Showing 114001 words to 117000 words out of 192750 words
karatun Amnah da hutun ta yake kokarin qarewa Dan haka sbd Amnah kawai zata koma idan lokaci yayi.
****Acan Nigeria kuwa Safnah kullum a bangarensu Umme take wuni duk da ta samu sanin Bena Bata qasar da 'yarta,
DD kuwa kusan kullum baida time na zama gida Yana dawowa yaci abinci ya shige shikenan babu Wani Abu na kusanci da juna koma fira haka ta kauna da kulawa data taba shiga tsakaninsu kullum baya Wani zama sbd ko baya office yafi zama gidansa dake highbridge,.yafi samun nutsuwa da kwanciyar hankali acan
Ya kasa sabawa da zama kullum kullum da mutum a guri Daya shiyasa duk inda yake tin asali baya zama cikin familynsa yafison yaje inda zai zauna shi Daya yayi rayuwan dayakeso gashi matiqan Yana cikin gidansa ba maabocin saka kaya masu nauyi ko tsayi bane Dan Hakan yake zaban zama gidansa shi Daya yayi rayuwansa ba takura ba damuwa.
Safnah hakurinta Yana qarewa gameda zaman Datakeyi da mutumin da takejin zuciyarta idan Bata samesa ba komai zai iya faruwa,
Zafi da baqin ciki sosai takeyi da irin zaman dasukeyi
Babu ranar da Bata Kai kanta dakinsa Amma Bai taba barinta ko shigaba Bare ta samu Daman Jan raayinsa ya kwana da ita Dan a yanzu tafi buqatan suyi kwanciyar aure akan komai sbd yanda yake fitowa daga shi sai dogayen wandina ba Riga kokuma guntayen wandina ba Riga jikinsa ya sakata qara mutuwa akansa sbd ita ko a turawanta datai rayuwa cikinsu DD kaante daban yake,
Komai nasa me aji da Jan hankali ne tareda daukan Ido.
Ahaka suka shafe sati biyar babu Wani gaba bare baya Dan haka itama ta rage zama gida kusan kullum saita fita sunfita da Mummynta sbd lamarin ya fara gundurarsu gashi hakanan Safnah takejin Bata qaunar matarsa ta dawo Bata gama samun Kansa ko hankalinsa akanta ba Dan haka daga ita har mummynta hankalinsu ya tashi suka kasa zama suka kasa tsayi.
******Watansu Bena 2 cif suka fara Shirin dawowa lokacin suna barin Australia Umrah suka wuce suka qara sati biyu kafin suka diro Nigeria,
Jirginsu da Asuba ya sauka Dan haka Fahad ne ma yaje da Kansa da lafiyayyan motarsa ya daukosu,
Kallo Daya yayiwa Bena ya dauke idanuwansa Yana kore shedan daga zuciyarsa sbd yanda kyanta ya daki kirjinsa,
Tafiyan wata biyu kokuma yace uku Amma komai nata ya qaru,
Kyau, lafiyan fata,hutu,nutsuwa,aji da burgewa duk komai ta qaro hakama harda cikowa tayi kaman wadda babu Abinda taje tayo sai hutawa.
Dd babba ma ya qara samun qarfi da lafiya sosai harma da kwanciyar hankali sbd kulawa da Bena ke Basa da yanda ya bar gida da hayaniyarsu yaje ya huta Abinsa.
Abbakar kuwa qibarsa yayo abarsa lafiya kalau ta hutu da cima me kyau duk da Baya Wani son abincinsu acan Amma cinsa yakeyi ya koshi Abinsa ya huta ya fita yawon Shan iska yaci Dadi San ransa.
Amnah ma sosai tayi jikinta da haske data qaro Daman ita ba skin din mamanta ta daukoba na baban Dan haka take fara tas kaman DD.
Koda suka shigo kaantes an shiga sallan Asuba Dan haka babu Wanda yasan ma sun iso, sai a lokacin ta Ciro wayarta jaka ta kunna ta kira Nafisat,
Nafisat ce ta kwasar musu kayansu zuwa ciki shikuma dd babba Abbakar ne ya shiga nasa kayan bangarensa kafin suka wuce masallaci sallah sbd alokacin ne aka tayar.
