Showing 12001 words to 15000 words out of 52375 words
tayi 'kasa dakanta taname jin zuciyarta na tsinkewa.
Sukainat yakira sunan ta akausashe"cike da tsoro ta'amsa batare data 'dago kanta ba dan tsoron ha'da fuskarta data sa take..Wato Sukainat rashin mutunci naki haryakai ki iya bude baki kizagi Nadiya agabana,kinsan irin matsayin datake dashi acikin zuciyata?,tunkafin na aureki na fada miki zaman lafiya nake bukata acikin gida na,bana son tashin hankali komai 'kan'kantar sa?Sannan tun kafin in aureki nafada miki ba wai dan Nadiya bata faranta min bane yasa zan aureki dan raya sunnar ma'aiki(S.A.W) yasani kara aure"saboda haka kiki yaye duk wani Abu dakikasan ze 'bata mata rai wannan yazamo shine karo na karshe da zansake yimiki kashedi akan Nadiya"Maza kitashi kije kibata hakuri akan bata mata rai da kikayi muddin kinason mishurya dake.Hawayen datake boyewane sukayi nasaran zubowa Cikin muryan kuka tace anma ai ita tafata zagina meyesa alokacin bakace tabar zagina ba,se yanzu zakace inbata hakuri bayan ita tafara,karfa ka manta Uba befi Uba ba dan haka ni babu wani hakurin da zann.....be bari ta karasa ba ya kwasheta dawani azabebben mari wanda seda shatin yatsunsa guda biyar suka fito a innocent face dinta.cike da bacin rai yace yaushe reni yafara shiga tsakanin mudake?, Har ina miki magana kina mayarmin saboda nazama tsaranki,wlh inbaki tashi kinje kin bata hakuri ba Sena yi miki abinda bakya tsammani shasha kawai.Mikewa tayi tanajin jiri na 'din bata ga goshinta dake radadi tamkar anbarba'da barkono"Cikin wani raunanniyar murya tace wlh bazan iya zuwaba jinake kamar kaina zefashe. "Wlh ko mutuwa zakiyi sekinje kinbata hakuri ni zaki rainawa hankali yafada atsawace"Da 'kyar take iya 'daga 'kafanta sakamakon duhu daya lullu'be mata idanu,tana zuwa kofar bedroom tayanke jiki tafa'di"Ihun azaba tasanya tare da dafe kanta hawaye na malala daga idanunta.Wani dogon tsaki Ahmad dake bayanta yaja ke banason munafurci da rainin wayo nizakiyiwa pretending wlh kokitashi kije kibata hakuri kokuma inyi miki abinda bakiyi zatoba!!Jin taki tanka masa ne yasanyashi sanya kafa yatake hannunta cike da mugunta, ga mamakinsa ko matsawa batayiba dan haka ya tsugunna ya dagota,gani yayi takoma baya, kanta yasake ido yazare cike da ru'du yasanya kunnensa ahancinta jiyayi bata numfashi,Cikin sauri ya dauke ta yadaurata akan bed sannan yadebo ruwan sanyi ya yayyafa mata.Numfashi taja da karfin gaske kana tafashe da kuka mai ban tausayi"hannun ta yarike Cike da lallashi yace dama baki da lafiya ne baki fada Minba??,Duk da tana cikin zafin ciwo hakan behanata dago kai takallesa ba, cike da mamakin rainin hankali irinsa wai batada lfy natasanar masa ba tasake maimaiwata aranta,banza tayi dashi sema lafesa datayi da ido
"Ganin irin kallon data ke binsa dashine yasa yasha jinin jikinsa cikin wayencewa yace ki kwanta bari na hado miki tea yana gama fadin haka yafice dasauri" Ido Sukainat tarintse tanajin bakin cikin abinda Ahmad yaimata aranta koda wasa bata ta'ba zaton ze iya aikata rashin adalci agidan sa ba anma gashi tun ba'aje ko inaba tafara fuskantar kalubale...Ba dadewa Ahmad yashigo hannunsa dauke da cup da kuma table's mika mata yayi yace gashi kisha sekisha magani, bamusu takarba dan wani azabebben yunwa takeji gakuma zazzabi dake Neman rufeta"bayan tashan yene tasha magani takwanta zuciyarta cike da tunani kalakal,batada de kwanciya ba baccin wahala ya dauke ta....
