Showing 36001 words to 39000 words out of 52375 words
mutanen unguwar nan suka dauke ki tamkar Uwa.Shiru mama hansi tayi,tana nazarin kalaman ta tasan gaskiya tafada,duk mutanen unguwar nabata kima da mutunci amatsayinta na Babba wacce takama kanta da mutunci ta awajen su.Numfasa wa tayi kafin tamike ahankali tadauki hijab dinta tasanya,suka fice...
"Sun dauki sama da minti goma atsaye awajen suna knocking kofar anma shiru ba abude musu ba"seda Mama hansi tayi magana kafin baba mai gadi yabude mata,yana ganin ta da Nadiya yayi saurin maida kofar zerufe,gudun kar yayi lefi awajen Ubangidan sa"cike da kamala tace"Yi hakuri bashiga zanyi ba sonake kayimin sallama da me gidan.Baba Mai gadi komai bece komai ba yajuya yanufi cikin compound din dan isar da sakon su"Mintuna ka'dan da shigar sa,se gashi yafito Ahmad na biye dashi abayansa.Koda yaga mai kiran tasa seya durkusa har kasa yagaishe ta cike da mutunci dakuma karramawa.Amsa wa tayi fuska asake tare dacewa dan Allah Alh alfarma nazo nema awajenka,ba danni ba sedan girman Allah dakuma darajan manzon tsira Annabi Muhammad(S.A.W).nake rokon ka dakaji kan wannan yarinyar kamaida ita dakinta,duk da kasancewar bansan wani irin lefi tayi maka ba!anma dan Allah kayi hakuri kamai da ita dakinta tarayu akan 'ya'yan ta,yanda zata basu tarbiyan daya dace sannan hankalin iyayenta ya kwanta domin zamanta adakin mijinta shine kwanciyar hankalin su."Shiru Ahmad yayi yakasacewa komai saboda kunya da nauyin matar dayakeji bakaramin kwarjini tayi masa ba"hakika bazeki bin maganar taba,kodan fitowa da tayi awannan Daren,gakuma girman Allah da darajan ma'aikin Allah data hada shida shi yaci, ace yahakura ko dan mutunta maganarta..Cike da jin nauyi yace hakika Mama ina ganin girmanki dakuma kimarki,anma kiyi hakuri bazan Iya maida Nadiya ba harse tayi hankali takuma koyi hakuri da zama da mutane kafin in mayar da ita dakinta!!..Durkushewa Nadiya tayi tare da rike kafafunsa, cikin muryan kuka tace dan Allah Dadyn Rufy kayimin rai, Wallahi bazan sake aikata kwatan kwacin abinda Na aikata abaya, ba natuba nabi Allah da manzo,nakuma bika" idan harka sake kamani da laifi akan Sukainat Wallahi nayadda kayanke min duk hukuncin dakaga yadace akaina;Nayi alkawarin zamu zauna lafiya tamkar yanda ko wasu abokanan zama suke zaman lafiya, sannan zan riketa kamar kanwata koda lefi tayimin zanyi hakuri da ita babu Wanda zeji kan mu,takarashe zancen cikin gunjin kuka... Kafin Ahmad yace"wani Abu Mama hansi tace"dan Allah Ahmad kadubi darajan Allah kakuma dubu yarinyar nan, kayafe mata lefin datayi tunda ta amshi lefinta,ta kuma yi alkawarin bazata sake aikatawa ba.Shiru Ahmad yayi nawasu mintuna kafin daga bisani yace"Shikenan Mama taci albarkacinki nayafe mata nakuma mayar da ita dakin ta, Allah yayafe mana lefin mu baki daya..Cike da murna Mama hansi tashiga yimasa Albarka tare da fatan gamawa da duniya lafiya."seda yarakata Har kofar gidanta kafin yadawo cikin gida ko kallon Inda Nadiya take beyiba yawuce sashen,Sukainat yayi kwanciyar sa lokacin goma da Rabi yagauta...
