Showing 45001 words to 48000 words out of 52375 words
da alamun bacin rai afuskarsa yace"a gaskiya kultum kinbani mamaki da girman ki da tunanin ki kike aikata Abu irin na yara kanana!? koda wasa akace min zaki iya aikata abin da kikayi bazan yadda ba segashi kin aikata,Ina hankalin ki da tunanin ki yaje alokacin da kike wannan katobaran"Bejira jin abinda zatace ba yaci gaba da cewa kultum kada ki manta yaya da dukiya ba a muguntar su sannan nasan bazakiso a aikatawa diyarki haka toh shin ke meyesa kike aikata haka ga 'diyar wasu kokina tunanin ita iyayenta basa kaunar tane kamar yanda kowasu iyaye ke kaunar 'ya'yan su...Cike da takaicin yanda yake mata sababi agaban suky tace"Alh Wallahi bakasan halayyar wannan makirar yarinyar bane,gabaki daya ta wargazawa Ahmad gidan sa tunda ya aureta yafara haduwa da masufu iri iri gaba ki daya nema take ta susutar min da yaro ga asara daya sakosa agaba aharkan kasuwanci bayan kuma da baya fuskankar hakan aharkokin sa wannan ba irin alkhairi bace kana ganin ta...Subhanallah!!Alh Ali yafada rai abace ,haba kultum meyesa bakida lissafine??kina Abu kamar wata yarinya karama taya zakice haka, Allah shike azurtawa asanda yaso yakuma kwace asanda yaso meyesa bazaki yadda da kaddara ba wannan yarinyar bata Isa tasa Allah yakwace arzikin daya baiwa Ahmad ba dan haka ki watsar da wannan camfin.
Baki Hjy kultum tatsuke alamar duk maganga nunsa basu shige taba.
Juyawa Alh Ali yayi yafuskanci Ahmad "Cikin kakkausan murya yakira sunansa"amsawa yayi kansa akasa.Ahmad katuna cewa wannan yarinyar amanace awajenka muddin kazalin ceta Allah baze taba yafe maka ba,domin matan mu da 'ya'yan mu kiwo Allah yabamu kuma seya tambayemu abisa kiwon daya bamu dan haka kakula kada Allah yatasheka gefe daya ashanye abisa rashin adalci daka keyi atsakanin su,sosai yashiga yi musu nasiyya me ratsa jiki anma baki daya tabayan kunnen su maganan yakebi.Cike da ladabi Ahmad yace"Dan Allah Baffa kayi hakuri in Allah ya yarda irin haka baze sake faruwa ba zankula yanda yakamata.Allah yasa cewar Alh Ali yana kallon Hjy kultum da Nadiya.murmushin dabe wuce saman labba ba Hjy kultum tayi yace"Mungode da wannan nasiyya taka kuma insha Allah zamu kiyaye Allah yabar zumunci."Kallon Sukainat yayi Wanda tunda suka shigo kanta nakasa yace" kiciga ba da hakuri 'ya ta Insha Allah kece da nasara domin mahakurci wataran zema mawadaci.Mikewa Alh Ali yayi yana tattare babban rigansa yace Nabarku lafiya bawanda yayi magana acikin su se Sukainat datace nagode Baffa Allah yakara girma da daukaka"Ameen ya amsa yana me ficewa...
Ahankali tamike da niyyan tafiya sashenta bayan fitar sa"Dawo ki zauna bakar munafuka annamimiya mekama da aljanu muryan Hjy kultum yadaki dodon kunnen ta..Jitayi kafafunta sun gaza daukar ta dafe kujera tayi tazauna tana karanto duk addu'ar datazo bakin ta.Mikewa Hjy kultum tayi ta Isa inda take Hannu tasanya tarike kunnen ta dake Cikin hijab cike da tsanar ta tace"ke annamimiya wato harkin kai matsayin daza kidinga kai kararmu ko!?,Nadiya da tunda akafara magana batace komai ba seyan zu tadago kai adakile tace"ai muddin ba atakawa wannan bakar munafukar burki ba nanga ba setayi abinda yafi haka!.
