Showing 15001 words to 18000 words out of 52375 words
dakin.Kallon ta tamayar kan Ahmad daya juyamata baya yana baccin sa cikin kwanciyar hankali. Dasauri tamaida 'kwallan dake shirin zubomata tuno da irin ihun dayayi mata a gaban matarsa. Mikewa tayi tashiga toilet ruwa ta watsa kana tadaura alwala tafito,sif tabude tadauki simple gownt tasanya"kusa dashi tatsaya cikin sanyin muryanta tace ya Ahmad katashi lokacin sallah yayi"Ahankali ya'bude lumsassun idanunsa masu matukar burge ta dasake dulmiyar da ita cikin kogin kaunarta.Jiki asanyaye tamike daga kusa dashi ganin irin Kallon daya kebinta dashi,pray mat tashimfida ta tayar da sallah seda ta gabatar da raka'atanil fajir sannan tayi asbah,kana tayi azkhar da bitar al'kur'ani mai girma"Ganin shida da Rabi yayi yasanyata rufe kur'anin tanufi kitchen da yimusu breakfast"jiki asanyaye take aikin,arish ta fere ta tafasa sannan tafasa 'kwai tasoya duk jikinta asanyaye take aikin. bayan tagama ha'da komai,tajuye tea acikin flaks Arish din kuma acikin warmers, direct sashen Nadiya taje bakinta dauke da sallama.Amsawa sukayi Har Ahmad dake zaune gefen Nadiya da alama daga masallaci yake, cikin girmamawa tagaishe da Ahmad "kamar ko yaushe amsawa yayi bayabo ba fallasa" Kallon ta tamayar kan Nadiya tace barka da safiya momyn rufy ya kwanan su rufy,Da Murmushi a fuskarta ta amsa tare dacewa ya gajiya.Bakaramin mamaki Sukainat tashiga ba ganin murmushin dake kan fuskarta,anma setakawar da tunanin tahanyar cewa me za'ayiwa surufy na school ne??,Harzuwa yanzu da wannan Murmushin akan fuskarta tace bakuyi magana da honey bane?,Kai suky tagirgiza alamar a'a tana kallon Ahmad da alamar tambaya afuskanta.Kawar da kai yayi kamar begane kallon datake yi masa ba"Ahankali tace bece min komai ba tafa'da kan ta a'kasa.'Dan Murmushi Nadiya tayi tace daman cewa yayi yakamata infara koya miki girki dan kar azo aji kunya agaba,jiya mukayanke shawaran da Honey"dasauri Sukainat tadago kanta jin rainin maganan Nadiya,cikin yanayin bacin rai tace kamar ya zaki koya min girki?koce miki akayi ban iyaba??,wannan aicin fuska ne da 'kas'kantar da 'dan Adam!! Rai abace Ahmad yace ke banason rashin hankali,da rashin tarbiya saboda girman kai baki iya ba sannan za akoya miki kice bazaki yardaba wannan halayyar taurin kan naki baze amfanar dake komai badan haka tun wuri gwanda kiwatsar da wannan bakin dabi'ar taki.Cikin 'kissa Nadiya tace haba Honey meyesa kakeson yimata fa'da koyaushe kasan yaro se anbisa Ahankali bada fa'da ba"Hannu Ahmad yadaga mata yace ya isa my Queen,karki sanya kanki acikin wannan maganan, wacece yarinyar Sukainat din ce yarinya??,yafa'da yana munata da hannu, banaso idan ina mata fada kina sanya baki rashin mutunci kawai kedamunta anma babu wani yarinta atare da ita.Wani irin tukukin bakin cikine yaturnuke zuciyar Sukainat mikewa tayi tabar wajen Cikin kunan zuciya da bakin ciki"cikin karaji Ahmad yakirata tadawo,tanajin sa tayimasa banza dan muddin intadawo za'ayi baceceni ya dan bazata zauna surika ya'ba mata magana ba.
