Showing 27001 words to 30000 words out of 52375 words
tsakar gida tana wanke-wanke tajiyo sallamar Aunty Nana"Daga Kai tayi da Murmushi a fuskarta tace Nana sannu da zuwa.Yauwa Ummi tafada tana kokarin karban wanke wanke data keyi,a'a kibarshi nakusa gamawa"zama tayi gefen Ummi suna hira jefi jefi harta gama.Ganin yanayin damuwa afuskar Ummi ne yasa Aunty Nana tambar ba'asin haka,numfasawa Ummi tayi tace Nana ina tausayawa Suky halin data keciki agidan mijinta..Shiru Nana tayi cike da tausayin Ummin tace wlh nikaina abin yana daure min kai Kuma jiya data koma Ahmad yahanata shiga gidan se agidan Baba idi takwana shine dasafe tazo labartawa Ummi komai tayi dakuma tafiyar datayi a yanzu...Tagumi Ummi tayi innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ta'fada cike da tashin hankali"Dasauri Malam Ahmadu yafito yace lafiya Maimuna??Cike da ladabi Aunty Nana tagaishesa amsawa yayi bayabo ba fallasa kana yana tambayar ta abinda yasa Ummi salati..cikin nutsuwa ta fada masa duk abinda ke faruwa..Cike da bacin rai yace wato Sukainat tayi girman da baza'afada mata magana tayi amfani dashi ba zatazo tasameni ina zaman zaman yana gama fadin haka yafice afusace..Wayan Yan uwa Ummi tasa Aunty Nana takira taji ko Sukainat tana can,duk wayar da Aunty Nana se ace batazoba Abu kamar wasa hardare babu Sukainat babu alamar ta Cike da tashin hankali Ummi tace kira Ahmad kode takoma gidan ne"Kai aunty Nana tagirgiza tace Ummi bana tunanin zata koma gidan Ahmad,kide kira kiji cewar Ummi,Aunty Nana batasake cewa komai ba takira layin Ahmad...
Zaune yake agaban Hjy kultum kansa akasa da alama magana me muhimmanci suke tattaunawa"Har yabude baki zeyi magana karan wayar sa yakatse sa,hannu yasanya yaciro wayar daga aljihunsa,Aunty Nana sunan daya keyawo a screen din wayar kenan seda yakusa katsewa kafin yadaga,murya acunkushe yayi sallama amsawa aunty Nana tayi batare data damuwa dayanda ya amsa mata ba tace"Ahmad Suky na gidanka dan tun safe munne meta mun rasa shine nace bari nakira ka inji,cikin halin ko inkula yace bata gidana tunjiya nakoreta yafada kansa tsaye, yana gama fadin haka yakashe wayar sa yanajan tsaki"Kallon sa Hjy kultum tayi tace kaida waye kake tsaki?cikin daure fuska yace yayar Sukainat ce take tambayar ta" tsaki Hjy kultum taja tace yo wannan gantalalliyar yarinyar meye bazata yiba ni wlh natsani wannan shegiyar yarinyar mara tarbiya gabaki daya iyayenta sun batata da rashin tarbiya badan abinda Allah ya kadarta ba meza ayi da wannan irin tasu..shide Ahmad shiru yayi bece komai ba hartayi tagama...
Abu kamar wasa yau kimanin sati daya babu labarin Sukainat duk inda suke zaton zataje ankira anma babu labarinta hankalin su Malam Ahmadu da Ummi bakaramin tashi yayiba.Koda wasa Ahmad beyi yunkurin zuwa nemanta ba haka zalika bezo gidan ba wannan abin bakaramin bakantawa Ummi rai yayiba...