Shiru Sukainat tayi kanta akasa burinta kawai su sallameta tatafi.Kallon Ahmad Hjy kultum tayi tace"Ahmad anata magana bakace komai ba, rai abace yace"Hjy Wallahi bansan wani irin hukunci zan yankewa yarinyar nan hankali na yakwanta ba shiyasa kikaga nakasa cewa komai yakarashe cikin kunan zuciya...Shiru yayi nawasu mintuna kafin daga bisani yace"Na rantse da Wanda raina yake hannunsa koda wasu kikasake daukan sirrin gidan kika kai waje sena dauki tsatstsauran mataki akanki Wanda ko karene baze daukaba domin sena wulakanti jahila kawai annamimiya ki bace min dagani kafin in kyafta idanu.Cikin sauri tamike tafita tana mai yiwa Allah godiya dayasa basu taba lafiyan ta ba..
Bayan fitarta Hjy kultum da Nadiya suka dinga ingiza Ahmad kan yadauki tsatstsauran mataki akanta aduk sanda tasake zuwa takai karansa"kwafa yayi yace"Wlh Hjy nasan muddin nasa Hannu na ajikinta da sunan duka sena kasheta shi yasa na kyaleta.kayi tunani mekyau anma nan gaba tasake kwatanta irin haka kada ka kyaleta...
_VOTE COMMENTS AND SHARE_
*_ESHAA CE~_*🤙🏻
[3/23, 15:13] ESHA: *KISHIYA KO BAIWA???.*
_(True life story)_
_Na Marubuciya_
*REAL ESHAA ~*
*WATTPAD*
_Realeshaa_
_Like my page on Facebook_👇🏻
https://www.facebook.com/REAL-ESHAA-FANS-114689303720405/
*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa zunubansa ya Allah kakai kaske kabarinsa ya Allah kajikan duk kan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani._*
*PAGE 53&54*🖊️
_________________________📖 *Bayan wata daya:*
Rayuwar gidan Ahmad yayi wa Sukainat zafi kullum Cikin bakin ciki da kuncin rayuwa take, tashin hankali da masifu babu kalar da bataga ni daga wajen Ahmad da Nadiya daga wannan se wannan duk tadawo kalar tausayi komai rashin imanin ka/ki idan ka kalli halin datake ciki seka tausaya mata.Bata da kata'bus da zatayi Wanda ze nuna cewa Ita matar gidan ce sede baiwa baiwar ma makaskanciya wacce basu da tushe...Domin shigarta da kuma aikinta kadai ze tabbatar maka da bakaramin bautu wa take ba."
Tayi baki tarame idanunta sun koma ciki ciki kana sundanyi ja saboda tsananin kuka datake har kasan idanunta sun dafe tayi wani irin canzawa kamar wacce tayi shekara da shekaru acikin jinya.
Nadiya takafa kujeran mulkinta agidan seyan da taga damar juya kambunta itake tsara musu komai acikin rayuwar su daga Sukainat har Ahmad se abinda da tace zasuyu."Ganin wannan dama da Nadiya ke da shine yasanya ta shiryawa Sukainat tuggu kala kala awajen Ahmad da farko se tace"dashi akullum dayasa kaga yafice Sukainat zatabi bayan sa bazata dawo ba har seta Dede ci lokacin daya kusa dawowa kafin tadawo idan kuma ta tambayeta daga inatake seta hau kanta da zagi da fada shuyasa tafita hanyar ta anma tafada masa ne dan yadauki mataki akai.Lokacin data gama sanar wa da Ahmad wannan maganan ransa bakaramin baci yayi ba,dan kalaman Nadiya bakaramin tunzura masa zuciya sukayi ba akan abinda suky ke aikatawa hakan yasa yasamu Sukainat yamaita dukan tsiya Wanda koda daga yatsartane takasa bare kuma ace tatemaki kanta,seda yaga ko motsi batayi yabarta.
