Showing 93001 words to 96000 words out of 192750 words

Chapter 32 - ZAFIN KAI COMPELET BOOK BY Mamuhgee.txt

12 Dec 2024

7157

ajikinta ta juyo da sauri a tare hannuwansu suka tarota tafin hannunta na sauka kan bayan tattausan hannunsa.


Amnah kuwa qanqame daddynta tareda riqe hannun Bena Daya tana kokarin fasa Kuka a tare suka ambaci sunanta cikin muryoyinsu masu nutsuwa da taushi.


Hannunsa da nata yake Kai ta kama ahankali zatai magana ya dago fararen idanuwansa ya zuba mata Wani Kallon Daya sakata Neman rikicewa tana sake kama hannun batareda tasan hannunsa take kamawa tinaninta na Amnah ne da rudewa tasakata kasa tantance girman hannun sbd taushinsa kaman na baby Amnah din.


Wani kallan ya sake zuba mata lokacinda ta sake damqe hannun da tafin hannunta da itama yakeda laushi,
Wanna Karan hannuwan nasu ya kalla Yana kame fuskarsa da ita firgitata kyawunta da tsananin kwarjininsa keyi..


Sai alokacin ta ankara da sauri Janye hannunta hannuwanta na Dan rawa da sanyin murya mara karfi ta furta "Sorry" ta juya da sauri tayi gaba a Dan rude ko gabanta Bata Gani Allah yasa flat Hermes shoes ne qafarta shi ya hanata faduwa.


Tana shiga Palo Bata tsaya ba gaida Umme tayi ta wuce dakinta ta shige.


Tana shigewa ya shigo da Amnah fuskarsa freshe as always kananun guntayen kaya ne jikinsa idan dai fitan Shan iska ce zaiyi.


Kallansa Umme tayi cikin farin cikin ganinsa ta miqa masa hannu tana masa sannu da dawowa.


Kama hannunta yayi da hannunsa Daya yana sake mata qayataccen murmushin farin cikin ganinta Shima.


Amnah dake jikinsa ta shafa fuskarsa tana Jan dogon hancinsa tace


"Daddy muje na nuna maka kayan da mummy ta siyo mun data dawo kaji."


Tashi daddy muje ka Gani please....


Saukowa tayi jikinsa ta tsaya ta kama hannunsa Daya da 'yan qananun hannuwanta biyu tana jansa.


Kallansa Umme tayi tana dariya tace


"Kaje ka Gani tukuna mayi magana hankali kwance sbd Amnah idan bakaga kayan Nan nata ba bazata bari kowa yayi magana da daddynta ba.


Miqewa tsaye yayi ahankali Yana daukanta batareda tinanin har lokacin dakinta Daya da mummynta ba tinda yasan ko uban siyayya Dayake Aiko mata dashi dakin ta ma bazai daukaba sai ana rage wasu bare ace daki Daya take da mummynta da itama tanada kayanta Dan haka ya dosa dakin Datake nuna masan suje.


Bude dakin yayi Kai tsaye suka shigo ya tura kofar ya rufe Yana juyowa ya tsaya cak Yana kallan dakin dake cike da qamshin Mummynta Daya gama kama dakin da sanyin Acn Daya dada sanyayasa.


White clovia bra dinta dake yashe kan lafiyayyan gadon dakin idanuwansa suka sauka ya dauke idanuwansa daga gefen Yana juyawa zai fice Amnah ta taresa da cewa


"Ga mummy Nan ma ta fito ta dauko ma ka Gani Daddy."


Benazir data fito Kai tsaye daga toilet daga ita sai short sleeveless gown me kwantawa ajiki wanka ta shiga Yi Amma ta kasa sbd Jin ana Kiran sallah sai tayi sallah tukuna Dan haka alwala tayo ta fito Daman ta cire doguwan rigarta da bra Daya dameta.


Maganar Amnah ta ankarar da ita suna dakin da sauri ta dago tana dubo gurin kofar daidai Yana dauke Kansa daga kallan fuskansa a fuske yaso juyawa Amnah ta hanasa shikuma Daman bazai batawa Amnah din ba Dan haka kaman baima San da wanzuwarta ba a dakin suka nufi kujera ya zaunar da Amnah din kafin yayi magana Benazir tini Takoma cikin toilet din tana Jin Amnah nata kiranta tayi kaman bataji ba.


Jansa Amnah takuma Yi har kan gadonsu ta ringa dauko masa duk Abinda takeson ya Gani Yana sauraranta kawai batareda ya iya magana me tsayi ba Daman sauraran surutun kawai Yana Basa nutsuwa da farin ciki.


