Showing 120001 words to 123000 words out of 192750 words

Chapter 41 - ZAFIN KAI COMPELET BOOK BY Mamuhgee.txt

12 Dec 2024

7158

Bena idan har munason cigaba da rayuwa baa gidan yari ba.


Shiru Safnah tayi sbd itama duk tsanani duk wuya bazata yarda tayi rayuwar ukuba ba bayan wadda tayi a baya idan kawar da Bena shine key din tabbatuwarta zama matar Dawood kaante da zamanta Safnah bulama to tabbas ta shirya Hakan Koda zasu rasa komai sai ta tabbatarda ita D zai fara sani a mace.


Da wannan kudirin suka samu dawowa hayyacinsu Badan hankalinsu ya kwanta ba Dan Kuma yanzu basuda kwanciyan hankali matiqar ba ganin sukai sun cimma sabon burin nasu na zamanta wadda ita zata amshe sunan matarsa ta gaskia ko a gaban shiria sbd idan ta rasa identity dinta na Safnah bulama zata amsa sabon identity na matar Dawood kaante.


Daqyar suka Dan seta kansu sbd kowannensu dai yana cikin rashin nutsuwan zuciya hakanan suka fito Palo momy ta Kalli Safnah
Safnah din tayi gaba taje ta sakawa kofar shigowa palon key ta dago tareda cakumo Rabi wadda idanuwanta suka fito take jikinta Yana daukan kakkarwa.


Cikin Riga momy ta saka hannu ta zaro wata qaramar pistol data saka Rabi fara Sakin fitsari jikinta na sake daukan rawa safnah ta sake shaqo rigarta momy Kuma ta Dora pistol din a saitin kirjinta ta danna mata ita da karfi har Saida Rabin ta kusa somewa tace


"Wallahi tallahi duk ranar da tsautsayi ya aikeki kika fada ko a toilet ne ke Daya kikai maganar Abinda ya faru anan saina fasa kanki da kirjinki da wannan Abar."


Kasa ko gyada Kai Rabi tayi sai zubewa datai qasa tana kama kafar Momyn tana cewa wlh zata mutu da wannan maganar babu me ji daga gareta.


Sakinta Safnah tayi sbd duk jikinta har lokacin rawa yake Bata cikakken hayyacinta
Sam zuciyarta ta kasa nutsuwa Jin takeyi kaman kanta zai kama da wuta ta haukacr ga Wani radadi da zuciyarta keyi na Jin idan Bata cika burinta ba na mallaka D zata iya mutuwa ko rasa hankalinta.
##MAMUH#
#DBENA
#SAFNAH
#ABABA
#KAANTES
[9/4, 1:07 PM] MG: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
67
Bayan tafiyan momy kasa zama Safnah tayi ta shige daki ta rufe kanta sai alokacin ta samu ta fasa Kuka tana Dora hannu Akai zuciyarta kaman ma a fashe da balai da masifa da taurin zuciya.


Itama Rabi bayan ficewan momy dakinta dake kofan baya ta kitchen din bangaren ta qarasa ta fada jikinta na rawa tana Neman tinawa kanta Abinda ya faru na wannan mummunan kaddarar.




DD yau Daya dawo ya tarar da palon tsit ba alamarta ba motsinta Kai tsaye bedroom dinsa ya nufa ya shige sbd sallan ishai yayo ya shige kawai sbd ciwon Kai dake Dan Jin Yana damunsa kaman zaiyi masa qarfi ma.


Tinda ta shige Bata fitoba sai washe gari data kwatanci karfe goma Bena ta Isa fitowa zuwa Aiki ta fito tareda dage curtain na makeken windon Palo ta zubawa Bena din idanuwanta dasukai jajir ta kwana a zaune tana sakawa da wararwa.


Har Bena ta gama tahowa cikin Wani irin nutsuwa da aji tareda burgewa ta Bude motarta ta shiga ta tayar tabar harabar kaantes din akan Idanuwanta.


Jikinta na Neman sake daukan rawa ta saki curtain din da bin bango ta koma dakinta sbd ko gani sosai batayi sbd baqin cikin Dayake cin wuta sosai a zuciyarta.




*****Bangaren Bena kuwa da safen tana barin gidan da motarta office ta wuce Kai tsaye yau meeting ne dasu Mai mahimmanci Kuma da DDs company Dan haka take Dan sauke ajiyan zuciya Akai akai duk da tasan ba lallai shine zaizo meeting din ba Zeenah ce da directors da sauran manyan company din mutum uku ko hudu zasu wakilta.