Suna shiga Kai tsaye bedroom din Zeenah suka shige Nafisat Kuma cikin duhun Asuban ta hau gyara dakin Bena din.
Sun shiga Zeenah Bata ma tashi sallan Asuba ba motsinsu da shigowansu dakin ya tayar da ita ta tashi zaune ahankali ta miqa hannu tana kunna wutan dakin taga Bena tsaye tana ajiye handbag nata Amnah kuwa gadon ta fada sbd bacci ne sosai a idonta.
Da sauri Zeenah ta sauko gadon bacci na Sakin idanuwanta gabaki Daya ta nufo Bena suka rungume juna tana cewa
"Oh ya Allah finally Bena kin dawo."
Murmushi Bena ta sake ahankali tareda rungumeta itama tana cewa
"Kin dauka bazan dawo bane?"
Mintsininta Zeenah tayi tana janyewa daga jikinta tace
"Kinsa me kikai kuwa?
Meyasa Zaki Kashe waya ki Hana kowa Jinki for more than 2months,
Kin kusa sakawa kowa heart attack da rashin Jinku.
Wani murmushin me sauti ta Kuma sakewa tana cewa
"Ba gashi na dawo ba"
Kayanta tahau cirewa ta fada toilet tayo alwala batai wanka ba ta fito ta saka Riga da wandon bacci tayi sallah ta fada gadon Zeenah din ta shige bargo take baccin dake cinta da gajiya ya dauketa.
##MAMUH#
#DBENA
#TOO HOT
#MARRIAGE
#ROMANCE
#SAFNAH
#KAANTES
*_HAMMAK KITCHEN UTENSILS_*
*_INA MAABOTA GAYU DA SON BURGE BAQI DA ME GIDA?_*
*_SHIN KUNSAN HAMMAK KITCHEN UTENSILS SUNA DA QAYATACCIN KAYAN KITCHEN MASU KUDI DA MASU ARHA NA WAJE DANA GIDA NIGERIA_*
*_BA IYA ZUWA SHAGO KADAI KU SIYO BA HARDA AIKAWA SUNAYI KOINA HAKAMA SUNA ADASHEN KAYAN KITCHEN MANYA DA QANANA,MASU SAUKI DA MASU TSADA,NA WAJE DANA GIDA NIGERIA,_*
*_ZAKIYI ZUBINKI A HANKALI KI KWASHI DUK ABINDA KIKESO A AIKA MIKI ABINKI CIKIN SAUKI DA AMANA DAN HAKA SISTERS KARKU BARI AYI BAKU MUN SANI MUN SHEDAR HAMMAK KITCHEN UTENSILS SUNE THE BEST👍_*
@hammakkitchenutensil
Tarauni market Abba hamisu plaza block A shop no 8
or dorayi sabon titi before gidan man b i
Wa.me/+2348067376035
[9/3, 9:58 AM] MG: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
64
Zeenah ma sallan tayi Amma farin ciki ya hanata komawa bacci Dan haka karatun Qur'an tayi a iPad kafin tana gamawa ta miqe ta hau Aiki a laptop Kuma.
Zata fita office 9 yau Dan haka time nayi ta shirya dole tabarsu suyi baccin hutu tukuna 8:30 nayi na fice.
Amnah ce ta fara tashi ta sauko gadon ta fito dakin ta nufi kitchen gurin Nafisat wadda sai alokacin ta samu ganin Amnah ta rungumeta cikin murnar dawowansu sbd lokacinda suka dawo da Asuba Amnah din na jikin mummynta sbd bacci.
Itama Amnah sosai tayi kewan Nafisat din Dan haka ta Haye jikinta suka dawo zuwa bedroom din mummynta.
Dakin Nafisat tai masa Wani irin gyaran tsafta da kyau koina sai qamshi da sanyi ke tashi tareda ni'iman tsafna.
