Showing 24001 words to 27000 words out of 52375 words
tayi idanunta nafitar da hawayen azaba"Ko ge zau Ahmad beyiba bare yayi yunkurin 'kwatarta daga hannun Nadiya sema gyara tsayuwarsa dayayi dan bega lefin ta ko ka'dan ba komai tayimata ita tajawa kanta.Dagudu Rufy taje tadauko moffer zata bugawa Sukainat"se asannan Ahmad yamike yarike mofar yace da it tafita,kana yajanye Nadiya daga kan Sukainat yana bata hakuri da 'kyar ya Iya janyeta koda tazo fita seda tasanya kafa tanaushi cikin"Ficewa sukayi daga sashen yana rarrashinta.Kuka Sukainat tafashe dashi cike da tausayin kanta, kasa mikewa tayi sakamakon wani azabebben ciwo da cikinta keyi,
.Tashafe sama da awa 'daya akwance awajen kafin daga bisani tamike ahankali domin baki daya gabban jikinta ciwo suke.Da kyar tashiga bedroom dogon riganta tadauka tasanya tana hawaye,da hijab dinta, drawer ta bude tadauki yan kudinta Wanda basu wuce dubu uku ba"Ahankali take tafiya idanunta nazub da hawaye,har ta isa compound din gidan...Cikin tsawa taji muryansa nacewa kada ki yarda ki fita!!Ko juyawa batayiba tasa hannu tabude kofar tafice zuciyar ta nakuna...Kallon unguwar tayi atsorace kasancewar sabon unguwace babu hayaniyar mutane,anma ta gwammace data kwana awannan Gidan,gwara taje duk abinda ze sameta yasameta ahanya"Cike da tsoro take bin gefen hanya tayi tafiye me tsawo kafin tasamu Keke napep tara tayi tasanar dashi inda ze kaita,runtse idanunta tayi tare darike cikinta datake jin kamar ze fita...Suna isa tabiya dan adedeta kudinsa kafin tashiga cikin gida"da Ummi tafara cin karo, tana ganin Ummi tazube awajen tare da sakin kuka mai ban tausayi"Cikin sauri Ummi takaraso kusa da ita tadaga ta, daki suka shiga harzuwa wannan lokacin Sukainat tagagara tsaida hawayen ta....Ummi batayi yin kurin hanata ba,bari tayi sedataga ji dankanta tasamu nutsuwa kafin ta tambayeta abinda yafaru??Wasu sabbin hawayene suka sake zubo mata tasanya hannu tashare...Tiryan tiryan tazaytanewa Ummi abinda ke faruwa tun farkon zuwanta gidan har yau,Cike da tausayi Ummi ke kallon 'yar ta hartakai karshen maganarta.Cikin sanyin muryanta tace kiyi hakuri da duk abinda ke faruwa dake acikin rayuwar aurenki jarrabawane kuma insha Allah ze wuce kamar betaba faruwa ba,anma kinyi kuskure tunda yace karki fito toda kinhakura domin hakan babban kuskurene...Har tabude baki zatayi magana sallamar Malam Ahmadu ya hanata,sunkuyar dakai kasa tayi ta amsa sallamar.Guri Malam Amadu yasamu yazauna yana kallon yanayin fuskar yarta sa tare da nazartanta"Cikin muryanta daya dishe aa kuka tagaishesa fuska asake ya amsa tare da tambayar ta ba'asin zuwanta adede wannan lokacin??. Cikin rawan murya tazayyane masa abinda yafaru."Shiru yayi nawasu mintuna kafin daga bisani yace naji duk abinda kikace Sukainat anma fa kisani damar rayuwar aure dan hakurine,duk hakurin da akecewa kiyi lokacin daza akaiki dakin mijinki shine wannan,Wannan fitowar dakikayi batare da izinin mijin kiba acikin tsinuwar mala'iku kike"Allah yana tsinewa duk matar data fita batare da izinin mijinta ba kekuma nasan bazakiso kizama daya daga cikin wa anda Allah da mala'ikunsa ke tsinewa ba, dan haka kiyi hakuri kitashi kikoma dakin mijinki shine mafi alkhairi domin ko wacce mace daki kagani adakin mijinta hakuri takeyi...Kuka tafashe dashi tace abba kayi hakuri da safe inkoma yanzu tsoro nakeji"Kai ya girgiza yace banaso kikwana cikin tsinuwar mala'iku Sukainat dan haka kiyi hakuri kitashi kikoma dakin mijinki insha Allah zakiga ribar hakuri...mikewa tayi tana hawaye tafice daga gidan lokacin karfe tara nadare......