*_ESHAA CE~_* π€π»
[3/23, 15:13] ESHA: *KISHIYA KO BAIWA???*
_(TRUE LIFE STORY)_
*NA MARUBUCIYA*
*REAL ESHAA ~*
*WATTPAD* _Realeshaa_
*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani_*
*PAGE 37&38*ποΈ
___________________________πZaune take da kwanan fura mai sanyi agabanta cikin kwanciyar hankali take sha tamkar bata da damuwa se lumshe dara daran idanunta take da alama tana jin dadin furar.Kallon ta Inna hajo tayi tana hararanta tace wai bazaki ragemin furan bane?ina magana kinyi min banza sewani rufe ido kike kamar sabuwar makauniya!!Cikin kosawa tace dan Allah Inna ki kyaleni, kinfiye takurawa wlh ko kinga na shanye ban bakiba bane?,Allah kika sake magana bazan bakiba shanye abina zanyi haba kinbi kinda meni da mita"Baki Inna hajo tatsuke tana kallon kwanan furar tasan ja irancin Sukainat muddin tace zata sake magana hanata zatayi...Seda takoshi dan kanta taturawa Inna hajo kwanan furan gaban ta tana hamdala ga Allah,'Dauke kai tayi kamar bataga furan ba"Murmushi Suky tayi tace haba My grany meye abin fushi bagashi narage miki ba ta'fada tana kunshe dariyar dake cinta!"Harara Inna hajo tamaka mata tace banaso kidauke abinki, bansha tafada tana turo daurin dankwali gaba...Kinsanfa bamu haka koso kike ai mana dariya, tafada tana nuna Fauziyya dake gefe tana Murmushin dramar tasu,hannunta Inna hajo ta bige daga jikinta tace yo tayi mana ai keki jawo tunda kinzama yar tsako samu kaki dangi.Aikuwa me fauziyya zatayi banda dariya muddin zaka zauna kusa da Inna hajo da Suky se cikin ka yacika da dariya dan bakananun comedians bane.Ganin haka yasa Suky mikewa tana tura baki tashige daki tare da cewa nayi fushi tunda de hade min kai zakuyi ke kuwa Inna ina zaman zamana zaki sameni."Harara Inna hajo tabita dashi tace kyaji dashi de magulmaciya,inkinga nazo wajen ki seki zaneni hankalinki yakwanta. itade fauziyya batace komai ba banda dariyar datake yimusu.Kallonta Inna hajo tayi tana maka mata Harara tace ke bansan shekiyanci kin wani sani gaba kina dariya kamar wata zautaciyya.Kinga ni banason Jan magana ko kinji nayi miki magana ne?,Banza tayi mata tajanyo kwanan furar da Suky tabar mata tafarasha"Dariya fauzy tafashe dashi ganin yanda take tandan baki,cike da zolaya tace kede wannan akwai iyayi dakin nuna bakiso anma yanzu kindauka kina wani tande baki,ko kallonta batayi ba taci gaba dashan furarta seda tashanye tass tamike tanufi daki...
Wasa wasa yau kimanin sati uku da barin Suky garin Bauchi,sabon rayuwa tafara agarin Gombe tare da kakarta dakuma fauziyya dasuke nuna mata tsantsar kauna da kulawa,tasake kiba haskenta yakara fitowa kirjinta sun ciccuko tamkar Wanda aka hurasu"Azahir tamanta da Ahmad"Abadini kuwa kullum da matsanacciyar begen sa take kwana take tashi.Tahuta da Fitinar Nadiya rayuwar ta takeyi cike da farin ciki da jin dadi duk abinda takeso shi Inna hajo da fauziyya ke mata musamman dasuka lura da tanada juna biyu basu barinta tadaga Abu mai karfi ko kuma tayi wani aikin,Kayan kwadayi kuwa kala kala suke hada mata Dede karfinsu.Aduk sanda Inna hajo zata bukaci Suky da takira mata su Ummi sugaisa setace network, suntafi hutu kuma bazasu dawoba se nan da wata uku,sannan tajuya sim card din tabaya,hakan yasa Inna hajo hakura dacewa ane ma mata Ummi sugaisa.Fauzy kuwa tasan dalilin zuwan Suky din hakan yasa tabata karfin gwiwar zama batare dawani daga Bauchi yasan tana nan ba kuma basusanar da Inna hajo ainihin abinda yakawo taba kawai de sun nuna mata kancewa mijin Suky yayi tafiya ne shiyasa tazo wajenta hutu kafin yadawo.Abangaren Fauzy kuwa tazage damtse wajen koya mata dabarun zaman da miji dakuma rayuwar aure,sosai Sukainat kejin dadin zama da fauzy domin tana wayar mata dakai dakuma fahimtar da ita abinda yashige mata duhu...