Toilet suka wuce Kai tsaye Nafisat ta taimaka mata tayi brush kafin Akai fitsari da alwala suka fito ta saka mata abayan sallah tayi sallah duk Nafisat na tsaye tana jiranta.
Tana gama sallan nata da zaa ce Allah ya Bada Lada
Nafisat ta dauke kayan sallan ta sake gyara toilet da dakin kafin suka wuce kitchen Nafisat na cewa Bara na hado Miki breakfast naki yanzun Nan.
Cikin tsalle Amnah ta fara cewa
"Aa ba breakfast nakeso yanzu ba Ina iPad Dina ki dauko ki sakamun charge inason Kiran Daddyna nayi missing nashi sosai sosai sosai sosai.....
Gyaran muryansa taji daga bayanta ahankali ya furta
"I miss my angel too sosai sosai....."
Da Wani irin gudu ta nufosa tin Bai qarasaba ta fada Kansa ya dauketa yayi sama da ita Yana Jin zuciyarsa na samun sanyin da tinda suka tafi ya rasa shi.
Dariya sosai Amnah keyi tana farin cikin ganinsa shi Kansa murmushi yake mata Wanda ya saka Nafisat silalewa ta kama hanyar kitchen Dan hado Abinda tasan dashi Amnah ke breakfast wato chocolate custard fa soyayyan farin kwai da tomatoes kawai.
Umme ma dariya da ihun Amnah ya sakata fitowa Daman dad kaante ya fada mata sun dawo sbd kowa a masallaci sallan Asuba kawai akaga dd babba da Abbakar,
Shi Kansa Daddyn Amnah din a masallaci ya gansu ya tabbatarda dawowan 'yarsa.
Amnah na ganin Umme ta sake shiga farin ciki itama tayi kanta ta rungume tana cewa tayi missing nata.
Daga jikin Umme ficewa tayi da gudu zuwa palon dad kaante Yana zaune Yana amsa waya yajita Kansa ta fado dole yayi sallama da Wanda yake wayar Yana cewa
"Zaki karyawa dad din daddynki wuya ai da wannan kibar da kika qaro acan."
Dariya tayi masa tana cewa
"Wuyanta baze karye ba ai yanada qarfi sosai kaman na Daddyna"
Murmushi yayi Yana zagayo da ita gabansa yace
" Wannan wuyan na Daddynki ai yafi na kowa qarfi."
Shigowan daddynta palon ya sakata barin jikin dad kaante ta koma gurinsa ya dauketa Yana qarasowa ciki ya gaida dad din kafin suka juya suka fice.
Palon Umme suka koma lokacin Nafisat ta gama hadowa Amnah din komai Suma sauran masu gidan angama nasu breakfast din an Jere a dining.
A dining din ya zauna shi da Amnah suna magana Yana amsa mata a hankali Nafisat na kokarin qarasa shirya mata breakfast din a gun.
Daidai lokacin 9:40 ta buga aka Bude kofan bedroom din Zeenah Bena ta fito ahankali tana Dan shafa wuyanta dataji yasamu sakewan datakeso sbd samun isashen bacci.
Kayan baccin jikinta masu tsantsi me da yanayin sanyi ya Dan sakasu lafewa jikinta tana fitowa Kai tsaye dining ta nufo tana Dan Kiran sunan Nafisat sbd ta kawo mata tea me zafi sosai yau takesan Sha.
Tinda ta tinkaro dining din ya dago fararen idanuwansa ya zuba mata bata ankara da Hakan ba Saida ta qaraso daf ta tsaya cak Wani irin sanyi da bugawan zuciya na samunta lokaci Daya.
Dagashi har ita kowannensu yaga sauyi sosai a tattare da dayansu,
Kowannensu ya qara sauyawa da samun hutu da kyan yanayi musamman ita da komai na Qarin data samu a bayyane yake.
Ahankali ta dauke kallanta da gunsa zuciyarta na Dan qara tsananta bugawa.
Juyawa take kokarin Yi Takoma Amnah tayi caraf tace
"Daddy bakaiwa mummy oyoyo ba gatanan ta fito."