Tana Isa lift tahau zuwa sama can inda office nasu na masu company din yake,tana Isa ta shige tareda ajiye handbag dinta Bata zauna ba ta zaro wayarta ta saka Kiran Fahad Dan Jin ko ya samu isowa kaantes din sbd 10 harta wuce Sosai Kuma 11 ne meeting din.


Ko data gama waya secretary dinta ya shigo ya ajiye mata documents na meeting din kan desk yafara Koro mata bayani cikin turanci yanda aka tsara komai sbd ba bahaushe bane ko hausa sosai bayaji.


Dan duka takardun tayi sama sama tana duba wayarta har time yayi ya shigo ya sanar mata time na shiganta meeting din yayi hakama baqin sun iso.


Ajiye wayarta tayi tareda sakata silent ta miqe tsaya tareda daukan documents din da kanta ta fice daga office dinta.


Qayataccen dakin meeting dinsu na Companyn na kaantes ta nufa Wanda yake Nan sama Basa meeting cikinsa sai Wanda zasuyi da manyan masu kudi sanannun da sukeda hannun jari a cikin kamfanin nasu.


Nan zasuyi wannan Taran sbd DDs nada babban share a gurinsu Dan haka tana Isa Secretaryn Fahad dake kofa ya Bude mata kofar ta shiga lokacin tini Dad kaante da Fahad tareda sauran manyan kamfanin suna ciki itama a natse taje ta nemi guri ta zauna sbd tsaruwan meeting room din kana shiga bazaka ma gane a inda kake ba.


Saida suka share mintina uku kafin DDs suka shigo da sauri aka Bude masa kofar shine a gaba kafin Naseer da sauran manyan DDs guda uku suka shigo cikin girmamawa da Basu tarba me kyau aka tashi tareda miqawa juna hannuwa aka gaisa Yana gama gaisawa da kowa Dora idanuwansa akanta yayi yayi mata Wani irin kallan Daya sakata Dan dauke Kai daga kallansa tana Maida kanta kan Abinda ya kawosu.


Duk Wani motsinta mayun idanuwansa akanta suke suna gigita nutsuwarta tana jinsu suna yawa akanta,


Kasa dagowa takeyi ta kallesa sbd mutanen dake tareda dasu zasu iya fahimtar Wani ga dad kaante a gurin da Wainda ma duk sun haifeta Dan irin wannan matsayin ma Bata Isa ace ta kaisaba ko shekara nawa zatai a Aiki Amma sbd kamfanin nasu ne ya saka take matsayin da Sam yafi qarfin mace ma.




Kusan awa daya da mintina masu yawa aka share ana meeting din zuwa lokacin tini zazzabi ya Dan kamata jikinta yayi Dan zafi sbd dukan idanuwansa,
Daqyar taga Angama ta kowa ya watse ta fito ahankali Takoma office dinta Kai tsaye.


Tana shiga wayarta ta jefar kan tsadaddiyar desk din office din ko juyowa bataiba taji anbude kofan office din tareda rufewa Jin an saka key ya sakata juyowa da sauri sukai Ido biyu dashi Yana tahowa inda take.


Bata motsaba sbd Daman jikinta a kashe yake kallansa takeyi duka zuciyanta na narkewa sauran kuzarinta na tsiyayewa sbd a yanzu iya ganinsa kawai narkar da zuciyarta yake.


Isowa yayi gabanta ya tsaya Yana kallan cikin idanuwanta dake Tona asirin zuciyarta ya saki Wani qayataccen murmushin da Bai taba sakar mata ba zaiyi magana ta nemi zube masa a gurin sbd murmushin Daya mata ya kusan suman da ita.


Tarota yayi jikinta tareda daukanta da hannuwansa biyu ya zaunar kan desk dinta ya tsaya gabanta tareda shige mata sosai suka matse.


Ranqwafowa yayi yakai hannunsa Daya ya shafa wuyanta cikin Wani irin sanyi Daya sakata lumshe idanuwa yakai bakinsa ya Dora kan kunnenta Saida ya saki numfashi me dumi a ciki kafin ya a hankali qasa qasa yace


"Daga yau idan Zaki office na kashe saka irin wannan rigan"...ya qarasa fada Yana zira hannunsa cikin rigar wadda dohuwar Kuwait jallabiya ce Amma wuyanta Turtleneck ne sai yake ganin ya fidda asalin tsayayun well shaped boobs nata duk da rigan is free size gown har qasa Amma gefe da gefen a tsage yake tin daga qasa har gurin cikinta sai Akai mata slim trouser da ake sakawa aciki.


Ta yankan ya sake zira hannunsa ciki ya shafo shafaffen cikinta da yau yake mata Dan ciwon mara na period dayazo Maya yau din.


