Showing 129001 words to 132000 words out of 192750 words
hanya,
Tinda taga Bena a yanzu batada nutsuwan ruhi da zuciyarta,
Kowane sekan,minti ko daqiqa datakeyi Bena barazanar rayuwarta ce.
Bazata iya daukan lokaci a cikin wannan boye boyenba.
Shin Tayaya ma Bena ta hadu da Bilal ne yayi mata ciki tin farko?
Ababa ya mutu ne kokuwa ya haukace ne da Bena har tayi ciki a gidansa Kuma take yawo a Raye haryanzu Dan kuwa idan Ababansu na Raye batajin akwai kudi ko muqamin da zai hanasa daukan matakin rashin Imani akan kawo cikin shege gidansa.
Tana Isa gidan aka wangale mata qaton gate din ta shige Mai gadi na mata barka da zuwa ko kallansa bataiba ta wuce ciki Rabi na bayanta suka wuce sashen momy batareda ta biya sashen hajiyarsu ba.
Kai tsaye bedroom din momyn ta wuce lokacin tana waya da yayanta dake can asalin garinsu Niger akan akwai yiyuwar tazo kusa idan abubuwanta suka fara rauni sbd tareda shi suke yawon dajin bin bokaye.
Safnah na Jin wayar da momy keyi ta zauna kan kujerar dakin tareda rafka mugun tagumi tana tafasan zuciya.
Gama wayar momy tayi ta kalleta tace
"Ki Kwantar da hankalinki na fada Miki ko zamu rasa komai muyi yawo tsirara bazamu bari asirinmu ya tonu ba,
Ke kina tinanin daula kawai zamu rasa Amma ba rasa daulan ne yafi firgita ba Abinda zai biyo baya.
Shiru Safnah tayi sbd azabar zafin dake cin zuciyarta ya hanata iya furta komai.
****Bena sukuku ta wuni a ranar sbd Abu biyu Daya tsaya ranta ya gajule farin cikinta da walwanta.
Na farko zuwan Dr Ashley ya tinatar da ita tareda tabbatar mata ba lallai gaskiyar haihuwar Amnah na cewan itace ta haifetaba ya boyu har abada,
Tayaya kowa zai karbi wannan gaskiyar?,
Tayaya lamarin zai zo mata?
Ita kanta Amnah idan taji ba itace ta haifeta ba wane halin zata shiga,Kuma kaman batai mata adalci ba sbd ko adduarta iyayenta da suka rasu Basa samu duk da kasancewarta yarinya qarama.
Duka jamaar kaantes dasuke so da kaunarta batasan da wane idon zata kallesu ba.
Numfashi ta sauke tareda rufe idanuwanta ta Bude ahankali tana sauko gadon da rigarta Daya cire mata kafin ya tafi.
Canja kaya kawai tayi ta lallaba ta fito ta zauna Palo tareda fara Kallo Dan hana kanta tsananta tinanin da batasan amsar duk Abinda take tambayan kanta ba.
Fruits qananu yanka Nafisat ta kawo mata a bowl me kyau da Dan sanyi kadan tafara ci ahankali tana Dan Kallo sama sama batama Wani Ganewa sbd hankinta cikakke baya kan Kallon.
Tana Palo aka aka dawo da Amnah daga school
Da kanta taje tayi hidimanta yau sbd Jin takeyi tsananin son 'yarta ya qaru cikin ranta sbd fargaban ranar bayyanar gaskia ga Amnah dinta tasan ba itace ta haifeta ba.
Gabaki Daya Sauran wunin tareda Amnah a jikinta ta qarasa shi ita kanta Amnah din saita tace Mata yau mummy kin qara sona ko?.
Murmushi kawai tayi tana sake shafa bayanta tace "Rabin Raina kullum qara sonki nakeyi koyaushe"
Sai dare ta kunna wayarta sbd Tama manta da wayar kashe take Dan haka tana kunnawa kira na shigowa fitowanta wanka kenan daga ita sai qaramin towel din Amnah da Bata rabo da daurawa wasu lokutan.