Alh Ali na isa kofar gidan; yakira number Malam Ahmadu batare daya fita daga motar ba.Koda Malam Ahmadu yadaga, se Alh Ali yasanar masa da cewa yana kofar gida,sannan ya sanar masa su fito da Sukainat ze mayar da ita dakinta"Har tafara bacci,Malam Ahmadu yasa Ummi ta tasheta"tashinta Ummi tayi,Malam Ahmadu yarike hannunta suka fito.Batare da bata lokaci ba yashiga motar yatayar.Se misalin shadaya dawasu mintuna suka isa"hong ya danna,Dasauri Baba mai gadi yataso yabude masa kofa yana parking yanufi sashen tare da knocking, Ahmad dake kwance idanunsa alumshe kamar me bacci anma ba bacci yakeba tunani da damuwa ne suka mamaye masa zuciyarsa haka kawai yake jin canji ajikinsa yana jin tamkar wani mummunan Abu zefaru da rayuwar sa,wanda besan menene ba...Karan knocking din yakatse masa tunani hakan yasa yamike jiki asanyaye yanufi kofar.Karo sukaci da nadiya da alama itama karan knocking dinne yafito da ita"Batare dayace da ita komai ba yakara sa yabude kofar."Alh Ali yagani atsaye fuskar sa amurtuke babu alamar sassauci atare dashi,Dasauri ya durkusa kasa yace"Barka da wannan lokacin Baffa, kallon banza Alh Ali ya watsa masa yace"Bana bukatar gaisuwar ka,kuma banzo dan ka gaisheni ba dan haka karike abinka bana bukata... Kasa da kai yasake cike da jin nauyinsa,cikin sanyin murya yace "Dan Allah Baffa kayi hakuri Wallahi bahaka bane.Tsaki mai karfi Alh Ali yayi yace" ai ita wancan dake matar so ne kaje kamayar da ita anma wannan dake dole akayi maka ka aureta dole ka wulakan ta ta kakoreta,Ahmad kaji tsoron Allah acikin rayuwar ka shin kanaso ka mutu ranan gobe kiyama Allah yatasheka gefen ka ashanye saboda rashin adalci atsakanin matanka!!?Jikinsa ne yayi sanyi dajin kalaman Baffan nasa yace"Dan Allah Baffa kayi hakuri Wlh duk bahaka bane ba abinda kake zato bane anma Insha Allah zankiyaye ka kuma tayani da addu'a kan Allah yabani ikon adalci atsakanin su.Addu'a kam munayi sede kaima ka kokarta kokuma rika kokarin boye San daka keyiwa ko wacce atsakanin su dan susamu zaman lafiya.Cike da ladabi yabaiwa Allah Ali hakuri kana yamaisa alkawarin adalci atsakanin su, albarka yasanya masa kana yasake dan ka masa amanar Sukainat...Wucesa tayi tashiga sashen ta batare datace dashi komai ba tayi kwanciyar ta,shima bayanta yabi ya kwanta egenta zuciyarsa acunkushe dahaka bacci yadaukesu..
****
Washe gari:kiran sallan farko yatashesa mikewa yayi yashiga toilet yayi wanka kana yadaura alwala,tashinta yayi kafin yafice yashiga saahen Nadiya seda yatabbatar tatashi kafin yafita tare da nufar masallaci.koda ya idar da sallah yadade azaune yana addu'ar Allah yayemasa abinda ke damunsa acikin zuciyarsa.Da sallama dauke abakinsa yashiga bedroom din akan sallaya yatarar da ita tana azkhar kusa da ita yaxauna,yana kallon fuskarta cike da so"Bayan ta kammala Azkhar din ta Shafa,shima shafa yayi yana mai lumshe idanunsa.Batare data kallesa ba ta gaishesa cike da ladabi"asanyaye ya amsa yana mebinta dawani irin kallo.Mikewa tayi daniyyan barin wajen ganin irin kallon daya kebinta dashi"Hannunta yarike tare da janyota izuwa jikinsa,kokarin kwacewa take tana bata fuska sake matseta yayi ajikinsa cikin sanyin murya yace"My Kainat lefin menayi miki kike shareni,kiyi hakuri bazan Iya juran fushinkiba!,dan Allah kiyi hakuri dani aduk yanda nakasance Wallahi,wani lokacin nikaina inajin bakin ciki da takaicin abinda nake miki,ni kaina bana sanin abinda nayi miki sedaga baya naita tunanin meyesa Na aikata haka agareki bayan baki cancanci haka daga gareni ba.Dan Allah kiyi hakuri kicigaba da zama dani aduk halin da nakasance kada kice zaki gujeni My Kainat ina yimiki son dani kaina bansan adadinsa ba,idan harkikace zaki gujeni bansan halin kuncin da rayuwa ta zekasance ba kece farin cikina kuma muradin Raina"ya karashe hawaye nabin kyakykyawar fuskarsa.Cikin sauri tasanya lallausan tafin hannunta tana share masa hawaye,cikin muryan kuka tace"Ya Ahmad kadena zubar da hawayen ka kasani ina matukar kaunar ka fiye da komai arayuwata bana tunanin akwai ranar daze zo wanda soyayyarka zefice daga raina,kai ka'dai ne namijin danakeso nake kuma burin karashe rayuwata dakai duk runtsi duk wuya bazan gujeka ba nayi maka wannan alkawarin."Wani irin rungumeta yayi hawaye nafita daga idanunsa yayin da kaunar ta kesake bin kowani lungu da sakon dake jikinta...