Bude idanuwanta tayi ahankali tareda kallansa kaman me koyan magana itama qasa qasa tace masa "ok"


Maganarta ta sakashi Jin jikinsa na zafin Shima sbd a duk lokacin da zatai magana irin wannan qasa qasa jefasa yanayin zafin jiki takeyi.


Ciro Kansa Dana kunnenta yayi ya sake kallan idanuwanta tayi qasa da idon tana Hana kanta kallansa,.ya gangara da idanuwan kan bakinta Daya Dan sake motsawa ahankali tace


"Zaka yi latti."


Boyayyan numfashi ya sake tareda Dan ragewa idanuwansa girma Shima qasa qasa yace


"Late for wat?


Kasa dagowa tayi bare Basa amsa Sai dataji hannunsa dake cikin rigarta kan cikin ya motsa zuwa sama a hankali
Ta dago tareda kallansa a kasalance tana Hana numfashinta Dayake rikicewa fitowa..


Kallanta ya sakasa cigaba da yin sama da hannunsa zuwa saman
Jin zai rabata da numfashinta sbd yanda yake tafiya da hannun a hankali da laushin fatarsa da Dan sanyin da hannunsa yake dashi na Ac Daya dauka take taji tana Neman shidewa ta Kai hannuwanta biyu ta qanqamesa tana Jan Wani shegen numfashin Daya sake kashesa.


Ranqwafowa yasake Yi Yana sake maimaita mata tambayansa ahankali Yana dosan bakinsa zuwa nata Saida ya Shaqi numfashinta me dumi cikin hancinsa tareda qamshinta kafin ya Dan lumshe idanuwansa dake shiga kasala ya hade bakinsu,saida yayi mata Wani sanyayyan tsotsa na minti Daya kafin ta fara kissing nasa Shima Yana sake matseta jikinsa suna zubar da Rabin kayan kan desk din qasa.


Duk yanda yanda yaso kada ya yamutsa Kansa Saida Hakan ta faru kusan mintina shida a kan dsk din suna duk Abinda yasan zai Basa Jin dadi da zafin jiki kafin tayi jarumtar dakatar dashi suka dakata kowannensu zuciyarsa kaman zata Faso sbd tsananin Abinda yakeji a zuciyarsa game da dayansa.


Da Kansa ya saukar da ita daga dsk din ya kamo hannunta suka zauna kan couch Ya lumshe fararen idanuwansa dasuka Dan sauya Yana daidaita nutsuwansa.


Itama shiru tayi tareda Hana tata buqatan nutsuwan bayyana ta kanne kaman babu Abinda ya faru da ita a mintinan.


Miqewa tayi ahankali cikin nutsuwa ta nufi inda fridge yake ta Bude tareda dauko ruwa mara sanyi sosai ta dawo ta kawo masa.


Bai karbi ruwan ba ita ya juyo ya zubawa idanuwansa yanajin Kansa na daukan zafi sai kawai ya miqe tsaye tareda karban ruwan a natse ya Dan sake kallanta yayi mata bye ya fice daga office din.


Yana fita Kai tsaye ya shige lift ya sauka ya fice
Yana Isa mota Naseer ya Bude masa ya shiga ya rufe suka bar kaantes din gaba Daya.


Highbridge yace kawai a wuce dashi sbd Kansa Daya dauko ciwo kawai.


Suna Isa yace Naseer ya koma office shi zai huta anan idan yagama zai koma gida da Kansa.




Itama can Yana ficewa daga office din ta zube kan kujera tareda Dafe kirjinta da zuciyarta ke bugawa da sauri sai alokacin tafara kokarin daidaita nata numfashin itama Daya gama yamutsa.


Da yamma Koda ta koma gida itama ciwon Kai takeji da zazzabi ga ciwon mara Dan haka wanka kawai tayi Tasha green tea me zafi sosai ya taimaka ya rage mata ciwon marar ta kwanta bacci da wuri.


Shima sai dare ya dawo Yana dawowa ya shige ya kwanta sbd ciwon Kai dakuma tafiyan data kamasa dole a jibi duk akan meeting din dayayi da Kaantes company.




Safnah ma kusan itama ciwon kan me tsanani dana zuciya take fama dashi sbd tinda ta shige daki ko palo Bata fitoba gabaki Daya firgice take a tsorace da kaante villa din gabaki Daya sbd ganin takeyi Bena zata iya ganinta,.
Jin takeyi gaba Daya gidan ya fita ranta so take tabarsa Takoma inda babu ko inuwan Bena Bare sunanta,
A daki take Kuma a bangarenta da yayi Nisa sosai danasu umme Amma ko waya zatayi Bata iya daga murya sbd Neman zautuwa Datake batason aji muryan kada mummunan kaddarar tsautsayi ta afko mata.