Cike da iya barikanci Nadiya tace haba Honey meyesa kakeson bata bakinka akan karamin Abu??,kafi kowa sanin banason ganin ka cikin damuwa pls ka kwantar da hankalinka tunda bataso sekabarta kar taga kaman takura mata akeyi.Shiru yayi nawasu mintuna kafin daga bisani yace inazuwa,yafada yana mikewa"inazaka Honey karfa kaje kayi abinda bedaceba??! Yanzu zanzo yana gama fadin haka yafice direct sashen Sukainat yanufa"Nadiya Na ganin fitarsa tafashe da dariya hadda rawa domin duk azatonta dukan Sukainat zeyi,Wayar ta tadauka takira lambar Hema ringing daya hema tadauka cikin zumudi Nadiya tace kawar dan Allah yaushe zakizone akwai labaraifa"dasauri Hema takatseta tahanyar cewa hmm ga Darling din najinki seki fa'da masa dankidena ganin kamarnice banason zuwa"tana fa'din haka Nadiya tadauhaske dan haka tace bashi,karban wayar yayi sukagaisa kafin tace dan Allah kabar hema tazo dan nasan kaikahanta Murmushi yayi yace toh zatazo insha Allah Uwar gida sarautar mata"Murmushi tayi tamaisa godiya sannan sukayi sallama, zama tagyara zuciyar Cike da farin ciki...Zaune yahangota tazabga tagumi fuskanta na bayyanar da damuwa 'karara,zama yayi agefenta yajanye tagumin datayi yanabin fuskarta da kallo,bayabo ba fallasa yace, meyesa kikeson sanya kanki cikin damuwa my kainat a'iya sanina dake bansan ki da taurin kai da rashin jin magana ba se yanzu, sannan kin dauki girman kai kin 'daurawa kani,narasa yaushe kika koyi haka yanzu meye lefin Nadiya danzata koyar dake girki azamanin yanzu dawuya kisamu Kishiya me halayya irin ta Nadiya me saukin kai dakuma son cigabanki ina rokinki dan Allah kizubar da wannan Sabin dabi'un dakika koya kuzauna lafiya konima hankalina ze kwanta yakarashe maganan yana langwa'bar dakai.Shiru tayi nawasu mintuna tana nazarin kalamansa kana daga bisani tace shikenan na amince takoyamin inde hakan zesanya ka farin ciki, takarashe maganan hawayen datake kokarin boyewa sukayi nasaran zubowa.janyota jikinsa yayi ya Rungumeta yana bubbuga bayanta cikin muryan lallashi yace haba my kainat meye abin kuka pls kidena zubar min da tsadaddun hawayen ki masu matukar daraja awajena,dago kai tayi tatsurawa fuskarsa ido tanajin kaunar sa naratsa duk wani gaba dake jikinta, karamin bakinsa dayake motsawa tatsurawa ido tanajin wani yanayin me wuyar fassarawa atare da ita,Ganin irin kallon datake binsa dashi ne yasanyashi hade bakinsu waje daya yayi yashiga kissing dinta tare da aikamata da sakonni masuwuyar fassarawa biye masa tayi sekushiga farantawa junansu rai sun dauki lokaci ahaka,kafin daga bisani yayi saurin janye jikinsa daga nata azabure Kamar Wanda aka tsikarawa allura se sauke ajiyar zuciyar yake"matsawa kusa dashi tayi za tarike hannunsa yayi saurin ja dabaya,mikewa yayi yanufi hanyar fita batare dayace da ita komai ba.Ya Ahmad takira sunansa yayinda take narkar da idanunta acikin nasa cikin wata kasalalliyar murya tace pls kadawo karkatafi kabarni ahaka,Ido yakura mata nawasu mintuna kafin yadawo cikin dakin jikinsa amace,rike hannunsa