Showing 3001 words to 6000 words out of 52375 words

Chapter 2 - KISHIYA KO BAIWA BY REAL ESHAA.txt

06 Mar 2025

3305

yakira sunan makiyiyarta,anma dayake 'yar duniya ce setace dashi haba Honey aibaka da matsala tamkar 'kanwa haka nadauketa inde tazo da zaman lafiya zamuyi ta inkuwa tazo da tashin hankali zatasameshi fiye da yanda tazomin dashi....kallon ta yayi cike da mamaki yace habade my Queen keda bakinki kike fadan haka??,Harta bude baki zatai magana wayarsa tadauki ruri,hakan yasa tayi shiru tana mebin screen din wayar da kallo"Second wife shine sunan dake yawo a screen din wayar"da murmushi a fuskar yadauka tare dacewa Amarya bakyalefi kokin kashe 'dan masu gida,murmushi me sauti Sukainat tayi tace kai ya Ahmad banda kisa de!!Cikin dariyar yace hakanaji masu Iya magana nafadi,uhm suma fada kawai suke tace dashi tana murmushi"hmm hakane kam,yace da ita.Ina yara na da momyn su amika min sakon gaisuwa ta"Duk suna lafiya suna jiran zuwanki domin sun shirya miki tarba ta musamman ya fada Cike da zumudi"Hannu Nadiya tasanya ta kar'be wayar daga hannunsa cikin kissa da Iya barikanci tace 'kanwata muna nan muna sauraran zuwanki nanda kwana ki ka'dan zaki samu tarba da karramawa ta musamman Wanda ba kowacce Amarya kesamun irinsa ba zakiga tattali tarairaya,'kanwata lissafomiki abubuwan dazaki fuskanta acikin Gidan nan 'bata lokaci ne anma duk sanda rugugin so yakaraso dake zakiga abubuwa kala-kala,'kanwata Mr's Ahmad to be fatan alkhairi"tunda tafara magana suky ta lumshe idanu tanajin kalaman Nadiya tamkar saukan aradu aka domin tafahimci da kuna acikin kalamanta,Cikin yanayin ta na sanyi tace Nagode da wannan karramawa taki,Allah ya shiga tsakanin mu da makiyanmu yakuma tsaremu daga sharrin abin ki,dariyan mugunta Nadiya tafashe dashi tace fatan alkhairi kanwata,tanagama fadin haka tamika wa Ahmad wayarsa,tamike tare dacewa Honey zanshiga ciki sekashigo"kar'ban wayar yayi da murmushi afuskarsa yace kinji bani ka'dai kemike tanadin zuwaba Har aunty ki da yaranki tanadi na musamman sukeyi miki a gaskiya kwana ki ukun nan sunyi mana yawa jimuke kamar mujanyosa yanzu, hakika Sukainat kinyi sa'ar abokiyar zama domin samun irinsu Nadiya nada matukar wahala,duk soyayyar datake yimin be rufe mata idanu ba, saboda haka ki kwantar da hankalinki kuzauna lafiya duk danasan cewa kema baki da matsala anma kikore jita jita kawaye da magulmata duk da kasancewar baki dasu kikiyaye kibi ta se kuzauna lfy"Wani irin tukukin bakin cikine yaziyarci zuciyar Sukainat jin yanda yake wani yaba matarsa,anma dayake bamai zafi bace ita din,setace insha Allah zakasameni me biyayya agareku.
Murmushin jin dadi yayi yace toh ya akayi yanzu,?akwai wani Abu dakike bukatane ko za'ayimuku?,Kai ta gya'da masa kamar yana gabanta,kana tace sofi'a tace zamu gabatar da kilisa dakuma bridalshowes,shine nace sena sanarmaka"murmushi yayi yace to keda bakida friends dawa zakuga batar kuma ai lokaci ma yakure yanzu"itama martanin murmushin tamayar masa tace wlh sofi'a ce tanace se anyi wai akwai friends dinmu na makaranta dazatayi inviting dinsu dan baza'ayi biki mukadai ba.
Toh shikenan zanturu Isah yakawo muku kudin daze isa" murmushi tayi tace to mungode,hira sukayi kana daga bisani sukayi sallama Cike da kaunar junansu"mikewa yayi yashiga ciki Inda yasamu Nadiya zaune tana waya,ganin shigowarsa yasanya ta kashe wayar,tare da maida hankalinta kansa cikin kashe murya tace Ango harka gama kenan,?kanwarta wa tabarka takarashe maganan cikin 'kunar zuciya da zafin kishi?murmushi yayi yashafa sajen fuskarsa,yace haka de kikace sauraniyar mata"harara tamaka masa aranta tace munafiki kawai kagama kalamanka da ita yanzu kazo kana fa'da min kalaman banza hadda wani sarauniyar mata,azahiri kuma se tace uhm ai nabarwa kanwata sarautar.