Bayan wannan yawuce ba dadewa Nadiya tasake dana mata tarko Na biyu kancewa akullum kafin magriba sewata mace tashigo cikin gidan sushige dakin Sukainat suyita shirya makirci kalala kana daga bisani suyita bunka maka sihiri suna kiran sunanka ,taci gaba dacewa alokacin dataga haka hankalinta bakaramin tashi yayiba shiyasa tayi gaggawan sanar masa dan yadauki mataki aikuwa nan ma haka yaje yasamu Sukainat yayita dukan ta kamar Allah ne ya aikosa tare da hanata abinci Na tsawon yini daya yakuma ce inwata tasake shigowa cikin gidansa adalilin ta seya karairayata ko laluran cikin dake jikinta basu ganiba suke azabab tar da ita.Wannan magana dayayi yasa Sukainat hana kowa nata zuwa gidan tasanar dasu kancewa tayi tafiya...
Rayuwar Sukainat yadawo abin ban tausayi ga duk wani mai imani dakuma tausayi duk Wanda yasanta ada yakuma ganta seya zubar da hawayen tausayin ta kana zeyi wuya yaganeta sede in farin sani kai mata shine zaka ganeta, hakika ko makiyin tane inde yana da digon imani a zuciyar sa to ze tausaya mata halin datake ciki bare kuma ace masoyan ta.Wannan dalili yasanya takasa sanarwa da iyayenta halin datake ciki kasancewar tasan hankalin su bakaramin tashi zeyiba idan sukaji halin datake ciki kuma babu wani mataki dazasu dauka face hakuri dazasu bata wannan dalilin yasanya ta shanye takaicin datake ciki takuma fawwala Ubangiji lamuran ta domin shi ka'dai ne ze iya yaye mata kuncin rayuwar datake fuskan ta agidan Ahmad.
Abangaren Nadiya kuwa burinta yacika domin se abinda tafada acikin gidan akeyi wannan dalili yasanya Nadiya yin abinda taga dama kasancewar baki daya ragaman gidan Na hannun ta. Ayanzu matsalan ta dayane ganin haryanzu Ahmad be saki Sukainat ba duk dakuwa irin wulakanci datake sanya shi yamata kan koza tanemi saki da kanta anma baki daya abin yaci tura wannan abin ne in tatuna yakesa ke sata jin tsanar Sukainat dakuma gallaza wa rayuwar ta fiye da tunanin mai tunani.Ganin duk irin cusguna war datake wa Sukainat taki tafiya yasanya ta fitowa da sabbin hanyar wulakan ta rayuwar ta tahanyar bautar da ita da ayyukan cikin gidan.kama daga wankin kayansu duk dakuwa cewa a akwai washing machine anma Nadiya tace"baza ayi amfani dashi ba tunda suna da baiwa,haka zalika sharan compound din gidan itakeyi duk dakuwa girman sa itakeyi,batun girki kuwa ba a magana domin rabon da Nadiya tayi girki har tamanta komai Sukainat keyi koda abinci tagama bata Isa taciba setajira Nadiya ta dibar mata wataran ko isarta bayayi haka za atsakura mata duk ranan datayi ganganci ci batare da sunsani ba kuwa insuka gane tofa seta karbi tsatstsauran hukunci...
Yayin da hema kesake ingiza Nadiya akan karta ragawo Sukainat kokuma ta tausaya mata ta musgunawa rayuwar yanda zata fita da kafafunta tabar mata gidan ta dana ya'yan ta.Aduk lokacin da hema tafadi haka se Nadiya tayi dariyar takaici tace"bata taba ganin mayyar yarinyar irin Sukainat ba domin duk abinda suke mata taki barin gidan da ace tanada zuciya ba shakka da tuni tabar gidan...