Kansa tadago tashiga share masa hawayen dake bin fuskarsa"cikin sanyin murya tace meyesa kake kuka ya Ahmad!? Hannunta ya matse acikin nasa yace"bansan meyesa ba My Kainat nima haka natsinci kaina cikin faduwar gaba da tsoro inajin kamar wani babban al'amari zefaru da rayuwata.Ido takura masa nawani lokaci kafin daga bisani tace"dashi kadage da addu'a ya Ahmad Insha Allah komai zezo maka Cikin sauki,aduk sanda kaji haka kadunga yin addu'a acikin ranka kuma nima zantayaka Insha Allah. Peck yabata asaman labbanta yace"nagode Ubangiji Allah ya albarkanci rayuwar ki da abinda zaki haifamin ina matukar kaunarku acikin raina ina fatan zaki kulamin da abinda zaki haifa koda bama tare...Jikinta yayi matukar sanyi dajin kalamansa hakan yasa tarungumesa tana mejin wani yanayi mara dadi atare da ita,shima rungumeta yayi dahaka bacci yadauke su....
"Abangaren Nadiya kuwa burinta yakusa cika domin saura kwana daya ta kammala aikinta takuma kudurcin niyyan wulakanta Ahmad da Sukainat,abisa abinda sukayi mata domin bata barin bashin gaba.
***
Arazane yafarka daga nan nauyan baccin daya daukesa mecike da rudani da ban tsoro,ba abinda ke fita daga jikinsa banda zufa,tamkam babu AC adakin.Dasauri Sukainat tamike da addu'a dauke abakinta"hannu tasanya tadafa kafadarsa cike da kulawa tace" Ya Ahmad wai meke damunka ne!?Ido yakura mata kamar mesan gano wani Abu aciki"sake girgiza kafadarsa tare da maimaita masa tambayar ta ta...Hannunta ya damke acikin nasa yace"My Kainat wani irin mafarki nayi mara dadi mekuma firgitarwa.Wani irin mafarkine wannan Wanda yafirgitar da kai haka!?.Ajiyar zuciya yasauke kafin yace"Gani nayi ina kwance acikin dakin mai haske,sekuma gawata mata atsaye wacce bana Iya kallon fuskarta tazo da wani Abu acikin boro tana zubarwa atsakiyan daki,Ahankali wannan hasken yafara dishewa yana komawa duhu,ganin haka yasa kika taho da gudu kina mikamin hannu domin kicireni daga wannan duhun dake neman lullubeni anma abin yagagara,haka kikai tamika min hannunki anma nakasa rikewa inaji ina gani kikatafi ki kabarni acikin wannan bakin duhun Wanda koda hannu nane bana Iya gani bare intemaki kaina,hakiki wannan mafarkin bakaramin razanar dani yayiba yakarashe cikin wata raunanniyan murya...Bakomai ya Ahmad insha Allah babu abinda zefaru se alkhairi"Allah yasa yafada yana kokarin mikewa,toilet yashiga ya watsa ruwa kana yadaura alwala yafito,da kallon tausayi tabisa ganin duk yanda yayi sanyi tamkar wani majinyaci...Ganin yanda tashiga damuwa ne yasanya shi boye tasa damuwar domin ya kwantar mata da hankali,domin a yanzu baya kaunar ganin abinda ze tayar mata da komai kan kantarsa"Ganin yanda yadan rage damuwa yasanya ta mikewa tashiga kitchen tahada musu abinci rana simple sukaci,bayan sun kammala ne ta tattare kayan tamayar kitchen...Se azahar yafi yanufi masjid."Bedawo ba se