Dariya yayi Wanda ya bayyanar da fararen hakoransa yace"kingama yanzu kiratayi akan program dazasu gabatar,zama Nadiya tagyara tace wani irin program kuwa honey??,Yanda sukayi da Sukainat yafa'da mata kan program dazasu gabatar"Hannunsa tarike cikin nata tace haba Honey wani irin program zasu gabatar kuma??,a gaskiya Honey nibanga amfaninsa ba domin duk anan ne ake haduwa da kawayen banza Wanda zasu hure mata kunne sannan suyi kulle-kulle dan haka gaskiya nibanga amfanin wannan abin ba kawai tahakura dashi inde bawani abin sukeson kullawa da kawayenta ba anma fa shawara ce nabaka"Kai Ahmad yajinjina Cike da gamsuwa da kalaman ta domin damashi duk wannan bidi'oin basu dameshiba dan haka yadauki shawaran Nadiya 100℅ yace haka za'ayi kuma ngd da wannan shawara taki.murmushin jin dadi tayi tace yauwa Honey yakamata kakirata kasanar da ita karta tasaka rai,ta'fada tana mika masa wayarsa"karba yayi ya danna kiran second wife ringing daya Sukainat tadauka tare da sallama cikin sweet voice din ta,lumshe ido Ahmad yayi bayaga jiya dajin muryanta ako yaushe zazzakan muryanta, yakansa shi manta yanayin dayake ciki"Takaicine yakama Nadiya ganin yanda yawani shagala, da'alama yamanta tana wajen,Dafa kafadarsa tayi Cike da haushin abinda yayi,se asannan yadawo daga duniya tunanin daya Lula,akuma dede lokacin da Sukainat kecewa ya Ahmad kayi kobakaji nane!?.
Nutsuwarsa yadedeta yace kina jina,ki saurareni da kyau maganan program dakikace za'agabatar dasu Ku hakura dan banga amfaninsa ba banda yajanyo cece kuce kuma kinsan bana kaunar tashin hankali komai 'kan'kantarsa dan haka inaganin kihakura kawai zefi inyaso se ayi bu'dan kai ko??'yakarashe da alamar tambaya.
Hawayen daya zubo mata tasanya hannu tashare tace anma kuma 'dazun ka'amince zakabari muyi kuma nasanarwa sofi'a,harma anfara shirya komai,anma yanzu kace bazeyi ba,da kasan tunfarko baza kabari ba seka fada min ai kuma...Katseta yayi tahanyar cewa Sukainat nima da farko banyi wannan tunanin ba seda Nadiya tafahimtar dani matsalan dake ciki saboda haka bana bukatar kice zaku gabatar da kowani irin program dan haka kikiyaye.
A'dan fusace tace wani irin magana kake haka ya Ahmad?,taya zatace program dazamuyi zekawo tashin hankali menene abin tashin hankali aciki,da kasan tunfarko baza kabarmu ba da bakayi mana alkawari ba anma yanzu mekakeso nace dasu bakomai ngd da hakan,tanagama fadin haka takashe wayar Cike da bacin rai tanajin zuciyarta na kuna.Aunty Aliyah da shigowarta kenan tahango Sukainat tadukufa kai tana hawaye,dasauri takaraso wajen Cike da kulawa tace suky me aka miki?,wayasa ki kuka?,dagowa tayi tare da share hawayen ta kana tazayyane wa Aunty Aliyah,yanda sukayi da Ahmad tunfarko kana ga abinda yasake fada mata yanzu.
Kai Aunty aliyah tadafe Cike da takaicin hali irin Na Sukainat komai kankantar Abu seta zubar masa da hawaye,wannan saurin kuka nata nakona mata zuciya"Cikin takaici tace wai ke Suky meyesa bakida tunani ne??atunaninki wannan koke koken dakikeyi shine mafita,kizauna kinayiwa kishiya kuka bazakiyi abinda yadace ba!toh tin wuri gwanda kigyara rayuwar ki inbahaka ba kina tare da aiki,tana gama fadin haka tafice dan Sukainat bakaramin takaici take bata....
"Da kallo yabi wayar Cike da mamaki shi Sukainat takashe wa waya tabbas seya nunamata kuskurenta setayi danasanin kashe masa waya da tayi" dafa kafadarsa Nadiya tayi tace lafiya kuwa Honey?, Cike da bacin rai yace ni wannan yarinyar zata fadawa bakaken magana hadda kashe min waya yafada Cike da matsanancin 'bacin rai"Sassauta murya Nadiya tayi tace kayi hakuri Honey kasan akwai yarinya ta atare da ita,aharzu'ke yajuya yace wani irin yarintane atare da Sukainat inbanda rashin kunya"hmmm irin abin danake fada maka kenan duk irin wannan abin kawayen banza ke ziguta kan tayi maka rashin kunya,kuma nasan ba Iya kanka abin ze zatsayaba nima seta sanyani aciki
Bece komai ba se 'kwafa dayayi shi ka'dai yasan matakin daze dauka akanta mikewa yayi ya shiga toilet tare da banko kofar bayin....