tayi tace meyefaru kowani Abu namaka??!Murmushi yasakar mata yace bakomai kawai de...sekuma yayi shiru bekarasa ba"ka tabbata babu komai tafada cike da kulawa"kai yajinjina tare da janyota jikinsa,suna lallatsa juna Sukainat se narkemasa take.Wayarsa dake kan beside drawer ne yahau ruri Ahankali yamika hannunsa yadauko tare da picking batare daya duba mekiran ba"Cikin kasalalliyar murya yayi sallama, dasauri yajanye jikinsa daganata,seda tatsorata lafiya meyafaru??,tace dashi tana ganin yanda jikinsa ke rawa...Ina zuwa yafada tare daficewa batare dayabata amsar tambayar datake masa ba.Cike da mamaki tabisa da kallo sekuma tayi saurin mikewa tabi bayan sa. Daf dazata shiga cikin parlour Nadiya taji muryan tana cewa ya isheka haka Ahmad bansan rainin hankali yaushe kazama makaryaci bansani ba?cikin rawan murya yace wlh babu abinda yashiga tsakanin da ita kawai fada nakemata akan abinda tayi...dalla rufemin baki makaryaci kayi azatonka bazangane muryan ka akowani yanayi kakeba?,shiru yayi yakasacewa komai sekasa dakai dayayi"wani takaici yaturnikewa Sukainat rai danhaka tajuya takoma harzata shiga daki tafasa,tashiga kitchen warmers din datazuba soyayyen arish tabude tasting tayi taji komai lafiya kamar yanda tayi dan haka tadauki kayan baki daya tanufi sashen Nadiya, harzuwa yanzu Nadiya na zazzaga masa rashin mutunci, ganin Sukainat dakayan breakfast yasa tayi shiru takebinta da kallo" 'dauke kai Sukainat tayi kamar batagan taba ajiye wa tayi tadauki plates da cup tayi serving kowa sannan tace bismillanku.Wani irin kallo Nadiya kebinta dashi zuciyar ta nakuna shin dayaushe ta ha'da breakfast batasani ba lalle yarinyar nan akwai munafuka"Ahmad kuwa kamar jira yake yanufi dining din zama yayi yafara ci dasauri yadago kai ya kalli Sukainat"Wani irin bugawa zuciyar Sukainat tayi dasauri tashiga karanta Addu'ar rinjaye a zuciyarta!!"Gani tayi Ahmad yajuya fuskarsa dauke da Murmushi yace my Queen zokiji yanda girkin kanwar ki yayi dadi kamar ba ita tayiba,dasauri Sukainat tabude idanunta tanayiwa Allah godiya dayasa abincin bebaci ba.Wani shegen kallo tawatsa masa tace meyesa bata tambayeni damezanyi breakfast ba??Taya zatayi abinda ranta keso dan haka nida 'ya'yana bazamuciba kusan yanda zakuyi dashi tanagama fadin haka tashige ciki. Mikewa Ahmad yayi zebita cikin kunan zuciya Sukainat tarike hannusa tace mehaka ya Ahmad ya zakaje?hannunta yanmbige daga jikinsa yace leave me alone duk kekija meyesa bakije kintam bayeta abinda take bukatar yin breakfast dashi ba zakiyi gaban kanki gashi kinsa tafusata.Rasa abin cewa Sukainat tayi sebinsa da ido datake yi Cikin sanyin muryanta tace toh anma naga nima inada yanci acikin gidan nan meyesa sena tambayeta abinda takeso kafin nayi?,banza yayi da ita yabi bayan Nadiya" jiki asanyaye taje tayi breakfast dinta sannan takwashe kayan tamayar kitchen.Ahmad nashiga yaita allashinta dakyar yasamu tahakura anma dasharadin duk abinda Sukainat zatayi acikin gidan seda izininta,kuma ya amince akan hakan...