dare,lokacin daya dawo,tana bedroom akwance kusa da ita yazauna yana sakar mata da lallausan Murmushi.mikewa zaune tayi tace"ina katsaya Se yanzu!?Nabiya wajen isa ne kasancewar mun kwana biyu bamu haduba,kinga harnaci abinci.Murmushi tayi takoma ta kwanta batare data sake cewa komai ba,jikinta yashiga ya kwanta yana yawo da hannunsa asassan jikinta,lumshe idanu tayi jikinta Na amsar sa konninsa"Cikin zakuwa tajuya tahade bakinsu tare da aikama da zafafan wasanni.Awannan Daren sunnu nawa junansu kauna da kulawa tamkar bazasu rabu ba"se bayan komai ya kammala tamike tashiga toilet ta tsarkake jikinta,tana fitowa taga yakara kudundunewa cikin bargo"cike da kulawa tace"ya Ahmad kaje ka tsarkake jikin ka karkayi bacci da najasa.Banajin zan Iya tashi yanzu,seda asbah in natashi zanyi,zata sake magana ya janyota tafada kansa,kankameta yayi yana shakar kamshin tularen wanka datake"bayan da ta Iya hakan yasa tagyra kwanciyar ta ajikinsa talumshe idanu dahaka bacci mai dadin gaske yadauke su...
β
_OTE,COMMENTS & SHARE._
*_ESHAA CE~_*π€π»
[3/23, 15:13] ESHA: *KISHIYA KO BAIWA???*
_(True life story)_
*Na Marubuciya*
_REAL ESHAA ~_
*WATTPAD*
_Realeshaa_
_Like my page on Facebook_ ππ»
https://www.facebook.com/REAL-ESHAA-FANS-114689303720405/
*_Ya Allah kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani._*
*PAGE 47&48*ποΈ
_______________________________πKansa yake juyawa yana shure-shure da kafafunsa cikin tsananin azaba da razana.Yayin da ko wanne lungu da sako najikin sa ke fidda zufa,tamkar wanda akasanya shi agidan bireda saboda tsananin zufa dake fita daga jikinsa"Juyi yake cikin tsananin damuwa da tashin hankali,duk da kasancewar bacci yake hakan baze hana ka hango tsananin dimuwa da damuwar dayake ciki ba.Ahankali yafara bude idanun sa yayin da ya dafe kansa dayake ji tamkar ze tsage gida biyu saboda yanda yake juya wa.
Dawani irin 'kunci da 'kunan zuciya yakara sa bude idanunsa dasuka yi wani irin ja dasu tamkar gautar daya kwana biyu aleda"Tsintar kansa yayi da wani irin bacin rai da tsantsar tsanar komai acikin rayuwar sa.Baya kaunar komai a wannan lokacin,ko sha'awar komai banda yayi tozali da sanyin idaniyar sa da Nadiya ita ka'dai yake da burin kallo da sauraro.Kallonsa ya mayar kan agogon dake manne abangon dakin, karfe uku da Rabi am" yagani Cikin sauri yadira daga kan gadon yanufi kofar fita dan yayi tozali da abinda zuciyar sa keda muradin gani.
"Jin motsinsa yasanya ta bude dara daran idanunta dasuke cike da bacci, tana kallon sa yana kokarin fita.Cikin sanyin murya,irin na me bacci tace"Ya Ahmad ina zakaje acikin wannan Daren!?Tamkar an watsa masa ruwan zafi ajikibhaka yaji saukan muryan ta adodon kunnen sa.Batare daya juya ya kalli Inda take ba,yaja tsaki mai karfi yafice daga dakin.Cikin sauri tadira daga kan gadon tajanyo hijab tasanya tabi bayan sa.