******
Yau kimanin kwanaki biyu da samun sa'banin tsakanin Ahmad da Sukainat"tunda ga wancan rannan besaki kirantaba,koda takirasa bedagawa ganin haka yasanya tahakura dakiransa"anma acan kasar zuciyar ta wani irin tausayin kanta takeji ganin shariyar dayake mata,gashi tana bukatar jin muryarsa anma dole tahakura tare dadena kiransa.....


Kallon ta Sofi'a tayi murmushi a fuskarta tace anya Sukainat idan Ahmad yaganki zegane ki irin wannan kyau haka?Kafin tace wani mai 'kunshin tace gaskiya Sukainat bakaramin kyau kiyiba dubi yanda kunshin nan yadace da hannunki,kallon kunshin dake hannunta tayi ja da baki Wanda yayi masifar kyau,Dan murmushi tayi tace ngd,hira suka cigaba dayi,Cike da raha se tsokanarta suke...Wayar ta dake hannun Sofi'a ne yahau ruri,Suky kinga ana kiranki da hidden number, kode Ahmad ne?, baki Sukainat ta tabe tace aishi be boye number dauka kisa a hands free muji.
Picking Sofi'a tayi tare dasanyawa a hands free tasanya mata wayar Dede bakinta,Cikin sanyin muryanta tayi sallama "batare data amsa sallamarba tace kee karamar Mara kunya wato duk maganan dana fada miki kancewa kada kiyi gangancin shigowa cikin gidane shine kikasanya kafa kika shure kikayi watsi da duk maganan dana fada miki kikasanya kafa kika shure,toh kisa aranki daga gobe duk wani farin ciki da jindadi ya yanke miki arayuwarki sannan kinsanya kafa da tashin hankali dakuma kuncin rayuwa acikin rayuwar ki,dazakiyi acikin gidana domin nafada miki sekin gwammaci zaman Gidan yari da shigowa cikin gidana karu....Aharzu'ke Sofi'a tace dakata karamar jahila wacce batasan menene rayuwa ba bakisan addini ba ke baki isa kihana Sukainat shigowa Gidan Ahmad ba wawuya dakikiya wacce batasan menene rayuwa ba,maganan tashin hankali kuwa muddin baki kwantar da hankalinki ba kingamu dashi"Ya isa haka Sukainat ta'fada hawaye nazuba daga idanunta kasancewar bazeyi takarbi wayarba domin kunshin hannunta. Tsaki sofi'a tayi tare da katse kiran,tana makawa Sukainat harara dake zubda hawaye,tace a gaskiya suky inde bazaki canza halayyarki ba wlh kina tare da wahala,Cikin sanyin muryanta tace Sofia kinsani banason tashin hankali komai kankantarsa,dan Allah kikiyaye.tsaki kawai Sofi'a tayi tace toh shikenan tunda haka kika zabarwa kanki anma kisani wannan abinda kikeyi bashi zekwatar miki 'yancinkiba, tana gama fadin haka tafice daga sashen Cike da bacin rai...


