Showing 42001 words to 45000 words out of 52375 words

Chapter 15 - KISHIYA KO BAIWA BY REAL ESHAA.txt

06 Mar 2025

3601

nakira sa ko kuma kina Ganin ze yadda da maganata ko da nakirasa kinsan fushi yake dani!??.
Hararan sa tayi tana kwabe fuska tace"yanzu kai bakasan mezakace ba idan kakira!!?, takarashe adan fusace tana kokarin mikewa daga jikinsa dan talura akwai rainin hankali acikin maganar sa.


Dasauri yajanyo ta yana sakar mata da murmushi kafin yace"Allah yahuci zuciyar sarauniyar mata farin cikin raina yanda kikeso haka za'ayi yafada yana Ciro wayarsa daga aljihu.Number Alh Ali yafito dashi yadan na kira
.Lokacin daya kira Alh Ali nashirin fita sallah magriba ganin kiran Ahmad yasa shi tsayawa yana kallon wayar cike da mamaki kasancewar ba'ariga da anshiga sallah ba akwai saurin lokaci.Kallon sa matarsa mesuna Hjy Bilki tayi kafin tace"Alh yakatsaya lafiya de ko!?,Murmushi yayi yace"Ahmad ke kirani,tun ranan danaje gidan sa nayi masa fada kan yayi adalci tsakanin matansa rabon daya kirani se yanzu yake nemana ko kome zan masa oho!.Kai Hjy Bilki tagirgiza tace"Wallahi Ahmad yabani mamaki koda wasa akace ze aikata haka bazan yadda ba se gashi yashayar da mutane mamaki yaro nitsats-tse mai hankali da sanin yakamata sede beyi dacen mace ba.Har Alh Ali yabude baki zeyi magana yafasa sakamakon kiran daya sake shigowa wayarsa akaro na biyu kasancewar tuni kiran farkon ya yanke.


Da sallama Alh Ali yadauka kana yana sauraran Ahmad dake gaishesa,adakile ya amsa tare da tambayar sa ya lafiyan iyalai.amsawa yayi dasuna lafiya"Masha Allah Alh Ali yace".Shirune yabiyo baya kowanne da tunanin dayake aransa,shi Alh Ali natunani kiran dayai masa awannan lokacin dan yalura da magana abakinsa sede yakasa furta wa.Yayin da Ahmad ke fargaban fadawa baffan nasa laifin daya shirya wa Sukainat dan besan yanda ze amshi batun nasa ba.


"Jin shirun yayi yawane yasanya Alh Ali cewa"se anjima tunda baka da abin fadi nizanje masallaci yafada yana kokarin kashe wayarsa.Zunguran sa da Nadiya tayi yasashi shiga taitayin sa,Harara tamaka masa kamar idanunta zasu zazzzago kasancewar wayar a handsfree take taji me Alh Ali yafada.Jarumta ya arowa ransa yace" am dama Baffa sekuma yayi shiru..yakasa karasawa.Tunda baka da abin fadi se anjima nizanje masallaci in nadawo mayi magana yana gama fadin haka yakatse layin tare da
yiwa matarsa sallama yafice yatafi masallaci yana surutun batamasa lokaci da Ahmad yayi kan shirmensa gashi har antada kabbarah....


Abangaren Ahmad kuwa kallo yabi wayar dashi dan yayi zaton fiye da hakan ma daga wajen baffan nasa dan yasan yamasa laifi."Yayin da takaici ya turnuke wa Nadiya makoshi jin har Alh Ali yakashe Ahmad befadi abinda yake gabansa ba.Cikin sanyin jiki yace My Queen.... Hannu tadaga masa afusace tace" karkace min Komai saboda tsaban wulakan ci da rainin hankali irin naka daman kasan ba sanar masa zakayi ba zaka bata min lokaci dan rainin wayo da tsagwaran cin mutunci!.