Bena na Jin haka ta juyo da sauri ta kallesa Shima ita yayiwa Wani Kallo da mayun idanuwansa
Tana ganin Hakan ta daga qafa da sauri zata gudu saidai ko taku daya Bata qarasa ba ya miqa hannu daga zaunen Dayake ya riqo hannunta Daya ya dawo da ita baya ta fado kansu shida Amnah Dake jikinsa.
Nafisat na ganin Hakan tayi saurin barin gurin kanta qasa.
Hade fuska Bena tayi tana kokarin cire jikinta Dana nasu Amnah tace
"Mummy ki tsaya mana oyoyo kawai zai Miki kin manta munce munyi missing nasa sosai fa."
Rintse idanuwa tayi ta budesu akan Amnah cikin takaici zatai magana Amnah ta sauka daga jikinsa tana cewa
Bari na dauko iPad dina nayi muku hot kanawa mummy oyoyo.
Amnah na barin gurin ta kallesa a hankali tareda Bude baki tace
"Ina buqatan tashi ka sakeni"
Cikin idanuwanta ya zuba nasa ahankali take ta rufe nata tana kokarin Hana bugawan kirjinta Dayake fara Hawa yana sauka.
Magana ta sake Bude baki zatayi taji hannuwansa sun qara zagayeta ahankali tareda zaunar da ita da kyau kan qafafunsa suna fuskan juna.
Yanayin zaman ya sakata dagowa ta kallesa zatai magana tana Bude baki ya kamo kanta ahankali ya hade da nasa tareda zira harshensa cikin bakinta.
Batai tsammanin Hakan ba ko a mafarkinta Dan haka ta qanqamesa tana rintse idanuwanta kafin yanda yake kissing cikin bakinta ya sakata lumshe idanuwa tana Jin zuciyarta na Neman sanyi da narkewa.
Motsin dawowan Amnah ne ya sakasa Sakin bakinta ahankali tareda Ciro nasa ya jingina bayansa da kujeran dining din Yana kallanta da kasalallun idanuwansa kaman babu Abinda yayi,
Itama kasa dagowa tayi ta kallesa bare Amnah hakama ta kasa tashi daga jikin nasa Saida Amnah tace su shirya tai musu hoton tukuna ya Dan dago bayansa ahankali tareda daukan Amnah din ya saka tsakiyansu Akai hoton tukuna Bena ta iya miqewa daga jikinsa ahankali jikinta a mace.
Umme ce ta qaraso itama fuskarta cikeda farin ganin Bena din Mai tsanani tana zuwa Bena ta rungumeta tana cewa
"Ummenah nayi kewanki sosai"
Cikin farin ciki Umme tace
"Mu da kika cinnawa hauka Bena,
Kika Hana kowa Jinki,
Amma dai koba komai kinyi kishi me tsafta Allah ya qara Miki hakuri..
Kasa amsawa tayi tareda Satan kallansa Shima itan ya kalla Jin kishi ne ya korata ta Hana kowa jinta.
Kunya da nauyin maganar Umme ya sata zaunawa a Dan fuske tana basar da zancen suka fara breakfast harda ummen duk da ta Dan ci breakfast tareda dad kaante a nasa palan.
A hankali take cin abincin batareda ta dago ba sbd idanuwansa na hanata walwala a gun.
Sama sama Shima yaci abincin Umme ta kallesa tace
"Matarka na can na jiranka kuyi breakfast kazo kayi anan......
Tsit gurin yayi har da ita ummen sbd sai datai maganar ta Tina da Bena dake gurin,.
Shima Bena din ya Dan kalla,
Bena kuwa ruwan tea din dake bakinta ta hadiye ahankali sbd Neman gagara wucewa da sukai Bata dago ga ta dauki tissue fuskarta babu Wani sauyi ta goge bakinta ta dago ta Kalli Umme cikin sakewan fuska tace
"Umme inaga yau zan koma office akwai pending ayyika sosai suna jirana,zan biya na dubo Anne kafin na tafi.