Batada niyar duba Kiran sai tagama shiryawa taga waye me kira a Time din.
Amnah Dake kan gado ta Kalli wayar taga ba sunan Amma take ta Gane numbern daddynta ne sbd duka Numbers dinsa ta haddace su a kanta da farin ciki ta dauki wayar Kai tsaye ta daga tana washe baki da farin cikin ganinsa sbd Vidcall ne.
"Daddy shine kayi tafiya Ina school ko"
Ajiyan zuciya ya sauke a hankali tareda kallan Amnah din yanajin nutsuwa nashigarsa sbd ganinta kawai farin ciki da nutsuwa yake sakasa.
Cikin nutsuwa yace
"Angel ta yafewa Daddy next time zai kiyaye,kina lafiya right?
Murmushi tayi tana cewa "ok na yafe Amma nxt time bazan yarda ba, lafiya na kalau"
Ajiyan zuciya ya sake a salihance kafin ya Danyi shiru na sakanni tukuna ya Bude baki cikin nutsuwa yace
"Mummynki fa?tana lafiya right?I mean taji sauki ta Dena ciwo da kukan ciwo??"
Amnah dariya tayi tareda juya cameran zuwa ta baya Dan yaga mummyn tata dake zaune gaban mirror kan kujera tana shiryawa cinyoyinta dake bayyane suna daukan Ido ta gama shafawa tsadaddan body oil da Dan body spray a jikinta.
Zubawa Bena din idanuwansa da sukai laushi tinda yazo yayi yanajin sauran nutsuwan da baigama samuba tana qarasa shigarsa kaman Wanda Akewa caji haka yaji energy dinsa na dawowa daidai.
Ganin yanda yayi shiru ya zubawa mummy dinta idanuwa Yana kallanta cikin nutsuwa batareda yace komaiba.
Kallan mummyn nata itama tayi ta dawo da kallanta kan daddyn tace
"Daddy zakayi Kuka ne sbd mummy ba lafiya??
Taji sauki fa,ta warke gashinan tana komai da kanta lafiya kalau"
Sai alokacin Bena ta juyo ahankali ta kalli Amnah din sbd batasan camera din baya na Aiki akanta bane
Hannunta Daya ta dada ta Dora kan baki tayi mata alaman tayi shiru.
Shi kuwa Hakan datai ya sakasa sakin murmushin da baiyi Niya ba na maganar Amnah da ita kanta Abinda tayi din.
Amnah ma dariya tayi zatayi magana Daddynta yayi mata alaman shima tayi shirun karta fadawa Mummy din Yana camera na kanta.
Gyada Kai Amnah tayi tana dariya tareda gyadawa daddynta Kai.
Ya jima a Hakan Yana kallanta sbd iya kallan ma a yanzu dayake nesa ya ishesa.
Bena datake Jin kaman idanuwansa na kanta sbd aduk lokacinda yake kallanta tana Jin kallansa kanta,
Da zata saka kaya hakanan taji Bata sakeba sai kawai ta koma closet na kayansu ta shiryo a can ya fito sanye da Riga da wandon bacci guntaye iri Daya Dana Amnah ta qaraso gadon lokacin Amnah tafara gyangyadi Kuma har lokacin Kiran Bai Yanke ba.
Cire wayar tayi daga hannun Amnah ta gyara mata kwanciya kafin ta hau gadon ta rufe Rabin jikinta ta dauki wayar ahankali zata duba Abu sai ganinsa tayi zaune sanyeda qananun kayansa dayafi sakawa Yana Shan Abu a cup ahankali da alama ko coffee ko wani abin me zafi sbd Dan tiririn Dayake Yi.
Hankalinsa baya kan wayar Shima Saida ya Dan juyo sai yaganta zaune itama tana kallansa ta Dan dauke Kai ahankali sbd batai niyar barin yaganta tana kallansa ba jikinta duk na mutuwa.