"Abangaren Ummi bakaramin tashin hankali take ciki ba narashin sanin inda Suky take domin duk inda suke zaton tana can sunje batanan duk gidan yan uwa da abokan arziki anje babu labarin ta"Inda yanzu tunanin ta yafi karkata kan cewa tana Gombe domin can ne ka'dai basu samun wayarsu,dan haka Ummi tanemi izinin Malam Ahmadu kan yabar ta taje ko Allah zesa tana can,'kin amince wa yayi dan haka tadurkushe tana kuka tana rokon da yabarta,da kyar ya amince taje domin bakaramin fushi yayi da Suky ba acewarsa tunda tazabi taguda batare da izinin suba toh yajanye hannunsa acikin lamarinta kuma muddin tadawo seta fuskanci bacin ransa,itade Ummi batace komai ba burinta bewuce hasashenta ya zamto gaskiya Suky na wajen mahaifiyar ta..
Misalin tara nasafe Ummi tahau motar Gombe cikin ikon karfe shadaya da wasu mintuna tashiga garin Bauchi,dan mashin ta tare tace yakaita ga bukka cikin mintuna kalilan suka isa,Da sallama dauke abakinta tashiga gidan, fauziyya da Inna hajo tahango zaune suna hira cike da barkwani"ganinta yasa suka Mike da Murmushi afuskar su"su naimata barka da zuwa.Kasa amsawa Ummi tayi lokaci daya jikinta yayi sanyi dan bataga alamar Suky tana nan ba"Taburma fauziyya ta shimfida mata tace Ummi bismillah kizauna,jiki asanyaye Ummi tazauna"Bayan sun gama gaisawa ne fauziyya tahadawa Ummi fura mai sanyi godiya Ummi tayi tafara sha ka'dan tasha tature kwanan furan daga gaban ta..Tasowarta daga bacci kenan wani azabebben yunwa yatasata gaba,Inna ina kika ajiye min furata...kasa karasawa tayi sakamakon ganin Ummi zaune!!"Ido Ummi tazuba bamata tanayiwa Allah godiya aranta dayasa yar ta nacikin koshin lafiya.Cikin sanyi jiki tazauna akusa da Ummi tare da gaisheta,kasa amsawa Ummi tayi se hawayen dake taruwa a kwarmin idanunta, cikin rawan murya tace Sukainat kin kyauta abinda kika, aikata yamiki kyau takarashe hawaye nabin fuskarta.. Subhanallah ke Maimuna lafiya daga zuwa se kuka cewar Inna hajo!!?Cikin sheshhekar kuka Ummi tafayyace wa Inna hajo abinda yafaru takuma sanarmata dacewa lalle Malam yace kafarta kafan Suky. Hawaye Inna hajo tashare tana cewa wannan kishiya ta Sukainat akwai lalacacciya haihuwar galligal sekace wacce aka kaimata baiwa, shima de wannan mijinata akwai lusari wlh duk yanda akayi dan farine",Yo kema de wannan akwai sakarya ni wlh kishiya bata isa natsaya tadakeni ba kota fi karfina aisena dauki muciya Na ragargaza mata kayi"Seda tagama surutanta kafin tashiga yimusu nasiyya me ratsa jiki takuma jawa Suky kunne da karta sake yarda ta tsaya kishiya tadaketa....Ko wanka Ummi bata bari Suky tayiba tatisa keyarta suka dawo garin Bauchi...