Sukainat kuwa yanzu tasake tabbatarwa da kanta cewa Nadiya tacika azzaluma tabugawa ajarida domin duk alwashin dataci akanta kafin ayi auren seda tacika domin ayanzu ta gwammaci tayi rayuwar gidan yari da wannan cin mutunci dakuma azabar dasuke gana mata baki daya rayuwar ta isheta domin bata dawani jin dadi sede bakin ciki da takaici dakuma kuncin rayuwa rayuwa datake fuskanta acikin ko wanne wayewar gari...
*****
Honey yanzu haka zaka zubawa yarinyar nan ido tarinka yin abinda taga dama nafada maka abinda take yi anma bakayi wani yunkurin daukar mataki akanta ba nifa ina tsoron taje takwaso mana wani masifan dan ban yadda da fitar datake ba!.Cikin furzar da iska mai zafi yace"My Queen ni Har narasa wani irin mataki zan dauka akan ta mutum sekace jaka duk irin dukar dazan mata baza tajiba ga shegen taurin kai.anma yanzu mekike gani zanyi mata Wanda yadace da laifinta!?.
Zama tagya tana me maida hankalinta kaco kam izuwa kansa"Shima zaman yagyara yana mai fuskantar ta dan jin meza tace.Dan murmushi tayi kafin tace"Why not kasaketa kawai tunda de batajin maganar ka aibabu amfani zama da ita nifa aganina kenan anma kai bansan mekake tunani ba takarashe tana me sanya kwayar idanun ta acinkin nasa.
Zazzafar ajiyar zuciya yasauke kafin ya girgiza kai yace"Wannan ba mafita bace My Queen kideno ma wani anma ba wannan beyi ba.
Tabe baki Nadiya tayi cikin takaici tace"shikenan idan taje takwaso mana wata cutar zaka san yanda zakayi damuwa aikin banza tana gama fadin haka tamike tanufi bedroom dinta cikin takaicin gwasale tan da yayi.Cikin sauri yariko hannunta yayinda yasanya hannunsa yaratsa kugunta Cikin kwantar da murya yace"Allah yahuci zuciyar ki My Queen kinsan bana kaunar ganin bacin ranki komai kankartar sa dan haka kiyi hakuri muddin nasake kamata da laifi zan dauki tsatstsauran mataki akanta.
Ok" kawai tace tana kokarin janye jikinta daga nasa"sake matsota yayi sosai kafin tace wani Abu ya hade bakinsu waje daya yashiga aika mata da Zafafan sakonni,yayin da hannunsa kekan nashanunta yana murzawa,Cikin sauri tajanye jikinta daga nasa tana maka masa harara kafin tawuce bedroom"Zama yayi yana sauke numfashi cike da bukatuwa ahankali yamike yanufi toilet yasakar wa da kansa ruwa...
Abangaren Sukainat kuwa baki daya.tamika al'amuranta ga Allah mabuwayi gagara misali mai kowa mai komai mai yi asanda yaso yakuma hana asanda yaso mai tsawa bayin sa abinda yafi zama alkhairi agaresu yakuma jarabcesu idan sukaci jarabawa seya canza musu da mafi alkhairi idan kuma suka fadi seya barsu da halayyar su.
Toh Hakanne yakasance awajen Sukainat domin baki daya tajanye damuwar ta akan abinda Ahmad da Nadiya kemata domin tasan haka Allah ya kaddara mata, bawa kuwa baya taba kaucewa kaddaran da Allah yadaura masa.dan haka ta rungumi kaddaranta da hannu bibbiyu burinta da kuma addu'ar ta ubangiji Allah yakawo mata karshen wahalar datake ciki yakuma karkato mata da hankalin mijinta kanta domin duk wannan abin dayake mata bata taba jin tsanar sa aranta ba duk dakuwa tana jin ciwon abinda yake mata aranta...