Shiru yayi kamar ruwa yacinyesa seda tagama zazzaga masa bala'i san ranta kafin tamike afusace tanufi bedroom din ta.Duk da yana jin anshiga sallan maghriba a masallaci anma yakasa tafiya sallan dan baze Iya zuwa sallah tana fushi dashi ba,hakan yasa jiki amace yabi bayanta.Cikin sauri yaja yatsaya,sakamakon wata razananniyar tsawan data buga masa tare dacewa karka kuskura ka shigo min dakina!.Kamar zeyi kuka yace"Dan Allah my Queen kisaurareni wlh ashirye nake da fada masa duk abinda kikace anma kiyimin afuwa naje masallaci indawo kafin nan shima yadawo se insanar masa.Dan sassauta fuska tayi batare data kallesa ba tace"kana idarwa kadawo tafada cikin bada umarni. Washe baki yayi cikin jin dadi yace"yauwa My Queen ina kaunarki.banza taimasa, hakan yasa shi ficewa batare daya sake furta komai ba.Bayan sun idar da sallah bedawo ba seda yajira isha'i kasancewar yasan muddin inya shigo bejira sallan ba dakyar zata barsa yakoma...


Sashen Sukainat yafara biyawa yana tura kofar dakin still yajisa arufe, kwafa yayi ya koma sashen Nadiya.Zaune ya hangota ta hakimce akan rantsats-tsen kujeranta, sanye take Cikin bonshort da top yayin da wayarta ke ahannunta da alama charting take kallo daya tayi masa tadauke kai.Rufy hanan da akram, ne sukataso da gudu suka rungumesa suna cewa oyoyo dady,murmushi yayi yana shafa kansu cike daso...


Atsorace suka sake sa, sukaja baya sakamakon tsawan da Nadiya tabuga musu sum-sum sukawuce dakin su kasancewar suna tsoron ta.Kasa da kai yayi dan baze Iya juran kallon kaskancin datake jifansa dashi ba.Jiki asanyaye yakaraso kusa da ita yazauna cikin sanyin murya da lallashi yace"please my Queen ki saurareni kiji, Wlh liman ne yatsai dani kancewa akwai tallafin da ake hadawa na marayu, shiyasa kikaga na bata lokaci bandawo ba anma ina neman afuwarki in har nabata wa saurauniyar mata rai."dan sassauta fuska tayi kasancewar tasan suna hada irin Wannan tallafin lokaci zuwa lokaci, ganin ta sassauta fuska ne yasanya shi cewa toh yanzu mekike so in fada masa??.


Zama tagyara baya bo ba fallasa tace"Idan kakira kuka gaisaa sekabashi hakuri abisa laifin daka masa,sannan kace tunda ga Wannan ranan kagyara ka ke kyautata musu Dede karfin ka,saboda nasiyyar daya maka yatsara maka jiki sannan kuma kaga ne kuskuren ka,kana seka daura dacewa anma yanzu baki daya Sukainat tarenaka batajin maganar ka baka Isa kasata ba,bakuma ka Isa kahanata ba se abinda tayi niyya shitakeyi ga yawo akullum kasa kafa kafita itama zata bi bayan ka,sannan kuma tayi yunkurin zubar maka da ciki shiyasa kakawo karanta dan kagaji da halayyar ta kawai zaka sauwake mata takoma gida dan bazaka Iya da halayyar ta Sam batada tarbiya...Innayi hakan ze faranta miki rai!?ya tambeta cike da kulawa.Baki tawashe cike da jin dadi tace"kwarai kuwa sannan ne ma zan tabbatar da irin son dakakeyi min.


"Batare daya sake furta komai ba yadauki wayarsa yakira number Alh Ali, har ringing uku bai dagaba jiki asanyaye yace kinga be daga ba" Kasake gwadawa ze dauka tace dashi...


Abangaren Alh Ali kuwa yana kallon kiran Ahmad din yaki dagawa kasancewar ka'idar sace idan yana cin abinci be daga kira.Kiran ne yasake shigowa akaro nabiyu hakan kuma yayi dede dagama cin abincin sa,tissue yasanya ya goge bakinsa.Anitse yayi picking din call tare da sallama.