Lokacin dasuka isa gida Malam Ahmadu natsakar gida yana jiran dawowar Ummi,ganin ta da Suky yasa yamike afusace, bejira komai ba yadauki wani injin belt dake jikin bishiyar gwaiban gidan yafara dukanta dashi ihu take tana buya abayan Ummi,ganin kamar Ummi nakareta yasa yafara zubawa ta ko ina yana hadawa da ita seda ya mata dukan tsiya koda mikewa tagagara da kyar Allah yatemakata yakyaleta ganin batada kuzari" Kanwarta se kuka take tana baiwa Malam Ahmadu hakuri...Cikin bada umarni yace wlh minti talatin nabaki kishirya kikoma dakinki inba haka ba sena illataki..Ummi kam kasacewa komai tayi jiki asanyaye tamike tadaura mata ruwan wanka cike da tausayin ta,hakika Sukainat naganin jarrabawa tarasa da wanne zataji akananun shekatunta abunuwa sun hade mata goma da ashirin ga matsalar kishiya da miji gakuma mahaifinta dake da zafi...
Tana shiga daki tazube akasa zuciyar ta nawani irin kuna tamkar ze fashe"Hakika da wannan rayuwar data ke ciki gwanda mutuwa shin ina akeso tasanya kanta taji sanyi,acikin rayuwar ta. gidan mijinta ba dadi sannan ace gidan mahaifinta ma babu dadi"wani irin kuna zuciyar ta keyi mata,Mikewa tayi Dasauri tashiga dube dube acikin dakin,Cikin wata leda taga maganin bera cikin sauri tabude takai bakinta"Ganin tana kokarin hallaka kanta yasa Naja'atu kanwarta kwalla kara tana kiran Ummi,Arazane Ummi ta ajiye towan ruwan zafin datake tashigo dakin agigice"Shigowarta yayi dede da sanda take zuba maganin abakinta,kuka Ummi tafashe dashi cikin matsanancin tashin hankali tace dan Allah Suky kada kisha wannan abin karfa kimanta hukuncin duk Wanda yakashe kansa wutane,sannan kin mutu kafira domin Allah baya taba gafartawa Wanda yakasheka Kansa.Cikin wata raunanniyar murya tace wlh,Ummi na gwammaci in mutu kafira da wannan rayuwar kuncin da bakin cikin danake ciki" nasan koda namutu kowa zehuta yadena tsanata Ummi nasan ke ka'dai ce zakiji ciwon mutuwa Na anma kiyi hak....bata karasaba Malam Ahmadu yakwasheta da wani azabebben mari,cikin tsawa yace kicire maganin daga bakinki kafin na illataki"dago rinannun idanunta tayi tace Abba kayi hakuri na gwammaci mutuwa da wannan rayuwar kunci da bakin cikin danake ciki, tanagama fadin haka tayi kokarin hadiye maganin cikin wani irin sauri Malam Ahmadu yamatse bakinta daduka karfinsa hannu yacusa abakinta yana kokarin Ciro maganin yayinda ita kuma kekorin hadiyewa" ganin inbeyi da gaske ba zata shanye yasan yashi matse wuyanta tare da dauketa da mari Wanda yayi sanadiyyar zubowar maganin dakuma fashewar gefen bakinta fusgewa take daga rikon dayake mata tana wani irin kuka me gunji.Cikin bada umarni Malam Ahmadu yasa Ummi takawo masa ruwa,bakinta ya wanke tare da tofa mata addu'o'i,dena fusge fusgen tayi sejan zuciya datake akai akai.Ido Malam Ahmadu ya kura mata cike da tausayi yake kallon ta cikin nutsuwa yace"Sukainat shiru tayi takasa amsawa se binsa datake da Ido,sake kiran sunan ta yayi akaro nabiyu, ahankali tadago rinannun idanunta dasuka rine tamkar gauta bata amsa ba sebinsa da kallo datake..Meyesa kikayi yunkurin kashe kanki?kinsan hukuncin duk Wanda yayi yunkurin kashe kansa amusulunci kuwa??!Cikin raunanmiyan muryanta daya dishe da kuka tace Abba nasani wuta!!Kallonta yake kafin daga bisani yace kinsani anma shine kikayi yunkurin kashe kanki...