*_ESHAA CE~_*π€π»
[3/23, 15:13] ESHA: *FREEDOM WRITER'S ASSOCIATION.* πποΈ
*KISHIYA KO BAIWA???*
_(TRUE LIFE STORY)_
*NA MARUBUCIYA*
*REAL ESHAA ~*
*WATTPAD* _Realeshaa_
*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani_*
*NOT EDERTING* ππ»
*PAGE 33&34*ποΈ
__________________________πKallonsa Ummi tayi asanyaye tace anma Malam daka barta takwana inyaso dasafe se takoma,kaga yanzu dare yayi ga anguwarsu sabuwar unguwace ina jin tsoron wani abin yasameta acikin wannan Daren.Kai Malam ahmadu yagirgiza cike da dattako yace,Haba Maimuna ki kyautata mata zato insha Allah babu abinda zefaru da ita se alkhairi"zata isa gida cikin aminci da yardan Allah,dan haka dan Allah ki kwantar da hankalinki banason ganinki cikin yanayin damuwa.Murmushin da bewuce saman labbanta ba tayi tace Allah yatsareta yakuma rabata da sharrin abinki!"Kokefa yace da ita yana kishigida"Batasa kecewa dashi komai ba tagyara shimfida takwanta aranta tana meyiwa yar ta addu'ar Neman tsari daga dukkan abinki...
Tunda tafita da gidan take share hawayen tausayin kanta,taso ace Abba yabarta koda kwana ne tayi,Inyaso dasafe takoma, anma yaki amincewa" tafiya tayi sosai daga cikin unguwarsu kafin tafita bakin titi,tatare adedeta sunfi biyar duk Wanda tace bayan Driving school se yawuce suce bazasu shiga cikiba"Tafiya tayi sosai da kyar wani ya yarda ze dauketa shima akan naira dubu,shigatayi suna tafiya tana kuka tare da kiran sunan Allah aranta harsuka isa unguwar tasu,'dan adedetan se surutu yakemata kancewa dayasan harciki cikine baze dauketa ba wannan unguwa akarshen gari.Itade shuru tayi addu'arta daya Allah yasa su isa lafiya dan tsoron cewa wani Abu take yasauketa...Suna isa tayi hamdala ga Ubangiji daya sa suka iso cikin aminci batare dawani Abu yasamesu ba.fita tayi tare da bashi kudinsa tajuya tanufi kofar gate din.Bubbuga gate din tashiga yi Anma shiru sake bubbugawa tayi da karfi nanma shiru ba alamar za abude mata"tsorone yafara kamata ganin duk bugawar datake shiru,Ta tashafe sama da minti ashirin tana knocking kafin taji alamar bude kofar,cikin sauri tashiga compound din bayan yabude mata,Cikin sanyin muryanta tace baba wani irin bacci kake tun dazu nake bugawa anma shiru?!"Kafin baba megadi yace wani abu, taji muryan Ahmad cikin nuna isa da gadara"yace"nina hanasa budewa.Cike da mamaki tace kananufin duk bugawan danake kanaji kahana abudemin?Cike da isa yace "eh saboda baki cancan ci kishigo ba.Ahankali tajuya tana kallonsa tadauki kusan minti daya ahaka,batare data janye idanunsa daga nataba"Saboda baki cancan ci kishigoba,tasake maimaita kalamansa acikin aranta??Danne zuciyar ta tayi tajanye idanunta daga nasa tanufi sashenta jiki asanyaye.Karki kara koda taku daya ne acikin gidan nan!! muryansa yasake karade mata dodon kunne akaro nabiyu.Shiru tayi batare data juyaba tacigaba da tafiya dan batasan meyake nufi da itaba.Cikin sauri yatari gabanta yana maka mata harara"kikoma inda kikafito yafada babu alamar wasa atare dashi!!Araunane tace Abba ne yace indawo, badan hakaba kaima kasan babu abinda zedawo acikin