Da kanta ta gaji Amnah din suka fito ba Dan Hakan ba shi zai iya zama taita masa surutun har kowane lokacin zasu Kai ba damuwansa bane.


Suna fita Benazir ta fito Dan tini tayi wankan data fasa.


Sallah tayi Shima lokacin an tada sallah tini ya fice zuwa masallaci.


Tana idar da sallah ta dauki wayarta tana duba sakonnin emails na yan ayyukan da dd babba yasa aka fara Bata Dan gwada zurfin hankalin ilimin data yo akan harkan business gashi akwai acct sosai cikin kanta kaman me.


Aje wayan tayi ta miqe tareda zare abayan sallarta ta fito jikinta sanye da Celine English straight gown da Hula mara nauyi akanta riqe da hannun Amnah Da itama tai mata wanka ta shiryata cikin black pyjamas na Yara masu tsantsi tana hammar bacci gashi Bataci abincin dare ba.


Gurin su Umme dake Palo zaune ta barta ta nufi kitchen da kanta Dan hado mata tea Dan yawanci idan taci abinci me nauyi da dare baya Bata lafiya sosai shiyasa da daddare an sabar mata baa Bata Abu me nauyi se light.


Chocolate custard ta damo mata da kanta ta zuba madaran sosai aciki Bata saka sugar ba ta fito riqe da cup din tana Dan juyawa a hankali ta dawo.


Zaunawa tayi gefen Zeenah tana sake juyawa sbd ya huce.


Sallamarsa ta sanyata kasa dagowa taci gaba da hurawa se gashi baima zauna ba yayiwa ummensa goodnight ya fice.


Tana gama bawa Amnah custard din ta kira Nafisat ta dauketa ta tafi sake gyarata Ta Kwantar da ita sukuma suka nufi dining cin abinci.


Tana gamawa taje ta Sako babbar jallabiya akan rigarta ta nufi gurin dd babba kaman yanda ta Saba duk dare kafin shigewa saita je ta gansa.


Bata Wani jima ba kaman yanda ta Dan Saba jimawa har dai idan takai masa abincinsa da kanta ne sbd mafi yawan lokutan idan tana gida itace ke masa girkinsa na musamman me qara lafiya da inganci.


Tana dawowa babu Bata time ta kwanta take bacci ya dauketa itama.




Washe gari zata fara zuwa office ganin Wani aikin da dd babba yasakata duk da bawai bar mata aikin yayi ba gabaki Daya ya sakata joining fahat kaante ne babban yayan Siyam din Mum Khadija.


Dayake da 'yar gaban goshin dd babba akafi saninta Dan haka ta samu tarba da respect sosai daga wainda suka samun ganinta Dan company din nada girman da kowa Yana can gurin sabgar gabansa ba kowa zai ganka ba harka tafi ka Gamo ka fito.




Fahat kaante yaji Dadin ideas dinta da wasu suggestions data Bada tareda Yaba nata ilimin Dan haka sosai yaji Dadin Aiki da ita a wunin sai yamma suka fito tare ta wuce kaantes Shima Yana biye da ita suna isowa shi ta gate din baya Wanda acan nasu bangaren yake ita Kuma ta shigo ta gate din gaba a Dan gajiye.


Tin a gurin parking taga Rolls-Royce black haraban gidan ta fahimci Daddyn Amnah na gidan Dan haka ta shigo a Dan natse cikin sa'a baya part dinsu Dan haka Kai tsaye ta wuce bedroom dinta.


Ko da tashiga tana waya Dan haka tana shiga Bata Kalli inda gadanta yake ba ta nufi closet tana ajiye handbag nata da key na mota tafara zuge zip din gaban doguwar jallabiyanta.


Rufe kofar dakin taji a juyo tana kallan kofar tana kashe wayarta cikin mamaki,


Bata ga kowa ba Kuma tabbas rufe kofar taji anyi,
Dawo da kallanta kan gadonta tayi ga mamakinta sai taga Amnah kwance tana bacci.


To waye ya bude dakin?
Shigowa Akai ko fita?


Numfashi ta sauke ta koma ta qarasa tubewa ta shige toilet kawai.


Bayan tayi wanka gajiyanta ya sake tayi sallah ta tashi ta nufi Amnah zata tada ita sbd baccin magrib zaisa ta kasa baccin dare.


Tana taba ta taji jikinta da zafi sosai
da sauri ta Kalli fuskatarta tana sake taba wuyanta zuwa goban kanta taji zafi sosai.


Mummunan faduwa gabanta yayi ta janyota jikinta tana Kiran sunanta ahankali cikin tsananin damuwa da kulawa tace


"Meya samu my baby."