Kallan da yayi mata ya sakata sauke Kai ahankali kafin ta Dan dago kadan tace
"Barka da Isa lfy"
Bai amsaba Saida ya kurbi Abinda yake hannunsa a natse kafin ya kalleta ya amsa Yana cewa
"Yaya jikinki?"
Kallan juna ta dago sukai kafin ta amsa tana Dan narkar da idanuwa sbd hakanan taji tana tinawa da yanda ta ringa Jin azabar marar kwana Biyun.
Duk yanda yaso suyi fira ko magana sosai Basuyi ba sbd baisan me zai ringa cewa ba,shi Idanuwansa ne maganarsa,zai iya wuni Yana kallanta da idanuwansa masu shegen kashe jiki da gigitata Amma bazai iya jero kalmomiba Dan baisan mezaita fada dinba.
Da kanta ta fahimci baisan me ake fada ba kokuma baisan me zai fada din ba Dan haka tayi masa goodnight ahankali tareda katse Kiran ta ajiye wayar tana Dan dafa kirjinta saitin zuciyarta ahankali tanajin wannan Karan bugawan datakeyi cikin sanyi da nutsuwa da Wani irin so Mai tsananin gaske na nutsuwa.
Zamewa tayi ta kwanta daidai tareda Jan rufarta har zuwa kirjinta tana lumshe idanuwanta da shi kawai suke buqatan Gani zahiran a wuni Daya kawai Jin takeyi kaman yabarsu kenan itada Amnah dinta.
Shi Kansa a can bangaren ajiyan zuciyan ya sauke me Dan sanyi tareda ajiye cup din hannunsa Yana rufe Ido sbd Jin kaman Kansa bazai iya daukan gudanar da har sati biyu a tafiyan ba.
*****Washe gari Bena bayan tafiyan Amnah school itama shiryawa tayi Dan tafiya office sbd zuwa office dinne zai hanata zama cikin tinaninsa da jiya zuwa yau yake Neman sauya mata nutsuwa.
Breakfast sukai dukkaninsu tare a dining tanaji Umme na tambayar Safnah kwana biyu Bata shigowa ko lafiya Kuma Bata kirata a waya ba.
A bakin Zeenah sukaji wai ta tafi gida sai D ya dawo.
Da mamaki Umme tace
" To shine bazata kira ni ta fadamun ba?
Ni banma San ta tafi gidan ba Dan ko Momynta Bata fadamun ba hakama hajiya munyi magana da ita jiya Bata fadan ba,
Ke waye ya fada Miki?
Batareda Zeenah ta Dena cin soyayyar doya da egg tareda chicken sauce din gabanta ba tace
"Umme meye na damuwa bafa yarinya bace,
Lokacinda tabar kaantes na hadu da motanta nikuma na dawo ta waya take sanarmun gida zata kafin D ya dawo."
Shiru Umme tayi tana mamakin Safnah din ta yanda koba itace ta haifi Dawood mijinta ba ai ita mamanta ne tinda qanwar mahaifinta ce Amma Bata fada mata ba babu Wanda ya sani ta bar kaantes ta tafiyanta,
Da zaman ne ita Daya bazata iya ba da sai itama ta dawo Nan bangarensu harya dawo tinda akwai isasun bedrooms lafiyayyi anan din.
Bena dai Bata dago ba bare nuna tasan ma me ake magana Akai bare Kuma saka baki sbd har cikin ranta mantawa takeyi wasu lokutan da yanada wata matar sbd ita tin farko ba guri Daya suke ba so koya koma gurin matarsa Bata tinawa.
Breakfast dinta taqara cikin nutsuwa kafin ta miqe tayiwa Umme sai ta dawo
Cikin kulawa itama ummen tayi mata adduan dawowa lafiya.
Tareda Zeenah suka fito ita Saida ta biya gurin dd babba ta share kusan 30 min acan kafin ta fito lokacin Zeenah ta jima da wucewa itama motarta ta nufa ta Bude ta shiga ta fice daga kaantes din.