****
Da rana lafiyeyyen jollof din shinkafa tayi musu Wanda yaji vegetables da namar kaza sannan tahada musu zobo me dadin kamshi,fita tayi daga kitchen din tashiga daki danyin wanka se tatuna ba tasanya zo'bon a fridge ba,dafe kai tayi kana tadawo rufaida tagani tabube zobon tazuba Wani Abu acikin kwalba tana kokarin bude abincin Sukainat takarasa wajen rai abace tace mehaka kikeyi rufy mecike sakamin cikin abinci??Cike da tsiwa tace abinda kika akaini wawuya wacce batasan metakeyiba,da kallo Sukainat tabita takasa tabuka komai,tadauki kusan mintuna goma atsaye awajen kafin daga bisani tazubar da sobon tasake ha'da sabo tafice a kitchen din,hartayi wanka batar al'ajabin zagin da rufy tayi mata ba dakuma abinda taga tanayi.Bayan tafito tadauko Wani swiss less ja da ratsin green tasanya abinka da black beauty bakaramin amsar jikinta kayan yayiba,kwalkiya ta tsantsara sannan tadibi abincin taje tayi serving dinsa asashen Nadiya Wannan umarnin Ahmad ne komai a sashen Nadiya zasudinga yi,lokacin datashiga babu kowa a parlour dan haka tanufi bedroom din tsayawa tayi tace aunty kufito angama abinci fitowa sukayi dujansu ita da 'yayanta serving din su tayi sukaci sukasha sabon zobon data ha'da musu, harsuka gama ci bawanda yace da 'dan uwansa komai bayan sun gama ne ta kwashe kayan tamayar kitchen sannan tawuce dakinta batare datasake bi takansuba.Fitar ta ba dadewa hajiya Kaltum tazo wato mahaifiyar Ahmad, dagudu su sufy suka Mike suka Rungumeta cike da farin Cikin ganinta,Itama rungumesu tayi cike da farin cikin ganin jikokinta,mikewa Nadiya tayi tana hararansu tace kusaketa koso kuke kukaryata ne?dariya Hjy kultum tayi tace baruwanki dasu,fride Nadiya tabude tadauko mata drinks kallon rufy tayi tace jeki karbawa Hjy abinci wajen Aunty Ku sannan kice tazo sugaisa,mikewa rufy tayi tafice tanufi sashen Sukainat.Sukainat na shiga daki tadauki wayarta tana game, sotake takira 'yan gidansu sede bata da katin kira tanaso tace Ahmad yasa mata anna tanajin nauyin tambayar sa hakan yasa tahakura taci gaba da game dinta cike da kewar yan gidansu.Jitayi anbanko kofar da karfi anshigo daga kai tayi dan ganin kowaye!!rufy tagani cikin yatsina da tsiwa tace Sukainat kibani abinci.?Kallon ta Sukainat tayi tana mamakin tsaurin idon yarinyar,anma yanzu kikagama cin abinci ko tace da ita?Ina ruwanki inade dadyna ne yakawo kuma dan muci yasiyo inkuma bazaki bani bane se intafi"mikewa Sukainat tayi batare datasake cewa komai ba tanufi kitchen plate tadauka tazuba mata sannan tafice tabarta a kitchen din.
"Parlour rufy tashiga hannunta rike da plate din abinci ba murfi tana zuwa ta ajiye abincin agaban Hjy kultum tace grany kiga a inda aunty tasanya min abinci kuma nasanar mata nakine shine tace wai ina ruwanta dake ko ke Uwar tace dazatasanya miki abinci akula me kyau Har zankara yimata magana tace idan ban barkanta seta dake ni taga gatana.Cikin kissa Nadiya tace ya isa rufy banhanaki irin wannan surutunba zuciyar ta cike da farin Ciki,Rai abace Hjy kultum tace lalle wannan tacika Mara mutunci dama tsiyan 'dan talaka kenan be iya samun wajeba tsaban rashin tarbiya za tasanya min abinci cikin plate yauzan nuna mata nafita iko dagidan 'dana,Nadiya jeki kiramin ita yanzu,jiki narawa Nadiya tamike tanufi sashen Sukainat zuciyar wasai...
_VOTE_ ✅
_COMMENTS_
_AND_
_SHARE_
*_ESHAA CE~_*🤙🏻
[3/23, 15:13] ESHA: *KISHIYA KO BAIWA???*
_(TRUE LIFE STORY)_
*NA MARUBUCIYA*
*REAL ESHAA ~*
*WATTPAD* _Realeshaa_
*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani_*
*PAGE 23&24*🖌️
________________________📖Da sallama dauke abakinta tashiga Har bedroom din ta,batare da Neman iziniba"zaune tahangota tana latse latse awaya,Murmushi take sakar mata wanda da ita ka'dai tasan ma'anarsa "wayar dake hannunta ta ajiye tana maida hankalinta kacokam zuwa ga Nadiya dahar izuwa Wannan lokacin da Wannan makirin Murmushi a fuskarta.Ido sukainat takura mata inhar bata manta ba Wannan shine karonta nabiyu shiga dakinta tana fatan Wannan shigowar yazama na alkhairi domin jikinta nabata babu alkhairi atare da Nadiya.Cikin dakiya tace wani abin kike bukata momyn rufy?,kai ta girgiza alamar a'a babu abinda nike bukata Mr Ahmad Hjy kultum keson ganinki wato mahaifiyar mijinki ko ince surukarki tafa'da cike da she'kiyanci" tanagama fa'din haka tajuya tace nabarki lafiya Amarya me maganar sugar.Takai kimanin minti uku tana tunani kafin daga bisani tamike, Sif tabu'de tadauko hijab dogon harkasa tasanya sannan tafito dan amsa kiran Hjy.Ahankali tasanya 'kafa cikin parlour tare da sallama 'dauke abakinta.
