bayan gama waya da Safnah da DD ta tsaya palon sukai magana sama sama akan yawan yawonsu da Daren dasuke Kaiwa a waje yace su Dena.


Duk da Bai fito ya fada ba tasan Kila akan Bena ya fada Hakan sbd ita yasan ta Saba a can foreign countries tana dare sosai a waje bakuma komai bane tinda ko saurayi batada shi bare ayi tinanin akwai Abinda yake shiga tsakaninsu.


Bayan sunyi sallama ta shige Shima ya Danyi mintina yana kallan kofan bedroom din nasu kafin ya Dan dauke Kai ya miqe ya shige.


Wanka ya tube yayi kafin ya shirya cikin white Balmain pyjamas ya jikinsa na tashin sanyin qamshinsa ya Kwanta.




Washe gari flight din 10 zai bi Dan haka 8 ya fito a shirye cikin D&G black shirt da Balmain slim jeans sai Fcap din flexfit me tsadan gaske.


Zeenah ce ta hada masa simple light breakfast ya zauna Yana cikin ci ahankali cikin nutsuwan
Bena ta Bude kofan bedroom dinsu ta fito fuskarta fresh sanye cikin kayan baccinta Riga da wando da suka bayyanarda shafewan cikinta kanta ko hula babu slippers ne kawai a qafarta ta nufo dining din cinyoyinta na daukan ido sbd lafiyan brown skin dinta.


Saida ta iso daf da dining din idanuwanta suka gansa zaune Yana jifanta da Wani irin Kallon da mayun idanuwansa.


Cak ta tsaya sbd duka tinaninta yaje akan ya Riga ya tafi.


Kasa juyawa tayi ta Dan dago ahankali ta Bude baki tace


"Good morning"


Sai Daya dago yayi mata kallan seconds kafin ya Dan dauke kallansa akanta ya amsa Yana cigaba da Shan tea dinsa.


Kokarin juyawa takeyi tabar gurin taji muryansa a natse yace


"Zaki bini zuwa gida yau din....


Dakatawa tayi daga tafiyan datakeyi ta juyo ahankali cikin mamaki da sanyi tace


"Yau??


Tasowa yayi daga dining din sbd ya gama ya ratsata ya wuce qamshinta na Dan shiga hancinsa ya nufi kujera ya zauna Yana duba agogon bighead Bottega veneta dake daure a hannunsa.


Rasa abin fada Bena tayi sbd mamaki da fargaba ga Kuma taro me mahimmanci da dd babba ya sakata halarta yau a matsayin me wakiltan department na account din kamfanin kaantes ita da Fahad Yana Nan zuwa Lagos din yau ma,
Yanzu gashi Daddyn Amnah na fadan haka Daman tasan zai iya faruwa Hakan tinda Amnah tayi maganar tanason zuwanta.


Cikin sanyi ta Tako ta iso gurinsa tana sake Dan shiga sanyin jiki a natse tace


"Akwai serious business meeting na kaantes da zanje tareda Fahad Yana hanya and gobe ne Ina buqatan tsayawa please."


Ambatan sunan Fahad datai ya sakasa Dan waiwayowa ya Kalli gefenta Kai tsaye yace


"Flight na 10 zamu bi."


Yana fadan Hakan ya miqe yayi bedroom dinsa ya shige.


Zeenah dake zaune tana jinsu kallan Bena tayi cikin kulawa tace


"Kije ki sake rokansa kina buqatan tsawa gaskia wannan meeting din,
Babban opportunity ne karki wasa da Hakan and dd babba zaiyi fushi idan kika koma batareda attending haduwan ba,
Kije ki sake Basa hakuri dole Zaki tsaya gaskia."


Jin tayi jikinta ya sake mutuwa sosai Sam itama Bata fatan ta tafi tabar wannan aikin datai kusan sati tana wuni da Raba dare aikinsa.


Numfashi ta sauke ahankali tareda nufan dakin tana Isa tayi knocking Ahankali.


Jin shiru ya sakata Bude kofar da hannunta ta tura ta shiga a hankali
Yana zaune Yana amsa waya ahankali cikin rashin hayaniya
Ganinta ya sakasa sallama da Safnah din a hankali tareda ajiye wayar ita kuwa Jin tayi kirjinta yayi nauyi tana Neman kasa mgn sbd fahimtar da matarsa yake wayan.