Zama Ahmad yagyara tare dagaishe sa cikin nutsuwa.Amsawa Alh Ali yayi bayabo ba fallasa"Cike da tsoron me ze biyu baya Ahmad yace"Baffa dama sona ke muyi magana idan baka komai,Toh ina sauraren ka, cewar Alh Ali dake zama akan rantsats-tsun kujeran su masa kama da fadar shugaban kasa saboda kyau da tsaruwan sa.Numfasawa Ahmad yayi kafin yashiga zayyane masa tsakanin sa da Sukainat kamar yanda Nadiya tashirya masa...Alh Ali yacika da mamaki a lokacin daya gama jin jawabin da Ahmad yamasa game da Sukainat.


Ina ita Sukainat din Alh Ali yafada a lokacin dayake kokarin mikewa,dama dama..sekuma ya hau kame kame yarasa mezece.Ok kakirata kujirani gani nan zuwa, yana gama fadin haka yakashe wayarsa batare daya jira jin abinda zece ba...Kallon sa Hjy Bilki tayi tace"Alh fita zakayi yanzu!?kai ya jinjina kana yace"eh domin banyar da da abinda Ahmad yafada ba babu mamaki makircin Wannan matar ta sace suka kulla mata,anma idan naje zan tabbatar da komai ke wakana"yafada yana kokarin ficewa daga parlour,Allah yatsare adawo lafiya tace dashi"ameen ya amsa yana mai ficewa..


Ahmad kuwa da kallo yabi wayar tasa kafin yamaida Kallon sa kan gimbiyar tasa data hakimce akan kushin tana girgiza kafa cike da bala'i...Har ya bude baki zeyi magana tadaga masa hannu afusace tace"kar kace min komai nalura Wannan baffan naka yafiye bin diddigin jaraba toh yazo ina dede dashi ta nagama fadin haka tawuce bedroom din ta afusace..


Kai yadafe cike da tunani,besan mezece da baffan nasa inyagane karya yamasa.Jin karan knocking yasashi mikewa jiki asabule yanufi kofar yabude.Barka da zuwa baffa yafada a lokacin dayake kokarin rufe kofar dan tuni Alh Ali yashige ciki.seda yazauna kafin yace"ina matan gidan??Cikin inda inda yace"bari inkira maka su yanagama fadin haka ya nufi bedroom din Nadiya kwance yasameta tana latse latsen waya,My Queen tashi muyi magana banza tayi masa kamar batasan Allah yayi halittarsa awajen ba, cikin sanyin murya yafara lallashin ta tare dayimata alkawarin zekareta awajen dakyar tahakura tabi bayan sa.Akan 2siter tazauna adakile tagaishe da Alh Ali kamar wacce akaima dole,se wani huhhura hanci take, amsawa yayi batare daya kalleta ba...


Ahmad kuwa Ahankali yake knocking din kofar Sukainat gudun karya yi da karfi Alh Ali yaji ya fahimci wani Abu anma yafi sama da minti goma beji alamunta taba hakan yasa yakoma jiki amace dan beson yagane da akwai matsala.Kallon sa Alh Ali yayi yace"ina ita suky din cikin rawan murya yace" Wallahi taki bude kofar Baffa.


Shikuwa Alh Ali bece komai ba yasanya hannu acikin aljihun babbar rigansa yaciro wayarsa,number Sukainat yakira...


Sukainat kuwa duk buga kofar da Ahmad keyi tanajinsa banza tayi masa dan tasan muddin ta bude wulakanci da tozarci ne zebiyo baya hakan yasa taki budewa,tana kwance taji ringing din wayarta hakan yasa tamike tadauka,Ganin mai kiran ne yasata saurin dagawa kamar yana gabanta haka tagaishesa cike da ladabi amsawa yayi cike da kulawa kafin yace"tasameshi a parlour Nadiya, Cike da mamaki ta amsa da gatanan zuwa aranta tana mamakin abinda yakawo sa.Dogon hijab tasanya akan dan figigin rigan baccin dake jikinta kana tafito Cikin nutsuwa tanufi sashen Nadiya yayinda zuciyar ta ke bugun tara-tara dan batasan me zata tarar ba....