Wurgi yayi da wayar asanda yagama jin record din da Nadiya tabashi Cike da matsamancin bacin rai yace yaushe yarinyar nan takoma haka yaushe tazama Mara kunya haka daharzata dauki waya tabawa wata taci miki mutunci sena nuna mata kuskurenta zatayi danasanin abinda ta aikata miki tunda biyewa kawayen banza ne aikinta"hawaye Nadiya tashare tace abinda nake fada maka kenan Honey game da kawaye a gaskiya yazama dole karabata da kawayen banza inde kana son zaman lafiya acikin gidanka,'kwafa yayi yace nasan matakin dazan dauka Sukainat ta bani mamaki banyi zaton haka daga garetaba"wani farin cikine yaziyarci zuciyar Nadiya danhaka tagyara zama tare da daukar wayarta,Ahmad nafita Nadiya takira hema Cike da farin ciki tace a gaskiya kawata wannan shawaran yayi kinga yanda yadauki abin dazafi ngd da shawaran da kikabani nasan bakaramin mataki zedauka akanta ba,jin alamar shigowar mutum yasanyata saurin katse kiran tare da juyawa......












_VOTE_ ✅
_COMMENTS_
*_And_*
_SHARE_












*_ESHAA CE~_ _*🤙🏻
[3/23, 15:13] ESHA: *KISHIYA KO BAIWA???*
_(TRUE LIFE STORY)_




*NA MARUBUCIYA*
*REAL ESHAA ~*


*WATTPAD* _Realeshaa_




*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani_*




*PAGE 7&8*🖌️


________________________📖Dasauri tatura wayar 'kar'kashin pillow tana kakalo murmushin dole"wuceta yayi batare dayace komai ba ya kwanta agefenta tare da lumshe idanunsa, matsowa kusa dashi tayi tadaura kanta afaffa'dan 'kirjinsa tare da sanya hannu tashafo sashen fuskarsa,cikin yanayi na damuwa tace dan Allah honey ka kwantar da hankalinka wlh bana kaunar ganin ka acikin damuwa bawai nabaka record din nan dankashiga damuwa bane a'a sedan kasan cewa Sukainat da kawayenta basa sona hasalima sede su 'kuntatawa rayuwa ta dubi irin zagin da kawarta keyimin wai hadda kirana jahila,!wai nice jahila?,takara mai maitawa hawaye nazuba daga idanunta.
Lumshe ido Ahmad yayi yanajin kukanta har cikin ransa,hakika beta 'ba danasanin yin wannan auren ba se yau"dayasan haka Sukainat take tunfarko to tabbas babu abinda zesanyashi cewa ze aureta bare harta dunga tozarta masa mata tana aibuntata"da dayanda ze gujewa wannan auren da babu shakka yaguje masa domin baze jure cin mutunci ba, sede kash!!bakin alkalami yariga da yabushe"Saide yayi alkawarin daukar tsatsauran mataki Wanda se sunyi dana sani daga ita har 'kawartata.
Kiyi hakuri nine sanadin janyo miki haka anma ki kwantar da hankalinki insha Allah zandau mataki dabasuyi zatoba"dasauri ta dago kanta dansan jin wani irin mataki ze dauka,!Cikin kissa da son jin abinda zece tace Honey nikawai kayi hakuri base kadau matakin komai ba tunda de kaga lokaci yakure Kuma kaga za'aceni ni nake shiga tsakanin ku,kuma wani irin mataki ma zaka dauka akai?,karkidamu ki kwanta ni nasan matakin da zandauka akai insha Allah"kwanciya tayi badan tasoba,anma taso ace cewa yayi yafasa auren ma baki daya"Rungumeta yayi dahaka bacci yayi awun gaba dasu,
Kowa da tunanin dake aransa musamman ma Nadiya da kishin mijinta ya addabi zuciyar ta ganin daga gobe yabar mallakinta ita ka'dai yakoma su biyu,yayinda Ahmad zuciyar sa kesake tabbbatar masa da hukuncin da yayanke shine daidai....