A office dukkaninsu suka wuni sai yamma suka dawo kowa da gajiyansa Da aikin gabansa Dan haka kusan kowannensu ma a dakinsa yayi dinner Bena ce ma Bata Wani jima tana duba abubuwa ba bacci ya dauketa Dan haka Koda ya kira Amnah ce ta daga ta nuna masa Bena din datai bacci
Sai dayayi mata kallan mintina shida kafin ya kashe wayar Amnah ma lokacin baccinta yayi ya kwanta jikin mummynta tareda shige mata ta maqalqaleta tukuna bacci ya dauketa.
**Safnah da momy gabaki Daya acikin kwana biyun sun haukace Basa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali sbd ta tabbata bokan momy ya mutu inji qaninta Daya fara zuwa dubo mata bayan sunyi waya sbd baa shiga dajin Kai tsaye sai andubo Maka sbd hadarinsa.
Tinda labarin nutsuwarsa yazo musu suke Neman zaucewa sbd duk qaryarsu da burinsu akansa yake,
Koda suke maganar kashe Bena kisan da bazaa Gane sune sukai ba zasuyi mata Amma yanzu da alama 'danyar kisa zasu mata ta jininta a hannuwansu.
##MAMUH#
#DBENA
#HOT
#LOVE
#ROMANCE
#ABABA
#BILAL KAANTE
#SUMAYYAH ABABA
#SAFNAH ABABA
*_HAMMAK KITCHEN UTENSILS_*
*_INA MAABOTA GAYU DA SON BURGE BAQI DA ME GIDA?_*
*_SHIN KUNSAN HAMMAK KITCHEN UTENSILS SUNA DA QAYATACCIN KAYAN KITCHEN MASU KUDI DA MASU ARHA NA WAJE DANA GIDA NIGERIA_*
*_BA IYA ZUWA SHAGO KADAI KU SIYO BA HARDA AIKAWA SUNAYI KOINA HAKAMA SUNA ADASHEN KAYAN KITCHEN MANYA DA QANANA,MASU SAUKI DA MASU TSADA,NA WAJE DANA GIDA NIGERIA,_*
*_ZAKIYI ZUBINKI A HANKALI KI KWASHI DUK ABINDA KIKESO A AIKA MIKI ABINKI CIKIN SAUKI DA AMANA DAN HAKA SISTERS KARKU BARI AYI BAKU MUN SANI MUN SHEDAR HAMMAK KITCHEN UTENSILS SUNE THE BEST👍_*
@hammakkitchenutensil
Tarauni market Abba hamisu plaza block A shop no 8
or dorayi sabon titi before gidan man b i
Wa.me/+2348067376035
[9/5, 11:20 AM] MG: *_Arewabooks@Mamuhgee_*
70
Mutuwar bokan Jin sukai gwara ace Wani jininsu ne ya mutu,
Safnah tawar jiki ta ringa zubawa tana Neman kamuwa da ciwon zuciya Dana qwaqwalwa.
Wuni biyu da kwana daya sukai babu me cikakken hankalin kama Wani tinanin duk da sun San komai rintsi dole Wani hanyar zasu Kuma samowa tinda ba tsayawa zasuyiba su rissina.
Cikin baqin ciki Safnah dake zaune palo ta Kalli momy idanuwanta jajir tace
"Momy dole cikin gaggawa fa zamu San abin Yi,
Ina cikin hadarinda kowane lokaci wlh Bena zata iya ganina,
Tsawon shekarun Nan Muna auren miji Daya nida ita,
Nazo na tare gida Daya nida ita tsawon lokaci Muna guri Daya Muna rayuwa rabo da Sa'a yasa bamu taba ganin juna ba sbd Allah Yana Sona yasa ko a yanxu din nice na ganta Bata Ganni ba,bansan tsawon Wani lokaci Saar Nan zata bini ba,
Kada sa'a ta tayanke batareda munyi Shirin hakanba,
A baya banajin komai nake rayuwata sbd tinanin suna can cikin rayuwar Dana barsu acikinta bantaba tinanin ko a masu aikin irin duniyarsu Kaantes zan samu Daya daga cikin 'yan uwanaba shiyasa na sake bana shayin komai Dan nasan duniya biyu mabanbanta muke rayuwa ni da su,
Momy wlh tallahi asalina na bayyana Ababa saiya mun ratayar da bazan mutu ba bazan rayu ba,
Momy sunan Ababa kawai idan na Tina bana iya Jan numfashi batareda azabtacciyar tsoro da tashin hankali ba......