A coridor daze sadata da sashen Nadiya tagansa yana kokarin knocking. Hannun sa tarike cikin kasa da murya tace"Ya Ahmad lafiya kakeson tashin ta awannan lokacin!?dubi dare ne fa be kamata ace kabuga mata kofa ba,Inma wani Abu kake bukata kabari gari yawaye seka karba!.
Fisge hannun sa yayi daga nata yana binta dawani matsiyacin kallo mecike da kaskanci"Kasa tantance wani irin kallo yake binta dashi,shin kallon tsanace ko kuwa naso!?Razanan niyar tsawan daya buga matane yasanya ta dawowa daga duniyar tunanin data tafi.Cike da hargagi yace"ke banason hauka,wawuya,dakikiya kawai,ke harkin kai"kice zaki hanani abinda nayi niyya wacece ke!?Ya karashe yana huci kamar wani kumurcin maciji.Cike da matsanancin mamakin bakaken magan ganunsa take kallonsa,kasa cewa komai tayi se kallo datake binsa dashi.
Tsaki mai karfi yasake ja akaro na barkatai yace" duk Maitan ki baki isa kici nama taba dan nafi karfinki mayya yar Jarababbu.Kasa danne bacin ranta tayi cike da bacin rai tace"ya Isheka haka!,wannan wani irin cin mutunci ne!?Iyayen nawane jarababbu,abin harya wuce kaina yakoma kan iyaye ne?mesuka tsare maka arayuwar ka?"aurena dasuka baka shine Jaraban?takarashe cike da takaici.Harara yamaka tama kamar idanunsa zasu fado yace"duk yanda kika dauka haka nake nufi"yana gama fadin haka yajuya yaciga ba da knocking din kofar da karfi"yayin da yasanya dayan hannun sa yadafe kansa dake yimasa tsananin ciwo kamar zefashe.
Nadiya dake jikin kofa arakube tanajin magan ganunsa kasa kasa sede bata fahimtar mesuke cewa takaici ne yaka mata taso taji mesuke cewa,Cikin tsawa tace"Waye wannan yake neman karya min kofa acikin Daren nan!?.
Kasa da murya Ahmad yayi yace"Nine my Queen,kai ne waye tafada kamar bata ganesa ba?"Ahmad ne yasake fada yana sassauta muryansa.Tsaki tasake ja akaro Na biyu tace" kakoma Inda kafito,bani da lokacin ka tana gama fadin haka takoma ciki ranta fari sol,ko bakomai tasan yau burin ta yacika Ahmad yazama mallakinta,Tunda haryazo yake buga mata kofa arin wannan lokacin"tsalle tabuga tafada kan gado cike da matsanancin farin ciki kasa komawa bacci tayi ta,gani take kamar gari baze wayeba takafa kujeran mulkinta agidan"tokuma idan ba'aikin ne ya kammala ba wani Abu yazo Nema!?ta tambayi kanta"Jitayi zuciyar ta yatsinke,Dasauri tasake baiwa kanta ansa da cewa bazeyi ba nasan komai ya kammala tunda nariga nagama kammala wa kamar yanda boka drogoni yace tayi.Hakan da tatuna yasanya zuciyar ta yayi sanyi,Jira take gari yawaye tasanarwa da Hema daddadan labari mai sanya farin ciki azuciyar masoyanta.
"Haushi,takaici,bakin ciki, ne suka lullubewa Sukainat zuciya,Ganin irin bakaken maganar daya yaba mata" Gakuma wulakanci da Nadiya tayi NASA"Ganin bazata Iya jure takaicin bane yasa tajuya tanufi sashenta ranta bakikkirin tarasa meke damun Ahmad.tana shiga tarufe kofar ta,fadawa kan gado tayi tafashe da wani irin kuka me ban tausayi shin wannan wace irin rayuwa ce daga wannan matsalar ta kau se wannan shin se yaushe Ahmad zegyara rayuwar sa suyi rayuwar me inganci tamkar kowasu ma aurata,Shin yaushe ne za tasamu farin ciki? rayuwar ta agidan Ahmad yazame mata jaraba"Ganin kukan baze fish-shiteba yasa tamike tashiga toilet ta daura alwala tazo ta tada sallah tana kuka tana rokon Allah daya kawo mata dauki acikin rayuwar ta...