Boyayyan numfashi ta sauke ahankali tareda daidaita kanta ta dago Bata kallesaba ta fara rokansa akan yabarta din.


Kame fuska yayi sbd baya buqatan Jin zancen nata.


Ganin yaqi ko kallanta ya sakata sake qarasowa daf da shi zatai magana ya dago ya zuba mata fararen idanuwansa
Take ta rude tafara kokarin magana wayarsa tayi ringing.


A tare suka duba wayan sunan Nass ta Gani ta fahimci Naseer ne Kuma tafiyan zasuyi kenan.


Daukan wayar yayi ya Dora a kunnensa cikin nutsuwa yace ok kawai ya kashe wayan ya ajiye.


Miqewa yayi zai wuceta take idanuwanta sukai narai narai sai hawayen data manta Yaya ake tsiyayosu ma.


Dakatawa yayi tareda kallan hawayen nata ahankali ya Kalli fuskanta datai qasa da Kai.


"Meye wannan?
Ya fada Yana kallan hawayenta.


"Shi wannan din Kuka ne ko meye?"


Shiru tayi takasa dagowa


Ajiyan zuciya ya sauke me sanyi kafin ya rabata ya fice daga dakin a sukwane ta biyo bayansa ta fito itama

Yana fitowa Palo ya tadda Naseer ya shigo Dan Haka ya juya ahankali ya koma Dan dakatar da ita daga fitowan sbd kayan jikinta
Yana dowowa tana Sako Kai Dan haka sukai Wani irin hadewan data sakata yin baya ya riqota zuwa jikin bangon kofan Yana zagaye da ita ahankali.


Numfashi me Dan qargi ta hau saukewa tareda kasa dagowa sbd yanayinda suke.


Jin jikinsu manne da juna ya sanyata Bude bakin kasalance batareda ta dago ba ta furta "please kabarni na tsaya"


Qamshin mouthwash dinta ne ya shiga hancinsa tareda numfashinta sbd kusancinsu Dan haka ya juyo da idanuwansa ya Kalli bakin nata tana sake motsasa ahankali gurin rokansa.


Zare hannuwansa yayi daga jikinta tareda janyewa sbd zafin dayaji Yana shigarsa.


Bai waiwayo ba ya gyada mata Kai kawai tareda ficewa daga dakin.


Kafin ta sauke numfashi da ajiyan zuciya ta fito tini suka fice shi da Naseer Dan haka Koda ta fito sun fice.


Ajiyan zuciya da numfashi ta sake saukewa tana godewa Allah cikin ranta sbd babu Abinda yakeda mahimmanci agunta yanxu ta bangaren cimma buri irin kammala komai ta koma ta tsayu da qafafunta tareda taka matakin nasarar da zata Siya yancin mahaifiyarta da kudinta ta dawo hannunta.


Breakfast tayi sama sama sbd Jin duk jikinta yayi sanyi Kuma.


Tana gamawa ta shige wanka ta shirya ta fita Aiki sbd yanzu kam bazata ringa fashi ba a yanda takeso tinda sun kusa gamawa su tattara su koma gida.
#MAMUH#
[9/2, 10:23 AM] MG: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
60


*_HAMMAK KITCHEN UTENSILS_*


*_INA MAABOTA GAYU DA SON BURGE BAQI DA ME GIDA?_*
*_SHIN KUNSAN HAMMAK KITCHEN UTENSILS SUNA DA QAYATACCIN KAYAN KITCHEN MASU KUDI DA MASU ARHA NA WAJE DANA GIDA NIGERIA_*


*_BA IYA ZUWA SHAGO KADAI KU SIYO BA HARDA AIKAWA SUNAYI KOINA HAKAMA SUNA ADASHEN KAYAN KITCHEN MANYA DA QANANA,MASU SAUKI DA MASU TSADA,NA WAJE DANA GIDA NIGERIA,_*


*_ZAKIYI ZUBINKI A HANKALI KI KWASHI DUK ABINDA KIKESO A AIKA MIKI ABINKI CIKIN SAUKI DA AMANA DAN HAKA SISTERS KARKU BARI AYI BAKU MUN SANI MUN SHEDAR HAMMAK KITCHEN UTENSILS SUNE THE BEST👍_*


@hammakkitchenutensil
Tarauni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login