daran nan"Kafada yadage yace toh sekinemi inda zakij,dan bazaki kwana anan gidan ba"tunfarko danace karki fita dakin zauna daya fimiki alkhairi anma sekiku nunamin taurin kai,Yanda kikasanya kafa kikafita batare da izinina ba,wlh bazaki kwana acikin gidana ba se kinfita.Wasu zafafan hawayene suka wanke mata fuska,ciki wata raunanniyan murya tace ya Ahmad ina kakeso inje acikin wannan daren?!Sake tamke fuska yayi yace"duk inda kike ganin zakije kije anma wlh bazaki kwana acikin gidan nanba kuma ke baki isa kisa inyi magana biyu ba" dan haka tun lokaci be kure mikiba kikoma inda kika fito...Hannu tasanya tashare hawayen fuskarta batare data kara furta koda kalma daya ba tajuya tafice daga gidan zuciyar ta natafarfasa Ahmad yafi kowa sanin yanayin unguwar nan anma shine yakoreni saboda rashin tausayi."Cike da tausayi baba megadi ke kallonta ta cikin tagar dakin, kasancewar yanajin duk abinda suke fada,cikin ransa yake mata addu'ar samun sauki acikin lamuranta hakika yarinyar na fuskantar wulakanci da tozarci agun Hajiya dakuma alhaji....
Tayi nisa Cikin tafiya taji alamun tafiya abayanta,atsorace tajuya "Ahmad tagani,yana dunfaro inda take"hamdala tayiwa ubangiji daya yasanya tausayin ta azuciyar Ahmad ido takura masa"Yana karasowa kusa da ita yasanya hannu a'aljihu tare daciro gudan dubu daya sabo dal ya mika mata"Kin karba tayi tana kallonsa da alamar tambaya afuskarta"Ki karba kibiya kudin transport yace da ita"Cikin muryanka tace dan Allah ya Ahmad kabarni inkwana dubi yanda dare yaja sosai banda kukan karnika da tsuntsaye babu komai acikin unguwar nan, baka tunanin wani mummunan Abu yasameni" Me zakace da iyayena dasuka baka amanata!!?kafada yadage yace nifa banbiyo ki dankiyi min dogon turanci ba yafada yana tura mata kudin jikin handbag dinta,lokacin dakika tashi tafiya bakiyi wannan tunanin ba se yanzu kikayi kenan?.Yana gama fadin haka yajuya daniyyan barin wajen,durkushewa tayi tare darike kafafunsa tace badan ni ba,ya Ahmad kadubi darajan Allah,kadubi hallaccin da mahaifana suka maka nadaukar amanata dasukayi suka baka, karkatafi kabarni wani Abu yacutar dani anan takarashe tana me fashewa da wani irin kuka me ban tausayi.Sosai tabashi tausayi anma yayi alkawarin nuna mata kuskurenta dan haka yafincike kafarsa,batare daya sake juyawa ba yabar wajen..Cikin yanayin tashin hankali da rudani tamike tafara tafiya,Hawaye wani nabin wani dahaka har ta isa bakin titin abin hawa daddaya ne suka wucewa" waje tasamu daga gefen titin tazauna tarasa,inazata nufa tasan muddin takoma gida,Ran Abba zebaci sannan ze dauketa mara biyayya dan haka taci gaba dazama abakin titin batare datasamu mafita ba,wata farar motace tazo wucewa haske mata fuska tayi,dasauri tasanya hannunta tatare fuskarta,har motar tawuce sekuma tayi revers tadawo baya, zuge glass din mamallakin motar yayi dan tabbatarwa idanunsa Sukainat dince acikin wannan Daren ko wata.Jin alamar tsayuwar mota akusa da ita yasata saurin daga kanta zuciyarta ne yatsinke sakamakon wanda tagani acikin motar,dasauri ta mike tana ja dabaya....