Cikin shesshekan kuka tace Abba menene amfanin rayuwa ta gwara mutuwa da wannan rayuwar danake fuskanta,baki daya kunkasa fahimtar halin kunci da bakin ciki danake ciki Abba gani kake kamar banason zaman aure ne alhalin bahaka bane Abba kunkasa zaunar da Ahmad kuji dalilin dayasa yake wulakantani kullum cikin ganin lefina kuke.
Hawayen fuskarta yashiga share mata cike da tausayin ta yace kiyi hakuri Suky insha Allah zan kwatar miki yancinki anma karki sake yunkurin kashe kanki.kai tajinjina batare datace komai ba.Ummi dake gefe kasa cewa komai tayi se godiya takewa Allah daya kubutar da rayuwar yar ta...Mikewa Abba yayi yafice wayar sa dake aljihu yaciro number alwalin Ahmad yakira,bayan sungaisane yasheda masa dalilin kiran nasa" bayan yakashe yasake kiran wayar Isa gaisawa sukayi da isa cikin mutunci da karramawa kafin Malam Ahmadu yasanar masa dayanason ganin sa agidan sa
Da yammaci misalin karfe hudu Alh Ali da isa suka iso gidan Malam Ahmadu cikin karramawa yatarbe su ruwa yakawo kafin yafara sheda musu dalilin kiransu...
*_ESHAA CE~_*π€π»
[3/23, 15:13] ESHA: *KISHIYA KO BAIWA???*
_(True life story)_
*Na marubuciya*
_REAL ESHAA ~_
*WATTPAD* _Realeshaa_
_Like my page on Facebook._ ππ»
https://www.facebook.com/REAL-ESHAA-FANS-114689303720405/
*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani_*
_Dedicated to Amnah el yaqub Ina tayaki murnan fara sabon novel din ki me suna INSAAF yanda kikafara Allah yasa kigama lafiya Allah yabada Ikon amfanuwa da darusan dake ciki._
*PAGE 39&40*ποΈ
_____________________________πRan Alh Ali bakaramin baci yayi ba dajin jawabin da Malam Ahmadu yaimasa game da halayyar da Ahmad ke nunawa diyar sa.Cike da kunya yace dan Allah Malam kayi hakuri wallahi koda wasa bamusan abinda ke faruwa ba kenan domin da munsani tuni zamu dauki mataki akai saboda munada Yaya mata kaga baza muso wani ya wulakan ta mana suba,anma insha Allah zandauki mataki akai, hakan bazesake faruwa ba zanyiwa tufkar hanci da yardan Allah ya karashe cikin sanyin murya da bakaramin kimar bawan Allah yake gani ba"Murmushi Malam Ahmadu yayi yace"Haba Alh meye abin ban hakuri aciki,aidama Wanda yace zo mu zauna toh yace zo musaba,bare rayuwar aure yagaji hakan sedebama fatar abin yayi nisa.Kai Alh Ali ya jinjina cike da gamsuwa da maganar sa yace hakane kuma Insha Allah komai yaxo karshe"Toh Allah yasa cewar Malam Ahmadu.