*****
Cike da dariyar farin ciki hema tace"Wallahi aminiyar nafiki farin cikin faruwan wannan lamarin domin bakiga yanda natsaneta ba ko mutuwa na ban tsana haka ba anma bakomai tunda komai yazo karshe dolenta ta tattara tsummo karanta takoma gidan tsoho..Murmushin jin dadi Nadiya tayi tace "shi yasa nake alfahari dake aminiyar domin nasan ko yan uwana najini bazasuyi min irin halarcin dakike min ba...sede wani hanzari ba gudu ba har yanzu Ahmad beson sakin yarinyar nan dan ko dazu da safe danace yasaketa kin amincewa yayi seda yaga nabata rai kafin yashiga bani hakuri kancewa wai ze dauki tsatstsauran mataki idan tasake takarashe cikin kunan zuciya da takaici..
Kafadar ta hema tadafa cikin muryan kwantar da hankali tace"karki tayar da han kalinki inde barinta gidan ne ai Abu me saukine kawo kunnenki kiji.matsawa kusa da ita tayi,hema tayi mata rada akunne dasauri Nadiya tajanye kunneta tana murmushi tace"kin tabbata idan nayi Hakan ze saketa!?,kai hema ta jinjina cike da gamsuwa da kanta tace" maganta dutse kijarraba kigani...farin cikine ya lullube Nadiya nan sukaci gaba hiransu kafin Nadiya tayi mata sallama tatafi cike da jin dadin shawar da tabata....
Fitowar ta daga toilet kenan tadaura alwala,dan gabatar da sallan la'asar taga mutum tsaye acikin bedroom dinta tana sakar mata da wani munafikin murmushi Wanda ita ka'dai tasan ma'anar sa...Cikin faduwar gaba Sukainat tashiga karanto duk addu'ar datazo bakinta tana neman rinjaye akan makiyu domin tasan ganin Nadiya adakin ta ba alkhairi bane duk da cewa zato zunubuni koda yakasance gaskiya.Katse mata tunani Nadiya tayi ta hanyar mika mata cup din dake Hannu ta mecike da fura da nono mai sanyi.Kallon tuhuma suky tamata batare data amshi kofin ba tace"mezan yi dashi!??.Wani killer smile Nadiya tasakar mata kafin tace"nakine nasan masu ciki da san kwalama shiyasa nakawo miki takarashe tana mai cigaba da sakar mata da murmushi.
Cike da mamaki Sukainat ke Kallon ta jin wai takawo matane yaushe ma rabon data samu kallon arziki daga garesu bare kuma Har ace tasamu damar da zasu bata kulawa,cikin sanyin murya tace"Nagode da kulawarki sede bana sha'awar shan fura..Atake fara'ar fuskar Nadiya suka gushe adan fusace tace wannan ai renin hankali line taya zan kawo miki abin arziki sannan kiki Karba!?
Baki Suky ta tabe domin ta tabbata yanzu hasa shenta sunzama gaskiya da abinda Nadiya tashir yamata,Cikin dakewar zuciya tace"toh Nide bana sha'awarsha dan haka seki koma da abinki takarashe tana mai mikewa dan gabatar da sallah.Cikin sauri Nadiya tasha gabanta tace"tunda nakawo miki se kinshs dan bazan koma dashi ba!"Ikon Allah Sukainat tafurta tana mai kallon Nadiya data babbanke mata agaba.
Juyawa tayi da niyyan barin wajen Nadiya tafinci kota da karfin gaske tafada kan gadon.hawa Nadiya tayi wai adalole seta durawa Sukainat furar cikin sa'a Allah yabawa Sukainat nasara takifar da kofin furar.
Ahaukace Nadiya tashiga dukan cikinta tana cewa baki isa kisa inyi asara ba Wallahi koda karfin sena fitar da wannan matsiyacin cikin dan 'ya'ya na bazasu ha'da 'yan uba da kowa ba.Cikin azabar fitar da numfashi tace"Ki dagani!,kin dagata Nadiya tayi sema sake bugun cikin datake.Seda tagaji dan kanta kafin tafagata tafice daga dakin tana huci.