Yana ganin tayi bacci yamike yanufi sashen Nadiya" 'Dakin 'ya'yansa yafara shiga time dayaje duk sunyi bacci"Rufo musu kofar yayi yawuce dakin Nadiya zaune yahangota kan tangamemen bed dinta, se danne danne take awaya ko kallon inda yake batayiba bare yasa ran zata amsa sallamarsa,ganin haka,yasa yashige toilet batare dayace da ita komai ba,wanka yayi yafeshe jikinsa da turaruka masu dadin kamshi bayan yagama kintsawa ne yamatso kusa da ita ya zauna" hannu sa yasanya yajuya da fuskarta zuwa tasa cike da lallashi yace haba gimbiyar mata Uwar yaya na Abin alfaharina,karfaki manta kece sarauniyar dake mulkin zuciyata duk wata mace dazata shigo cikin fadarki to baiwar kice domin ke dayace sarauniya acikin masarautar ina fatan zanga murmushi daga fuskar matar da tafi duk matan duniya kyau da ado"Wani irin runguma tayi masa tana kyalkyale dariya tace harnaji sanyi acikin raina,murmushin samun nasara yayi yace kokefa inkina dariya bakiga yanda kike kara kyauba.Batace dashi komai ba se zama data gyara tana fuskantar sa,shima zama yagya yana me maida hankalin sa kanta"Gyaran murya tayi tace Honey Maganan raba kwana da akiye kwana bibbiyu ne kamar yanda kasani mafiya yawan mata haka suke yi, toni gaskiya babu tsarin kwana bibbiyu anawa ra'ayin dan haka nayanke cewa kwana 'da'd'daya zamurikayi ma'ana tayi girki yau inyi gobe,kaga nayi yau toh gone zata karbi girkinta dan haka sekasanar da ita tun wuri takarashe tana wani daure fuska dan karya ki amincewa.Murmushi yayi yace tunda hakan ya mike shikenan zansanar mata"fadawa tayi jikinsa tace ngd da wannan kauna Honey Allah yabarmu tare "Ameen y amsa yana me gyara kwanciyar sa matsawo tayi tarungume sa da haka bacci yadaukesu...
Washe gari:bayan tatashi tayi sallah da azkar,bacci takoma kasancewar baccin be ishetaba, cikin baccin takejin anabugun kafar ta tare dacewa kizo inji dadyn na"Ahankali tabude idanunta bataga kowaba,ganin bakowane yasata koma wa tacigaba da baccin ta dan haryanzu batajin karfin jikinta...Rufaida nafita daga sashen Sukainat tanufi wajen mahaifinta tana share hawaye,Hankalin sa tamayar kacokam kanta Cike da kulawa yace 'Yar dadynta meyesa meki??,Fashewa da kuka tayi tace Wai Aunty Sukainat ne dan nace tazo injika shine tamareni wainafita nabata waje batasan damuwa,hawayen yashare mata yace kiyi hakuri kizauna zan ramamiki kinji,Dady zaka mareta kamar yanda tayimin??,Kai ya gyada mata alamar "eh" Nadiya datashaka batace komai ba dan takaici, taso ace da rufy tace Sukainat tamareta mikewa Ahmad yayi yaje yaramamata anma seya shashantar da maganan... Se misalin 11:00am tatashi toilet ta'fada wanka tayi sannan tasaka simple gownt ko mai batashafa ba dan wani azabebben yunwa kedamunta"Da sallama dauke abakinta tashiga parlour amsawa sukayi batare dasun kalletaba direct dinging area tanufa zama tayi tacika cikinta sannan,tamike tadawo parlour kujeran dake kusa da Ahmad tazauna,Cike da ladabi tace barka da safiya ya Ahmad"bayabo ba fallasa