******
Makil cikin Gidan yake da al'ummah tako wanne lungu da sako mutane ne suke hidindimu Cike da farin ciki,baki daya Gidan yakaure da hayaniya masu aiki nayi masu surutu nayi sede fuskar kowa bayyane yake da farin ciki dakuma jin dadi wannan auren daza'ayi domin Sukainat nada shiga ran jama'a saboda kyawawan halayyarta"hakan yasa tayi jama'a sosai duk dakuwa kasancewar ita bame magana bace....
Babban masallacin juma'ar dake bayan federal sectaria na Jahar Bauchi, Cike yake makil da al'ummah babu ko masaka tsinke,Daga cikin masallaci najiyo 'daurin auren Ahmad Isma'il Ahmad"da Amaryarsa Sukainat Ahmad waziri"abisa sadaki naira dubu 'dari al'ummah suka shaida.
Daga can gefe Ahmad da Isa ne tsaye cikin wasu fararen gezna masu kyan gaske anyi musu dinkin babbar riga da yar ciki,bakaramin kyau Ahmad yayi ba tamkar kasace shi kagudu fuskarsa tamkar gonar auduga danfarin ciki da murna" 'yan uwa da abokan arziki se Allah sanya alkhairi suke yimasa dakuma Allah yabada ikon rikewa, Cike da farin ciki yake amsawa.....


****
Haba, haba, Nadiya wai dan Allah kukan nan be isa haka bane?, wannan ma aise kisa ayi mana dariya sekace akanki akafara kishiya?,duk kibi kitashi hankalinki da koke koke da me wannan yarinyar tafiki?karfa ki manta Ahmad atafin hannunki yake se yanda kikaga damar juyasa, tomeye abin tashin hankali da damuwa aciki? dan kinji andaura auren,dubi yanda duk kika bata kwalliyarki"dan Allah kigoge hawayen ki kafin munafukai suzo susami abin ya'dawa...hannu tasanya ta goge hawayen tare dacewa wlh bakomai keyimin ciwo ba hema se idan natuna wai zamu raba Ahmad da wata wannan Abu yana kona min zuciya ni Ahmad zerabawa kwana dawata ayau"tsaki Hema taja tace haba Nadiya sekace bakisan kankiba ko kuma bakisan waye Ahmed ba?, kisa aranki cewa *BAIWA* za akawo miki cikin gidanki ba *KISHIYABA* dan haka ki kwantar kitashi kije ki wanke fuskarki kizo asakeyi miki make-up kinuna musu cewa auren beda mikiba"sake share hawayen tayi tace taya kike tunanin zan Iya nunawa bedameni ba bayan kuma kinsan nafi kowa shiga tashin hankali da dimuwa akan wannan auren..
'Daure fuska Hema tayi tace tunda bazaki yiba shikenan kije kiyi duk abinda ki kaga dama.dasauri Nadiya tamike ta shiga cikin toilet sake wanka tayi tazo aka tsantsara mata make-up Cikin wasu rantsatsun kaya tashirya masu kyau da daukar hankalin me kallansu,hannu ta hema tarike sukazo Cikin compound din gida"manya manyam woofer da speaker suka kunna inda suka sanya wakar Burna boy,me taken any body,rawa suka dinga tika daga wannan wakar yakare se sukoma wancan tamkar basu da matsala kaya kuwa tacanza sunfi kala goma acewarta batason reni dole ta nuna wa makiyanta tafi karfinsu....