"Wani irin kuka mai ban tausayi Suky tafashe dashi cike da tsananin azaban ciwon da cikinta ke mata,dakyar ta Iya janyo wayarta dake gefen beside drawer tashiga contact dinta number Ahmad tafito dashi Wanda rabon data kirasa koshi ya kirata har ta manta,ido tasake rintsewa cikin tsananin azaba da kunan zuciya jin babu kati awayarta.Please call me tashiga tura masa anma kusan minti goma be kiraba.Hannu tasanya tasake share hawayen ta kafin ta aro kudi a kamfanin MTN takirasa anma har ya katse be amsa ba cigaba da kiran tayi tana murkususu yayin da hannun ta daya kekan cikinta.Cikin tsawa taji muryan sa yana cewa"Kiran uban mekike yimin awannan lokacin ko bashi kike bina dazaki addabeni da kira..Cikin muryan mara lafiya irin Wanda yake jin jiki tace" Dan girnan Allah ya Ahmad ba danni ba kazo katema keni kakaini asibiti Wallahi jinake kamar zan mutu"Duk da tsanar ta daya keji Hakan beha nashi jin wani iri ba dayaji ta ambaci mutuwa,Bayabo ba fallasa yace"meke damunki??Dan sanyi taji aranta jin yanda ya amsa mata da 'dan sakin fuska.Momyn rufy ce tayimin dan Allah kazo kakaini asibiti kar inrasa abinda ke cikina,Adakile yace Ok sannan yakatse kiran.
"Cigaba da murkusuwa tayi akan gadon ganin har tashafe sama da awa daya babushi babu alamar sa gawani damshi dake bin cinyoyin ta.Cikin tsananin ciwo tafara rarrafawa tafita dan bazata Iya mikewa ba.
Dede zatashiga falon tajiyo muryan Nadiya nacewa karki damu aminiyar tunda batasha yazube cikin sauki ba aini nazubar dashi ta karfin tsiya dan bana zaton cikin ze zauna,bataji me nawayar tafada se dariyar da Nadiya ta kece dashi tace"ai karshen za manta yazo agidan nan insha Allah.Ahankali tasanya hannun tashare hawayen dasuka zubo mata Hannu tadaura asaman cikinta tana rokon Allah daya kubutar mata da abinda ke cikinta daga sharrin su.Karasa shiga falon tayi adede lokacin da Nadiya kecewa yaushe zamu koma wajen boka drogoni dan...kasa karasawa tayi ganin Sukainat,zamuyi magana anjima aminiyar tafada tana datse kiran.Wani shegen kallo tawatsa mata kafin afusace tace" Uwar mekike nema adakina dazaki shigo batare da kinnemi izinina ba.Cikin yanayin sanyi ta tace"Dan Allah kitaimaka kikaini asibiti Wallahi jinake kamar zan mutu!"
Harara Nadiya tamaka mata kamar idanunta zasu zazzago kasa tace"ai tsakanina dake babu temako ko dakuwa shure shuren mutuwa kikeyi ta nagama fadin haka tashige bedroom dinta tare da banko mata kofa...
Da kyar ta Iya ja tafita lokacin dataji jine ya balle mata akuma dede lokacin ne Ahmad yashigo yaganta jini yaba tamata jikinta.Dur kusawa yayi akusa da ita yana cewa meyasa meki haka!?bejira jin amsar taba yanufi bedroom din Nadiya,tana ganin sa tataso dagudu tafada jikinsa tare da fashewa da kukan kissa!.
Dasauri yadagota yana tambayar ta meyake damunta!?hawaye tashare kafin tace matarka nazargina da San zubar mata da ciki bayan kuma ni yunkurin hanata nayi datake San zubuwar ni bansan irin kiyayyar da yarinyar kemaka ba!?.Janyeta yayi daga jikinsa,yajuya afusace yanufi hanyar fita...Dasauri tajanyo hannunsa tafada jikinsa Cikin muryan kuka tace"karkayi mata komai yanzu kaje kakaita hospital tukunna in kundawo sekazo kadauki matakin daya dace..Kamar wani soko ya gyada mata kai cike da gamsuwa da maganan ta har bakin kofar sashen ta tarakosa inda Sukainat