ya'amsa tare da tambayar tayajiki?dasauki tacedashi tare dagaishe da Nadiya, fuska acunkushe ta'amsa ganin yasa tamike daniyyan barin wajen..Sukainat taji muryan Ahmad, Ahankali tajuyo tace na'am"zo inason magana dake ba musu tadawo tazauna a'inda tatashi,Batare da yakalleta ba yace yau zaki amshi girki danhaka kishirya,kanta a'kasa tace toh Allah yakaimu anjiman lafiya,shiru sukayi babu Wanda ya'amsa kanta a'kasa tace zan iya tafiya?,"eh yace da ita yana nazartan yanayin ta yalura baki daya jikinta asanyaye,sekuma yaji tabashi tausayi.Har takai bakin kofa yace dawo kizauna anan inkinje dakin mezakiyi?,kanta a'kasa tace sonake inkwanta danbanjin dadin jikina.Kidawo nan inkina Cikin mutane aizakifijin dadin jikin,bamusu takoma tazauna.Baki Nadiya ta ta'be cike da jin haushi tayi zaton Ahmad zemata kaca kaca kan tamari rufy anma kuma bece komai ba sema wani shish'shige mata yake"Cikin murtuke fuska tace Sukainat me rufy tayi miki daga zuwa tatasoki kika mareta tafada tana tsareta da 'kananun idanunta"Cikin yanayin rashin karfin jiki Sukainat tace wace rufy kuma??Harara Nadiya tamaka mata tace ke bansan rainin wayo dama rufy nawa kikasani agidan daza ki yimin tambayar banza??,Kau da kai Sukainat tayi tace banga abin tambayar banza ananba dan ni banfahimci inda zancenki yadosoba.Har Nadiya ta bude baki zatayi magana Ahmad yadaga mata hannu alamar tayi shiru"kallon sa yamayar kan Sukainat,yace dazun natura Rufaida takiraki kizo kuyi breakfast...tiryan turyan yafada mata abinda rufy tace.Baki tarike cike da mamaki tace ni yaushe ma naga rufy wlh ya Ahmad inba yanzu ba nibanga rufy,dazun de Cikin baccina naji kamar anamin magana koda na farka banga kowa ba danhaka nacigaba da baccina takarashe tana kallon rufy cike da mamaki...Bakomai zaki iya tafiya yace da ita,Ahankali tamike tabar wajen cike da mamakin karyar da rufy tayi.Mikewa Ahmad yayi yashiga bedroom batare dayace da Nadiya komai ba hakan dayayi bakaramin kona ma Nadiya rai yayiba anma datatuna abinda tashirya musu setaji zuciyarta tayi wasai kinshingida tayi tana sakin murmushi masu ma'anoni da dama...
Ko da Nadiya tagama dinner zama tayi ita da 'ya'yan ta sukaci batare data nemi Ahmad ko Sukainat ba...Ganin time yawuce yasa suky nufar sashen Nadiya, da sallama dauke abakinta tashiga idan kushin din dake dakin ya'amsa to Nadiya ma ta'amsa"Sukainat bata damu da kin amsa sallamar ba tace momyn rufy ina abinci na?,Banyi dakeba tace da ita!!cike da mamaki tace kamar ya?kamar yanda ki kaji nafada miki tafada tanashigewa bedroom"tadade atsaye awajen kafin tajuya takoma sashen ta.Nadiya nashiga daki tasamu Ahmad Cike da 'kissa tace Honey kagafa nakira kanwata tazo tayi lunch taki wai takoshi,kuma naga bakomai taciba shine nace bari nafada maka kaje kabata hakuri ko fushi tayi kan maganan da akayi 'dazu ne yasata fushi.Kafa'da yadaga yace ki kyaleta inace cikinta ne tahusher da kanta"haba honey yaushe zakace haka aibaza kabiye mata ba dan Allah kaje