Cikin tata masifar data addabi zuciyarta momy ta katseta da jajayen idanuwanta itama tana cewa
"So nawa zan fada Miki ki Dena kira mana ranar tonuwar asiri?
Kin manta inda dukkanmu muka fito?
Ni kaina anfada Miki ko rayuwar Dana fito a baya Ina buqatan tinawa bare fatan komawa
Wallahi bazan yarda na koma ba,
Asirin da kike magana akansa idan ya Toni nice zan fara kwabewa nabi hanya da hauka kafin ke,
Mutuwar Bashara ba shine karshenmu ba,yanzu ne zamu tashi tsaye muyi Aiki da qwaqwalwa da qarfin zuciyarmu,
Waye Benazir da zata kashemu da ranmu tsaye?
Wlh ba Bena ba ko 'yarta sai mun janye sbd kada ta tafi ta barmana baya da qura sbd yanda Dawood Bai iya hada komai da kowa da 'yar.
Cikin Dan Jin sassaucin zafin dake cinta Safnah tace
"Daman Banda niyar a bar 'yar,tabi uwarta su tafi sbd barinta na nufin inada sauran alaqa da dangina na baya"
Cikin zurfafa tinani sosai da tabbatarda cikin biyu bazasu yarda su rasa duka ba momy ta sake juyawa ta juya tinaninta tace
"Ko zamu rasa komai na bulama bazamu yarda mu rasa DD ba sbd idan muka riqesa ta hanyarsa zamu tsira daga sauran tonan asirin"
Cikin baqin ciki sabo Safnah tace
"Tayaya bayan kallan namiji yakemun,
Wata na nawa a gidan Bai taba barin ko kalan gadon Dayake dakinsa na sani ba bare shiga,.
Wallahi wannan tafiyar da yayi dole kafin ya dawo muyi shirinda babu Abinda zai hanasa bani matsayin matsarsa.
Jinjina Kai momy tayi tana cewa
"Wannan matsalar na gama da ita sbd sakonmi Yana hanya,
Idan kika ga ya dawo Bai mayar dake matarsa ba to wlh ba namiji bane mace ne kokuma babu mazakuta a jikinta,
Maganin biyu ne dayan na bulama ne zamu aje Incase,
Idan asirin gaskiyarmu na ke ba jininsu bace ya kusa bayyana aikasa kawai zamuyi batareda sanin kowa ba ko Ganewa kowa a gama zaman gaisuwa a raba gado a kwashe Rabi a baki matsayin yarsa qwalli Daya mu San da Benazir din zamuji mu huta.
Sai alokacin Safnah taji sanyin ranta ta sauke ajiyan zuciya da numfashi a tare tana Jin sauran hope da nutsuwa na shigarta ta saki dariyan Jin dadi da farin ciki zatayi magana idanuwanta ya sauka kan hajiyarsu dake kofa tsaye kaman ta Suma tana kallansu hannunta riqe da wayar data gama da Umme akan safnah Bata sanar dasu zata koma gida ba ta taso tazo Dan yiwa safnan fada kunnuwanta suka Jiyo mata Abinda yafi karfin rayuwarta da tsufanta.
Ganin kallan da Safnah kewa kofa idanuwanta na Neman fadowa qasa jikinta duka Yana daukan rawa ya saka momy hadiye tata dariyar ta juya taga hajiya tsaye tana kallansu.
Hawaye ne kawai suka gangarowa tsohuwar ta Kalli momy bakinta na rawa zuciyarta na radadi tace
"Me kunnuwa na suka jiyemun Nuratu?
Balain da masifar da muke ciki kenan bamu sani ba a hannunku.
Kallan juna sukai tareda nufota Safnah na cewa
"Hajiya bakiji daidai bane ba.....