Washe gari;
Se wuraren karfe bakwai Nadiya tabude kofar ta"tana budewa taji mutum ya fado dakin"Dasauri ta kalli kofan Ahmad tagani,cike da mamaki take kallon sa, da alama bacci ne ya daukesa awajen.Wani irin farin ciki ne ya lullube mata zuciya,jitake kamar ta taka rawa tsaban farin ciki,shikenan aikinta yariga ya kammala burinta yacika Ahmad yazamo mallakinta se yanda tayi dashi"ganin yanda yakafeta da birkitattun idanunsa ne yasanyata dedeta nutsuwar ta.tana mai daure fuska tamkar wacce taga,makiyinta."Malam me kakeyi min akofa!?tafada babu walwala afuskarta.Cikin kwantar da murya yace"kiyi hakuri My Queen Wlh so nike in ganni kusa dake,bani da burin daya wuce inganki agefena,tare da kallon wannan kyakykyawar fuskar taki me sanya min nutsuwa.Dan sassauta fuska tayi jin abinda yace.Tace"ni banason karya da dadin baki inace tarewa kayi adakin amaryan ka kana wulakan tani,kanuna nida banza daya mutake kanuna bani da muhimmanci awajen ka,kanuna waccan kucakar yarinyar tafini muhimmanci da daraja A idanunka"Har dukana kayi akanta,Dan haka ka tattara ka koma wajen ta dan ni bana zama da makaryaci kuma mayaudari.
Marerece fuska yayi kamar zeyi kuka duk yadawo kalar tausayi yace"Dan Allah kiyarda dani My Queen ina matukar kaunar ki ke ka'dai ce sanyin idaniyata kuma Uwar yaya na.Jin kalaman sa yasanya taji, zuciyar ta yai sanyi dan haka sedata gama jamai aji kafin ta hakura.
Bayan ta idar da sallan walha ne tamike ahankali tanufi kichen,baki daya batajin karfin jikinta ga yunwa dake nanukar cikin ta"Hakan yasa ta kunna gas tadaura indomie guda daya hungry man, tasanya mai kwai da gesher tare da hada masa kayan lambu,sosai girkin yayi dadi se tashin kamshi yake.
Nadiya dake parlour ta hakimce akan tangamemen kujeranta tana danne danne awaya yayinda Ahmad ke yimata massing a kafafunta suna hira jefi jefi.Baki daya kamshin indomie ya karade parlour ta Kallon Ahmad tayi cike da kissa tace"Honey kamshin girki nakeji ko amaryar ka keyi?,Bata fuska yayi yace"aini banida wata amarya data wuceki my Queen.Tabe baki tayi aranta tace yanzu daka shiga hannu kenan,!Azahiri kuwa seta langwabar dakai tace"Pls honey ina so inci abincin dake kamshin nan,bari naje tasammin tafada tana kokarin mikewa"sake mata kafafunta yayi,yakoma yajingina bayan sa da kushin tare da lumshe idanun sa yana jin wani yanayi atare dashi....
Madede cin plate tadauka tajuye indomie dataga yamata kyau a idanu,Bare kwoyin tayi,kana tayi silaizin dinsa akai,se hadiyar yawu take abinka da mai ciki kasa hakuri tayi yayi sanyi,Hakan yasa tanemi kujera tazauna a kichen din tafara ci da zafi.
Cokali hudu tayi taji ajanye plate din daga gabanta.Dasauri tadaga kai tana kallon Nadiya dake rike da plate din ahannunta tana hararanta da kananun idanunta."Wani irin Neman magana ne haka mumy rufy!?kibani abincina bana son abin tashin hankali, takarashe cikin sanyin muryan ta!.Dariyar rainin hankali Nadiya takece dashi kafin tace"nakarfine,inza ki Iya kikar ba,matsiyaciya yar matsiyata ba asaba ci agida ba shine akazo nan ake rawan jiki wajen ci,tana gama fadin tajuya ranta fes tayi hanyar fita.Rai abace Sukainat tamike