_Kuyi manage da wannan bayawa pls kunsan yanayin makaranta Na bukatar nutsuwa_
*_ESHAA CE~_*π€π»
[3/23, 15:13] ESHA: *FREEDOM WRITER'S ASSOCIATION.* πποΈ
*KISHIYA KO BAIWA???*
_(TRUE LIFE STORY)_
*NA MARUBUCIYA*
*REAL ESHAA ~*
*WATTPAD* _Realeshaa_
*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani_*
*PAGE 35&3&6*ποΈ
__________________________πDasauri mamallakin motar yafito wanda akalla shekarunsa zasukai hamsin"cike da Mamaki yace Sukainat kece ko kuwa gamo nayi??! inazakije atsohon Daren nan!?meyafito dake daga gida kikazo tsakiyar titi tamkar mara galihu??Duk alokaci daya yake jero mata wa'annan tambayoyin domin haryanzu yakasa tabbatarwa kansa ita ce...Cike da tsoro tace nice Baba!,Kece!?meyafito dake a irin wannan lokacin daya kamata ace kina gidan mijinki? yasake jefo mata tambayar??Shiru tayi takasa cewa komai se hawaye take ga ciwon Ciki da ke addabarta, gakuma wani sabon tashin hankakin datake ciki.!"Tsawa yabuga mata yace ba tambayar ki nakeba kinyi shiru??Rasa abincewa tayi,Tunani take kota fada masa gaskiyar abinda yafito da itane,tana cikin wannan tunanin wata shawara tafado mata.Cikin Sauri tace dama daga tafiya nake shine motar ya lalace ahanya bamusamu shigowa da wuri ba seda aka tsaya akayi gyara,lokacin da muka iso shine motar yasake baci anan,to kuma anme bakanike ba'asamu ba shine driver yabamu hakuri ya ajiyemu anan yace kowa yanemi abin hawa"Kuma tunda yasauke mu bansamu adedeta, daze kaini gidaba kuma tsoron shiga unguwar mu nakeji ni kadai saboda yanayin sa, shiyasa nazauna anan ko Allah zesa in samu abin hawa anma harzuwa wannan lokacin bansamuba"ta'fada still hawaye nabin fuskarta...Ash'sha!!kaji shirme kuma shine kika zauna gefen titi kina wannan kukan maza taso inkaiki gida"Cikin sauri tace"a'a Baba kakaini gidanka in kwana idan yaso gobe se in koma gida dan nasan konaje yanzu anrufe kofa.Kai Malam Iliya datakira da Baba yajinjina cike da gamsuwa da maganarta yace taso mutafi,Cikin sauri tamike tashiga motar yaja suka tafi, sosai sukayi tafiya me nisa kafin su Isa Unguwar Gudum fulani"Kasancewar tsakanin Unguwar gudum da Driving school akwai rata me tsawon gaske"Lokacin dasuka isa gidan dare yayi kasancewar akwai rata dake tsakanin unguwowin,koda suka shiga gidan direct Dakin uwar gidan sa Malam iliya yanufa yabuga mata, dasauri tabude kasancewar tasan da dawowarsa batayi bacci me tsawo ba.Cike da mamaki Uwar gidan sa take kallonsa ganin sa da Sukainat"Malam daga ina naganka da Sukainat acikin wannan daren!?Numfashi Malam Idi yasauke kafin ya labartawa Mama hansi yanda yahadu da Sukainat din...Durkushewa Sukainat tayi awajen tana rike da cikinta sakamakon wani murdawa daya kemata,Dasauri mama hansi tarike tace sannu Sukainat meke damunki?,Cikinta tanuna tana matsar kwallan wahala,Ayyah sannu bari najuye miki ruwan zafin Malam kiyi wanka dashi kozaki ji dadin jikinki"tanagama fadin haka tawuce tahada mata ruwanka mai zafi"shiga bayin tayi tagasa jikinta dake mata tsami,tana fitowa tasamu anyi mata shimfida kwanciya tayi dahaka bacci yadauketa...Washe gari se misalin bakwai tafarka koda tatashi tsamin jikin yaragu se ciwon Cikin dake damkarta