Da sallama dauke abakin ta tashiga Alh Ali da Ahmad ne kawai suka amsa mata yayin da hakimar tacure baki waje daya tare da kankance kananun idanunta alamar rashin mutunci.Cike da girmamawa Sukainat tagaishe da Alh Ali kanta akasa,amsawa yayi yana mejin tausayin ta har kasan ransa.
Gyaran murya yayi tare da kallon Ahmad yace" mai maita abinda kafa da min awaya,yafada babu alamar wasa atare dashi....




_VOTE COMMENTS AND SHARE_




*_ESHAA CE~_*πŸ€™πŸ»
[3/23, 15:13] ESHA: *KISHIYA KO BAIWA???*
_(True life story)_


*Na Marubuciya*
_REAL ESHAA ~_


*WATTPAD*
_Realeshaa_


_Like my page on Facebook_ πŸ‘‡πŸ»


https://www.facebook.com/REAL-ESHAA-FANS-114689303720405/


*_Ya Allah mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani._*




```Dan Allah masu cewa ga yanda zanyi suyi hakuri subarni in karasa labarina a yanda nafara be kamata ace Ku zakuna fada min abinda zanyi ba wacce taga zata karanta ayanda natsara fakat wacce bazata Iya ba kuma seta hakura anma dan Allah kidena yimin kutse cikin lamarina πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»```




*PAGE 51&52*πŸ–ŒοΈ


_______________________πŸ“–Murmushin samun nasara tayi kafin tace"Shin awatan nin baya irin haka nafaru da kai!?Batajira jin amsar saba taci gaba dacewa Katsaya kayi tunanin meyesa se ayanzu hakan ke faruwa dakai,Na tabbata zaka gane inda maganata tadosa.
Shiru yayi nawasu mintuna yana nazarin maganin ta,ganin bai tuna komai bane yasanya cewa"A gaskiya niban fahimci komai ba, kawai de nasan kaddara ce tafado min kuma ina fatan Allah yamayar min da alkhairi dama shi kasuwanci yagaji haka bazeyu ace kullum mutum na samu ba dole wataran seya rasa.Kai Hjy kultum tajinjina cike da gamsuwa da maganan Ahmad tace"Kwarai kuwa dama shi kasuwanci yagaji haka wata ran samu wata ran rashi,inde ba ma hassada ke yimaka jifa ba to bana tunanin wani abu daban,dan haka seka dage da addu'o'i inma wani sharrin suke binka dashi zeko ma musu kansu kaciga ba dayin addu'o'i dan shine mafita.


Haushi ne ya tokarewa Nadiya makoshi,jitake kamar ta makesu dan takaici ganin basu fahimci abinda take nufi ba.Danne bacin ranta tayi tace"Hjy wai kina nufin kema baki fahimci abinda nake nufi ba?,ko dayake shikenan tunda baku fahimta ba abar maganan!.Cikin sauri Hjy kultum tace"Kamar ya abari ai seki yimana bayani yanda zamu fahimta inkinsan wani Abu akai,ko baha kabane Ahmad takarashe tana juya akalar tambayar kansa.Kai ya jinjina alamun hakane.Zama tagyara kafin tace"Ni azatona aduk maganan da akeyi agari yana kunnen ku,kancewa Sukainat farar kaface!,Domin gado tayi wajen mahaifiyar ta, dan lokacin da babanta ya auri mahaifiyar ta yanada dukiya anma tunda tashiga gidan yafara rasa komai seda yatsiyace kaf yadawo bashida komai shi yasa Dadyn rufy nazuwa Neman Aurenta suka bashi saboda sunsan insukaja lokaci za'a fasa dan za a Iya fada masa abinda ke damunsu...Hannu Hjy kultum tadaga mata dasauri tace"base kin karasa ba nariga na fahimci abinda kike nufi,anma meyesa baki sanar damu tun kafin ayi auren ba?Cikin yanayin damuwa tace"Hjy ai a wannan lokacin kona fada bazu yardaba cewa kazuyi kishine.Haba Hjy kultum tarike cike da jimami tace"Wannan yarinya akwai tsinanniya,Mara imani saboda zalinci irin na iyayenta sunsan annoban dake damunsu shine zasu kakabawa Dana!?toh Wallahi bazata sake koda minti daya ne acikin wannan gidan ba seta fice"Cikin bada goyon baya Ahmad yace kin kyauta Hjy tunda aka munafurceni toh bazata zauna min agida sutalau tani ba dole takoma gidansu.Dolen ta mata fice ai cewar Hjy kultum gama fadin haka tamike afusace tanufi sashen Sukainat...