Motsawa Amnah din tayi ahankali tareda Dan Bude idanuwanta tana ganin mummynta ta sake shigewa jikinta tana lafewa ahankali tareda Dan Kiran sunan Mummyn.


Rungumeta Bena tayi tana cewa


"Baby zazzabi kikeyi?
"Meyake Miki ciwo?
"Kinsha ruwan sanyi sosai kokuma qasan ruwa right?


Numfashi ta sauke tareda saukowa gadon ta mayar da Amnah din ta Kwantar ta fito Kai tsaye kitchen ta nufa inda maganinsu suke cikin Wani Dan qaramin fridge Daya da aka ware a kitchen kawai sbd saka maganin Amnah.


Paracetamol ta dauko ta Kalli Nafisat dake kokarin jera kayan da aka wanke tace ta hadowa Amnah white indomie ta kawo mata.


Daki ta koma tana shiga ta zauna bakin gadon tareda janyo Amnah jikinta ta rungume duk ranta na dagulewa sbd Amnah itace kuzari da farin cikinta bayan Annenta,.
Hankalinta ba qaramin tashi yake ba idan Amnah tafara zazzabi sbd komai qanqantar ciwo jigatar da ita yakeyi sosai taita wahala Dan haka hankalinta ke Neman tashi.


Maganin ta bata cikin kulawa da lallabawa kafin ta goge mata fuskarta da tissue tana ajiyewa sai ga Nafisat ta kawo mata Abinda tace din.


Zaunar da ita tayi jikinta cikin lallabawa da kulawa ta fara Bata indomie din Nafisat kuwa ta tattara kayan maganin da tissue zata fita dasu.


Kawar da Kai Amnah din keyi tana girgizawa tace


"No mummy banaso na koshi."


No please sweety kici kadan ok???


Sake girgiza Kai tayi tana lafewa jikinta tace "No I don't want"


Kallan Nafisat tayi ta miqa mata plate din jiki ba qwari tace


"Ki hado mata tea mara zafi sosai"


Karba Nafisat tayi tana cewa to ta fice da sauri.


Bayan fitan Nafisat shafa kanta Bena tayi cikin kulawa kaman zata hadiyeta tace


"Sweetyn mummy me kikeson kici to?
Zaki Sha warm yoghurt?


Girgiza Kai Amnah tayi a hankali


Bena tace "but baby you have to take or eat something before going to bed ga Kuma magani kinsha"


Kuka Amnah ta fashe dashi ahankali tana cewa


"No mummy ni banason abinci,bana Jin yunwa."


Numfashi me dumi Bena ta sauke tana rarrashinta zuciyarta ba dadi.


Nafisat ce ta kawo tea din ta karba ta saka Amnah Shan nasa dole cikin tausasawa Yana gama shiga tafara Amai sukai toilet.


Aman datayi ya saka Dan kuzarinta tafiya tareda tsananta zazzabin ta fara Kuka daqyar Bena tai mata wanka da ruwa me zafi ta dawo da ita ta shirya ta Kwantar tini Nafisat Daman ta sake gyara dakin ta sauya zanin gado sabo duk da aman be taba ba Amma sbd tsafta da kiyayewa.


Rage sanyin Acn tayi sosai kafin ta fice daga dakin.


Itama Bena din Saida ta sake wanka tea kawai Nafisat ta kawo mata Tasha ta kwanta Batama iya fitowa ba.
##MAMUH#
#HOT
#DBENA
#ROMANCE
#DEEP
[8/29, 9:06 PM] MG: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
52
Kasa bacci tayi sbd zafin jikin Amnah datakejin Yana shigarta ahankali Yana dumama nata jikin,


Umme ce tashigo jinta shiru ta tadda cikin wannan halin itama cikin damuwa tace ko Akira likita cikin dare.


Cikin nutsuwa da sanyin jiki Bena tace


"Kodai a bari zuwa da safe Umme sbd dare yayi Kuma ta samu bacci may b kafin da safen ta warware inshallah."


Ok Allah yasa Hakan Amma dazu fa Rana tana tareda daddynta har yamma har fita sukai suka dawo
Shima inaga Bai San zazzabin ya shigeta ba harya wuce.


Numfashi kawai Bena ta sauke sbd gwara da Bai sani din ba Dan dole dayansu zai kasance da Amnah din ita Kuma idan Amnah na ciwo Bata iya barinta sbd damuwa da susucewan datakeyi.


Bayan fitan Ummen Zeenah tashigo ta hawo gadon Tana shafa Amnah din daga Nan bacci ya daukesu su duka anan Zeenah ta kwana dasu.