dan haka tafita tsakar gida tadaura alwala,Sallah tagabatar tana mai rokon Allah daya kubutar da ita daga sharrin Nadiya yakuma juyo mata da hankalin mijinta izuwa kanta...Cikin gida tashiga tagaishe da Mama hansi da kishiyarta,Fuska asake suka amsa suna tambayar ta gajiyan hanya?anutse ta amsa da hanya Alhamdulillah"Kallonta mama hansi tayi cike da kulawa tace gacan abin karin ki kije kikarya"mikewa tayi tana mata godiyar karamcinsu dakin tashiga Koko tasamu da 'kosai saikuma dumamen tuwo miyar kubewa zama tayi taci abincin sosai bayan ta kammala karinne tafita da kwanikan"Hijab dinta tasanya tafito cikin gidan cikin nutsuwa tayiwa su Mama hansi godiyar dawainiya dasukayi da ita"Murmushi mama hansi tayi tace aiba bu komai Sukainat tamkar ya kike awajen mu danhaka kibar yimana godiya.kai tasunkuyar cike da kaunarsu tace toh se anjima idan Baba yashigo ayimasa godiya ni zantafi"Addu'a suka bita dashi hartafice...
Tana fita tasamu mashin hawa tayi tace yakaita dutsen tanshi"suna isa tabiyasa hakkinsa,sauka tayi tashiga gidan bakinta dauke da sallama"Dasauri Matar dake kokarin shiga kitchen da flaks rike a hannu ta tajuya tan kallon Sukainat,Ajiye flaks din hannunta tayi cike da mamaki tace Suky lafiya? Naganki awannan lokacin??Murmushin yake tayi tana kokarin boye damuwar ta tace lafiya Aunty Nana,Ta'fada tana kokarin zama akujeran dake gaban farandan"Kai Aunty Nana ta jinjina, batasake cewa komai ba tawuce kitchen dan bata tunanin lafiya kamar yanda tafada mata. Hadawa yayanta breakfast tayi tasanya ko wanne launch box dinsa,temaka mata Sukainat tayi suka shirya yaran cikin kayan makaranta.Bayan ta sallami yaran suntafi makaranta ne ta zubo musu abin kari,takai daki inda ta umarci Sukainat dasuyi breakfast"Kai Suky tagirgiza tace takoshi,Aunty Nana batasake cewa komai ba tafara cin abincin zuciyarta se sake sake yake mata kan Sukainat domin talura da akwai damu atare da ita.Bayan takammalane tatat tara nutsuwarta baki daya tamayar kan Sukainat tana nazartan yanayin kanwar tata datake hango damuwa acikin kwayar idanunta tadauki lokaci ahaka kafin tace"Meye kedamunki naga duk kin rame?Anya kuna zaman lafiya tsakanin ki da abokan zamanki??Hawayen datake kokarin boyewa ne suka zubo mata,har ta bude baki da niyyan magana taka sakamakon wani kuka daya kufce mata.Cike da tausayin ta Aunty Nana take kallonta batayi yunkurin hanata kukan ba domin tasan intayi za tasamu sauki abinda ke damun zuciyar ta.Seda tayi me isarta kafin tayi shiru tana ajiyar zuciya.Kallonta aunty Nana tasake akaro Na barkatai cike da tausayin ta tace fada min abinda ke damunki kuma banason kukan nan!!.Cikin rawan murya tace Aunty Ahmad da matarsa suna zalunta na tare da kuntatawa rayuwa ta wlh danasan haka aure yake da banyiba dana dauwama agaban iyayena Aunty matar Ahmad batasona ta tsaneni tasa yayanta sun rainani basu ganin mutuncina amatsayina Na matar mahaifinsu,wani abin takaici duk abinda Nadiya zatayimin ya Ahmad baze taba daga ido ya kalletaba ko kuma yace batayi dede ba sedema yabi bayan ta koda kuwa nice da gaskiya haka ze bani rashin gaskiya sannan yanuna min bacin ransa"Jiya akan gaskiya ta Nadiya