Murmushi Umme ta sake tana waskewa itama ganin Bena din Bata nuna damuwa ba tace
"Ok ba damuwa ki gaida Annen Taki tareda Ababa Shima duk Muna gaidasu."
Bata kallesa ba ta miqe daga dining din ta wuce tana Jin idanuwansa akanta har ta shige bedroom.
Tana shigewa ta tube kayan baccin jikinta ta daura towel din Amnah da yayi mata qarami sosai ko dauruwa bayayi saidai ta riqe
Nata duk Nafisat ta kwashe da safen ta wanke sbd bazata iya daurawa sai an kwanke tin Bata Nan sun kwana biya a ajiye
Na Amnah kuwa sabo ne ta fasa yanzun ta daura itama tana buqatan shopping din sababbi da wasu daga cikin toiletries nata.
Kofan dakinta aka Bude Kai tsaye aka shigo tareda rufewa Bata juyoba tana duba undies nata strapless bra zata dauko sbd tinanin Amnah ce sai dataji shiru ta dakata sai a lokacin taji qamshinsa ya shiga hancinta sai kawai ta qi juyowa tareda fasa dauko bra din ta nufi hanyar toilet zata shige yace
"Na dakatar na zuwa Aiki da fitanki gaba Daya."
Cak ta tsaya tareda juyowa Bata shirya ba sbd rashin fahimtar zancen da kyau.
Kallanta yakeyi fuskansa ba sakewa yace
"Yes you hard me right."
Dawowa tayi zatai magana Bai tsaya sauraranta ba ya juya ya fice daga dakin fuskansa a hade sbd Bai dauka Yana zaune zata fadawa Umme fitanta da Abinda ya yankewa kanta ba batareda ko kallansa ba Yana matsayin Wanda shine yakeda ikon da Damar badawa din.
Wani irin baqin ciki ne me nauyi ya danne zuciyarta takasa ko motsawa daga inda take tsaye.
Ta jima a gurin tsaye kafin ta iya shiga toilet jikin na zafi da zazzabin bacin Rai Daya saukan mata a take.
Wankan ma ba acikin Dadin Rai tayosa ba ta fito ta shirya cikin Riga da skirt da coffee brown lace Mai tsananin tsadan tsiya ta kira Zeenah ta turo mata numbernsa a Karo na farko data taba samun numbernsa bare kiransa a wayanta.
Kira uku tayi Bai daga ba da alama yasan numbern tata Dan haka itama aje wayar tayi tana cire maganar daga ranta.
Gurin dd babba taje tai masa bayanin zancen murmushi kawai yayi yace
"Ki shirya kije ki dubo Annenki kawai karki je aikin bari sai kinsake magana dashi,
Bazan masa magana ba kiyi magana Dashi zuwa gobe ko anjima idan kin dawo daga gurin Annenki ki samesa gidansa na highbridge kuyi magana."
To kawai tace Amma bataso Hakan ba hasalima bazata sake nemansa ba.
Shiryawa tayi itada Amnah da Nafisat dake kulawa da ko saka talkalmin Amnah suka fita.
Shopping sosai suka fara yiwa Anne kafin suka wuce gidan saidai murnarta komawa ciki tayi sbd tararda yau din jikin Annen ya tashi Sam bata Wani hankalinta sosai ganinsu ne ma ta Dan Yi kaman ta dawo daidai sbd Bena cikin tsakiyan ranta take.
Hande duk Abinda zuka zo dashi karbewa tayi tace sai Ababa ya dawo abasa kafin ya bawa Annen Abinda zai Bata da Kansa.
Bena Bata damu ba Dan haka ta zauna ta yankewa Annenta farce dasukai tsayi,
Ta kunce mata Kai ta wanke mata tas tareda taimaka mata da kanta tayi mata wanka tas
Nafisat kuwa dakin ta sakata ta gyara tayiwa Annen wanki duk da sun siyo mata sabbin kaya Amma duk hande ta karbe sai Ababa ya dawo.