kararrasheta,dan Allah ki kyaleni dawaya hanataci?,'bata fuska tayi tace gaskiya kaje kabata hakuri danbe kamata kabiyetaba.mikewa yayi yace shikenan tunda kinnace bari naje,murmushin jin dadi tayi tace kokaifa bece komai ba yafice direct sashen ta yanufa"Zaune yahangota tazabga tagumi tunanin duniya ya isheta,zama yayi agefenta yace kidena Wannan tagumin bashida amfani,Kallon ta tamayar kansa tanajin wani son sa naratsa kowani lungu da sakon dake jikinta" 'daure fuska yayi yace meyesa kikaki cin abinci??,Kallon sa tayi tace bakin ci nayi ba naje wajen momyn rufy tace wai batayi girki daniba"wani irin kallo yamata yace yaushe kika koyi karya ne Sukainat da bansanki da karya ba anma yanzu baki daya kincanza halayyarki da Wanda nasan ki dashi ada,Nadiya ce taturoni nan tace takiraki kici abinci kinki shine tace inzo inji meya hanaki?.Shiru tayi tamarasa mezatace kawai se kallo datake binsa dashi,"magana nake dake kinyi shiru"kanta tasanya akafadarsa ta kwantar Cikin yanayin damuwa tace kayi hakuri insha Allah hakan bazesake faruwa yanzu muje inci.Bece komai ba yamike tare da rike hannun ta,Nadiya na ganin sunshigo hanunsu sarkafe dajuna wani irin takaici yaturnuke mata zuciya.Kallon ta Ahmad yayi yace Wannan kanwartaki yar rigimace tafiso komai ayita lallashin ta,yake tayi tace aikuwa de Daga haka bata sake cewa komai tazubawa TV ido.Zama sukayi a dining sunaci suna hira harsuka gama,Nadiya dan takaici kasa zama tayi awajen takoma daki"Bayan sun gama lunch din ne Sukainat tace ya Ahmad wani irin girki za'ayi??,Shiru yayi nawasu mintuna kana daga bisani yace kitambayi My Queen "Murmushi tayi " tace toh,mikewa tayi tanufi bedroom din Nadiya"stayawa tayi tanemi izini,seda tabata izini kafin tashiga"kwance tahango ta dawaya ahannun ta da alama charting take,cikin rashin walwala tace lafiya??Murmushin dake kona mata zuciya Sukainat tayi tace ya Ahmad ne yace intam bayaki me za'ayi na dinner? Ta'be baki tayi kafin tace tuwon shin ka fa zakiyi miyar aghusi"Sukainat nagama ji tajuya tafita batare datace komai ba dan Wannan gadaran yafara isarta....
Da yammaci Sukainat tashiga kitchen dan shirya musu dinner, lafiyayyan tuwon shinka miyar aghushi da farfesun kayan ciki ta musu kana ta ha'da musu juice din gwoba dana mango"a sashen Nadiya tajere komai a dining sannan taje toilet wanna ta tsantsara cikin wasu English wear's green riga da Wanda masu kyangaske tasanya,Wanda yaimatukar fitar mata dasuran jikinta.Cikin takun kasaita tanufi dining din inda su Ahmad ke jiranta,tunkafin takarasa shiga sashen kamshin dadda'dan humranta ya mamaye musu hanci,shagala Ahmad yayi da Kallon ta dan bakaramin kyau tayimasaba musamman yanda kayan ya amshi jikinta"zama tayi akujeran dake kusa da Ahmad tace barkanku da Wannan lokacin "Ahmad ne kawai ya iya amsamata dan Nadiya bakin kishi yahanata magana.Mikewa tayi tafara serving din su rufy ce tafara kai abinci bakinta Wani irin furzar da tuwon tayi tana kokarin amai......