****
Bayan anwatse daga wajen taron 'daurin auren ne Ahmad yanufi wajen Malam Ahmadu wato mahaifin Sukainat shida Isa,Malam Ahmadu yana hango nufowar Ahmad wajen sa seya fita daga cikin taron mutanen dayake ya tunkarosa"Har kasa Ahmad da Isa suka tsugunna tare dagaisheda Malam Ahmadu,Cike da fara'a Malam Ahmadu ya amsa fuskarsa bayyane da yalwataccen murmushi,shiru Ahmad yayi nawasu mintuna kana daga bisani yace baba daman ina Neman alfarmane?,wace irin alfarma kake nema Ahmadu??Yatambayeshi yana kara murmushin fuskarsa"sajen fuskarsa yashafa,Wannan yana daya daga Cikin dabi'un Ahmad shafa sajensa aduk sanda yake magana ". yace daman banason tarone dawasu bidi'o'i hakan yasa nace anjima da daddare zanzo indauki matata base ankaika ba idan babu matsala yin hakan yafada kansa a'kasa.
Shiru Malam Ahmadu yayi kana daga bisani yace bakomai Ahmadu ai matar kace duk shawaran daka yanke yayi kuma wannan ma shawarace me kyau"Baki ya washe yace mungode baba ubangiji Allah yakara girma"ameen malam Ahmadu ya amsa tare da cewa da misalin karfe nawa zakazo Daukarta?,karfe 9:00 insha Allah zanzo"
toh Allah yakaimu, ameen suka amsa sannan sukayi masa sallama sukatafi.....Bayan sunshiga mota Isa yamaida kallon sa ga Ahmad Cike da kulawa yace Ahmad meyesa kayi haka taya zakace bazasuyi taro ba kuma bakasanar musuba se yanzu zakafadawa mahaifinta?.
Hakan shine dede domin Sukainat batada tunani batasan meson ta dagaskiya ba irin yanda Nadiya kenuna mata kauna aibata cancanci wulakanci awajenta ba,anma sekaji irin zagin cin mutuncin da Sukamata itada kawayenta,yakarashe Cike da takaicin abin"Kai Isa ya jinjina yace anma hakan dakayi bashine mafita ba tunda tunfarko baka fada musuba,sannan kasan mata da kishi baka tunanin plan Nadiya tashiryawa Sukainat "Aharzu'ke yadaga masa hannu yace ya isheka haka taya kakeson daurawa Nadiya laifi bayan kasan kokadan batada fitina.Kai Isa yajinjina akaro na biyu yace da alama haryanzu Ahmad ba kasan mata ba kaidinsu da sharrinsu yawuce inde kake tunani danhaka kabi Ahankali. Shiru Ahmad yayi bece komai ba dan kalaman Isa bakaramin bata masa rai sukayi ba,Shima Isa tsuke bakinsa yayi dan yalura sam Ahmad besan lefin matarsa"dahaka suka Isa Gidan Isa batare dakowa yace da dan uwansa komai ba...


Wani irin kyau Sukainat tayi naban mamaki tamkar kasaceta kagudu sanye take cikin wani golden din material me masifar kyau Wanda yayi matukar amsar fatar jikinta, yayinda aka kawata fuskarta da make up meban sha'awa duk Wanda yakalleta yaga Amarya,aunty Aliyah da sauran mutane seyaba kyawun datayi suke,Sofi'a ma bakaramin kyau tayiba,kowa kagani acikin Gidan masha Allah...


Lokacin da Malam Ahmadu yasanarwa da Ummi cewar Ahmad da kansa zezo daukar matarsa bata nuna damuwar komai ba sema fatan alkhairi datayimu su.Murmushi Malam Ahmadu yayi yace seki fadawa 'yan uwa da abokan arziki,dan masu tafiya sutafi kar sutsaya jira....Kamar yanda Malam Ahmadu yafada haka Ummi tamayar ma aminanta dakuma yan uwanta,Rai abace Aunty Aliyah tace anma wannan airenin hankaline Yaya tayaya baze fada da wuriba harseda lokaci yakure,a gaskiya wannan yaron akwai gyara acikin al amuransa taya zedinga yiwa mutane ra'ayi da gadara sekace....Hannu Ummi ta daga mata cikin taushin lafazi tace in banda abin ki Aliyah menene abin tashin hankalin aciki a yanzu Ahmad yafimu iko da Sukainat kinga kuwa in haka ne! yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login