Washe gari da safe jikin nata da Dan sauki ba laifi,.
Kaman bazata iya fita tabarta haka ta ringa tarairayarta har kusan 10 kafin ta shirya ta fice zuwa office bayan taje gurin dd babba suyi magana.


A office yau hankalinta ya Dan rabu biyu so Bata Wani jimaba taba gama aikinta ta juyo gida tareda fahat Daya baro motarsa office suka dawo tare.


Ta gate din gaba suka shigo sbd yace zai duba Amnah din da babu lafiya.


Tare suka fito motar Yana kallan yanda duk batada kuzari ya saki Dan murmushi me sanyi Yana mamakin soyayyar datakewa Amnah duk kawaicinta akan komai Banda Amnah.


Itace a gaba gurin shigowa palon kafin shi a kan Amnah dake jikin daddynta idanuwanta suka sauka Shima Kallo Daya yayi musu ya dauke Kai Yana cigaba da wayar Dayake Yi da likitan dazaizo ya duba Amnah jikinta ya sake rikicewa da yamman.


Tana ganin mummynta ta miqa mata hannu Daya tana fara hawaye da Kiran sunanta ahankali.


Qarasowa Bena tayi ta kama hannun Amnah din wadda ta janyota ta zauna ba shiri tana kokarin matsawa ba dama sbd riqetan da Amnah din tayi tana hawaye cikin zafin ciwo.


Jikinta dake gugan nasa sbd kusancin da yayi yawa yasa ta Dan kallan gefen Umme dake gaisawa da fahat
Shi kuwa har lokacin Bai motsaba barema ya nuna yasan da Wani ya zauna gefensa.


Ahankali daqyar ta iya Bude baki murya a sanye tace


"Amnah muje daki naji Yaya jikin naki,
Na sake baki magani.


Lafewa tayi jikin daddynta tana Dan girgiza Kai ahankali Bata iya magana.


Fahat Daya gama gaisawa da Umme dawo da kallansa kan DD yayi ya masa magana suka Dan gaisa sama sama sbd Dawood din da hankalinsa ke kan Amnah.


Miqewa yayi ya tafi bayan duba Amnah itama Bena data kasa nutsuwa da zaman nasu ahakan ta zame hannunta daga na Amnah ta miqe ta bar palon.


Daki ta Isa tana sauke ajiyan zuciya a boye kafin ta wuce tayo alwalan sallar laasar data wuceta ta fito tayi.


Tana idarwa ta fito sbd takasa samun nutsuwan jikin Amnah.


Ko da ta fito likita yazo yana duba Amnah din.


Gefen Umme ta silalo ta zauna a hankali tana sauraran Abinda likita ke fadawa DD.


"Sanyi ne kawai yake son Dan shigarta sai a kiyaye barinta wasa da ruwa gaskia"


Juyawa yayi ya Kalli Bena dake bayan Umme likitan yace


"Madam ai last time na fada Miki Hakan please a sake lura sosai a kiyaye."


Ajiyan zuciya ta sauke tana gyada masa Kai ahankali.


Magani yace zai Aikowa Amnah din yayi musu sallama ya wuce.


Bayan fitansa bacci ne ya dauke Amnah din har lokacin tana jikinsa.


Shima zazzabin yakejin Yana Neman kamasa sbd zafin jikinta da tin dazu yake shiga jikinsa Kuma shi fatansa batada Wani karfi da wuri wasu abubun ke saurin shigesa.


Abincin dole Bena ta miqe taje dining taci tana gamawa tayi dakin Zeenah Datake ta fama da nata aikin kwana biyu sbd itama zatai joining kamfanin Amma Kuma tana buqatan attending wasu online classes na sati uku ga service dasuke Shirin zuwa wannan Karan inshallah itada Bena din.


A dakin suka zauna itace ta ringa fahimtar da Zeenah din wasu abubuwan na course nata datai attending Wanda ya banbanta dana online da Zeenah keyi Kuma gashi Wanda Bena tayi dama ce da sai Dace ake samunta yanzu bazaa sake course din ha sai after like 3 years.


Har kusan 9:40 tana dakin kafin ta fito Takoma dakinta tana mamakin Ina Amnah ko tana dakin Umme.


Bedroom dinta ta Bude ta shiga Kai tsaye..
Ac din Dayake kashe ya saka mahaukacin qamshinsa yiwa dakin Wani irin gaurayar data sakata kallan gado Kai tsaye.


Zaune yake bakin gadon har lokacin Amnah na maqale dashi taqi yarda ya tafi yabarta.