Isa kam kasacewa komai yayi,dan yasan hakan na iya faruwa domin, wannan shedaniyar Matar zata iya aikata fiye da abinda aka fada, domin tunbayan zuba yagane shu'uman cinta da makircinta"Shiyasa Sam basa shiri da matarsa,ba wacce ke ziyartan gidan yar uwarta acikinsu domin halayyar su batazo daya ba"su suke zumunci tsakanin su,anma matan su ko wacce tabi hanyar ta daban.Cikin nutsuwa yace"Dan Allah baba kayi hakuri ni wallahi bansan Sukainat bata gidan ba! dan ko jiya muna tare dashi awajen aiki nake tambayar sa ya iyalai yace duk suna lafiya anma besanar dani kan cewa Suky na gida ba,da inada masaniya Akai, Wallahi da bazan bari takai tsawon wannan lokacin a gida ba.Kwafa Alh Ali yayi yace bar ja iri taya kake tunanin ze sanar maka bayan beshuka abin arzikiba ai abin kirki mutum ke fadar yayi.Maza kirawo minshi awaya"Cike da ladabi Isa ya amsa tare da sanya hannun sa a aljihu yaciro wayarsa, number Ahmad yafito dashi yakira, ringing daya yadauka tare da sallama" bayabo ba fallasa Isa ya amsa sannan suka gaisa,kafin yace"Baffa Ali keson magana dakai"Shan jinin jikinsa yayi da wani abin akasa, cikin kasa da murya yace meke faruwane?"Cikin basarwa Isa yace gashi nan koma meye zakaji daga garesa, bejira jin abinda zeceba yayi saurin mikawa Alh Ali wayar.Batare da Alh Ali ya amsa gaisuwar daya ke masa ba yace" kasameni agidan su matar ka yanzu- yanzu, yana gama fadin haka yakashe wayar batare dayajira amsar saba...
Da kallo yabi wayar Zuciyarsa Na sake sake,dafa kafadarsa Nadiya tayi tace"Honey lafiya kuwa naganka haka kowani abin yafaru!??Kai yashiga girgizawa kafin yace bana tunanin haka kawai de Baffa Ali keson gani na yanzu.Shiru tayi nawasu mintuna kafin daga bisani tace"toh kaje kaji ko menene ma inaga hakan zefi?"Hakan za'ayi yafada yana mikewa,haryar fita yanufa kasancewar yana cikin shirin sa,har compound Nadiya tarakasa shiga hadaddiyar motarsa yayi yana daga mata hannu haryafice daga gidan..Cikin mintuna kalilan ya isa gidan zuciyarsa se cike da tunani kala kala..Bayan yayi parking a inda yasaba parkin motarsa aduk sanda yazo, yakira wayar Isa tare dashe da masa yazo yana kofar gidan,kashigo kawai yace "dashi yana katse layin...
Yana yin yanda yaga fuskar Alh Ali da Isa ya tabbatar masa da ba lafiya ba jiki asanyaye yanemi kusa da Isa yazauna.
Gaishe da Malam Ahmadu yayi cike da dattako Malam Ahmadu ya amsa fuska asake yana tambayar sa ya iyalai!?,Kallon Alh Ali daya daure fuska yayi cikin sanyin murya yagaishe sa,Kallon banza Alh Ali yawatsa mai batare daya amsa gaisuwar Saba yace"Ahmad Ashe baka da mutunci baka da tunani!! ina maka kallon ni tsatstse mai hankali Ashe bansan ceaa kai shasha mara tunani da hangen nesa bane,Ta Inda yake shiga batanan yake fita ba seda yaimasa wankin babban bargo kafin yace"Ya baiwa Malam Ahmadu hakuri,cike da jin kunya yabaiwa Malam Ahmadu hakuri"Fuska asake ya amsa tare dacewa bakomai aidama zo mu zauna so musaba ne.Shide Ahmad bece komai ba se Alh Ali daketa faman sababi, sannan yace maza yadauki matarsa sutafi"Godiya yaimusu yamike jiki asanyaye yafita, mikewa Malam Ahmadu yayi yashiga cikin gida yace da Suky tafito sutafi da mijinta.Lokacin data fito Alh Ali da Isa suma sun fito zasu tafi Har kasa ta tsugunna tagaishe dasu Alh Ali cike nutsuwa"amsawa sukayi da Murmushi afuskarsu asanda suke yaba nutsuwar ta dakuma tarbiyan ta,bani number ki duk sanda Ahmad yasake yimiki badede ba kikira, kisanar dani muryan Alh Ali yadaki dodon kunnen ta.Ahankali tace aibani da waya Baffa!Cike da mamaki yace"Ina wayar taki?"Ya Ahmad ya karba,kai ya girgiza yana mamakin sauyawar Ahmad lokaci daya"inda Ahmad yayi parking motar yanufa cikin daure fuska yace"Ina wayar ta yake?kai akasa yace"yana