tayimin duka agaban Ahmad anma be daga ido ya kalle taba, ko kuma yanuna mata abinda tayi ba dedeba karshema ita yake baiwa hakuri,Wannan wace irin rayuwa ce Aunty sekace a kanta akafara yin kishi aduniya tafada hawaye nabin fuskarta.Hawayen fuskarta Aunty Nana tasanya hannu tashare mata,Abinda muke guje miki kenan tunfarko Suky anma kika ki fahimta,Tun kafin Ahmad ya aureki matarsa ke nuna miki karfin ikon datake dashi a gidan anma haka kika yadda kika aureshi,kinga kuwa dole kijure duk abinda zakigani daga garesa,najin dadi ko akasin haka sannan ki kwaci yancinki awajen Nadiya ki zama jarumar mace mai aji da kwatar yan cinta awajen miji da kishiya sannan kidage da addu'a domin shine ta kobin mumini."Cike danada ma tace Aunty wannan yawuce sede ayi kokarin kiyaye gaba,Insha Allah daga yau zanyi kokarin kwatar yanci na awajen su bazan sake bari tayi min abinda taga damaba. Numfasawa aunty Nana tayi tace"Allah ya kyauta yakuma kawo mana karshen wannan abin,se Abu nagaba gaskiya bazamu zuba ido munagani sunacutar dakeba dan haka gwara araba auren yaje Allah yahada kowa da rabonsa tunda shi baze Iya daukar mataki agidan saba!!.Arazane!!take kallon yayar tata cikin cikin yanayinta na sanyi tace a gaskiya Aunty bazan Iya rabuwa da Ahmad ba sede ace yacanza min Gida inyaso ko haya seya kamamin muzauna tunda yana sona, kawai de fitinar matarsa yake tsoro,Kibar ni in zauna agidan ki harseya samamin wani gidan zankoma dan banason Abba su sani..Harara Aunty Nana ta galla mata tace banason sakarcin banza,ana kokarin kwatar miki yanci kina kawomin shirme,Tunwuri gwanda kirage wannan mahaukacin son dakike gwada masa,Domin ba ze samar miki yan ciba, sede ma wulakanci!!baki daya kin dauki san duniya kindaura masa sekace shine autan maza wlh muddin bazaki rage wannan soyayyar dakike masa ba toh kina da aiki agaban ki kuma kitashi yanzu muje gida tun Abba befita ba asan abinyi.Kuka tafashe dashi tace dan Allah Aunty karki mai dani gida wajen Abba ni wlh bazan koma gidan Ya Ahmad har seya nemamin gidana kuma yanunawa matarsa muhimman cina.Ko kallonta Aunty Nana batayi ba tamike tashiga daki mayafinta tadauka babu wasa afuskar ta tace tashi mutafi!!Kuka Suky tafashe dashi tace dan Allah aunty kibarni wlh banason komawa gidan sa seya dauki mataki akan abinda matarsa tayimin.Kai Aunty Nana tajinjina cike da tausayin ta tace nifa ba gidan Ahmad zankaiki ba gidan su Ummi zamuje dan su Abba sukwatar miki yan cinki..Batace komai ba tamike tadauki hangbag dinta tana hawaye tafice"key aunty nana tasanya ta rufe kofar gidan kasancewar ba kowa,Jingina bayanta tayi dajikin bangon gidan tayi tana tunanin rayuwa,ta nadaga kai tahango dan adedeta ze wuce da gudu taje tafada ciki tace sutafi,cikin sauri aunty Nana tabiyo bayan su tana tsayar da dan adedetan anma Sukainat tace karya tsaya sutafi...Bayan sunyi Nisa 'dan adedetan yace Hajiya ina za akaiki?? tashar Max tace dashi tanabin shawaran da zuciyar ta tabata,suna isa tashar Max yan Union suka taso ina za akaiki Hajiya??Kai tsaye tace dasu Gombe,wajen motar dake lodin gombe suka kaita cikin sa'a saura mutum daya motar yacika tanashiga motar yatashi....
Ummi Na