KUYI HAKURI BAKO DA YAUSHE ZAKUDIN GA JINA BA SAKAMAKON KOMAWA SCHOOL DA'AKAYI ASATI BEFI KUJINI SAU HU'DUBA INA FATAN ZAKUYIMIN UZIRI
_VOTE_ β
_COMMENTS_
_AND_
_SHARE_
*_ESHAA CE~_*π€π»
[3/23, 15:13] ESHA: *KISHIYA KO BAIWA???*
_(TRUE LIFE STORY)_
*NA MARUBUCIYA*
*REAL ESHAA ~*
*WATTPAD* _Realeshaa_
*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani_*
*PAGE 19&20*ποΈ
________________________πDasauri Nadiya tamike tana cewa rufy lafiya meke damunki me yasameki haka?me akasanya miki acikin abincin??, cikin kidima take maganar"Cikin muryan kuka tace momy Wannan abincin ba dadi kamar ba'asa komai acikin ba nide bazan iya Ciba,Inde naci cikina ze 'baci tana fadan haka tafara sheka amai tamkar zata amayar da hanjin cikinta,tadauki lokaci tana aman kafin daga baya yatsaya.Rungumeta Nadiya tayi cikin karaji tajuya tace mekika saka acikin abin cin nan?, Sukainat niyar kashe mu kikeda shi komeye?,dubi halin da kikasanya min 'ya aciki!!.Kai Sukainat tashiga girgizawa cikin damuwa tace wlh bansaka komai aciki ba lafiya kalau nayi girkina dan Allah kuyarda dani mezesa insanya wani Abu acikin abinci na cutarwa"wani 'kas'kantaccen kallo Nadiya kemata mecike da tsantsar tsana tace wlh inhar wani Abu yasamu 'yata bazan 'kyakekiba azzaluma kawai me bakar aniya.Hawaye Sukainat tashiga sharewa jin kalaman Nadiya jiki asanyaye ta matsa kusa da Ahmad hannunsa tarike cikin raunanniyar murya tace ya Ahmad kayar da dani Allah babu abinda nasa acikin abincin bansan ya'akayi hakan yafaruba takarashe hawaye nabin fuskarta.Sosai Ahmad kansa ya kulle da lamarin yamarasa abin cewa,dan haka yasanya hannu acikin abincin yakai bakinsa dan jin ta ina matsalar yake"furzar wa yayi sakamakon wani 'karni da hamamin da girkin keyi da tuwon yayi gashi yayi danye"Dasauri ta dafa kafadarsa cike da ru'du tace ya Ahmad kaima kaji akwai wani Abu aciki ne??.Hannunta yature daga jikinsa yana binta dawani shegen kallo Wanda takasa gane na mene ne!!Cikin daga murya Nadiya tace ke banasan rainin wayo kina nufin babu abinda kika saka acikin abincin haka kawai yarinya zata hau amai sannan kizo kinayiwa mutane pretending??,Allah dagaske bansa komai... Hannu Ahmad yadaga mata yace naji bakisa komai ba,hakan nanufin baki iyaba girki ba kenan?,Dasauri takallesa jin furucin dayayi"Ya Ahmad nice ban iya girkiba ta tambayeshi cike da mamakin furicinsa"hannu yasanya yashafi sajensa fuskarsa yace gaki ga abinci zaki iya ci,sekibawa kanki amsa dan bakinki baze miki karyaba.komawa jikin dining dintayi tasanya hannu tayi testing din abinci,runtse ido tayi sakamakon wani irin test da abincin keyi,kai tadafe tamarasa yanda yanda zata misalta rashin 'dan'dan abincin.Yanzu kin tabbata ba kazafi akayi miki ba ko tunda kinji dandanon abakinki??muryan Ahmad yakatse mata tunani"Kai ta gyada cike da rashin abin cewa harga Allah tasan lafiya lau tayi girkinta anma gashi yanzu abincin yabaci.Pls ki dauke abincin anan kije kisamo mana simple din abinci Wanda zamuci yanzu"jiki asanyaye takwashe warmes din tanufi kitchen.Wani shegen harara Nadiya kebinta dashi kamar idanunta zasu zazzago jitake kamar taje tashake mata wuya tamutu kowa ya huta.Tana zuwa kitchen din tarufe fuska tafashe da kuka me ban tausayi"seda taci kukanta takoshi sannan tashare hawayen ta ganin babu me rarrashinta"Ganin time yawuce ne yasa tayi