Haka ta Kuma kwana a zaune ko kaftawan Ido babu bare Wani bacci,.
Tinanikan dake cikin Kai da zuciyarta tini suka saka idanuwanta firfitowa zagayensu yayi duhu cikin kwana biyu sbd rashin rintsawa,


Bayan ruwa Datake Sha Suma hannuwanta na kakkarwa babu Abinda take iya ci,
Duk wannan masifar da balain da tashin hankalin akan Bena,
Shin menene amfanin Bena din a rayuwarta tinda ta zama mukullin buduwan sirrinta da komawa rayuwar dataci alwashin kome zata iya Yi da ta koma wannan rayuwar,


Idan tin farko har zata iya amfani da mahaifiyar data haifeta Dan guduwa daga wannan rayuwar to zata iya aikata komai ga koma waye Dan Hana kanta komawa baya.


Da wannan tinanin ta sake busar da zuciyarta dan cimma mummunan burinsu.
Dan haka ta shirya boye Kanta da Hana haduwanta da Bena duk tsanani duk wuya har sai cikin biyu sun samu Daya ko kawar da Bena daga doran duniya ko samun zama cikakkiyar matar da DD zai fara kusanta a tsakaninsu.
##MAMUH#
#DBENA
#TOO HOT
#WELCOME BACK ABABA
#SAFNAH BULAMA
#KAANTES
#HOTHOT
#ROMANCE
#LOVE
[9/4, 1:20 PM] MG: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
65
Pepper soup na qatan catfish ne da Kuma white rice da aka dafa tareda veggies sai sauce na kidney qanana aciki,


A cikin dakin suka zauna Amnah na jikin Nafisat tana Bata da spoon abaki ahankali ita Kuma Bena tana bawa Annenta cikin tsananin kulawa da soyayyan mahaifiyarta me tsanani.


Saida ta tabbatarda Annen ta Koshi kafin ta Bata fruit drink me mara sanyi Tasha tukuna Nafisat ta tattara kayan ta mayar basket ta Maida mota.


Har yamma tana gidan tana jiran dawowan Ababa taso rokonsa yabata Daman kai Annen taga likita Amma har magrib Bai dawoba Dan haka Suka tafi Annenta na kallanta kaman zatai Kuka,
Itama Saida tayi hawayen kafin ta iya tafiya tabar Annenta.


Gida suka koma Kai tsaye daki ta shige sbd ranta ya gajule da yanayin Annenta Kuma gashi dd babba Yanata tausanta sbd matiqar ba asirin kafin da Ababa yai mata a karya ba ko sace ta Akai kokuma akai dole aka dauketa zata iya ransa ranta sbd Hakan Sai Kuma idan shine da Kansa Ababan yace ta tafi yayi freeing dinta.


Data shige daki bayan tayi sallan magrib kasa riqe kukan Datake dannewa tin a gaban Anne tayi ta fasa kukan a hankali tareda cusa kanta cikin qafafunta.


Amnah data shigo ta taddata tana Kukan qarasowa tayi ahankali ta shiga jikinta ta lafeta tareda yin shiru sbd Bata taba ganin Mummyn nata na Kuka ba.


Saida Bena tayi kukanta me isanta hardana DD Daya da Abinda yayi mata da radadin kishinsa Datake ta dannewa duk sai datai kukansu Daman suna ranta danqare.


Wata alwalan tayo tareda wanka tazo tayi sallan ishai tana gamawa a daki Nafisat ya kawo mata yoghurt a glass cup Tasha ya isheta ta kwanta tareda cewa batada lafiya zazzabi takeji sbd tasan Hakan ne kawai zai saka abarta taji da Abinda yake cin ranta da ruhi.


Daga Zeenah har Umme sin shiga damuwan rashin lafiyan nata Amnah kuwa sukuku tayi sbd Daddyn da Mummynta sune walwanta,farin cikinta da rayuwanta.


Da daddare Shima Bai shigoba sbd Bai sauko ba,
Washe gari ma Bai shigoba ya tafiyarsa office.


Safnah gantalinta Bai bari tasan Bena ta dawo ba sai data kwana biyu tukuna sbd kullum Bata wuni gida idan ta fita sai dare.


Dd babba taje ta gaida harda yimasa girki na musamman
Baya cin girkin kowa yanzu saina Bena Amma Bai nunawa Safnah din ba ya saka mata albarka tareda godia.