Wani gigitaccen Mari ta saukarwa Safnah din Daya sakata kifewa qasa ta dago idanuwanta nayin ja ta Kalli hajiyar zatayi magana momy tace
"Yanzu da kikaje hajiya to me zakiyi?
A zafafe ta Kalli momy tace
"Zakiga Abinda zanyi"
Juyawa tayi tana Bude wayarta Dan saka kira ko taku biyu batayi ba momy ta dauko qaramin glass stool din dake palon me shegen nauyi ta daga da qarfi ta kwada mata bayan kanta Saida glass din ya fashe duk nauyinsa.
Cak hajiya ta tsaya kaman Bata daku ba ta Dan motsa kadan wayar hannunta na faduwa qasa jini ya fara zuba da qarfi ta Yanke jiki a gurin ko waiwayowa batai ba.
Da sauri jiki na rawa Safnah ta tashi tana kallan hajiyar kafin ta Kalli momy muryanta da jikinta na rawa ta ce
"Momy idan Bata mutu ba zata fadawa dady da kowa gaskiyar Abinda taji,.Kuma ya zamuyi yanzu da ita Idan aka sameta anan haka zaa ce mun kashe,innalillahi,momy wlh banason zuwa prison,momy Bena zata samu DD ni Ina prison,Dan Allah momy ki.....
Tsawa momy ta daka mata tana cewa
"Haukarki zata saka asan munyi Wani abin ki nutsu babu Abinda zai faru damu."
Safnah na Jin Hakan tayi shiru suka kama hajiyar zuwa bakin kofar shigowa palon suna ajiyeta kwance kanta daidai kaifin stairs.
Wayarta Safnah ta dauko da sauri bayan ta saka hannunta leda kadama Wani abin ya biyo baya a ga hannunta a jiki.
Cikin hannunta suka Bude suka saka mata wayar.
A tare suka koma palon suka share glass din cikin sauri bayan sun share Sabon towels uku suka dauko suka goge jinin Daya zuba suka zuba tirarika da kayan qamshi sosai.
Glass din dasuka kwashe toilet sukaje sukai floshin nasa towels din Kuma a cikin toilet momy tahau konesu itama Safnah ta fito ta tsaya kan hajiyar ta kwada Wani irin ihun Daya saka masu aikin gidan kaf fitowa tafara ihu tana cewa hajiya ta Fadi a stairs da sauri aka fara salati ana ihun Kiran sunan hajiyan.
Momy kuwa a cikin toilet kaman hayaqi zai kasheta haka ta Kone towels din tsaf ta Bude window hayaqi ya fita ta wanke toilet din tas da kanta ta fesa tirarika ta fito
Lokacin tini driver da Safnah dake Kuka suka kwashi hajiyan zuwa Asibiti.
Hankali tashe masu aiki sukaiwa momy data tambayi meke faruwa taji hayaniya tana toilet.
Tanajin haka itama hankalinta ya tashi ta zari mota ta bisu Asibitin tana saka Kiran bulama ta sanar masa hajiya ta Fadi a stairs bayan kanta ya bugu anyi asibiti da ita.
Hankalinsa tashi yayi sosai gashi Yana porthacort Dan haka Shima Umme ya kira ya sanar mata.
Koda aka Isa asibiti da hajiya ko dubata baa fara Yi ba Rai yayi halinsa take Safnah ta ringa Kuka tana rusa ihu,
Momy ma haka ta ringa kukan tana Kiran sunayen Allah a baki.
Umm Koda ta iso Asibitin tareda Zeenah hajiyan ta Riga ta rasu Dan haka sai kawai ta Yanke jiki ta Fadi.
Daukanta Akai aka shiga emergency da ita Bata taimakon gaggawa.
Su Safnah kuwa shiga taitayinsu sukai suna Kuka suna waige waige sbd fargaba da sanin akwai yiyuwan zuwan Bena dole Asibitin sbd Umme.
Rasuwar hajiyan yasaka baa tsaya Wani kwaje kwaje ba