Sukainat nashiga daki tawuce bedroom dinta direct, kwanciya tayi da hijabin batare data cire ba hawaye na kwaranya daga idanunta dasuka kankance saboda kuka tarasa me ta tsarewa Hjy kultum aduniya databi tadaura mata karan tsana,komai tayi bata burgeta sede hantara da kyara yabiyo bayan abin alkhairi da mata...


Tana Cikin wannan tunanin taji an fincikota da karfin gaske seda tafadi kasan tiles din.Cikin hargagi Hjy kultum tace"tashi kifita tunda ba gidan uban kiba ne yar matsiyata! mai farar kafa!,baki isa ki talauta min da ba kamar yanda uwar ki ta talauta ubanki dan haka dole kibar min gidan dana takarashe tana me fincikar ta da karfi...Kuka Sukainat tafashe dashi tare furta _(Alhumma ajirni fi musibati wa'ahlif khairan minha)._ Mari Hjy kultum ta kwada ma tace"dan ubanki nice masifar!?Toh kome zakiyi se kinbar min gidan dana Wallahi!, maza wuce Irin jaraba tafada tana hankada keyarta zuwa waje.Hannu Sukainat tasanya tadauki wayarta dake kan beside drawer, tafice Hjy kultum na bayanta tana tura kayar ta.Seda takaita Har kofan gate din kafin tadawo.


Kai Baba mai gadi ke girgizawa cike da tausayin yarinyar hakika da'ace shi wanine toh daya bawa iyayenta shawaran su dauketa takoma gabansu,dan muddin taci gaba da zama agidanan wataran sede abude kofa atsinci gawarta ciwon zuciya yakasheta,sede kash!!shi ba kowa bane daze Iya bada wannan shawaran, Anma hakika yana tausayawa rayuwar ta shida yake mai gadi ma yafita samun kwanciyar hankali da nutsuwa...


Direct sashen Nadiya Hjy kultum takoma tana kumfar baki.Kallon ta Ahmad yayi yace"Hjy ina fatan kinfitar min da ita daga gida?,Kai ta jinjina tana haki tace"Wallahi Ahmad narasa a inda ka kwaso wannan annobar da hannunka dakuma kudinka.Cikin sauri Nadiya tace"Hjy nifa ina tunanin ba ahaka banza ya aureta ba da asiri suka hada in ba haka ba mezeyi da ita irin masifa!.Kai Hjy kultum ta jinjina tace"shakka babu maganan ki gaskiya ce da akwai mana kisar dasuka kulla karfin auren.shide Ahmad shiru yayi besake cewa komai ba baki daya hankalinsa yatafi wani tunanin daban.Zama Hjy kultum tagyara amaimakon tatafi kamar yanda tayi niyya seta fasa acewarta se bayan sallan isha...


Sukainat nafita tanemi waje tazauna tana tunanin inda zataje a yamman nan,tasan muddin takoma Gida acikin wannan halin datake hankalin iyayenta zetashi,takuma sanya su cikin damuwa.Hakan data tuna yasanya ta yanke shawaran da zuciyar ta kebata kan tasanar wa da Alh Ali. Shawaran zuciyar ta tabi tashiga contact dinta tafito da number sa ta danna kira.Ringing daya Alh Ali yadauka fuska asake ya amsa sallamar ta.Cikin rawan murya tagaishe sa,Am sawa yayi yana yana tambayar ta lafiya jin yanda muryan ta kerawa!?.Kukan datake kokarin danne wane ya samu nasaran subce mata tashiga rerewa cike da tausayin kanta...Cike da damuwa yace"yata me yasa meki?,Kiyi shiru kisanar dani damuwar ki insha Allah zan miki maganin matsalarki.Kasa tsayar da kukan tayi sakamakon wani Abu me nauyi daya tsaya mata akirji.cikin muryan lallashi yace"kiyi shiru kisanar dani abinda ke damunki,ko Ahmad ne ya miki wani abu kisanar min nayi miki alkawarin hukunta sa dade da lefin sa!".Da kyar ta iya tsagaita kukan tana Jan zuciya tashiga labar tamasa abinda yafaru tun farko harzuwa yanzu da Hjy kultum takoreta...