Idanuwansa Wani laushi sukai da suka sakata rikicewa tana rudewa da kallansu tafara kokarin juyawa a hankali cikin Wani lazy sauti yace


"Kinsan meye time kuwa?"like kinsan ana duba time kuwa??


Dakatawa tayi tareda kasa fita tana daidaita numfashinta dake Dan fita da qarfi ta juyo ahankali batareda ta kallesa ba ta Kalli Amnah wadda da alama tana Jin zazzabin sosai har lokacin sai taji jikinta ya mutu ahankali ta Dan dago tanasan kallansa Amma ta kasa iya sake kallan idanuwansa ta Bude baki ahankali ta furta "sorry na bari kayi having time naka da ita ne"


Bai iya cewa komai ba sai kallan da yayi mata na minti Daya kafin ya Dan sauke numfashi Mai dumi da zazzabin dake cinsa Shima yakai hannu zai Zame Amnah ta sake qanqamesa cikin bacci da radadin ciwo tareda ambatan sunansa cikin bacci da qaraman muryanta me taushi.


Shiru sukai dukkaninsu suna kallanta shi Kuma zuwa lokacin zazzabin yakeji sosai Yana buqatan zuwa gida sosai.


Lumshe idanuwansa dasuka sake saka Bena Neman rudewa ga ciwon Amnah da riqesan da Amnah tayi ga idanuwansa da duk ya motsa su saita ji tana Neman rudewa.


Ahankali ya dago ya Kalli Bena din jinta shiru takasa qarasowa ta karbi Amnah din daga jikinsa.


Ganin kallan da yayi mata ya sakata takowa ahankali ta iso gurin hannuwanta na Dan rawa ta ranqwafo takai hannuwanta cikin sanyi ta Dora akan na Amnah dake qanqame da jikinsa.


Dumin numfashinsa Mai zafi ne ya sauka wuyanta zuwa cikin rigarta ahankali take rawar hannunta ya qaru ahankali ta Dan rintse idanuwanta tana Kai hannunta Daya zata Ciro Amnah numfashin nasa Mai dumi ya sake saukar mata a fatan wuya ta Bude idanuwanta dake rintse ta kallesa daidai Shima ita din ya kalla ganin hannuwanta na rawa ahankali.


Kallansa tamkar wata fitina ce ga duk Wanda yayiwa irin wannan kallan na cikin tsakiyan Ido Dan haka haduwan idanuwansu ya sakata miqewa ahankali daga raqwafan da tai tana cika masa hanci da qamshinta Daya sake tsananta zazzabinsa.


Hannunsa Daya taji akan nata daidai lokacinda taso matsawa baya zata bar gurin sbd saukan dumin numfashinsa fatan jikinta zazzabin itama zai saukan mata.


Tinda take rayuwanta yau ne ranar farko da namiji yayi mata irin wannan rikon Dan haka Saida bugun zuciyarta ya tsaya cak ta rufe idanuwanta ahankali kafin tayi Wani motsi ya Dora hannunta kan Amnah ya Zame a hankali ya miqe ya fice daga dakin yabar dakin da fitinanniyar qamshinsa.


Kasa motsawa tayi tsawon seconds tukuna ta iya motsawa ta silale ta zauna bakin gadon inda ya tashi har lokacin tana sake Jin saukan dumin numfashinsa akan fatarta.


Gyarawa Amnah kwanciya tayi kafin ta miqe ta shiga toilet Bata Wani jima ba ta fito ta saka pyjamas masu tsantsi ta hau gadon ta kwanta tareda hade kanta dana Amnah pillow Daya tana Jin qamshinsa na shiga hancinta a duk numfashin da zata ja.




Qarfe 3 na dare jikin Amnah din ya sake tsananta zafi ko Kuka da rigima Bata iyawa Wanda ya saka hankalin Bena mummunan tashi ta fara hawaye tana shafa Amnah din.


Magani ta sauko ta sake Bata ko gamawa batai ba Amnah ta amayo sa jikinta na sakewa Dan haka hankali tashe ta janyo wayarta ta kira Nafisat daga bangaren masu aiki saiga Nafisat din tana wartsakewa daga bacci.


Motsin shigowan Nafisat sashen ya saka zeenah fitowa itama sbd Bata jima da kwantawa ba itama karatu ta kwana Yi.


Ganin halinda Amnah ke ciki ya saka Zeenah dauko wayarta ta kira DD sbd Umme na sashen dad.


Bena kuwa toilet ta shiga tayo Wani wanka sbd Amai dake jikinta ta fito daure da towel purple,lokacin Nafisat ta sake sauya zanin gado ta gyara dakin duk da tsakiyan dare ne Amma dole tayi aikinta.


Amnah ma tini aka goge mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login