Shigarta yayi dede da lokacin da Nadiya ke fa'din halin tane Hjy sede kiyi hakuri Sam batada tarbiya muma hakuri muke da ita badan haka da yanzu ankai ruwa rana,ni wlh ko bako ne bazan bashi abinci a wannan plate din ba bama ba'ko ba kowanda bansan shiba bazanyi masa Wannan wulakanci ba"cike da takaici Hjy kultum tace yo aima bazanci abincin ba,Har Nadiya tabude baki daniyyan magana taha'diye sauran dake bakinta sakamakon ganin Sukainat"Ko ba'a fa'da mataba tasan sukarta Nadiya ke kaiwa wajen Hjy kultum duba da yanda hajiyar tamurtu'ke fuska,Dede ta yanayin fuskarta tayi kamar bataji komai ba takarasa shiga cikin parlour.Da yalwateccen fara'a a fuskarta ta tsugunna a'kasa kusa da Hjy kultum tace barka da zuwa Hjy fatan kunzo lafiya ya mutanen gida??,ta'fada kanta a'kasa cike da baiyayya.Cikin 'kaskanci Hjy kultum tace dakata!!bana bukatar gaisuwarki!,gaisuwar mezakiyi min?,bayan kingama yimin diban albarka abayan ido na fitsararriya Mara kunya wacce batasan mutinciba tsiyar dan talaka kenan baku iya samun wajeba se kunnuna bakugaji arzikiba Har ni zaki zubawa abinci a plate ta'fada tana nunata da plate din datasanyawa rufy abinci,kince niba Uwar kibace bare kizubamin akwa no me daraja,Naji niba uwarki bace anma na haifi dan dakike zaune akar kashinsa kuma zan nuna miki nafiki gadara dashi mara tarbiya dagani iyayenki basu baki tarbiyan daya daceba domin dakina da tarbiya dabazaki yimin hakaba gayyar tsiya.
Tunda tafara magana Sukainat ke kuka jitake ina ma mutuwa yazo yadauketa da Wannan kaskancin da cin mutincin datake fuskanta gidan Ahmad tarasa meta tsarewa Nadiya da 'ya'yan ta agidan dasukeso su tozarta ta ba damuwa in Har Hjy kultum tayi mata domin matsayin Uwa ce agareta"cikin wata raunanniyan murya tace Dan Allah mama kiyi hakuri wlh koda wasa bansan cewa abincin kibane banma San cewa kinzoba seda momyn rufy tasanar min,kuma koda rufy taje cemin tayi insanya mata abinci zataci bata koshiba anma wlh koda wasa bansan cewa keza kiciba.Dasauri rufy tace wlh grany karya takeyi nafa'da mata kece zakici abinci shine tace wai ina ruwanta dake..Rai abace Sukainat tace anma rufy kiji tsoron Allah yaushe kikace mama ce zataci abinci?bakomai kema macece kuma gidan Wani zaki tafi...Hannu Hjy kultum tadaga mata afusace tace dakata!!kar kice zakimata baki kuma ba'abinda za tagani agidan auren ta banda alkhairi aniyarki tabiki"Cikin kuka tace ba baki nake mataba kawai ina fa'da mata gaskiya ne..ketashi kibani waje banason fitsara Mara tarbiya ta'fada tana nuna mata hanyar fita.Jiki asanyaye tamike batare datasake cewa komai ba tafice.