Kai Alh Ali yake jijjigawa Rai amatukar bace yarasa yaushe Ahmad yazama Mara imani da tausayi,Danne bacin ransa yayi yashiga bata hakuri,tare dacewa tajira sa awajen gashi nan zuwa.
"Bayan takashe wayar ne takife kanta akan cinya tashiga rera kuka meban tausayi a zuciyar duk wani me tausayi...
Ba adau lokaci ba Alh Ali yakaraso,awaje yayi parking motarsa daga can gefe ya hangota tahada kai da gwiwa da alama kuka take.Fita yayi amotar yanufi inda take,Sunanta Yakira cike da tausayin ta hakika yana tausayawa rayuwar yarinyar domin ya fahimci batada kwanciyar hankali agida.Dago kai tayi tana share hawayen dake fuskarta,Cikin sanyin murya yace" taso mushiga.jiki amace tamike tabi bayan sa tana tsoron abinda zata tarar aciki.


Tun kafin suka rasa shiga parlour sukajiyo sautin dariyar Hjy kultum da Nadiya tamkar zasu tsaga gidan.takaicine ya tur nukewa Alh Ali makoshi Sam yarasa kultum wace irin macece Mara tunani da hangen nesa.
Cikin kakkausan murya yayi sallama tare da jiran izinin shiga,Ahmad ne yamike yanufi kofar dan ganin ko waye kasancewar basu gane muryan sa ba.


Ahmad Na ganin Alh Ali tsaye da Sukainat abayansa seda hanjin cikinsa takada tsaban furgici da ru'du,domin yasan halin baffan nasa muddin ransa yabaci ze Iya yin komai musamman ma ace bakada gaskiya.Cikin dauriya yace"barka da zuwa Baffa...Kafin ya karasa Alh Ali ya kwashesa da wani razanen nen mari amatukar fusace.Ba Ahmad ba hatta Sukainat dake bayan sa se da tarazana da Marin, bata taba zaton zafin mutumin yakai haka ba,batasake tsinkewa ba seda taga yasake kifa masa wani Marin daya fi na farko.Cike da bacin rai Alh Ali yace"Ashe Ahmad baka da mutunci?nizaka ciwa mutunci ka wulakanta Ahmad!? inje har gaban iyayen yarinyar nan subani ita nadawo maka da Ita shine zaka wulakan tata saboda ba ni dakima da daraja a idanunka??yakarashe cikin hargagi tamkar zetsaga gidan.Shiru Ahmad yayi tamkar ruwa ya cinyesa yakasa koda daga kansane tsaban bakin ciki tunda yake da baffan sa betaba sanya hannu ajikin sa da sunan duka ba se yau ta dalilin Sukainat, ji yayi zuciyar sa tayi bakikkirin yayinda tsanarta kesake mamaye zuciyar sa.


Jin kamar haya niya na tashi a compound din yasanya Hjy kultum da Nadiya fitowa cikin sauri dan ganin meke faruwa.Ganin Alh Ali tsaye fuskarsa amurtuke, yasanya su dedeta nutsuwarsu domin duk abinsu suna shakkarsa.Karasawa wajen Hjy kultum tayi cikin girmamawa tagaishe sa,adakile ya amsa batare daya kalle taba"Dan Allah kakaraso mushiga ciki Alh tace"dashi,banza ya mata seda tasake maimaiwa kafin yawuce batare dayace da ita komai ba"bayan sa sukabi suka dun guma parlour.


Bayan sun zauna ne Alh Ali ya kalli Hjy kultum

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login