Abincin lafiyayyan dasuka zo dashi Daman sbd Annen suka fara barinsa mota Bena ta saka Nafisat ta dauko hande na ganin babban basket zata amsa Bena tace Mata abincin Amnah ne Batacin komai sai shi.
Dole hande ta bari sbd duk masifar Ababa ya Hana a taba Amnah wadda itama ta Dan yinsa sbd Yana sonta.
##MAMUH#
#DBENA
#LOVE
#TOO HOT
#ROMANCE
#ABABA
#KAANTES
*_HAMMAK KITCHEN UTENSILS_*
*_INA MAABOTA GAYU DA SON BURGE BAQI DA ME GIDA?_*
*_SHIN KUNSAN HAMMAK KITCHEN UTENSILS SUNA DA QAYATACCIN KAYAN KITCHEN MASU KUDI DA MASU ARHA NA WAJE DANA GIDA NIGERIA_*
*_BA IYA ZUWA SHAGO KADAI KU SIYO BA HARDA AIKAWA SUNAYI KOINA HAKAMA SUNA ADASHEN KAYAN KITCHEN MANYA DA QANANA,MASU SAUKI DA MASU TSADA,NA WAJE DANA GIDA NIGERIA,_*
*_ZAKIYI ZUBINKI A HANKALI KI KWASHI DUK ABINDA KIKESO A AIKA MIKI ABINKI CIKIN SAUKI DA AMANA DAN HAKA SISTERS KARKU BARI AYI BAKU MUN SANI MUN SHEDAR HAMMAK KITCHEN UTENSILS SUNE THE BEST👍_*
@hammakkitchenutensil
Tarauni market Abba hamisu plaza block A shop no 8
or dorayi sabon titi before gidan man b i
Wa.me/+2348067376035
[9/4, 1:07 PM] MG: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
65
Pepper soup na qatan catfish ne da Kuma white rice da aka dafa tareda veggies sai sauce na kidney qanana aciki,
A cikin dakin suka zauna Amnah na jikin Nafisat tana Bata da spoon abaki ahankali ita Kuma Bena tana bawa Annenta cikin tsananin kulawa da soyayyan mahaifiyarta me tsanani.
Saida ta tabbatarda Annen ta Koshi kafin ta Bata fruit drink me mara sanyi Tasha tukuna Nafisat ta tattara kayan ta mayar basket ta Maida mota.
Har yamma tana gidan tana jiran dawowan Ababa taso rokonsa yabata Daman kai Annen taga likita Amma har magrib Bai dawoba Dan haka Suka tafi Annenta na kallanta kaman zatai Kuka,
Itama Saida tayi hawayen kafin ta iya tafiya tabar Annenta.
Gida suka koma Kai tsaye daki ta shige sbd ranta ya gajule da yanayin Annenta Kuma gashi dd babba Yanata tausanta sbd matiqar ba asirin kafin da Ababa yai mata a karya ba ko sace ta Akai kokuma akai dole aka dauketa zata iya ransa ranta sbd Hakan Sai Kuma idan shine da Kansa Ababan yace ta tafi yayi freeing dinta.
Data shige daki bayan tayi sallan magrib kasa riqe kukan Datake dannewa tin a gaban Anne tayi ta fasa kukan a hankali tareda cusa kanta cikin qafafunta.
Amnah data shigo ta taddata tana Kukan qarasowa tayi ahankali ta shiga jikinta ta lafeta tareda yin shiru sbd Bata taba ganin Mummyn nata na Kuka ba.
Saida Bena tayi kukanta me isanta hardana DD Daya da Abinda yayi mata da radadin kishinsa Datake ta dannewa duk sai datai kukansu Daman suna ranta danqare.
Wata alwalan tayo tareda wanka tazo tayi sallan ishai tana gamawa a daki Nafisat ya kawo mata yoghurt a glass cup Tasha ya isheta ta kwanta tareda cewa batada lafiya zazzabi takeji sbd tasan Hakan ne kawai zai saka abarta taji da Abinda yake cin ranta da ruhi.
Daga Zeenah har Umme sin shiga damuwan rashin lafiyan