Qin zuwa sashen Umme tayi tinda taji Bena ta dawo Dan haka ta sake haukacewa tareda mayar da hankali ga Jan hankalin mijinta Wanda haryanzu suke yanda suke.


Bena kuwa cikin kwana biyu ta shiga Wani mummunan halin sanyi da damuwa,.Sam ta Dena zaman Palo sai ta tabbatarda lokacinda bazai shigoba take fitowa ta zauna cikinsu Umme
Zeenah ma aikinta baya barinta zama gida sosai itama Kuma.


Amnah halinda mummynta take ciki itama ya taba ta Sam ta Dena walwala da Hayaniyan yarinta Datake sosai ta sauya.


Shi Kansa a kwanakin gabaki Daya ya sauya baya cikin walwala ko sakewan,koyaushe ransa ba Dadi a hade fuskansa take
Duk sai abin ya sake taba Amnah Takoma kaman iyayenta ba walwalan.


Shine yafara kokarin dawowa daidai sbd Amnah data fara harda rashin lafiya sbd Bata Saba da qunci ba batama San Saba.


Duk yanda ya sauya Yana shigowa yanzu kullum Bena Bata taba yarda ya ganta ba gabaki Daya ta kaucewa duk Abinda zai hadasu.


Amnah idan zatai vidcall dashi barin dakin takeyi hakama idan har taji alaman Yana bangaren Bata fitowa saiya tafi.


Babban Qarin kame kanta ma harda matarsa Bata shaawan haduwa da ita Sam bare shi.


A haka suka share kusan sati biyu
Duk lokacinda matarsa akace ta shigo Bata fita sai ta fice hakama Shima duk akace Yananan Bata fitowa din.


Dd babba idanuwa ya zuba musu hakama umme sbd batasan meke damunsu ba kowannensu Kansa ya dauki zafi,dad kaante kuwa baimasan meyake faruwa ba.


Yau Zeenah bazata office ba hutawa zatayi Dan haka Suka shirya itada Bena din suka fita outing ko kansu duka zai sake.


Sunyi shopping sosai sunci tsadaddiyar abinci a restaurant na kaantes hotels and suites daga Nan sukas shiga VIP saloon and beauty parlor dake cikin kaantes hotels and suites din.


Ba Wani gyara dasuke buqata sbd kusan duk sati zuwa sati biyu saisunzo gyaran Amma tinda sun shigo Basu fitaba saida suka sake shiga Akai musu manicure and pedicure dasu gyaran Kai da sauransu.


Suna fitowa Bena tace Zeenah ta ajiyeta gidansu zata duba Annenta.


Bayan sun Isa Bata bari Zeenah ta shiga ba tace ta tafi kawai idan ta gama zata kira Abbakar ya turo driver ya dauketa.


Hakanan Zeenah ta barta ta wuce Amma taso duba Annen itama Amma Bena da dubara ta hanata sbd Bata son a ga Annenta cikin halin Datake ciki.


Yau dinma Bata tadda Ababa ba Dan haka gyara Annenta tayi fes ta sake tsaftace mata dakinta tsakan gidan kaman bola sbd babu me shara sai Anne ta Dan dawo daidai tayi musu shara
Shi girki kuwa yanzu Ababa kusan kullum na Siya yakeci lafiyayye hande ma wataran na Siya wataran Anne keyi idan tana daidai, Annen ce kawai kusan yunwa tafara shigowa cikin ciwon nata sbd saisun rage suke Bata.


Ganin Hakan sai Bena ta kawo Mai Aiki gidan ta ringa shara da wanki da girki Amma wahala tasaka me aikin kwana daya tayi ta gudu,
Bayan ita wata ta sake kawowa itama kwananta biyu ta yiwa Ababa Satan da Saida Bena din tayi masa ranko Kuma ya Yanke babu me aikin da zata Kuma kawo masa gidansa daga lokacin.


Ana gama sallan magrib akazo daukanta ta koma gida.


Wanka tayi ta saka straight pencil Sisley doguwan Riga me laushi data kwanta jikinta gabaki Daya bawai matsewa ba.


Qaraman hula ta saka tareda ziro slippers tana fitowa palon Yana shigowa Shima sanye cikin black Ralphs da slippers na chanel fuskansa fresh Yana fidda Wani kwarjinin da sirrin kyau.


Bata dakata ba ta juya kawai zata nufi hanyar kitchen babu tsammani ya riqota sbd ya kasa Hana kansa barin ta tafi.


Baya ya dawo da ita bayanta ya jingina da kirjinsa qamshinta ya shiga hancinsa take ya rufe Ido Yana son magana ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login