"Hjy kinga ka'dan daga cikin halayyar tako?ko dadyn rufy bata ragamasa in tafara yimasa fa'da kamar danta kuma koda ya fa'da mata magana bataji bata ganin kowa da mutunci agidan nan bakiga yanda ta tsani yarannan ba koganin su ta tsani yi bare tajasu ajikinta,cewar Nadiya tana matsawa Hjy kultum kafa"Aina gani da idona dan Wannan yarinyar ba yar mutunci bace tagani idanunta batafa kunya"Ganin yanda Hjy kultum tadau zafi da Sukainat yasa Nadiya da rufy sukadinga yimata famfo 'karya da gaskiya sukadinga fa'da mata basubarta seda suka tabbatar suncusa mata kiyayyar Sukainat fiye da tunanin mai karatu...
Jiki asanyaye tashiga sashen tana hawaye,tare da mamakin karya irin na rufy suwar wayarta taji dasauri takarasa tayi picking muryan Sofi'a taji yakarade mata kunne Amaryan Ahmad,baki da kirki,baki daya Ahmad yasa kin manta damu saboda zumar soyayya nadibanki ta fa'da cike da shekiyanci.Duk yanda take kokarin danne Kukan ta seda yasubuce mata tashiga rera shi cike da ban tausayi"Cike da tashin hankali Sofi'a tace Lafiya Suky meke damunki me akiyi miki dan Allah kiyi shiru kibani amsa ko hankali na ze kwanta.Da'kyar ta iya tsagaita kukanta tace Sofi'a nashiga uku narasa inazan sanya kaina inji sanyi rana zafi Inuwa kuna...Cike da damuwa Sofi'a tace ki nutsu ki yimin bayanin abinda kefa ruwa yanda za fahimta.Tiryan tiryan tazayyanewa Sofi'a duk abinda kefa ruwa tunfarko zuwanta gidan har zuwa abinda yafaru yau...In har ran Sofi'a yayi dubu toya'baci dajin maganan Suky,cikin bacin rai tace wato irin rayuwar dakike fuskanta kenan Suky??,shine kika zauna kowa yake miki cin kashin dayaga dama! yanzu Har wancan karamar alhakin yarinyar tadunga sanya ki kuka bazakici ubanta ki karya mata Hannu ba, anma kin tsaya asaranci sezubar musu da hawaye kike Abu ka'dan kitsaya ki na kuka aidole ma surenaki tunda kin zama lusara... Wlh Sofi'a Duk inda kike tunanin Wannan yarinyar da Uwar ta sunwuce wajen"Tsaki Sofi'a taja tace kefa Amarya ce kuna yarinya me tunani shin bakisan yanda zaki kwatarwa kanki yanciba...Dasauri Suky tace hakane nice Amarya ya Ahmad kuma Uwar gida Nadiya ce mijin domin seyanda tayi damu kinga kuwa duk akar'kashin ta muke.Duk da Sofi'a nacikin bacin rai hakan behanata fashewa da dariya ba tace wani irin magana kike Suky taya zakice Nadiya ce miji akar'kashin ta kuke... Hmmm bazaki gane bane Sofi'a inhar Nadiya na magana haka zakiga jikin ya Ahmad narawa wlh nalura tsoranta yake"murya Sofi'a tagyara tafara bata shawarwarin dazata 'kwaci 'yancinta cike dajin dadi tace....jitayi anwafce wayar daga hannunta tana daga kai taga Ahmad fuskarsa amurtuke a hands free yasanya wayar inda, Sofi'a kecewa wlh karki sake barin Wannan Mara kunyar yarinyar tasake rainaki in tayi ki nada mata duka inkuwa Uwar ta tace bahaka ba itama ki ha'da da ita muddin kinason samun yanci.'kit yakashe wayar bayan yagama jin abinda take cewa Wani irin kallo yake binta dashi na asirinki yatonu cikin matsanancin bacin rai yace wato Sukainat bakyajin magana?? duk abinda nake fada miki sekinsanya kafa kin shure,duk wulakanci dakikayiwa Hjy be ishekiba shine sekin kara diban sirrin gidana