musu lafiyyen jolof din taliya Wanda yaji kayan hadi da kifi,wasu warmers masu kyau tadauko tajuye acike spoon tasanya tayi testing din abinci lumshe ido tayi dan test din abinci bakaramin dadi yamata ba"Har tadauka zatafita ta tatuna bata zubar da abinci dazun ba, hakan yasa ta ta'ajiye warmers din hannunta ta dauki warmers din tuwon backyard tazagaya tazubar acikin dosbing sannan tadawo tadauki warmers din tanufi parlour.Da sallama dauke abakinta tashiga Parlour hannunta rike da warmers,zama tayi a dining din tasake serving dinsu cikin sanyin jiki tace bismillan ku"wani irin Kallon reni rufy taimata cike da rashin kunya tace Nide bazan sake cin Wannan abincin cikina ya kumbura ba,baki nadiya dake gefe ta ta'be tace yo daman wazesake ci kalan a illatamu.Ahmad de bece komai ba yamike yazauna dan abinci bakaramin kyau yaimasa a ido ba spoon yasa yakai bakinsa" ido yaruntse yakasa cewa komai sakamakon wani azabebben zafin barkono da gishiri daya gauraye masa baki gashi taliyar yayi kamar jikasa aruwa akayi akicire,cikin matsanancin bacin rai yature plate din yafadi a'kasa abinci yatar watse,Wannan wani irin rashin mutunci ne kikwashe abinci nan anan kafin na watsamiki afuska"Wani irin farin cikine yamamaye zuciyar Nadiya jitake kamar tamike tataka rawa"jiki asanyaye takwashe warmers din tamaidasu kitchen zuciyar ta cike da al'ajabin abinda yake faruwa.Cikin kissa nadiya tace rufy tashi kije ki dauki snacks da mineral kisha kinji"tana tura baki tamike tare dacewa toh momy.Sukainat nafita Direct dakin ta tawuce, zama tayi a bedroom din ta tarasa meke mata dadi aduniya taya zatayi abinci me lafiya sannan ace idan anzo ci seyabaci yazama babu test."Kallon Ahmad Nadiya tayi tace agaskiya Honey Sukainat bata iya girkiba,dubi abincin datayi nide gaskiya bazan jure Wannan abinba yakamata ace kayi wani Abu"karkidamu zata gyara insha Allah nasan abinda zanyi."Honey inada shawara tace dashi tana tsare da ido"wace irin shawara yace da ita yana tsareta da dara daran idanunsa"cike da kulawa tace why not indinga koya mata girki tunda de naga bata iyaba inde harzata yadda"kai Ahmad ya jinjina cike da jin dadi yace nagode my Queen hakika ina alfahari dake abisa nuna kulawarki ga duk abinda nakeso.Karkadamu Honey kafi haka awajena"hira sukayi sosai bashi yabar dakin ba se misalin shabiyu lokacin daya shiga Har Sukainat tayi bacci atakure da alamar bata shiryamasa yadauketa.Batare daya gyara mata kwanciyar ba kokuma yatasheta tagyara ba ya kwanta agefenta,ko Addu'a beyi ba da haka bacci yadaukesa....
_Kuyi manage da Wannan bayawa_
_VOTE_ β
_COMMENTS_
_AND_
_SHARE_
[3/23, 15:13] ESHA: *KISHIYA KO BAIWA???*
_(TRUE LIFE STORY)_
*NA MARUBUCIYA*
*REAL ESHAA ~*
*WATTPAD* _Realeshaa_
*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani_*
```I hide my tears when I say your name. But the pain in my heart is still the same although I smile and seem care free. There is no one misses you more than me.My lovely Father may Allah forgive all ur sin Short coming and make jannatul fiddausi be your final destination. Happy juma'at Kareemππππππππππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»```
*PAGE 21&22*ποΈ
________________________πKiran sallan farko yatasheta daga wahalallen baccin daya dauke ta batare data shirya masa ba,Addu'an tashi daga bacci tayi,kana takunna hasken